Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fara Yar Shehu Complete Hausa Novel by Shatuuu

Author :  SHATUUU Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 23

45K to 48K   out of 67.2K words

ta: daga
nan OT na wuce, na samu sun shirya kawai jurana ake hakan yasa na kira dan a kawo patient din. Ana
kawo ta na dubi scrub nurse din nace



“Sister, waye zamuyi surgery din dashi?”



Dariya tayi tace



“Baki sani ba dama”



Kafin na bata amsa naji wannan deep voice din tashi, dukda sau daya na taba ji amma hakan baisa na
manta da ita ba.



“Evening everyone”



Juyawa nayi da sauri tareda bashi hanya nace
“Welcome sir”



Kanshi ya gyada min sannan ya bawa mazan gurin hannu sukai musabaha ya shiga ciki yayi changing
sannan muka fara. Tunda na mika masa scapel yake min tambaya akan conditions din matar, God so
kind nima book worm ce so yana tambaya ina amsa shi inda gyara yana min yana kara clarifying min
abubuwa. Haka mukai almost 4hours muna abu daya, se bayan maghrub muka gama aka maida ita ward
mukai sallah sannan yace a kawo masa folder yayi documenting. Ni na kai masa yace



“Sit please!”



Zama nayi kamar yadda yace, idanunshi ya maida kan folder yana going through hx matar.



“What’s your name?”



Dagowa nayi na kalleshi amma bani yake kallo ba amma nasan dani yake tunda ni dashi ne kadai cikin
office din



“Asmau Shahada”



Kanshi ya gyada yace



“A ina kikai training dinki?”



Shortly nace dashi



“BUK, sir”
“Good!”



Daga haka baice komai ba se can ya mika min folder yace nayi rubutun. Zama nayi yana kallo ina
rubutawa yana kara guiding dina har na dan saki jikina. Muna gamawa yace min



“You’ve done a good job. We meet some other time”



Kaina Na gyada ya fita ni kuma na koma na zauna ina maida numfashi. Tun daga lokacin shi kenan indai
zaiyi aiki kowa yasan I’m his partner tun abin yana damuna har na sake na saba.



Wata Wednesday mun gama ward round, banyi breakfast ba ranar saboda kadan ya rage ban makara ba
hakan yasa na tafi cafeteria dan cin abinci. Tsirarin mutane na tarar suna cin abinci, wasu sun gama, seda
nayi order sannan na dawo na zaune ina jiran a kawo min. Nayi nisa sosae a cikin wayata ina chatting
naji alamar an zauna gefe na. Da sauri na dago wani mutumi ne in his mid thirties ya tsareni da idonshi,
the gaze was so intense hakan yasa nace



“How may i help you”



Wani murmushi ya saki yace



“Finally, na samu ganin workaholic Dr Shahada. How far?”



Bansan amsar da zan bashi ba hakan yasa nayi shiru tareda maida hankalina kan wayata, i knew him
somewhere amma na rasa a ina na sanshi. Shima bai kara cemin komai ba seda aka kawo min abincin se
na maida shi akan ayi packaging ba anan zanci ba. Se naji yayi dariya yace



“Doctor, ya zaki ce ayi packaging?”
Dagowa nayi na kalleshi nace



“Ka takura min”



Murmushi yayi yace



“Tun yanzun, ai abinda zuciya ke so no way ta bar abinnan”



Mikewa nayi naje counter cashier na biya sannan na fice kawai, ashe yana bayana seda nayi nisa sannan
yace



“Doctor, you shunning me?”



Tsayawa nayi nace



“Idan abu kake so ina ganin wannan is not right kazo ta haka, dan Allah idan wani abunne follow the
right route”



Daga haka na juya zan tafi, to my utmost amazement kawai se ya ruko hannuna cikin sauri na juyo,
mamaki kamar ya kashe ni, kafin nayi yunkurin cire hannun se ji nayi ance



“Asmau!”



A tsorace na dago idanuna only to see MD a tsaye ya tsareni da idanunshi da suka kada sukai ja, sunkiyar
da kaina nayi tareda kwace hannuna, tuntuni idanuna sun fara kokarin kawo ruwa. Yana isowa gurin
yace
“Meet me in my office yanxunnan!”




