Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RAI DAYA Inkiya JAN ZAKI by Ikilima Adam

Author :  Ikilima Adam Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 13

24K to 27K   out of 36.3K words

bishi hannu ya musu yace Akira su Kira Inna Fatima tazo ta kwashe wannan kayan ciye-ciyen da aka jera mishi .
Gyada masa kai sukayi .
Shiko kai tsaye matakalan step yaringa hawa ahankali Har iso kusa da wasu dakuna .

Kallon dakin yake kamar me nazari hakan nan cikin rashin kuzari yabude kofar
Yana shiga ya Salam yafurta ganin yanda Nuriyat ke jin jiki sossai yarinya ce da bawata wuce shekaru 16 ba

Akun ya kalle shi yace Uban mu , meze hana mu tafi da ita cen Makabarta.
Gyada masa kai ya yi Alamun gamsuwa.

Amma azuciyar sai wasi wasi yake ya zeyi ya dauke ta ,kuma inyakaita inta samu lafiya saidai ya barta cen dan baze dawo da ita nan ba.
Kusan mintina bakwai yana tunani akarshe dai ya yanke shawaran barin ta.

Tsintar Muryan sa tayi yana Fadin Nuriyat yanda yaja sunan nata jitayi wani zirrr acikin zuciyar ta.
Duk da batada lafiya ne hakan be hanata dagowa ba.

Kauda kansa gefe ya yi befiye son kallon kurilla ba , yawwa yajikin naki yafurta .
Gyada masa kai tayi alamun dasauki .

Shikuwa mikewa ya yi tsaye yace ki zauna cikin shiri zansa akai ki Asibiti duk Abunda kike bukata kiyiwa Inna Fatima magana daga haka be kara cewa komai ba yafice daga dakin.

Cikin hanzarin sa yasauko daga kan matakalan step din .
Koda ya iso kasan wani daki yashiga Shima dakin akwai Wata kofa acikin Wanda bazaka taba sani ba sai shi da yasan kayan sa.
Ahankali yabude kofar yashiga shida akun sa sai gasu tsakiyar titi dan tafiya yayi da bewuce mintina goma ba ya iso dai-dai Wata motar taxi dake ajiye .

Kayan jikin sa yasoma rarragewa yashiga motar tareda danna mata key yabar unguwar cikin hanzarin sa.
Akun nata masa surutu mai San yanayi ba dan yatara uban gajiya beda burin daya wuce yaje gida ya yi uzurin sa .
Yasamu ya sake fitowa dan yin wani Aiki na daban.


*******************


Dangin Mahaifiyar Khairi ne suke meeting akan yakamata su dauko khairi daga Hannu baffa .
Ya za'ayi ace suna Raye zuria Amina suna wahala .

Kakar khairi ta wajen uwa ce zaune take ranta abace duk yanda ya za'ayi a dauko mata khairi.
Shima Saifudeen yadawo wajen su akwai ayyuka Masu kyau da kawo kudi da zasu daura shi akai Amma ace abun kunya doya suke tallah a kasuwar Sheme.
Da Arzikin mu da komai muga jinin mu na wahala wallahi bazeyuba.

Kallon Alhaji Abdul Aziz tayi tace wallahi duk yanda za'ai kayi kokarin amso mana jikar mu.
Itama Sultana inda yanda za'ai akashe auren .
Yanzu haka wallahi Alhaji hamisu kullum maganar Sultana yake dan haryanzu yana son ta.

Alh yace zuwa jibi InshAllah zanje dauko ta.
Sai idan ya mana gardama zamu makashi kotu dan bazeyu ba wankan kuturu da sabulu.

**********************



Saifudeen zaune adakin shi yanata hada kayan sa daya wanke da agobe zewuce da Baffa yadawo.
Jin Sallama ne yasashi fadada murmushin sa .
Yace Akramakallahu harka iso tundazu nake ta zuba idanun ka ,shine sai dare zaka Zo ko.

Murmushi Akramakallahu ya yi hannun sa rike da jakar sa yace yau hanya akwai go slow ne afuwan yayan mu.
Tareda karasa shigowa cikin dakin yazauna .
Sukayi musabaha tareda gaida juna cikin mutuntawa da kewar juna.

Abinci Saifudeen yakawo masa , yana bude abinci ya hada rai Amma afili ya yi murmushi yace Kash saidai fa harna ci Abinci ahanya nakoshi.

Fiddo kayan dake cikin leda yayi ,yafito da gwawanin madara Milo da sugar yace wannan nasu Khairi ne .

Wannan kuma namu ne yafada yana kallon saifudeen dayaga murmushi kwance kan fuskar shi.

Saifudeen yace harda dawainiya haka MashAllah Allah yasaka maka da Alkhairi Amma ka rage dawainiyar nan haka nasan kaima mabukaci ne irin mu.

Amsa masa ya yi da Fad'in karka damu Saifudeen mun zama yan uwa nidakai karka damu.
Sallamar Khairi ne yasasu maida kallon akan ta suka amsa mata waalaikum Salam.

