Author : SHATUUU Category : African Stories & Novels
mukai ta hira har ta shirya zata tafi night duty sannan taga motar dan bance mata da ita nazo
ba da dauki bazai batta muyi hirar ba.
Ayshatuuuuuu
[5/29, 4:32 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_TWENTY EIGHT_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Chromic din hannuna na aje sannan aka miko min gauze na rufe muka rufe da plaster sannan na kalli
kowa tareda sakin murmushi bayan na cire google din idanuna nace
“Alhamdulillah, nice job everyone!”
Dukka team din murmushi sukaimin kowa yana kokarin karasa abinda ya kamata, Apron na cire na wulla
cikin bin, fitowa nayi tareda cire mask din dake fuskata na danyi mika sannan na tafi lounge dinmu dake
cikin OT bayan na karba patients folder a gurin chief anesthetist naje na zauna kan cushion ina
documenting aikina. Koda na kammalla banida wani aiki daya rage min hakan yasa na zauna tareda
lumshe idanuna kamar wadda take bacci amma ba baccin nake ba, ina naga idon bacci? Matar da ko da
daddare se nayi da gaske baccin ke daukeni balle yanzun ido na ganin ido, da dinma guri na samu amma
yanzun babu halin hakan, dan damuwar da nake ciki kadai ta isa ta samin insomnia. Bansan adadin
lokacin dana dauka a hakan ba se naji an bubbuga min kujerar da nake kai hakan yasa nayi firgigit na
bude idona da sukai ja. Dr. Fadima ce tana tsaye ta zubamin ido, zama na gyara tareda kirkiro murmushi
nace
“Doctor yaushe kika shigo?”
Zama tayi kujerar dake facing dina se center table dake tsakaninmu, coke ne a hannunta chilled dan
kadan ya rage yayi kankara. Tunda nake ban taba ganin coke addict irinta ba, kullum muka hadu se nayi
mata fada amma sede tayi dariya kawai tace ai ina exercise ko kuma ace min inada glucometer. Haka dai
take tana da kirki tare mukai medical training dinmu a Bayero.
“Dr Shahada, me yake damunki?”
Dan murmushi nayi nace
“Me kika gani? Am I looking terrible?”
“More than”
Ta fada tana hararata, murmushi na kumayi nace
“Kinsan yadda rayuwa take, mutum baa rabashi da matsala sede addua kawai”
Gyara zama tayi tace
“Amma naki ya fito da yawa, kowa ya kalleki yasan kina cikin damuwa. Kinga yadda kika koma kuwa?
Idanunki are all sunken, you hardly concentrate.”
Dan runtse idanuna nayi sannan nace
“I’m trying”
Shi kadai ne abinda ya fito daga bakina, kanta ta gyada tace
“Anjima ki shirya tunda baki komai se mu fita, you need a fresh air”
Kaina na gyada nayi mata godiya sannan muka koma hirar aiki anan take bani labarin MD ya kusa retire,
duk se naji babu dadi dukda bansan shi personally ba amma mutumin yasan me yake, i happened to
attend a seminar dashi.
Da yamma kuwa muka fita wani hanan hangout, mukai ta hira da ita sannan muka ci abinci danni ko
lunch banyi ba, dama kyaftun ke takurani naci, to taje off se ni daya. Sahad mukaje mukai shopping
sannan muka koma asibiti. Se naji tamkar ta bani therapy ne. Washegari saturday, kuma shi ne ranar
daurin auren Amratu, tun jiya akai kamu da mothers’ eve dama bazanje ba, koda su Ummaah suka kirani
nace ai aiki ya cabe min bazan iya zuwa ko ina ba, Ummaah tayi fadan ta tareda jadadda min akan next
weekend na tabbatar naje kwalam bikin wata neice dita, wannan nasan bazan tsallake ba, dole ne naje
idan kuma ba wani problem nake son karawa kaina ba.
Ranar sunday muka hadu, Dr lamin, Dr Hafiz, Dr fadima, Dr Habiba, kyaftun dani muka shirya zuwa rock
climbing. Tunda na tashi da asuba nayi wanka nayi mana toasting bread sannan na daukar mana drinks.