Ayshatuuuu

[6/10, 2:15 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻



_THIRTY FOUR_




✍🏻 *SHATUUU❤*

_Jakadiyar kainuwa_




💖Shatuuu095@ wattpad




*‫*بسم الله الرحمن الرحيم‬
*____________________________________*




*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*____________________________________*




Tamkar an daddatse min joint dina haka naji, ilahirin jikina yayi sanyi na rasa abinda yake min dadi.
Lumshe idona nayi na dubi useless, unreasonable Ashole dake tsaye yana wani irin smirking, idanuna na
lumshe raina a mugun bace kawai na juya na tafi. Once in a lifetime kowa yana experiencing such
embarrassment, tunda nake ban taba jin kunya irin wadda naji ba. Tamkar anmin duka haka na tafi ina
tunanin ta inda zan fara hada idanu dashi. Taya mutum zaiji ace mutumin dake ganin mutumcin ka ace
yaga wani ya rike hannunka nasan Allah kadai zao fitar dani.



Banyi gigin zuwa office dinshi ba saboda bansan wanne ido zan kalleshi ba kawai se na juya na tafi mota
ta nayi mata key se gida, dukda hankalina yana kanshi Amma zuciyata gargadi na take akan kada fa na
zake, tayi kuwa nasara haka na basar na tafi daki naci abinci sannan na kwanta, a raina ina fadin aikin ma
na yau na fasa bazanyi ba.
Shikam acan a mugun fusace ya isa office dinshi, yana shiga yayi slamming kofar da karfi tareda fadawa
kan cushion ya zauna, cushions ne guda hudu tsakiya center table ne me kyau covered with glass baki
daya. Zama yayi ya daura kafafunshi akan table din. Wani zafi ne ke karyo masa se gumi yake ka rantse
da Allah yana karkashin kwalleliyar rana ne, nan kuwa cikin niimar split yake har biyu a cikin office din.
Coat dinshi ya cire ya aje gefe sannan ya sassauta necktie dinshi tareda kurawa kofar idanu yana
expecting shigowar Asmau amma har awa daya ta shude babu Asmau babu alamar ta. Mikewa yayi ya
fara pacing a cikin office din, me yarinyar nan take nufi dashi yace tazo sannan taki zuwa ta sameshi,
kanshi ya girgiza daidai knocking a kofar hakan yasa a sukwane yace



“Yes, come in please”



Kofar aka turo idanunshi a kafe yana jiran ganin wannan farar fuskar tata amma maimakon ganinta se
yaga ashe Director Admins and finance ne, se lokacin ya tuna sunada magana dashi. Daidaita kanshi yayi
cikin sauri ya koma seat dinshi tareda masa izinin zama, seda suka gaisa kafin ya bude file ya fara briefing
dinshi amma rabin hankalin Dr Kwaccido baya gurin tunnainshi kodai mutumin da ya gani tareda Asmau
ya gudu da ita ne? Kodai dama saurayinta ne cikin sauri ya matsar da wannan thought din a ranshi, it
took him almost 2 months yana bincike a ciki da wajen asibiti akan Asmau, babu inda yaji tana da wani
tsayayen magana a kanta....



“Sir, you’re not concentrating, ko mu hadu gobe?”



Kanshi ya dafe cikeda damuwa yace



“I’ll be glad, thank you”



Haka ya tattare kayan shi ya tafi shi kuma ya cigaba da jiran tsamanni amma har yaje azahar ya dawo
bata zo ba, sau da dama se ya fara dialing numbers dinta da yayi storing dinsu a kwakwalwar kanshi tun
ranar da Dr halima ta bashi ita amma ya kasa, baisan abinda zaice mata ba, zuciyatshi tasha gargadin shi
akan wannan kallon ruwan da yake kada wankin hula ya kaishi dare. Ko kuma garin bari ya huce har ya
zama rabon wasu, kanshi ya girgiza dan baya tunanin zai iya bari hakan ta faru.



