Author : SHATUUU Category : African Stories & Novels
dayazo Ya dauketa ita kadai
yace Abbana zai zo ya daukeni, tafiyarsu kuwa ba dadewa Abba da Ummaah sukazo tare, Ashe basa
Kano, an tura Abba Delta state wani official assignment na wata daya, shi ne ya taho da Ummaah.
Dukkansu sunji dadin ganina da kuma result dina, Haka muka dauki hanya wadda banda bacci babu
abinda nakeyi, saboda Daren jiya bamuyi bacci ba, munata hada kayanmu da murnar zuwa gida.
A Mobile Base accommodation din yake, flat gida ne da two bedrooms se parlor, toilet da kuma kitchen.
Ni na dauki daya su kuma suna daya. Idan ya tafi aiki se nida Ummaah mu danyi hira, muyi aiki Haka
muke zama abinmu.
Satina daya amma zan iya irga sau nawa na leka kofar gida, ranar Ummaah Kamar an saukar mata da
bacci, se bacci take, ni kuma na gaji da zama, kallon ya isheni kawai se na fito na zauna kofar gida, time
to time Ina ganin wucewar mutane mazauna Base din. Na jima a zaune naji an kwado min ball a Kaina,
da sauri na mike ina sosa gurin saboda ta shigeni bugun. Bakina na turo Ina jujjuyawa dan naga wanene.
Wasu maza su biyu suka karaso se haki suke dukkansu sanye da jersey, Babban baifi saan Adda Habiba
ba se karamin da baifi saan Adda Maryam ba. Suna zuwa karamin yace
" Ina ball din? "
Ya tambaya yana waigawa alamun nemanta yake, harara na wurga mishi tareda dauke ball din na nufi
kofa zan shige gida, saboda rainin Wayo ne, by mere looking sunsan sun buga min tunda gashi ina sosa
Kaina amma su ta ball din suke.
"Ina zaki Kai mana ball dinne? Bakyaji ne? "
Babban ya fada yana Hararata, wani haushi naji na dauki ball din na wulla mishi, take kuwa ta sauka a
kirjinshi nace
"Feel the pain! "
Daga Haka na wuce gida na buga kofar tareda jingina a jiki ina maida numfashi, did I seriously hit him?
Na tambayi Kaina, kafadata na girgiza na wuce zuwa kitchen na dakko ruwa nasha sannan na zauna ina
maida numfashi. Ban kara fita ba Tundaga ranar saboda Ina ganin Kamar idan na fita to zamu hadu dasu.
"Ummaah Wai Haka zamuyi ta zama, ba zamu fita ba?"
Aje kayan hannunta tayi tace
"kin gaji da zama ne?"
Kaina na gyada nace
"Muje ko cikin gari ne mana"
Kanta ta gyada, daga nan ban kara cewa komai ba na maida hankalina kan kallon da nake, da daddare
Abba ya dawo yace zamuje gidan abokinshi a cikin Base din, nafi kowa murna, Dan ni na Fara shiryawa
na zauna jiransu, a Mota mukaje, gidan sak irin namu. Tun a kofa nake jin muryar maza sunata hayaniya,
hannun Ummaah na rike Har muka shiga ciki, Maza ne guda uku suna game ta Chisel, ga board din a
gabansu, saboda ihunsu ko sallamar da mukai I'm not sure idan sunji, wata mata wadda bata Kai Saar
Ummaah ba, Ta fito daga dayan bedroom din tana fadin
"Wai Meye Haka duk kun cika gida da ihu, Iyeee! "
Take duka suka shiga taitayinsu, Se lokacin ta hango mu nida Ummaah a tsaye, yadda ta karbe mu
fuskarta a sake ta karaso tana fadin
"Ihunsu bai barni naji sallamar ku ba, Dan Allah ku shigo"
A take naji ta birgeni, saboda na yadda da bahaushe da yace shimfudar fuska tafi ta tabarma. Bayanta
muka bi, Ummaah ta zauna saman cushion ni kuma na zauna Kan carpet nace
"Anty Ina yini? "
Kanta ta girgiza tace
"Call me Ummiey, ya sunanki? "
"Asma'u" na bata amsa Ina Dan Murmushi, lokacin ne na fuskanci su waye 'ya'yanta, sune Wanda na
bugawa ball last week, bata rai nayi Inaji suna gaida Ummaah, Babansu ya fita ya shigo da Abba, nan aka
kafa hira Se ni daya a gefe, su kuwa sun cigaba da game dinsu. Abbansu yace su matsa min nayi nima. A
dadare na zauna gefen Babban, na tsakiyan shi ne Wanda ban gani ba ranar, Yana gwada min yadda ake
chisel, dashi muka buga Ya cinye ni, aka kara yi yayi winning. Aje king din nayi kan board din nace
"Wayo kake min ko? "
Dariya yayi, Juyawa nayi na Kalli Babban yayansu, ya matsa gefe amma idonshi a Kaina. I can say ban
taba saurin Sabo da mutane ba irin yadda nayi dasu ba. Matsowa yayi ya dauki king din yasa min a
hannuna, dagowa nayi na kalleshi cikin ido shima kallona yake cikin ido and I can swear time stuck,
saurin kasa nayi da idona inajin wani discomfort a tare dani, a hankali cikin nutsuwa ya gwada min and
take na fahimta, dashi mukayi na cinye dukda nasan he gave me that chance. Kafin lokacin tafiyarmu
yayi na ware Duka na saba dasu amma Abu daya na manta shi ne sunayansu, the only name that ring in
my head sunan Mamansu UMMIEY!