Khairi Tace Akramakallahu wajen ka nazo tareda karasowa cikin dakin Alamun tarin damuwa kwance akan Fuskar ta .

Wani irin Faduwar gaba yaji gab gab gab cikin karfin halin canjin yanayin sa ,ya maida kallon sa akan khairi yace inajin ki Khairi .
Shida Saifudeen zuba mata idanu sukayi danjin me zata fad'a.

Cikin tsananin damuwa tace Akramakallahu headmaster ne yakoremu daga Makarantar JAN ZAKI babu laifin kwabo in ban mance ranar farko da muka fara haduwa dakai a makarantar cewa headmaster kayi JAN ZAKI ne yaturo ka .

Akramakallahu azabure ya tashi tsaye yace kora........?


Taku Har kullum kyauta daga Allah

09069070825
*RAI DAYA*🦜


*JAN ZAKI*🐆



Mallakar

Ikilima Adam ( Kyauta daga Allah)


*Paid book*


Page uku yarage ingama free page wayanda basu siya ba ,su hanzarta kada abaku labari.




1️⃣2️⃣



Azabure ya tashi tsaye yace what ?
Bangane ya kore Ku ba .
Nan da nan duk Wata annurin dake kwance kan fuskar sa ta kau .
Ciza labban sa yayi yana mai Kallon ta da idanun sa da suka kada jajir kamar an watsa masa barkono .

Khairi ina takardan Koran yake yayi magana cikin kakkausar murya .
Saifudeen ne yadauko kusa dashi tareda mika masa .

Yana karba yashiga karantawa ,yadade yana kallon Papper kamar mai nazari sannan daga bisani yace Okk babu matsala tareda mika mata takardan yana girgiza kansa .

Kallon su yayi yace Ku bari zuwa gobe zanje Na bashi hakuri InshAllah ze barsu.
Saifudeen yace inhar be hakura ba tunda khairi tace JAN ZAKI yaturo ka Makarantar please nasan ganin sa zeyi wuya Amma ka kokarta koda ta Sako ne atura masa ,tareda shaida masa Makarantar dake nan cikin Funtua tana Neman Agaji .


Akramakallahu kallon sa yayi yana jinjina kalaman sa ,cikin Muryan sa dake nuna raunin sa yace Khairi dan Allah kuyi hakuri.
Makaranta kamar Kun koma InshAllah keda yar Uwar ki zanyi iya kokarina .

Sossai Khairi da Saifudeen sukaji dadin kalaman sa .
Samun kanta tayi da ce masa na gode Saida safe tayi musu tareda fita daga dakin ranta fes da Farin ciki.



Rashida Mahaifiyar Najwa ce suke fira da Malam Adamu akan wannan gasar auren da za'ayi .
Mummy tace Allah yatsare mana zuria da shiga wannan gasar kamar tallan kai ne.

Malam Adamu yace kwarai kuwa , wayanda ma yayan nasu ke shiga gaskiya basu San zafin su ba .
Kinga in Allah yayi nan da shekara biyu ko uku zamu aurar da Najwa itada Khairi InshAllah .
Mummy cike da jindadi tace wallahi Malam maganar ka gaskiya ce karmuyi gaggawa wajen aurar dasu .
Bashi labarin yanda Innaro ke kula da Khairi tayi .
Rike da bakin sa yace Anya Matar Nan babu Wata akasa kuwa .

Mummy tace haba ya zakace haka ,muyi mata kyakyawar zato
Hakane kuma cewar Malam Adamu Allah Yasa dan Allah take yi.
Suka amsa da Ameen.


******************


Kashe gari


Tunda wuri yau Akramakallahu yatafi makaranta tareda rakiyan Saifudeen.
Koda ya isa Makarantar ,kai tsaye be bata lokaci ba shida Saifudeen office din headmaster suka nufa .

Kowannen su zaune bakin kofar suna kallon kofar arufe.
Saifudeen yace Kaga ni bara inje kila ma ba yanzu ze Zo ba.

Akramakallahu ne yakatse shi ta hanyar fadin please ka tsaya ayi komai agaban ka.
Jin takun tafiya ne ya tabbatar musu dashi ne.

Mamaki ne yacika shi ganin Akramakallahu da Saifudeen kofar office din sa zaune .
Suna ganin sa ,suka tashi tareda bashi hannu sukayi musabaha.
Sam be kawo komi aran sa ba , akan Neman da suke masa ba.
Hakan yasa yabude office din sa .

Yana shiga suka take masa baya .
Kowanne samun wuri yayi yazauna yana kallon sa.
Headmaster cikin iya taku yace Akramakallahu yaushe kafara zuwa Makaranta nan Har kafara fashin zuwa yau kwana biyu kenan baka Zo ba.

Kallon Juna sukayi Akramakallahu da Saifudeen .
Akramakallahu yace kadauko takarda ta kaduba akwai ranakun da aka sa bazan ringa zuwa koyarwa ba koda akwai Makaranta ba.