Wajen laasar ya kammalla komai na ayyukan ranar, hannunshi rikeda briefcase da suit dinsa yana waya
ya fito, messenger dinshi ya karba tareda kai mishi mota, godiya yayi masa sannan ya wuce cikin motar
yana baza idon ganin ta inda zata bullo amma bai ganta ba haka ya tafi dik babu dadi, haka nan yaje
gida. Kamar yadda ya saba ganin gidan it was so empty ya zaiyi tunda haka kaddra ta zabar masa kuma
hakanan zai karbeta babu yadda zai iya. Straight bedroom dinshi ya wuce yayi wanka yayi alwala sannan
ya zura jallabiya brown me gajeran hannu ya dawo parlor ya zauna. Babu jimawa yaji ana knocking
wanda yasan ba kowa bae illa sabiu cook dinsa, sunyi waya yace masa ya fita dan yun wata gaisuwa.
Shigowa yayi ya risina ya gaisheshi sannan ya wuce kitchen dan hada masa abinci, idanunshi ya lumshe
yana bin parlon da kallo, ko ina a share yake, tiles din se kyallin mop suke amma kana kallon yadda
komai Na parlon yake kasan babu mace a gidan. It’s obvious kana shiga zaka fahimci hakan, kanshi ya
shafa yana jin lokaci yayi da zaiyi uncaging zuciyarshi hakanan, ya kamata ya fito daga dreadful past life
dinshi ya cigaba da rayuwa, wannan zuciyar tana bukatar aboki, ya kara kallon katon parlon da hasaso
gadon shi, yana bukatar living partner, he sure needs a soulmate.




Washegari ranar alhamis, kamar kowanne sati ita ce ranar da muke surgery ni da Dr Kwaccido. So ranar
tunda nayi asuba na ko wanka banyi ba Na tafi Paediatric surgical ward, nan patient din yake. Yaron
shekarashi biyar yana fama da umbilical hernia. Though condition din is a minor one amma a haka yayi
mana booking. Ina zuwa anesthetist din tana zuwa, tare mukai reviewing dinshi kowa yayi documenting
abinda ya samu sannan muka rabu. Gaba daya ji nake inama inada excuse din da zan bayar dan bana
sam haduwa dashi kwata kwata amma ina na babu wannan, se goma na safe sannan na fito, fuskata tayi
yar fayau tsabar fargaba da damuwar da nake ciki idanuna duk sun fada sunken in. Yanayi na ma kawai
zaka kalla kasan akwai tambaya. Ina zuwa office na samu kan sofar dake gefe na dan kwanta ai bacci
yace idan kaci bashi na se ka biya and it happen.



Bansan ashe har time ya tafi ba, se can naji ana knocking kofar office dina, ko kafin na tattara guntun
karfin da ya rage na tashi, tuni kofar was flung open. Wannan kyakyawar fuskar tashi me cikeda haiba da
kwarjini tasa nayi saurin tashi ina lalubar veil dina, wannan idanuna nashi that always shine me kamar an
zuba musu mai cikinsu ya tsareni dasu, a take naji kamar anyimin duka, yunkurun da nake na daina se
kasa da nayi da kaina ina jin an takura ni da yawa. Yana tsaye tareda harde hannyansa a kirjinshi shi bai
zauna ba bai kuma nema gurin zaman ba. Kafin na kara yunkurawa naji yace



“Sleeping on duty?”



Da sauri na muskuta tareda girgiza kaina nace
“Sir, banida lafiya ne”



A take naga yanayin fuskar shi ya canja, shigowar shi tamkar wani zaki haka ya shigo ranshi a hade amma
yanzun se naga damuwa ta dauke bacin ran dake ciki. Daidaita tsayiwarshi yayi cikin wata tattausar
murya wadda babu wani da namiji daya taba amfani da ita wajen yimin magana yace



“Sannu, kinsha magani?”



Kaina Na girgiza nace



“I was about to, se bacci ya daukeni.”



Kanshi ya gyada se kuma ya fita, hakan yasa na sauke nannauyar ajiyar zuciya tareda lumshe idona, ni
nasan banda lafiya amma a matsayina ta likita bana tunanin nasan me yake damuna, ban kuma san
wanne irin taimako zan bawa kaina ba, nasan kilan tarin damuwar da nasa a zuciyata ce take neman
kayar dani.....Soft knock akai jikin kofar, bakina a hankali na bude tareda bada izinin shigowa, shi dinne
ya dawo sede wannan karan ya samu rakiyar head of medical department da kuma chief pharmacist.
Inata kokarin mikewa ya hanani tareda bawa Dr Mansur damar ya dubani, BP na ya fara dubawa, kawai
gani nayi ya cire glasses dinshi yace



“Her BP is reading 70/40mmHg sir”



Yana fadar haka se naji tamkar an saukar da min symptoms, baice komai ba illa bina da yake da
idanunshi me tuhumata akan Me ya faru? Nidai kasa kawai nayi da kaina ina jin ana min prescription
sannan aka kira pharmacy suka kawo. Drip aka fara daura min yana fara shiga wani wahallalen bacci yayi
gaba dani. Se can bayan wasu awoyi sannan na farka , ina office dina amma ba kamar dazun ba, ina bude
idona da kyaftun na fara cin karo tana sallar laasar. Cikin sauri na yunkura inajin karfi a jikina ba Kamar
dazun da nake jin jiri ba.

