Author : SHATUUU Category : African Stories & Novels
har school sannan ya wuce
abinshi. Wannan yasa muka saba sosae dashi, indai muna tare kuma mutane suna tare damu to tabbas
se Kasan Inada wani special feelings akanshi.
Ranar da admission list Ya fito, nayi murna Kamar zan zauce,duk wani me sona seda ya tayani murna na
samu Medicine , Rayhana ta samo biochemistry dukka a Bayero. A ranar ina kwance a dakina, nida Adda
Meeyna Tazo, Sega Luba me mana Shara Tazo tace Nazo Inji Yaya Mukhtar, ko amsata banyi ba na mike
zan tafi, wani fizgowa Adda Meeyna tayimin tace
"ke dallah zo, daga ya kiraki ke kuma busy body kin wani tashi, at least take your time mana, kija class
dinki. "
Dariya nayi nace
"Kaji Adda Meeyna, is not as if saurayina ne fa"
Dariya itama tayi sosae tace
"Lallai yarinyar nan, wa zaku mayar Yara daga ke har Yaya Mukhtar din, ko makaho ya shafa yasan akwai
magana "
Zamana na gyara nace
"Dan Allah sona yake? "
Se tayi sakale tana kallona, sannan tace
"To Dama baiyi proposing ba amma har kike wannan zakewar. Lallai Asma'u, ki maida hankalinki fa. Ba
ayiwa maza haka"
Tabe Baki nayi jikina Yayi sanyi, nace
"Nifa kawai mutunci muke dashi babu wani abu"
"Mutunci ba, ni ban taba ganinki kin saki jiki da mutane kamarshi ba, to ki saurareni Dan abinda jikinki da
idanunki ke fada you're deeply in love with him, ki zauna kiyi sorting out kafin dare yayi miki. "
Bance komai ba na fita kiran amma Kamar an zare min laka haka naji, duk yadda nake daukin abin se naji
Ya fita akaina and I found myself questioning myself me nakeyi? Da gaske sonshi nake? Bansani ba tunda
gaba daya na shiga rudani.
Ayshatuuu
[3/27, 9:24 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_NINE_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*Assalamu alaikum! Hi pipu. I was in a scenario today, I wanted to leave Kano to Jigawa because of the
sudden boarder shut by the states. When I went to park, I spent more than two hours no vehicle, when
it came you have to pay one thosand and above, what I noticed is that, people are just waiting for an
opportunity su uzzurawa mutane, believe me wallahi in this plaque and Pandemic era, idan baka
tausayawa talaka ba, ba zaka takura masa ba. I'm calling all of you, da suke Sana'a and stuffs suna
fakewa da wannan anmobar, fear Allah, wallahi this will not make you rich, it will destroy all your earns,
bazaka zama Dangote ba. I pray Allah SWT see us through, may he curb this illness. Thank you!*
🎶....So let me be the one and only, can I be your friend and honey, I'll be your better man.........If you're
my girl I'll take you round the world, I'll take you places where you've never ever been before, so give
me your...... 🎶
Wakar da kullum Lubna se ta jita a dakinmu, amma da yake I'm not a fan of Nigerian music, ban taba
fuskantar abinda Psquare ke fada ba se yau, may be hakan yana da nasaba da zafin da zuciyata keyi min,
amma jin wakar se naji wani bakon yanayi yana mamaye min jikina, tamkar ana fizgata Ina jin wani
tsumammen abu ya karade dukkan zuciyata. That's Love, a hankali na karasa gadona na kwanta Ina kara
nutsuwa da bude kunnuwana inajin wakar, har ta kare. Ta kara maida ita, tanayi tana miming dinta
cikeda nishadi.
Anty Zubaida itama roommate muke, tana zaune gefen gado tacr
"Nikam Lubna shi wannan Hayaty yaushe zai tura ne? Wannan ban taba ganin irin soyayyar ku ba"
Idanuna na mayar kan Lubna da ke ta Murmushi amma ta kasa magana, I'm sure tuna shi take. Se naji
Kamar nayi kuka, ko se yaushe zanji abinda ake ji? Ko se yaushe zaa furta min, a so ni kamar yadda nake
so? It might never happen Kila?
