Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fara Yar Shehu Complete Hausa Novel by Shatuuu

Author :  SHATUUU Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 23

3K to 6K   out of 67.2K words

suke dokin
dawowata amma ni jinta kawai nake, muna nan Sega su Adda sun fito kusan lokaci daya gaba dayansu,
se Yaya Halifa fuskarshi a murtuke ya samu guri ya zauna yana wurga min harara, cikin rashin saa Inna ta
lura da hararar, kawai gani nayi ta dada mishi Duka a bayanshi tareda fadin



"Dan banza kawai, uban me tayi maka da safiyar nan zaka kafa hararar ta? Dole yarinya tabi ta lalace,
kun saka ta a gaba kamar mayu"



Idaanuna sukai raurau alamar kuka, su kuwa banda dariya babu abinda suke, a Haka Abba da Ummaah
suka iske mu, abincin duka babu wani armashi haka mukaci, ana gamawa Inna ta dubeni tace



"Maza Kawata tashi dakko kayanki kizo mu tafi"



Kowa a parlon zuba min idanu yayi, suna jiran ganin abinda zanyi. To everyone utmost amazement
kallonta nayi nace



"A'a Inna Ade, kije ni bazanje ba"
Wani mugun kallo Tayi min zatayi magana se kuma ta juyar da kanta zuwa inda Adda Sa'ada ke zaune
hannunta da tea mug tana kurba,



"Ahaf! Ni nasan zaayi Haka, wannan yayan suna gidannan ai na daina ganin daidai. Sa'adatu da Aminu
ba. Nagode sosae Kunyi kokari. Amma ku sani Fara 'yar shehu Ko kunso Ko kun ki tawa ce, barazanar ku
babu abinda zatayi mata! "



Tana gamawa ta Mike tareda kallon Abba tace



"Zan wuce Shahada"



Abba da Ummaah Wanda suka rasa bakin magana suka mike tareda bin bayanta, Nikam dakin Ummaah
na koma Inata kuka, wayaga samu da rashi.



A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya na hakura da zancen zuwa Kwalam na rungumi sabuwar rayuwar
dake gabana. A wannan hutun sosae nayi Karatu, Yaya Halifa ba karamin kokari Yayi a Kaina ba. Babu
Wanda yake min magana da Hausa seda turanci. Kafin Hutun ya kare har na Fara mayarwa. A bangaren
islamiyya shima sosae nake abin kirki, hakan ba karamin dadawa su Abba yayi ba, shikenan aka daina
takura min, tunda na riga nayi blending da yadda suke son na zama.



Duk Hutu idan akai Zaa kaini Kwalam nayi sati daya sannan na dawo. A Haka shekaru sukai ta ja har nakai
shekaru goma sha biyu, lokacin ake ta cukwukun kaini secondary school. Matsalata daya ce wadda kusan
kullum se anjini da Ummaah da Sauran sisters dina, bana Aikuwa, I'm very lazy, laziness dina Har ya saka
jikina kanshi na gyara se ya zama abu, wanka se Ummaah tace min naje nayi, balle gashina, se nayi sati
biu ban taje shi ba, idan aka samu nayi kitso zan iya 3 months ban tsefe ba. Kuma nafi kowa Baki idan
akace Ni kazama ce, kuma deep down inside me nasan ni kazama ce, kuma san jiki shi ne ummul aba'isin
kazantar.



Wani yammaci mun dawo daga islamiyya nida Adda Salma da Adda Maryam, tunda muka taho bakina
yake a cunne Kamar Karin kunama, saboda Adda Salma tace kaina yana wari, Bance komai ba Har muka
isa gida. Ina shiga dakinmu na tarar da kayana duka na cikin wardrobe an fito dasu an watsar a tsakiyar
dakin.
Takaici kamar zanyi me, ciki na karasa Ina bin kayan da kallo, gaba daya an cakuda wankakku, gogaggu
da masu datti. Idanuna taf da kwalla nayi kofa zan Kai Kara naji an bude kofar toilet an bude, komawa
nayi, Adda Meeyna ce hannunta rikeda face towel tana goge wet face dinta.