Toilet na shiga nayi alwala sannan nazo na zauna dan har lokacin jikina gashi nan dai, a zaunen nayi both
zuhr da asr sannan na kwantar da kaina akan cushion ina lumshe idona.
“Ya jikin Twin?”



Bude idanuna nayi tareda yin kalar tausayi na dubeta har lokacin uniform ne jikinta alamu sun nuna kilan
ko ward ba taje ba, ga Afeeyya ‘yar 5 months ta shimfidar da ita a yar corner se baccinta take peacefully.



“Twin Alhmdllh. Yaushe kika zo? Waye ya fada miki?”



Wani kallo tayimin wanda ta saba yimin idan gulma ta motsa, hakan yasa na cuna bakina ina dauke kai.
Dariya tayi wadda tasa dole nima nayi sannan ta matso tace min



“Boss ne, da kanshi yazo har ward ya tafi dani, he left here not long ago.”



Kaina na gyada kawai ba tareda nace komai ba, dan bansan me zance din ba. Sake matsowa tayi kamar
zata shige jikina hakan yasa na ture ta baya da dan guntun karfin nawa daya rage nace



“Ke munafuka ce”



Shrugging shoulders dinta tayi tace



“Oho! Baby bude baki zakiyi kimin bayani, me yake faruwa. Kinga yadda ya rikice? Ni daya shigo ward
dinmu I thought something terrible happened ashe Twin ce babu lafiya”



Hararata nayi nace



“Kede Allah ya sawwake miki, he’s none but my boss and partner aiki na”



Tsareni tayi da idanu irin she needs more, tsaki nayi nace
“Dan Allah ki bani abinci I’m starving”



Hakuri ta bani sannan ta hada min wani tea me kauri, yayi min dadi kodan ina cikin yunwa ne oho, seda
na shanye tas sannan tace an tafi a kawo abinci. Bata kara min zancen ba tunda tasan da akwai wani abu
da zan fada mata, tsakani na da ita babu boye boye so we still maintain the status. Tunda nayi shiru na
fada tunani, anya yadda zuciyata ta adana Dr Kwaccido matsayin shugabana da kuma partner aiki? Ina
tantamar hakan, duk wanda nayi aiki dashi zai nuna yaji dadi kuma zaiyi kokarin maintaining dina tun ina
house job amma shi nashi salan caring din ya banbanta dana kowa. To amma someone like him....
Sallamar shi yasa nayi saurin bude idanuna, a hankali na amsa wanda iya bakina ne kawai ya motsa,
muna hada ido ya sakar min wani murmushi. I swear seda tsikar jikina ta tashi, those eyes of his will
definitely not allow me to live in peace sede idan kullum zan kasance ina kallonsu ne.



Gaisawa sukai da kyaftun sannan ya mika mata ledar hannunshi yace abinci nane, gefena ya dawo ya
tsugunna yace



“Are you ok?”



Kaina na gyada nace



“Much better. Thank......”



Shush yayi min sannan yayimin murmushi yace



“Kici abinci zanje office”



Se na samu kaina da yi masa murmushi nace



“Allah ya bada saa”
Kanshi ya gyada ya dubi kyaftun dake rike da Afeeyya data riga ta tashi ya bata sallahun lallai naci abinci.
Aikuwa yana fita ta fara tsokanata wai wallahi so na yake nidai ban kulata ba dan bazan saka abin a raina
ba balle ayi back stabbing dina!




Your comments keep me going........