Shigowar Rayhana a hargitse yasa na dago ina kallonta, zama tayi gefena tace
"Zo ki rakani"
Mikewa nayi na dauki hijab din dana aje muka fita bayan nayiwa su Anty Zubaida sallama, a kofar hostel
muka tsaya, hannunta cikin nawa amma jikinta rawa yake, hakan yasa na dubeta nace
"Me yake damunki, jikinki rawa yake fa? "
Kanta ta girgiza ba tareda ta furta komai ba, amma har lokacin jikinta bai daina rawa ba, gaba daya se
naji jikina Yayi sanyi, tunda baifi two hours muka rabu ba, amma bansan me ya kada ta haka ba, it's
unlike her saboda ita mutum ce me taurin zuciya, kafin kaga abu ya saka ta cikin Haka zaka dade. Na
bude baki da niyyar kara tambayarta se naga motar Abdul saurayinta Yayi parking a gidanmu, hannunta
na saki daidai fitowarshi, Ko tsokanar da ya saba min baiyi min ba Illa, bude mata front seat da yayi ta
shiga sannan ya bude min yace
"Bismillah"
Kallonshi nayi Amma Se yayi saurin zagayawa Ya koma seat dinshi, baki daya Kaina ya kulle na kasa
tunanin abinda yake faruwa. Shiga nayi na zauna, ina jinshi suna magana kasakasa shida Rayhana, bana
jin su hakan yasa na rike wayata gyam a hannuna, and na rigada nayi concluding cewar nothing is right,
nothing is in place, dole akwai abinda ke faruwa. Jin anyi parking yasa na dago, se ganinmu nayi a kofar
gidan mu, cikin sauri na bude kofar saboda yadda naji wani mugun Tsoro ya shige ni, Ashe banga komai
ba saboda kofar gidan iya ganinka motoci ne Anyi parking dinsu, ta karamar kofa na shiga seda jiri Ya
kusa yar Dani saboda gawa dana gani cikin makara, a ajje. Waye ya rasu? Na tambayi Kaina Sabida Abba
da Yaya Halifa na tsaye sede kallonsu kadai ya isa yasa Kasan cewa suna cikin Tashin hankali. Tsayawa
nayi na kasa gaba balle nata, se bin mutane nake da kallo kamar yadda ake kallona, mafi yawancin
mutanen basu lura Dani ba.
Tattausan hannu naji cikin nawa, hakan yasa nayi saurin dago idanuna, fes cikin na Yaya Suleiman,
idanunshi Sunyi jawur, ga jijiyoyin kanshi sun firfito waje, baice min komai ba haka zalika Nima Bance
komai ba, se cikin gida, da Adda Salma na Fara Karo, Tana zaune a kofar parlor Tana waya, ba kuka take
ba amma kallonta kawai zai saka mutum yaji ya karaya, inda take na nufa da sauri, tamkar duk wani
kuzarina ya dawo nace
"Adda waye ya rasu? "
Hannuna ta rike tace cikin lallashi
"Kiyi hakuri....."
Hannuna na kwace bansan me ya fusata ni ba, amma a lokacin gani nake idan banyi ihu ba, Adda Salma
bazata jini ba, tamkar we're miles apart Haka nake gani, nace
"Ki sakeni! Ki fada min waye ya rasu? "
A hankali naji abu me dumi Wanda babu ko tantama hawaye ne, ya fara zarya akan kumatunshi. Banyi
Ko kokarin gogewa ba, se naji an dafa kafadata hakan yasa na juya da sauri, Ummaah ce, Idanunta Sunyi
ja, sun cicciko da kwalla tace
"Mukhtar ya rasu! "
Tamkar saukar aradu, haka naji saukar Maganar nan cikin dodon kunnuwana, lokaci daya ganina, jina
baki daya suka dauke bansan iya adadin lokacin Dana shafe ba, all I know bayan na nutsu na ganni a
dakin Inna Ade, tana zaune da carbi hannunta tana ja, hawaye na diga mata.
"Inna Wai da gaske Yaya Mukhtar ya rasu? Ya tafi gaba daya? "
Bata amsa ni ba, se rungumoni da tayi hakan yasa na saki kuka me ciwo, babu abinda nake maimaitawa
Se conversation dinmu da ko awanni uku bamui da rabuwa ba. To me ya sameshi? Ashe rabuwar kenan?