Ayshatuuu
[3/21, 4:54 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_SIX_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Bamu Kara komawa wannan gidan ba, kamar Hadin baki suma basu zo gidanmu ba, sede naji Abba yace
da Ummaah, Ummiey na gaisheta, su Assignment dinsu ya kare sun tafi, duk se naji babu dadi cikin
zuciyata, the least thing I should do is to know their names, amma ta Yaya? Babu wata hanya, dan koda
mukaje gidan Banji an ambaci sunan kowa ba a cikknsu.
Muma a Haka hutuna ya kare aka maida ni Minna, nan muka cigaba da Karatu. Duk Hutu xaazo a dauke
mu, sannan visiting sau daya ake zuwa mana a term, so har mun rigada mun saba hakan. A Haka naje
SS1, Adda Habiba, Adda Meeyna Da Adda Ummiey Sunyi aure, Adda Salma ma tayi aure dukda bata
gama university ba amma Ance ta karasa a gidanta.
Gidan Ya rage daga ni se Adda Maryam da Yaya Halifa, Adda Maryam tana Kuwait Tana Karatu, so ko
Nazo Hutu sede mu, zauna da Yaya Halifa, muyi Karatu Wanda a gurinshi baya karewa, Har ya samin
mugun son karatun, na rigada na saba, hobby dina Karatu ne.
"Rayhana Kinsan na kasa karasa Haddar last page din suratul Nisa'i"
Na fadawa Rayhana, ina rikeda qurani ita kuma tana zura uniform zamu tafi Quran class dinmu.
"Bansan me yasa take baki wahala ba, ki Kara maimaitawa kafin time ya cika"
Idanuna na runtse sannan na bude, na tattara dukkan hankalina akan karatun, seda time Yayi ta gama
shiryawa sannan muka tafi, gabana se faduwa yake, dan na tsana embarrassment, Allah Ya taimaka ina
shiga akace Anyi mishi rasuwa he can't make it, naji dadi hakan na wuce can extreme din class din nayi
ta bita Har ta zauna sannan na dawo gefen Rayhana.
Lokacinda muka shiga final year, ni nayi applying medicine and surgery, ita kuma Rayhana tayi applying
Biochemistry, Kaf class dinmu Rayhana batada na biyu a chemistry, ita ce overall best chemistry student
a duka set dinmu, bana jin ba zata iya ba.
Munyi graduation gaba daya daga secondary, Yaya Halifa ne yazo ya daukemu daga Minna, Kamar zanyi
flying Haka nake ji, ko babu komai nasan at least na taka wani mataki a rayuwata.
Straight daga Minna Kwalam muka wuce saboda akwai bikin cousin dinmu da akeyi kuma Duka family
dinmu sun hadu. A cikin gida muka sauka, ko Rayhana ban jira ba nayi ciki abuna, da Adda Meeyna na
Fara haduwa hannunta dauke da Aarif, rungumeta nayi itama cikeda murna ta rungumeni sannan na
karba Aarif nayi ciki. A dakin Inna na tarar dasu Ummaah, kowa yana tayi mana murna, muka gaisa
sannan na shige cikin uwardakin Inna, bata cikin dakin hakan yasa na fada gadon Ina Murmushi tuna
yarinta da yadda na rayu a dakin, irin bacin da nayi. Ina kwance idanuna a lumshe naji shigowar ta tana
fadin
"Kawata, kina ina? "
Dagowa nayi tareda riko hannunta nace
"Ganinan Kawata, na sameku lafiya? "
"Lafiya lau, ya hanya? "
Fuskata na shafa Dan tun eight muka dakko hanya amma Se Yanzun laasar muka karaso, na gaji sosae.