Cikin leggings da knee length top maroon na shirya, nasa hula maroon se nayi rolling veil karami sannan
nasa wani black canvas na tsaya a meeting point. Anan na tarar da Lamin da Habiba. Muka gagaisa sega
kyaftun da fadima. Dr Hafiz ne ma yadan yi delaying har muka so makara. Garu mukaje inda zamu wani
mutumi yazo danyi mana rakiya , tunda muka fara hawa dutse na fara ihu saboda abin ba na wasa bane,
a daddafe wani lokacin se an ja hannunmu sannan muke iya hawa a haka dai muka kai karshen gurin.
The amazing veiw ever. Aerial view din was wow mukai ta hotuna, nayi farin ciki, nayi dariya wadda take
from the bottom of my heart bawai yake ba kamar yadda na saba yi. A wannan lolacin na manta cewar
inada damuwa na manta da duk wasu matsalolina na kalla sama saboda yadda nake very high se naga
kamr zan taba gajimare. I was so happy.
Wajen sha daya muka koma prison dinmu, kowa ya tafi dakinshi, ina zuwa na cika bath da ruwan dumi
na shiga da towel na gasa jikina, ina fitowa na sha pain reliever naci pasta sannan n kulle dakin na fara
bacci, God so kind period nake bani Na tashi ba se wajen biyar da rabi shima knocking ne ya tadani. A
kasalance na mike tareda tambayar waye amma babu amsa hakan yasa kawai na wuce toilet na sake
wanka sannan na shirya.
Sati na kamawa ranar Friday, muna gama rounds na dauki hanya zuwa kwalam. Lokacin da naje zanyi
sallama da kyaftun seda ta cemin nayi hakuri duk abinda zan tarar. Tabbas nasan ba wani abin arziki zan
tarar ba, banda tsangwama da kuma nuna ni da zaa dinga yi. Anan sakkowa a massallacin jumaa ina
shiga garin. Straight Cikin gida na wuce nidai nasan ba tarbar dana saba gani zan tarar ba a gurin Inna
amma dukda haka na rugada na saba, indai nazo kwalam da dadi da babu dadi to gurinta nake zama
saboda ko me inna zatayi min bazan taba manta alkhairin ta akaina ba. Wannan rikon da tayi min ma
kadai ya isa balle yadda ta fifita ni akan sauran jikokinta.
Acan gefe nayi parking sannan na ciro trolley ta na rataya hand bag dita a kafada na doshi gidan. Muna
dan gaisawa da mutane har Ikram yarinyar Adda Habiba da Badar yarinyar Yaya Hauwa sukazo suka
karba kayan nawa muka shiga ciki. Gidan a cike yake anata kidan kwarya wasu na rawa, gefe ana sauke
abinci a haka na kutsa kai ina gaida mutane wasu su ganeni wasu suce ai na girma duk kammani na sun
canja, nidai nawa murmushi kawai.
A dakin inna na tarar dasu Adda da wasu daga cikin cousins dinmu, sunata shiri zaaje gurin kamu banma
shige ciki ba na zauna cikinsu munata gaisawa yawanci na jima banga mutane ba kowa se cewa yake na
zama babbar mace nayi kudi aure kawai ya ragemin. Sede inyi murmushi kawai. Adda Maryam ita ta
tayimin ankon so gurinta na karba nawa na saka ko Inna bamu hadu da ita ba na tafi.
Wajen sallar ishai na dawo a gajiye seda na biya ta gida na gaida Ummaah sannan na taho. Nanma banga
Innar ba, babu mutane sosae hakan yasa nayi shirin bacci bayan nayi wanka nazo n haye gadon cikeda
kewarshi. Rigingine nayi ina kallon roofing din gadon tareda tuna rayuwar da nayi akan gadon, lokacin i
was living peaceful banida wani tashin hankali daya takura min amma yanxun wace ni. Wayata na janyo
na bude wani Emdex application ne na drugs, na cigaba da studying magungunan. A hankali bacci yayi
gaba dani ba tareda na sani ba dama nayi addua kafin na fara karatun.
Na jima da yin baccin kamar daga sama naji ana tashi na, da kyar na bude idona raina duk a jagule
saboda i hate it idan aka katse min baccin dare. Inna ce a tsaye tana kallona hakan yasa na tashi daga
kwancen da nake tareda gyara zaman hular kaina nace
“Inna an wuni lafiya? Ya taro?”