Ayshatuuuu

[6/12, 1:36 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻



_THIRTY FIVE_




✍🏻 *SHATUUU❤*

_Jakadiyar kainuwa_




💖Shatuuu095@ wattpad
*‫*بسم الله الرحمن الرحيم‬




*____________________________________*




*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*____________________________________*




Ina kammalla cin abincin naji wani karfi yazo min, duk wannan kasalar babu ita, mikewa nayi na tattara
gurin sannan nace da Kyaftun mu tafi gida dan ina son nayi wanka na canja kayan jikina. Babu musu ta
tattara kayanta muka fita, bani da wani karfin da zan iya driving hakan yasa kyaftun karbar key din ita
kuma Afeeyya na karbe ta, mun saba da ita sosae bata min kiwa dan wani sa’in se tayi ta kallona ni da
kyaftun tana tantamar gurin wa zataje tunda kowa yasan nida mahaifiyar ta kama muke sosae, banbanci
na da kyaftun nafi ta haske ita kuma ta fini tsayi sannan ita ba a rame take ba, wadda tashin hankali da
damuwa yasa na koma hakan.
Muna shiga na aje Afeeyya na shiga wanka, simple gown nasa ta wani pure cotton yard maroon, free
gown ce se stones da aka mata ado dashi. Scarf milk na dakko Na daura sannan na murje jikina da
turaren kullum La’eeqa da soft. Lumshe idanuna nayi na dawo na zauna inajin wani daddan yanayi a
jikina. Kallon kyaftun nayi da take kokarin hada pap din Afeeyya,



“Ki kirashi kice kin dawo gida, let him not waste his time checking on you a office”



Dan bata fuska nayi tareda fadi



“Is there need for that?”



Kanta ta girgiza tana hararata tace



“Kina da matsala kinsan da hakan? How....?”



Se tayi shiru tareda daukar Afeeyya ta daura ta cinyarta ta fara feeding dinta, wayata dake gefena naji ta
fara ringing hakan yasa na kai hannuna na dauka, Adda Sa’ada ce cikin sauri nayi picking dan ta rigada
tasan banida lafiya, i texted her though ina tunanin se lokacin ta gani. Ina picking tace



“Fara what happened?”



Dan murmushi nayi jin muryarta duk da damuwa nace



“Ba wani abu bane kawai BP na yayi low”



Ai fa kamar famfo ta fara zuba, tana tamin fada akan tasan na takurawa kaina ne shiyasa hakan ta faru,
seda ta gama fadan sannan ta dawo nasiha tana fadin
“Komai da kike gani is a matter of time, da ace tsangwama da takura kai yana sawa kayi abu, da tuni
kinyi aure amma shi Allah is wonderful, he’s a perfect timer. Lokaci ne da zarar yazo zakiji it worth the
wait!”



What will life be without Adda Sa’ada? Hell na ayyana a raina, bazan iya fadar abubuwan da matar
tayimin a rayuwa ba amma she sticks around bata taba nuna min laifina bane da banyi aure ba, Anty
Bintu, Yaya Halifa da Adda Meeyna. Banda kamar su. Ina aje wayar kyaftun ta mike tana fadin



“Kada ki zama kina manta alkhairi kuma kada ki bari a golden opportunity like this ya wuce ki. Zan tafi
gida, se dare zamu dawo da Daddyn Afeeyya.”



Mikewa nayi a hankali dan bawai malaise din dake damuna ya tafi duka bane, yanzun ma jina nake
kamar zan fadi dan dai ina daurewa ne. Hannunta na riko nace



“Ki fahimci abinda nake nufi, i can’t just throw myself on him kamar yadda nayi akan mukhtar (RIP) da
kuma Suleiman. I was back stabbed kuma laifin waye? Nawa ne saboda ina ganin dukkan wanda yadan
nuna kulawa akaina sona yake. Kina son na kara haka, repeating same mistake is nothing but
foolishness”



Zaunar dani tayi dan taga alamar zan iya faduwa ta rike hannuna tace



“Ki fahimci abinda nake nufi nima, ba ina nufin you start chasing him, stalking him and stuffs. Kinsan dai
ya miki abin kirki to ko thank you ne he deserves it.”



Kaina na gyada in agreement na dauki wayata and I sent him



Thank you, jiki yayi sauki. Na bar office ina gida



A gurina they were only a plain words amma a gurinshi yayi ta nanatawa saboda dukkan abinda zai fito
daga gurina yana daukar abin me muhimmanci. Baiyi min reply ba har kyaftun suka kawo min abinci naci
suka tafi na kulle dakin na kwanta tunanin rayuwata yayi min rubdugu, addua a bakina kan Allah yasa
Ummaah ta fahimci rayuwa, ta fahimci cewar lokacin zai zo. Da wannan bacci yayi gaba dani se can cikin
baccin naji

16 / 23