Ashe shi kenan mun rabu? Ashe bazan kara ganinshi ba? Kukan da nake se naji is insufficient, wani
kululun abu ya tokare min makoshina, sakin Inna nayi na kwanta a dandanyar tiles, may be hakan zaisa
na rage jin abinda nake ji amma tamkar ana babbaka wuta cikin zuciyata Haka nake ji, duk yadda Inna
taso na daina kuka abin ya gagara.
Bayan mun rabu nida Yaya Mukhtar, kuma bayan sun gama magana da Rayhana se ya tafi, tunda dama
yace mata tafiya Zaiyi, yana fita daga cikin campus dinmu Ko kofar famfo bai je ba ya bugi wata Mota
dake fitowa daga cikin wani layi. Da yake a karar kwana abin yazo, kafin azo rescuing dinshi Har ya rasu
shi kuma Wanda sukai Karon kafarshi ta karye. Shi ne aka kira Abba saboda shi ne last call dinshi kuma
akai saa Umma Falmata da Abba Imam sunzo gida, so tare sukaje asibiti aka dakko gawarshi, aka Kira
mutanen Kwalam da yan uwan kusa!
Hawaye kam bai Ko tsaya ba, zuciyata ta kasa sukuni, ni nasan baa wasa da mutuwa amma da tabbas
zan karyata rasuwar Yaya Mukhtar. Da kyar da sudin goshi aka samu nayi shiri, ko kanneshi da sukeuba
daya bazasu nuna min jin rasuwar Mukhtar ba, I can't believe cewar komai ya zama tarihi, his smile, his
laughter, his caring. So komai na karshe ne.
Zuciyata bata karye ba seda naga Umma Falmata, se naji wani reason nake dashi na yin kukan rashinshi,
abinda ta mallaka kwaya daya tak, ya tafi ya rasu lokacin da ake tsananin bukatarshi, haka rayuwar take.
🎶Show me the meaning of been lonely, is this the feeling I need to walk with? Tell me why I can't be
there where you are? There's something happening in my heart 💖
Washegari se lokacin na hadu da Rayhana, tun safe nayi wanka saboda Inada test din 1301, babu Wanda
ya sani ma, amma ni nayiwa Kaina fadan na tafi, dan idan banyi test din ba, nasan nida medicine sede na
Tara wata Shekarar. Dakin Ummaah naje na samu Umma Falmata da kishiyarta, tayi kuka marar har ta
gaji, Har kasa na tsuggunna na gaisheta sannan na musu gaisuwa saboda a jiya babu wannan halin,
Numa tausar nake so, kuma na samu Dan su Adda kusan a Kaina suka kwana Har nayi bacci, Dan kowa
har ita Umma Falmata Sunyi tunanin soyayya muke basu San one sided feelings bane.
A kitchen na tarar da Ummaah nayi mata sallama tayi mamakin ganina a Haka amma fuskarta ta nuna jin
dadi. Yaya Halifa ne ya kaini nida Rayhana bisa umarnin Abba. Duk wata nutsuwa da nasan Inada ita
tattara ta nayi guri daya saboda nasan my future relies on each thing I wrote on that paper, Hakanan
nayi sannan muka gama, naje hostel na kwaso abinda ya kamata, ban Tarar da kowa ba kasancewar sun
tafi class. Se a bakin hostel ne naga Anty Zubaida, Tana kallona tace
"Asma'u me ya samu fuskarki? "
Tamkar an bude famfo na fashe da kuka, rikeni tayi tace
"Kiyi Shiru Kinji? "
Kaina na gyada sannan na fada mata abinda ya faru, ta jajanta min dukda bata sanshi ba, kuma ni ban
sake dasu ba balle suji cikina. Kuma tunaninta muna tareda Rayhana shiyasa bata kirani ba.
A Napep Rayhana ke cemin
"Fara 'yar shehu, kin yafewa Yaya Mukhtar? "
Kallonta nayi sannan nace
"Me Yayi min? "
Hawayenta ta share tace
"Ki yafe masa ko zai samu gafarar Allah saboda niyyarshi akanki Bamai kyau bace. Naji mutuwarshi
kasancewata mutum ta karshe da tayi magana dashi. Ina fata zaki lura da darsain da Allah Yayi a
rasuwarshi"
Nidai Bance da ita komai ba amma maganarta Se echo take min, niyyarshi bamai kyau bace? How
comes? Nidai abinda na sani har zuciyata na yafe masa!