"A gajiye nake Inna"
Hannuna dake cikin nata ta saki, tace
"Maza sakko kije kiyi wanka, kizo kici abinci. Se Ki huta"
"Fauziyya! Fauziyya!! Fauziyya!!! "
Inna ta kwalla mata kira, Se gata ta shigo da ciki a gaba, cousin dinmu ce sannan yayar Rayhana ce tare
akai aurensu da Adda Salma, kuma kusan sa'anni ne Dan dai Adda Fauziyya ta bata watanni biyu.
"Maza jeki Ki hadawa Fara 'yar shehu ruwan wanka"
Nasan halin Inna Ade, so banyi mamaki ba amma Adda Fauziyya da mamaki tace
"Haba Inna Ade, Wanne irin ruwan wanka kuma? "
Kugu Inna Ade ta kama kamar me shirin fada tace
"Ruwan wanka nawa ne? Ki wuce kije kiyi abinda na saki, yarinya ta dawo daga makaranta ko tausayinta
bakwaji"
"Inna wallahi ina fama da kaina Bazan hadawa Asma'u ruwa ba, sede kada tayi wankan. Muma ai 'ya'ya
ne kuma jikoki, amma sede ki ware bi..... "
Bakinta Inna ta buge tana huci tareda fadin
"Eh lallai, ni Fauziyya ke yadawa magana, to idan bazaki hada ruwan ba, Uwarki ta hada"
Jin hakan yasa nayi saurin cewa
"Inna, ni bana jin wanka Yanzun, bani Abinci naci tukunna"
Allah Ya taimaka se ta fita kawo min Abinci, Itakuma Adda Fauziyya tasa hannunta ta dada min duka a
cinya Sannnan ta fice, bakina na turo Ina sosa gurin, se kuma nayi dariya. Inna Ade Tashin hankali, Yanzu
fa tsaf zata iya kiran Anty Hauwa ta hada ruwan, Aikuwa da na fadawa aya zakinta.
Ina nan kwance Sega Nu'aimah ta shigo da kwanukan Abinci, a gabana ta aje ta gaida ni sannan tace
"Adda Asma'u, Inna tace Wai ki fada idan kina son wani abu"
Kaina na girgiza nace
"I'm ok da hakan, kirawo min Rayhana muci"
Kanta ta gyada ta fita, kwanukan na bude Abinci Kala uku, kwadon rama da first, ga sachet water me
sanyi da Fanta. Rayhana Tazo muka fara ci naji isowar mutanen Adamawa, Umma Falmata da tawagar
ta. Babu Wanda ya tashi cikinmu seda muka gama sannan muka je muka gaida ta. Wajen shida muka
shirya mukaje gurin kamu.
"A Ina zaki kwana? "
Ummaah ta tambayeni bayan an gama kamun, Adda Sa'ada tace
"Kiji Ummaah da bata Baki Kema kin sani ai"
Dariya nayi nace
"Allah Ya bamu alkhairi "
Daga Haka na koma gidan Inna Ade, parlonta duk Anyi shimfida, da yawa mutane sun Fara kwanciya,
tsatsallake su nayi cikin dakin, ina zuwa na tarar Inna na sallah babu kowa kan gadonta, kwabe kayana
nayi na canja sannan na kwanta akan gadon, ni nasan ba bacci nakeji ba kawai dai hutawa nake sonyi ga
Inna idan ta Fara sallah har Se mutum ya gaji da jiranta. A hankali bacci ya Fara cin karfin idona, ban jima
da baccin ba naji muryar Adda Fauziyya tana tashina, tashi nayi na zauna raina ya baci nace
"Adda na Fara bacci fa"
Harara ta tayi tace
"Na sani ai, sakkowa zakiyi ki wuce ki samu wani gurin ki kwanta"
"Saboda?"
Inna ta fada, Ashe ta idar da sallah, Juyawa Adda Fauziyya tayi tace
"Inna wallahi bana iya kwana a kasa dole se a gado, idan ba Haka ba da kyar nake tashi"
Tsaki Inna tayi tace
"Shashanci kenan, ke Kawata koma Ki kwanta, ke kuma Fauziyya kiyi ta tsayuwa amma gadonnan bazaki
haushi ba"
Kawai se ta Fara kuka Wai Inna bata sonsu, ni take so to itama jika ce, Kaina na girgiza Dan halayen Adda
Fauziyya basida kyau. Komawa nayi na kwanta, zuciyata babu dadin abinda ya faru.