"Yawwa kwashe kayannan ki fitar dasu, yarinya kamar 'yar daji se shegiyar kazanta"



Tura bakina nayi na juya na tafi gurin Ummaah, Tana kitchen tana kada miyar dare,



"Ummaah kinga Adda Meeyna Gabaki daya ta Watson da kayana waje ko? "



Seda ta kashe Gas din sannan ta kalleni tace



"Ba kazanta kike ba Asma'u? Shekara goma sha biyu ace wanka se nace miki kiyi? Wallahi dama kisani ba
NTIC kike so ba? Allah Bazaa kaiki ba, Gwaram zaki tafi, yadda ko sunana kikaji se Kinyi kuka, se seniors
sun miki dukan da ko cewa akai kiyi kazanta bazakiyi marmarin hakan ba"



Ai daga jin hakan na Fara kuka ina bata hakuri amma ko kulani Batayi ba ta tafi daki, komawa nayi dakin
Inata kuka, na tsugunna na Fara tsitsince kayan, Adda Maryam ce Tazo ta tayani muka gyara kayan,
Wanda basuda guga na kaisu inda ake Tara kayan guga. Marasa wankin kuma na kaisu cikin laundry bin,
ni Kaina dana kalla wardrobe din seda naji dadi, saboda yyai kyau. Sallah mukai sannan muka zauna ta
tsefe min Kaina Dama kitson guda goma ne, ana cikin combing Adda Sa'ada ta shigo, gefenmu ta zauna
bayan ta dage curtains sannan ta kura fanka tace



"Wannan se mutum Yayi suffocating saboda warin da Kanki yake"



Ni magana Tana min wahala, amma da ina magana nasan tabbas rashin kunya zanyi, so instead of rashin
Kunyar sede na murguda Baki, bakin na murguda daidai shigowar Adda Salma, hannunta tasa ta gwabe
min bakina tace
"Zaki sani, sena fasa fitsararren bakin nan naki"



Adda Meeyna dake kwance tayi saurin cewa



"Ku kyaleta Dan Allah, kada taji Kamar an takura mata"



Dage kafada Adda Salma tayi ta kara Ficewa, wata Uwar harara nabi bayanta dashi, ribbon nasa na tufke
kan in a bun, inajin Adda Maryam na mitar gashina baida zuciya. Adda Sa'ada ta wanke min shi tas,
tayimin drying sannan tayi min kalba Manya, ta saka nayi wanka ai ji nayi kamar an sakeni, wata fresh air
tana shigata ta ko ina a Haka bacci ya daukeni.



Duk tunanina zancen zuwa Gwaram wasa Ummaah take, amma bayan sati uku lokacin Zaa shiga sabon
session Naga anata shiri, tunda naji Ni Zaa kai nake ta kuka, saboda har ga Allah bana son zuwa. Hatta
Abba dake bani goyon baya wannan Karon ban samu ba. The only person that stands for me was Yaya
Halifa, shima dalilinshi kada background dina ya lalace amma yadda Ummaah ta dage nasan babu me
juyata.



Da daddare naje dakin Abba na gaisheshi, Yana ta tsokanata yar boarding, kiran Inna Ade ya katse mana
hirar, katsewa yayi ya kira suka gaisa sannan yace mata gani a kusa. Da murnata na karba sannan na
mike na fito waje, cikeda murna na gaisheta, Tana tambayata yadda nake, nan kuma na Fara kuka ina
fada mata Ummaah bata sona, ta takura min tace Abba ya kaini Gwaram. Dariya Inna tayi tace kada na
damu karshen sati tana hanya.



Ranar asabar kuwa da sassafe se mukaji isowar ta, lokacin Inata bacci ban tashi ba, Maganar ta yasa na
fito, gaba daya ta hade gidan da sababi da kuma fada. Gashi Abba da Ummaah basa nan so babu Wanda
ya kulata a cikinsu. Tana zaune naje na zauna kusa da ita nace



"Inna kinzo? Sannu ya hanya?"



kaina ta shafa tace
"Lafiya kalau yar albarka"



Mikewa nayi na tafi kitchen na dakko abincin da aka riga aka hada mata na kawo mata, Tana ta saka min
albarka, jin dadin hakan yasa duk wannan laziness din nawa naje na bude dakinta na share har da
mopping lokacin ta gama cin Abinci, muka koma dakinta ina tayi mata complain akan zaman gidan. Nan
kuwa ta hau Tana ta masifa har su Abba suka dawo.



Can Ina kwance Tun kayan Dana tashi daga bacci shi ne a jikina, ko wanka banyi ba, ga zafi da ake a gari,
jikina Har stinky yake yana bashi amma ina kwance Kamar sarauniya, su kuma sisters dina suna can suna
aiki. Sallamar Inna naji hakan yasa na tashi na zauna ina Mata Murmushi Dan nasan zancen zuwa
Gwaram ya rushe. Gefena ta zauna tace



"Kawata, Ashe kazanta kikeyi? Nidai Allah Ya sani ban tashe ki da kazanta ba, Haka zalika bansan Saude
da kazanta ba. Dan Haka ni bana goyon bayan rashin gaskiya, Gwaram zakije ta kodan kiyi hankali"



Hannunta na kama ina fadin



"Inna Allah zan dinga yin tsafta, Dan Allah Kice Ummaah tayi hakuri"



Kanta ta girgiza, wannan shi ne karo na farko da Inna ta juyamin baya, shine sanadin tafiyata GGSS
Gwaram!