Ayshatuuu
[4/2, 10:40 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_TEN_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
_Astagfirullah Wa'atubu ilayka_
🎶 Walking down the street of Nothing ville, where our love is young and free, can't believe what an
empty place it has to come to be, I'll give my life away, if it only be the same! Cuz I can hear a voice
inside of me, that's calling out your name..... 🎶
Wannan wakar mistakenly naji ta a wayar Yaya Halifa, shikenan na tura ta, se naji tamkar danni da
Mukhtar Westlife sukai wannan wakar. Kullum naji ta Se nayi kuka, kuma naki na daina jinta, harseda
Lubna ta fadawa Rayhana sannan tayi deleting dinta daga wayata, amma a banza it already stuck in my
upstairs!
A Haka na cigaba da rayuwata, dukda tabon rasuwar Mukhtar yana cikin zuciyata, ban kuma ga abinda
zaiyi nasarar goge shi ba. Amma Allah yafi kowa sanin me zai faru, me kuma zai kasance, kuma shi daya
ya tsara mana yadda rayuwar mu zata kasance.
Watan shi daya da rasuwa na Fara semester exams, na maida hankalina sosae wajen Karatu, ga kuma
nasihar Ummaah da Abba da suke min akan it's now or never, Haka Yaya Halifa kullum mukai waya se
yace min, idan na Bari damuwa ta saka na fadi exams na sani na gama da rayuwata, ga Adda Sa'ada sun
dawo Kano baki daya, kullum se ta aiko min da Abinci, dukdan nayi Karatu. To idan na tuna hakan se naji
Kamar ya tafi karatun kawai nake son nayi.
Sati biyu muka dauka muna Exams, Dama nafi gane Karatu cikin dare hakan yasa ranar da aka gama
exams, kamar zan fadi saboda baccin da nakeji, hakan yasa nayi deciding tafiya gidan Adda Sa'ada nasan
anan zanyi bacci son raina, Dan Ummaah tace min jikokin duka suna gida, Nikam I can't be that reckless.
Wajen Karfe biyar na yamma na isa gidan, kofar a bude take hakan yasa na tura na shiga, a parking lot na
tadda Mijinta Yaya Bilyaminu da wani abokinshi, dukkansu Juyawa sukai suna kallona, gurin na isa na
gaishe da bakon sannan na gaida Yaya Bilyaminu.
"Young Doctor, Ya exams"
Hamma nayi, cikin sauri na rufe bakina ina A'uziyya tareda yin murmushin nace
"It's over Alhamdulillah! "
Kanshi Ya gyada, hakan yasa na dan saci kallon abokin nashi, kwatakwata hankalinshi baya kanmu, se
naji Banji dadi ba, at least I deserve a second glance, tunda ni mace ce, Fara ce nasan kuma abinda maza
suke rubibi kenan, amma ni me yasa bana samun hakan. Se na fita fin a kirga amma ko kallo ban ishi
maza ba, na rasa Wanne irin jini gareni. Kuma most mutanen da basu kaini ba, a kyau din, nutsuwa da
komai zakusha mamakin yadda ake rubibinsu amma ni ko Oho!
Wucewa nayi ciki saboda idan na kara dadewa akwai matsala. Allah Sarki Addata ta kaina, Ina tunanin na
manta ban fada muku Adda Sa'ada ita ce favorite sister dita ba, she's the best I can ever ask for. Tana
zaune akan cushion, Idanunta sanye cikin farin medical glasses dinta, ko ban Kalli karamin glass table din
dake gabanta ba nasan aiki take, Architecture ce.
Tana jin sallama ta, ta aje HB pencil din dake hannun ta, ta taho inda nake a tsaye, tasan me nake nufi I
need a hug. Rungumeni tayi nima Haka tace
"Oyoyo Lil Sis, Ya Exams din? Oh kinga yadda kika kode kuwa? "
Dariya nayi na saketa Ina tattaba kumatuna, nace
"Kai Adda, ina wuni "
"Lafiya "
Ta amsa ni sannan muka wuce dakinta spare din, gado na fada Ina fadin
"Its been a while gaskiya"
Dariya tayi ta shige toilet nasan ruwan wanka take hada min, hakan yasa na tashi na cire kayana, Tana
fitowa na shiga, na jima ina wanka kafin na fito, Har Kaina seda na wanke, dukda bawai opinion dina
bane, Adda tace na wanke Dan akwai barbushin kazantar in store.