Washegari aka daura aure, wajen laasar na shigo dakin Inata mika saboda gajiya, wata Hamma na buga
daidai shigata dakin Inna, cak hammar ta tsaya saboda abinda na gani a gabana, Yaya Mukhtar yana
zaune ya baje yana cin Abinci. Dagowa yayi ya kalleni sannan ya saki Murmushi tareda kallon Inna yace
"Inna Fara yar shehu ce haka, Aah yarinya ta girma"
Bata rai nayi na karasa shigowa ciki na zauna saman gado nace
"Kaima ai ka girma"
Dariya yayi yace
"Still with the futsara, Ashe baki canja Hali ba"
Se kuma nayi dariya na gaisheshi, ya tambayeni Ya makaranta, Inata jin dadi nace na gama secondary
dina. Se kuma mukai Shiru, na kwanta inajin yana ta cewa Inna yadda na girma, na zama Yan mata.
"Ko dai kana ciki ne Mukhtar? "
Dariya yayi ya mike yana fadin
"Inna kenan! "
Ko kwakkwaran motsi kasa yi nayi, zuciyata ta Fara ayyana Ko dai Yana sona da gaske ne? Se nayi
Murmushi saboda wani excitement da naji Ya lullube ni lokaci daya. Yaya Mukhtar sa'an Yaya Halifa ne,
shi ne Babban yaron Umma Falmata, so a Adamawa suke shiyasa Haduwa dasu ba sosae ba, musamman
shi da bai dade da dawowa daga Estonia ba. Mikewa nayi na zauna dan naji fitar Inna, kallon gurin da ya
zauna nayi sannan na sake wani murmushin na canja kaya na Kara fita.
Ayshatuuu
[3/22, 10:34 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_SEVEN_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Ana gama biki muka koma Kano, Abba yasa Yaya Halifa yayi min registration a gateway computers inda
zanyi certificate, saboda kada na zauna bana komai. Babu laifi naji dadin wannan shawarar. Ya zamana
morning classes ne, 9am to 12noon, da yamma kuma naje islamiyya, so I'm always kind of busy hakanan.
Ranar jumaa ina ciwon ciki ko makaranta banje ba, Ummaah ta shigo ta kawo min magani da ruwa
nasha, ban wani jima ba bacci yayi gaba dani bani na farka ba se bayan Sallar laasar. Ina tashi nayi wanka
na canja kaya sannan na fito parlor. Da mamaki a fuskata ganin Yaya Mukhtar a zaune shi da Yaya Halifa
suna hira.
Basu lura dani ba seda na zauna Kan cushion din dake gefen Yaya Halifa sannan yace
"Asma'u rikici"
Dan Murmushi nayi nace
"Yaya Ina wuni? Yaushe kazo? "
Kanshi Ya Dan shafa se Murmushi yake yace
"Lafiya lau, dazun nan"
Kaina na gyada tareda tambayarshi su umma Falmata, sannan Yaya Halifa ya tambayeni saukin jiki.
Da daddare Ummaah tana parlon Abba, Se ni daya a parlor, na kudundune kafafuna, dukkan hankalina
yana kan kallon da nake, naji sallamar Yaya Mukhtar, dagowa nayi na kalleshi, murmushin nan nashi Yayi
min, nima na mayar mishi inajin yadda Wasu knot ke kulluwa cikin cikina, kasa nayi da kaina har ya
zauna gefen kujerar da nake, ya aje mug din hannunshi akan center table din yace
"Me kika kalla haka?"
Kallon allon TV din nayi, Kamar ban San me nake kalla ba nace
"Uhmmmm! Korean drama ne "
Kanshi Ya gyada yace
"I see, amma how do you differentiate between cast din?"
"It's simple " na fada Ina gyara zamana nace " Basu kama fa as long as you continue to watch film dinsu
zaka gane each of them"
Kanshi Ya girgiza yace
"I doubt much, saboda komai nasu iri daya ne fa"
Murmushi nayi bance komai ba, saboda idan na biye shi I'll miss some important scenarios. Shima kamar
yasan thought din dake running cikin raina bai sake magana ba, Se maida hankalinshi da yayi akan
kurbar only God knows what dake cikin mug din. Nima duk se hankalina ya rabu biyu, rabi yana ayyana
abinda yazo yi gidanmu, Dan dazun naji Ummaah tana fadawa Baba Zulai zancen zuwanshi, akan a Kara
Abinci dashi. Rabin hankalina yana kan kallon da nake.