“Lafiya lau”
Ta bani amsa sannan tace
“Asmau wannan gadon da kika kwanta akai ki sakko ki dawo kasa”
Kallonta nayi da rashin fahimta nace
“Ai zai ishemu mu kwanta ni dake, se kace nayi kiba”
Kawar da kanta tayi tace
“Kinga Amina da Nusaiba ne zasu kwanta akai saboda kinga su ciki ne dasu, kuma me aure bai saba
kwanciyar kasa ba”
Kallonta nake sosae, maganar ta dakeni idan tacemin sakko Asmau wasu zasu kwanta saboda ciki, ni ai
ba hauka nake ba nasan me ciki need something comfy babu yadda zaayi me ciki ya kwanta dandaryar
kasa but meye se ance me aure bai saba kwanciyar kasa ba wato dole se an nuna min ni din banyi aure
ba kenan. Kaina na gyada nace
“To ni ina zan kwana kenan?”
Tabarma dake gefe ta nuna min tace
“Ki sakko ki shimfida ta”
Wani mugun takaici ya kamani nace
“Inna, kinfi kowa sanin bana bacci akan tabarma, ina laifin waccan katifar”
Na nuna mata extra katifar ta da take jingine, a hasale tace min
“Ke sakko daga gadonnan, idan baki son tabarmar kina iya tafiya wani gurin. Yarinya se tsirin masifa da
ruwan ido, dole ki kasa aure”
Yadda nake kallonta seda yasa ta dauke kanta naji haushi sosae yadda har bazan iya fada ba, kaina na
girgiza tareda sakkowa daga gadon na finciki hijab dina da wayoyina nayi waje amma se na dawo har
lokacin tana tsaye bance mata ci kanki ba na janyo trolley na da hand bag dita na nufi kofa se ta biyoni
tana fadin
“Matsalata dake kawata zuciya, meye abin hada kaya?”
Juyowa hawaye ya cika min idanu nace
“Aure Allah yake sawa ayu, idan lokacina yayi zanyi, gorinku da duk wani tsangwama ta bazai saka nayi
ba.”
Kafin na gama tuni wasu daga cikin mutanen dake parlor sunzo suna tambayata me ya faru babu wanda
na kula nayi ficewata Allah yasa bankai motata gida ba hakan yasa na bude motar na shiga tare da kifa
kaina jikin steer wheel na fara kuka, a raina ina rokon Allah ko aron wucin gadi ne yasa nayi, ko ma
wanene kawai Allah yasa nayi aure na huta. Seda na gaji da kukan sannan na kira Adda zannira akan ta
bude min gida ina nan tafe. A takaice dai acan na kwana, juyin duniya Yaya Halifa yayi akan na fada masa
meye matsalata naki suka hakura suka kyaleni.
Washegari ban fita ko ina ba ina daki ina jinyar zuciyata bansan waye yace ma Inna ina gidan ba se gata
tazo da kwanuka wai na kari nace mata ni na koshi bazan ci ba, ta kada ta raya naki, ko ji tayi abinda
tayimin bai dace ba oho mata dai. Da yamma kuma sega Ummaah itama abin mamaki lallashina ta dinga
yi har ta tsareni naci abinci sannan ta tafi. Da daddare mamansu Rahina taxo biko akan na koma can
gurin inna amma nace ni sede wata kuma, ba dai aure bane to nayi alkawarin ko dan cocaine ne yace
yana sona aurenshi zanyi, na gaji da wannan masifar har ina?
Ayshatuuuu
[5/30, 6:21 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_TWENTY NINE_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Wayata na kalla a karo na barkatai ina kallon text din da Ummaah ta turo min kusan awa daya data
shude , numbers ne har guda biyu na GLO da MTN a kasan an rubuta Barr. Ishaq. Kifar da wayar nayi
kawai ina jiran inji kiranta dan tayi min karin bayani amma shiru bata kira ba, nima kuma ba kira zanyi ba
saboda ina tsoron abinda zatace min, bana son hooking stuffs dinnan gwara no matter how bad a
situation is gwara ace shidin ya fara ganinka yace yana so, dan bahushe yace matar cushe bata da
kwarjini. I believe in that also.