Ayshatuuu

[3/18, 5:03 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻



_FOUR_




✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_




💖Shatuuu095@ wattpad




*‫*بسم الله الرحمن الرحيم‬




*____________________________________*




*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*____________________________________*
Bayan sati biyu duk wani shiri ya kammalla, I was tired of crying Dan Haka na hakura na zubawa sarautar
Allah idanu, Ina ganin ta yadda zaa Fara. Saura kwana biyu na tafi, duk Yan gidanmu suka zo. Adda
(Babbar yayarmu) ita ta hada min kayana, kana kallon kayan zai Baka insight din daga gidan Dana fito.
Duk fadan da akai min akan tsafta ne, Adda tace min Ummaah tace indai ina tsafta to Zaa canza min
makaranta naje dreamy NTIC dina.



Ranar Monday very early, Adda Sa'ada da Yaya Halifa suka rakani, Garin Yayi min nisa sosae amma its all
sightseeing. Tunda muka shiga na Fara kuka, kuma na lura suma duk jikinsu Yayi sanyi. A office din
principal muka shiga, Dama ta rigada tasan da zuwanmu, ina shiga na gaisheta suma suka gaisheta, ta
zagayo inda nake ta tsaya tareda shafa kaina tace



"Asma'u how are you? "



"I'm fine" na bata amsa da dasashiyar murya, Dan Murmushi tayi ganin ina kuka, zama mukai bayan tayi
mana tayin seat, seda tayi cikecike sannan ta tura aka kira VP academic ta hada ni dashi. Nan sukai mata
godiya, Har naje kofa tace



"I wish you a nice stay kinji"



Kaina na gyada kawai, a raina Ina ayyana Wanne nice stay kuma a wannan uban dajin. A lokacin ji nake
gaba daya rayuwata an gama tarwatsa min ita. Office din VP academic mukaje ya buden student file
sannan ya tura SS3 aka kira masa head Girl, Nidai ina zaune babu uhm babu uhmm uhmm, Haka Tazo ta
gaisheshi sannan ta gaida su Yaya Halifa fuskarta a sake.



"Ga Sister na baki, Dan Allah ki kula da ita"



Kai ta gyada tareda nufo inda nake tsaye ta riken hannuna, daga nan mukai sallama bayan su Yaya Halifa
Sunyi mata alkhairi sannan aka bata amanata. Tunda naga fitar motarsu nake kuka, tana ta rarrashina ji
nayi kamar nayi tsuntsunwa na koma Kano amma babu halin hakan. Haka na bita ta kaini class, gashi
makarantar unity school ce, so you got to see different people from different places having different
religion, what makes us united is that we're Nigerians. Kamar munafuka haka na shiga ajin na zauna, se
surutu ake, amma wannan head girl din na shigowa sukai Shiru. Seda nayi settling sannan ta koma nata
class din. Tunda na zauna ban tashi ba haka kuma bance uffan ba Har aka fita break, kuma Kamar sun
hada Baki babu Wanda ya kulani, ina nan zaune duk suka fice se baifi kadan suka rage ba. Durkusar da
kaina nayi nayi ta kuka Kamar raina zai fita, na jima a Haka sannan wata Tazo ta kirani Inji Anty Rashida,
ni bansan Wacece Anty Rashida ba but I guess wannan head girl dince. Binta nayi muka tafi, fuskata tayi
jawur saboda yadda nayi kuka, ina wucewa anata nuna ni Wai new comer ce.



Ana tashi a class muka tafi zuwa hostel nabi ayari, Dutse hostel aka kaini kwanar Anty Rashida, ruwan
wanka tasa aka kaimin nayi, ta gyaran kayana, nayi sallah sannan na bita dining, ana Fara zubawa aka
zubamin wata taliya, masifar yunwar da nake ji tasa na daure naci, daga nan se prep na yamma, wannan
slow slow din da nake har seda aka tareni ban samu sallar ishai ba, aka zanemu kuwa. Har na kwanta
ranar kuka nake.