So ba komai na fahimta ba, har episode din ya kare, Se kawai na mayar Aljazira Dan na Kalli news,
wannan yana daya daga cikin horon Yaya Halifa a Kaina. Shirun da mukai se yasa atmosphere din ta
zama so dull and tense, gashi ina jin idanunshi a Kaina so se na Fara wasa da fingers dina, at least I want
to break the silence. But how? Na tambayi Kaina,
"Ehn... Yaya Mukhtar so Hutu kazo yi kenan?"
Kanshi Ya girgiza yace
"I've been employed ne"
Take faraa ta, ta karu nace
"Oh! Congratulations, amma nayi maka murna "
Wink yayimin, Idan da yasan yadda wink dinnan ya taba ni, bana tunanin zai Kara min, ji nayi kamar
zanyi melting cikin kujerar, na fada muku how Charming Yaya Mukhtar yake? Kyanshi kadai will make
someone fall for him over and over again. Jinin Fulani Dan Mahaifinshi asalin 0 Adamawa ne, so kana
kallonshi kaga hakan.
"So ya makarantar, medicine dinne? "
Kaina na gyada nace
"Shi ne, nayi passing Post UTME kuma score din yayi tallying "
"Mashaaa Allah what a great news, so mun kusa samun Doctor in the family kenan? "
Dan blushing nayi sannan na kalla agogon dake kafe a parlor, idanuna na dan zaro nace
"Bari naje na kwanta, its late"
Hannunshi ya watsar cikin iska yace,
"Oh nima bari naje na kwanta"
Daga Haka na juya zuwa daki amma ban kai ga shiga ba naji yace
"Asma'u! "
Juyawa nayi na kalleshi, Murmushi yayi min sannan Yayi min waving yace
"Sweetest of dreams"
Take naji wani blood rush gaba daya jikina, hannuna nasa na dafe cheeks dina saboda wani Hot da naji
Sunyi, ban bashi amsa ba na shige ciki, kofar na mayar na rufe sannan na jingina da ita, ji nake kamar
faduwa zanyi, tamkar kafafuna bazasu dauki jikina ba, na jima a tsaye a gurin Inata Murmushi sannan na
janye jikina Na fada gado, ranar tsabar farin ciki da annashuwa ko addua banyi ba nayi bacci balle canja
kaya. Se wajen past two na farka a gigice, seda nayi yadda na saba sannan bacci ya daukeni.
Washegari kamar yadda na saba, bayan nayi sallah, wanka nayi na Nemo kaya Marasa nauyi saboda
yanayin zafi Ya Fara shigowa. Kitchen na wuce na kwaba batter Banana pancake na Yaya Halifa, baifi 4
pieces nayi ba se abincin su Abba da Ummaah, babu wani Yawa abincin amma har Yaya Halifa yazo cin
nashi ban gama ba.
"I wonder how you will become a doctor, Dan nasan watarana tabbas kafin Ki yunkura patient zai mutu"
Tura bakina nayi Dan wannan furucin kullum se najishi, sede idan banyi wani abu slow ba. Zama yayi ya
ci sannan Yayi min sallama Ya tafi office. Ina kammalla breakfast dinsu Abba nayi parlonshi dashi,
fitowarsu kenan, na gaishesu sannan na aje komai na koma kitchen Dan dafa noodles, Ina cikin duba
wayata naji kamshin Elope, Wanda nasan mammallakin kamshin nan Yaya Mukhtar ne, se na samu Kaina
da kasa Juyawa balle mu hada ido. Kaina na gefe nace
"Yaya Mukhtar an tashi lafiya? "
"Lafiya lau Princess"
Da sauri na kalleshi sede to my utmost amazement Bama kallona yake ba, hankalinshi yana Kan lemun
daya shigo dashi, I was kind of disappointed. Amma Se nake ganin Anya ban zake ba, anya am I on the
actual and right path? Allah kadai ya sani amma nasan one thing, akwai wani abu da nakeji a gameda
Yaya Mukhtar, Wanda a hankali ya Fara gina kanshi cikin zuciyata. Ban taba tunanin ni sokuwa bace Ko
kuma nace wawiya Se akan Yaya Mukhtar. Shidai bai taba cewa yana sona ba, sede yadda yake shiga
al'amurana is different than any other.
Daga ranar tare muke fita, office dinshi a cikin Depot yake amma Se ya kaini