Hakan yasa na mike na cigaba da gyaran daki. Ranar call nake so yamma nayi Na shirya na dauki
stethoscope da key din mota da wayoyina na fita. Call room naje Na zauna a gefe ina chatting a wayata
ni kadai ce cikin dakin, se can aka kirani a Emergency hakan yasa na tashi na tafi na tarar da wani fatal
accident. Tabbas aikin asibiti dole yasa ka kara gaskata iko da daukaka ta ubangiji, mutum ba komai bane
a rayuwa duk wannan dagun kai da dagawa amma lokaci daya Allah zai iya reforming halittar shi muga ta
karshen girman kai. Mutanen da sukai accident su goma ne cikin wata golf, i wonder yadda sukai
squeezing kansu cikin wannan karamar motar.
Ina shiga na adana wayoyina da sauran abin amfani, O'C dake duty su uku muka hadu dasu dan ceto ran
mutanen, amma uku seda suka mutu babu yadda zakayi, sede you will be contented kayi abinda ya
kamata tunda duk munsan death is inevitable. Haka sauran bakwai muka sakasu cikin class din daya
dace bamu muka zauna ba se bayan sallar ishai. A matukar gajiye mukai sallah sannan na dawo dan nayi
documenting aikin, sannan mukai sallama na koma lounge anan na tarar da missed calls din Ummaah.
Ina zama na fara kiranta ta dauka nace
"Ummaah inata aiki kika kira, ya gida?"
"Lafiya lau"
Ta bani amsa sannan tace
"Kinga numbers da na turo miki dazun?"
Seda gabana ya fadi nace cikin sanyin jiki
"Na gani Ummaah, inata son na kiraki"
"Ni dana matsu ai na kira, kinsan Hajiya Barira right?"
Kaina na gyada kamar tana ganina nace
"Eh, Ummin Kaduna ko?"
Kawar Ummaah ce irin childhood friend dinnan ce , kowa yasan yadda Ummaah ke ji da ita haka itama
indai zatazo kano to se kin ganta tazo gurinta.
"Yawwa, wannan Ishaq din danta ne na uku zaiyi aure shine nake son ku daidaita kanku, kinga kema kya
samu ki huta da gorin mutane"
Se nayi shiru tareda adduar Allah yasa ba nufinta in kirashi ba, jin nayi shiru yasa tace
"Baki jina je Asmau?"
"Ummaah to me zanyi yanzun?"
"Kiranshi zakiyi mana, me kike jira da? Come on ki kirashi kice kece wadda Hajia tayi mishi magna akai"
Se naji raina ya baci ni zan kirashi ma bashi ba, ok ya raina ni kenan. Ni na gaji da yadda Ummaah ke
hadani da yaron kawayenta suna raina min hankali dan wannan shine third time ana hakan.
" Ummaah, dan Allah karki sani nayi haka, shi ku bashi number ta ya kirani mana amma hakan kamar irin
neman kai akeyi dani ne?"
Baki bude Ummaah tace
"Oh da baki gane ba? Shi ai bashi yake nema ba mu muke nema so mu zamui proposing kingane?"
Kaina gaba daya se ya kume, I couldn't think straight wanne irin ni nake nema ni zanyi proposing? Kawai
se nace
"Shikenan"
Kafin muyi sallama ta tambayeni ni na tura mata kudi nace eh, tayi ta shimin albarka har naji dadi
sannan na kashe wayar inajin wani abu ya tokare min kirjina, da kyar nake iya fuzgar numfashi na, idona
yayi ja ina fatan Allah ya kawomin dauki a rayuwata, ya kawo min miji nayi aure. Dan nasan bani kadai ce
a duniya nakai shekarun nan banyi aure ba amma kowa ya takura min an hanani zaman lafiya da
kwanciyar hankali. Hannuna nasa na rufe fuskata nayi ta kuka kamar raina zai fita ina fatan as my tears
cascade down my cheeks, all my worries will be gone and my pains will be ease!