Bankai 30 minutes ba na gama shiryawa, wata carbon color gown na saka, irinta na Bubu ne, so babu
inda ya kamani, bakin veil na yafa akai har ya sakko kirjina sannan na tsaya gaban dressing mirror ina
kallon fuskata wadda ta zama pale tsabar yadda nash wahala kwana biyunnan. Chappette din dake aje
kan Vanity Table na goga a tattausan siraran labbana, numfashi naja me karfi inajin wani sanyi a raina
saboda kamshin vanilla da ya bugeni.
A parlor na zauna, Har lokacin mijinta bai dawo ba, Abinci naci muna Dan hira jefijefi, Har muka gangaro
kan hirar Mukhtar, tace
"Amma Yanzun you're over that ko? "
Dan Murmushi nayi nace
"Adda, Mukhtar bai taba cewa yana sona ba da. Kawai yana nuna min alamar Yana sona"
Glasses dinta ta cire, tamkar cirewar zaisa ta gaskata abinda nace. Kaina na gyada mata irin na
tabbatarwa dinnan. Kai ta girgiza tace
"Tab, ban taba tunanin hakan ba, amma ke kina sonshi Ko? "
Dan dariya nayi, se naji ruwa ya Fara tarar min a idona, Kaina na girgiza nace
"Babu amfani Yanzun, tunda ko ina sonshi babu abinda zai canza cewar shi din ya rasu"
Kaina ta shafa tace
"Abinda nake son naji kenan. Ina son kisan, ke din me daraja ce, ke mace ce a priceless and uncut
diamond, Wanda ya aureki shi daya yasan worth dinki. Kiyi hakuri da hukuncin Allah, rabonki yana nan
zuwa. Dama Mukhtar is just a passerby. Kin gane? "
Kaina na gyada, ina share hawayen da ya Fara zubamin saman fuskata, Bance komai ba amma zuciyata
ta nutsu, idan da ace victims Irina Zaa dinga tuna musu Allah yana sane dasu kuma yanada plan ga
rayuwarsu, tabbas da basu zama abinda suke Yau ba.
🎶.....When you worry the most, there's no easy way out, when you ready to go and your heart left in
doubt, don't give up on your faith. Love comes to those who believe it! And that's the way it's! 🎶
Karfe takwas tuntuni bacci yayi gaba dani, bani na farka ba seda akai assalatu, nayi sallah Ko azkhar Se a
gado na karasa, shima ban tabbatar ba Ko na kai karshe, bacci ya daukeni. Ban tashi ba se goma da rabi,
wanka na farayi inajin tamkar wata sabuwar halitta ce Ni din, duk wannan gajiyar ta tafi, se wani karfi da
nake ji, fuskata normal wannan paleness din da nake hangowa babu shi. Haka na kara kwana daya
sannan na tafi gidan Ummaah . Ashe rabon zanyi tsintuwa ne, tsintuwa Babba kuwa sede a lokacin is
insignificant a gurina.
A kofar gate Naga Abba shida wani mutum da ban taba manta fuskarshi ba, suna tsaye se hira suke,
kuma alamun sun nuna cewar sun jima basu hadu ba. Da sallama na karasa Inda suke na gaishesu, Abba
farin ciki sosae a fuskarshi, Mutumin yace
"Badai Asma'u bace ta girma haka ba? "
Dariya Abba yayi, yayinda na rufe fuskata da hijab din jikina ina Murmushi, naji Abba yace
"Ita ce fa, Yanzun level 2 zata shiga tana Medicine "
"Mashaaa Allah, amma naji dadi sosae. Kasan Abdujjabbar shima medicine Yayi, Yanzun Haka residency
yake. "
Kai Abba ya gyada yana ta san barka, wucewa nayi inajin hirar ta koma ta Abdujjabbar da yawa, amma a
raina tunani nake cikin su ukun waye Abdujjabbar???
Tunda na tashi Kaina ke ciwo, da kyar na fito zuwa kitchen, na bude emergency kit dinmu na balla Pcm
guda biu na kora da ruwan dana taro daga sink din kitchen. Zama nayi kan stool tareda daura kaina kan
kitchen island din dan naga Inada Sauran time daya rage na daura abinci. Ina nan kwance naji shigowar
Ummaah, ban