A hankali kuma na Fara warewa, sede kafin na ware a kalla nafi sati biyu a Haka, amma daga baya se na
Fara yiwa mutane magana Kamar yadda Nima naga suna shiga harkata, ko ina na wuce se Anyi maganata
saboda kwatakwata I don't match with that environment. Zancen tsafta kuwa, ba koda yaushe muke
samun ruwa ba, ni a Haka ma Inada Uwar kwana amma dukda haka se nayi kwana uku banda alwala
babu ruwan dake zuba a jikina, tunda ba wani amfani take min ba, se nice ma take amfaniwa dani. ga
Rana ga wuya da dealing a makarantar da kuma azabar aike. Kafin wata daya farar fatar da duk gidanmu
mu biyu muke da ita ta Fara dafewa, na rame Kamar marar lafiya. Lokuta da dama idan naje class banida
aiki idan ba kuka ba, na kasa sabawa da rayuwar. Ga duk yammaci da safe se nayi zazzabi to banida
Wanda xan fadawa Dan Haka ni daya nake abuna, idanba wata Rumasa'u ba, to Anty Rashida kawai
Wayo takeyi min.



Ana haka ranar visiting tazo, ana gobe visiting Anty Rashida ta tsefen Kaina ta wankemin tayi min Sabin
kitso, Washegari tasa nayi wanka Wanda duk nasan na ganin ido ne. Ta dakko min sababbin check
Wanda ban taba sawa ba, na saka take kuma se nayi kyau, idanun nan nawa Kamar na mujiya, Dama
girma ne dasu to gashi na rame, hancina ya Kara tsawo, idan aka kalleni abinda ake gani kenan.



Muna zaune nida Rumasa'u, class dinmu daya haka dakinmu, so ita ina sakin jiki sosae da ita mun kuma
saba.



"Asma'u ban taba ganin dariyarki ba irin ta yau, kodan visiting day ne"



Dariya nayi Ina rufe fuskata data dashe, kamar banida jini, Haka tafukan Hannayena suma duk Sunyi
fayau dasu.
"Bazaki gane irin farin cikin da nake ciki ba Rumasa'u"



Kanta ta gyada tace



"Ai naga alama kam, amma..... "



Bata karasa Maganar tata ba, wata yar SS1 Tazo ta kirani Inji Anty Rashida, babu yadda banyi ba akan
Rumasa'u Tazo muje amma taki, haka na hakura na tafi abuna. Tundaga Nesa na hango Ikhram yarinyar
Adda, da wani irin gudu na kwasa, su basu ganni ba Dan Haka babu sanarwa na fada jikin Adda Meeyna,
gaba daya suka jiyo suna fadin



"Yar boarding, Iyeee! "



Zama nayi gefen Adda Inata Murmushi amma na kasa magana. Duk se naga yanayinsu ya canja gaba
daya se bina da kallo suke Kamar irin it's the first time of them seeing me.



"Ummaaah bata zo ba? "



Kafin a bani amsa Sega motar su tayi parking, Yaya Halifa, Ummaah, Abba. Muna hada ido kawai na rufe
fuskata Inata kuka, from nowhere naji wata irin karaya ta saukar min. Dukkansu sukai Shiru har nayi me
isata na gama, sannann naja Adda Maryam muka Kira Anty Rashida. Ina dawoa na sauka Kan Abinci, duk
yadda nake dauki amma haka na kasa cin abincin, su dai basu ce komai ba amma yanayinsu kadai ya
nuna min they're not happy da yadda suka Tarar Dani.



Har akai Sallar laasar sannan suka Fara shirin tafiya, Inata daurewa saboda kada nayi breaking, amma
seda nayi kuka. Lokacin Abba ya dawo daga office din principal, kallona Yayi yace



"Akwai abinda kike bukata a hostel zaki dakko? "
Cikin rashin fahimta nace



"Abba? "



Kallon Yaya Halifa yayi yace



"Gobe kaje ka samo mata wani admission din, Bazan iya barinta a Haka ba"



Maimakon naji farin cikin da nake tuanin ji, se naji zanyu missing makarantar, gaba daya kayana na
tattara na bawa Rumasa'u. Muka tafi gida, shima asibiti muka fara tsayawa Naga Likita sannan muka
dawo gida. Ina shiga dakinmu toilet na wuce na dinga wanka Kamar zan cire fatar jikina, na fito na
kwanta se bacci peacefully and calm.