Ina gama kukan lokacin already goma tayi ko lunch banyi ba balle dinner, yunwa nakeji amma bana
tunanin inada nutsuwar zama naci abinci. Mikewa nayi na fito daidai shigowar kiran kyaftun , se naji
wani sanyi cikin raina at least someone cares. Ina dauka ta tambayeni inda nake , ko minti biyar ba ayi ba
se gata da basket a hannunta, tunda ta kalleni se naji jkinta yayi sanyi , zama tayi ta hadamin tea ta bani
babu musu nasha sannan ta zuba min Arabian sphaghetti tasha vegetables haka naci sannan tace
"Wannan kuburin na ido me ya faru?"
Lumshe idona nayi ai kamar ance lacrimal glands su sake hawaye se suka wanken fuska, hannuna ta rike
batace min komai ba se kallona da takeyi , se can tace
"Asmau menene akan aurenne?"
Kaina na gyada na fada mata komai daya faru, se cemin tayi
"Ki kirashi kinji"
Wani kallo nayi mata irin are you mad dinnan? Murmushi tayi tace
"Ummaah ce tafi karfin komai, just do it saboda haka Ummaah tace"
Haka na kwana ina tunanin yadda zan bullowa koda safe dana fadawa Adda Sa'ada cewa tayi nayiwa
Ummaah biyayya hakan kuwa nayi dukda jikina a matukar sanyaye yake haka Na kirashi, tunda ya dauka
ko sallamar da nayi bai amsa ba yace
"How may i help you?"
Duk se naji na muzanta amma haka na daure nace
"I'm Asmau shahada, ni ce wadda hajianka tayi maka magana akaina"
Maimakon naji tone dinshi ya canja se naji ya kara tamkewa yace
"Ya akai to?"
Na kasa cewa komai se wasa nake da hannuna tareda jin mugun haushinshi kamar na shako shi haka
naji, jin nayi shiru se cewa yayi
"Kinga idan kin shirya bayanin kanki kya kira but I've better things to do!"
Kit! Ya kashe hannuna na rawa na ciro wayar ina kallonta da gaske yayi hanging, take nayi deleting
numbers dinshi daga wayata baki daya inajin tamkar na shake kaina tabbas Ummaah ta gama dani. Da
daddare ta kirani akan ko na kirashi na fada mata yadda muaki dashi, tsaki tayi tace na kyaleshi to
wannan ya dan sayaya min rai.
Ana fara tafiya aikin hajji na tafi nima, i badly want to talk to Allah, lokacinda na ganni gaban kaaaba se
kuka na rasa abin roka, se kankame jikina da nayi saboda yadda dukkn tsikar jikina ke tashi. Na jima
sannan na samu nayi addua dake lokacin mune daukar farko i got the space. A wannan lokacin alkawarin
Allah ya cika kyaftun ta auri Dr Lamin.
Bayan na dawo nigeria da hope akan nasan da izinin Allah kukana ya zo karshe. Nasan soonest alkawarin
Allah zai tabbata kaina amma shiru har shekara take neman zagayowa, banma kara saurayi ba duk yadda
nakejin nakai babu wanda ya kalleni da sunan yana sona, nasha tsayawa gaban mirror na kalli kaina, inga
ina nake da makusa. Ni fara ce fari sosae har wani yellow yellow nake, idan nayi mirmushi bayan dimple
dake lotsawa a both sides na kumatu na, akwai wata jijiya green dake fitowa rado rado a goshina.
Idanuna normal suke kamar na kowa sede eye balls dina manya ne kuma deep chocolate orbs nake
dashi. Hancina dogo ne bakina daidai ni da kaina nasan im a beauty, akaina na fahimci kyau baya kawo
miji se lokaci yayi.
Pressure kam se wadda ban fada ba amma akwai lokacinda nayi wata hudu banje kano ba ina dutse
saboda Ummaah kamar ta dakeni idan muka hadu ga inna kamar danni ta koma kano saboda girma,
kullum gorin yau daban na gobe daban. So se na daina zuwa gidan gaba daya, sukai cigiyar duniya suka
rasa. Ranar wata monday na shiga OT yin Appendectomy, ina fitowa straight dama daki nayi niyyar tafiya
dan na shirya zanje wata seminar, da sauri na kalla office din Chief Anaestethist saboda jiyo muryar da
Abba da nayi. Banma yi niyyar shiga ba haka na