Ayshatuuu

[3/20, 5:50 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻



_FIVE_




✍🏻 *SHATUUU❤*

_Jakadiyar kainuwa_




💖Shatuuu095@ wattpad
*‫*بسم الله الرحمن الرحيم‬




*____________________________________*




*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*____________________________________*




Washegari ana Fara kiran Sallar farko na tashi, na jima a zaune ina karewa dakin kallo ina kuma godewa
Allah, da tuni ina can daji ga sanyin asuba Kamar zai kwashe ka. Kaina na girgiza tareda sakin murmushi
na sakko daga gadon na nufi toilet. Nayi alwala sannan na dawo Ina karewa dakin kallo, yadda Adda
Salma da Adda Maryam ke baccinsu hankali kwance, a raina na ayyana basu san irin abinda na gani ba,
basu san yadda boarding take ba saboda ni daya tal nayi boarding a gidanmu. So I gat the best and weird
experience.



Seda aka Fara iqamah sannan nasa hannuna na tashi Adda Maryam, ni kuma na tada sallah abuna. Kowa
a gidanmu yasan ni da kaunar baccin bayan asuba amma tunda aka kaini Gwaram bana tunanin nayi
baccin bayan Sallar asuba sau uku, so har na rigada na saba da hakan. Suna idarwa ko magana bamui
dasu ba, suka wuce gado suka sake kudunduna, Nikam Shiru nayi a raina Ina jin tamkar an canja ni, I'm
not that lazy Asma'u again, I'm a new person.



Kafin bakwai na safe nayi wanka na saka kaya sannan na fito parlor, babu kowa, gidan Shiru kowa
baccinsa yake. Se can cleaners dinmu suka zo, kowa ya ganni se Yayi mamakin ganina a gida, sannan
Tashin da nayi da wurwuri. Kitchen na tafi dan taya Baba Zulai me yi mana girki aiki. Ina shiga ta juyo da
mamaki tace



"Asma'u yaushe kika dawo? "



Dan Murmushi nayi nace



"Jiya, aiki zan tayaki"



Seda ta kalleni for some seconds kafin ta amsa min da to, haka Inata tayata tana koya min abubuwa, Dan
babu abinda na iya, idan kaganni a kitchen to aiko ni akayi. Wajen Tara naji mutanen gidan sun Fara
fitowa, ban leko ba, ina juya Irish din dake cikin mai. Muryar Ummaah naji tana fadin to ina Asma'u
zataje da sassafen nan? Kun duba ko ina kuwa? Dan dariya nayi sannan na saki leak spoon din nace da
Baba Zulai, bari naje gurin Ummaah, Dan da alamun ita bataji abinda naji ba.



Ina lekowa naga Sunyi cirkocirko harda Abba, karasa fitowa nayi Ina gaishesu, kowanne mamaki ne a
fuskarshi, Abba yace
"Asma'u me kikeyi a kitchen? Kin tsoarata mu, yan uwanki basu ganki ba"



Dan Murmushi nayi nace



"Abba ina taya Baba aiki ne, bansan zaa nemeni ba"



Kanshi Ya gyada yace



"If that's the case, naji dadi "



Daga Haka ya juya zuwa dakinshi, hannuna Ummaah ta kama tace



"Ya kika tashi da wurwuri? Keda bakida lafiya "



"Ummaaah ai na samu sauki, kuma a school Baa komawa bacci, so na rigada na saba"



"At least, yarinya ta gyaru ko Ba komi"



Adda Sa'ada ta fada, kafin muka zazzauna ana ta hira, yawanci su suke abinsu dan ni kawai jinsu nake.
Da yammacin ranar Sega Inna tazo, Ashe Abba ne ya kirata, Tana ganina tace Bazan koma ba, Ummaah
tace Dama wata makarantar Zaa canja min. Kwananta biyu ta koma Kwalam.



Satina biyu na warware gaba daya, babu wani abinda yake min ciwo, da Adda zata tafi tace zata tafi Dani
Ummaah ta hana, a cewarta nema min admission ake. Wannan zaman da nayi kowa seda ya lura da
transformation din da aka samu a tattare dani. Dukda ko aikin nake amma bana sauri, zan jima ban gama
ba amma zanyi, Haka halitta take banida sauri.
New horizon college dake Minna nan aka samo min admission, wannan karan babu Wanda Yayi
protesting haka aka kaini, nida cousin dita Rayhana amma ita tun Farkon term din aka kaita, so se nayi
joining dinta.



Naji dadin zaman makarantar, Dan aljanna ce compared to inda na baro, ga Karatu both western and
Islamic, saboda dama Islamic union suka kafata.



Hutuna na farko Daddyn Rayhana ne yazo, munata murna zamu tafi gida,

2 / 23