Headmaster hannu yasa yafara nemo su file dake ajiye na malamai , yana ganin nashi zare shi yayi yasoma karantawa ,ganin inda akasa duk bayan sati biyu kwana biyu zeyi beje ba.
Yasa shi ajiyar zuciya yana girgiza kai kan rashin nasaran sa.

Akramakallahu yace daman mun zone akan wayannan yaran da kora jiya khairi da Najwa .
Kuma nasan a dokar Makarantar babu kora Saida izinin manager ko Shugaban Makaranta.
Ya akai kayi gaban kanka?

Headmaster murmushi yayi yace ai babu Shugaba daya wuce ni ,kuma laifin yarinya mai girma ne dole ne yasa na kore su.
Bakuma Zan Amshe su ba yakarashe zancen yana mai fadin kuna iya fita na sallame ku.
Saifudeen cikin bacin rai yace wallahi baka isa ba zakaga Abunda zefaru inbanda zalinci da kun dauki mutane dabbobi laifin me yarinya tayi.

Akramakallahu kama Saifudeen yayi yana mai bashi hankuri .
Kallon headmaster yayi yace karka damu kanada gaskiya kai akan aikin ka kake .
Shikuma akan hakkin sa yake to bari mu gani wa zeyi nasara cikin Ku.

kama Saifudeen yayi suka bar Makarantar tareda masa rakiya Har gida sannan yakoma makaranta dan koyarwa .

Itakuwa Khairi jin labarin Abunda yafaru yasata rushewa da kuka tana fadin shikenan ya cuce mu.
Innaro ta dafa ta ,tace karki damu akwai makarantu dayawa sai acanza muku .
Khairi cike da takaici tace ni babu Makarantar danake so fiye da JAN ZAKI .


Akramakallahu koda yakoma makaranta cigaba da koyar da dalibai yayi cikin rashin karfin gwuiwa .

Test yamusu dan yana son yagane ko suna fahimtar karatun .
Duk Ajin tsit kake ji cike da nutsuwa suke rubutun su Banda Sakina dake zaune tana tauna cingam Kara's Kara's haka sautin ke fita.

Kallon ta yake yana nazartan yanayin ta , cikin kakkausar murya yace kee Sakina tashi tsaye .

Hada rai tayi tana cika tana basewa ta tashi hade da turo baki gaba.

Ya sunan ki ?

Sunana Sakina Kamal

Sossai yashiga nazarin sunan nata ,Mahaifin ki a ina yake da zama babu alamun wasa a tattare dashi.

Hakan yasa tace yana zaune unguwar locowst yan wanki.
Shiru yayi na wasu dakiku sannan yace inason ganin Mahaifin ki daga nan zuwa gobe .
In bazaku Zo tare ba to lallai ki zauna gida Har sai yasamu lokaci dafatan ki gane yana mai daga mata gira.

Gabadaya daliban class din ta kasa kasa suke dariya cike da Farin ciki ,yau ansamu malamin daya iya gayawa Sakina magana , sossai suka yaba da jajjircewan Akramakallahu akan aikin sa.

Samun kanta tayi da Fadin ni Mahaifina ganin sa ,ba abun wasa bane kafadi Abunda kake bukata ze turo wasu inma kudi ne ,Amma karka sa ran ganin sa agobe .

Sossai ran Akramakallahu yabace hakan yasa yace mata get out cikin bacin rai.
Yakara da cewa ki tafi gida na sallame ki.

Dakyar tafito daga Ajin tana Ayyana aranta wannan wulakanci dayayi mata saita rama , zatasan hanyar da zatabi dan ta aure shi .

Shiko tana fita yacigaba da koyar dasu har suka tashi , be bata lokaci ba kai tsaye gidan su khairi ya nufa dan suyi sallama da Saifudeen dake shirin tafiya.
Koda ya iso Har saif yashirya zuwan sa kadai yake jira .
Cikin tsananin damuwa yace Saif yanzu idan katafi sai nan da sati zaka dawo .
Saifudeen yace kwarai kuwa ai munayi muna hutawa ne nida Mahaifina ina isa cen ze baro garin yadawo gida.
Akramakallahu yace gaskiya kuna kokari wlh.

Innaro ce ta kunna redio tana sauraren sabon fadarkwa JAN ZAKI akan illan cin Amana da zanba cikin aminci .
Kwabe baki tayi tace oh wannan Jan zakin Allah Yasa ba Aljani bane .

Daga Saifudeen Har Akramakallahu juyowa suka yi suna kallon ta.
Khairi dake sauraren Redio tareda ita tace haba Innaro ya zakiyi wannan furucin nifa JAN ZAKI nan yana burgeni , da Allah ze hada ni dashi sujjada zanyiwa Allah dan godiya , Zan iya kwana inajin Muryan sa batareda gajiyawa ba .

Innaro zazzare idanu tayi tace khairi kodai kin Kamu da son Jan zaki ne.

Eh nakamu da son sa tabata Amsa tana turo baki gaba , tunda haka kike son ji.
Kece kikasan me ake kira da so nikam ban sani ba.

Akramakallahu cikin karfin Hali yace Khairi Amma da dukan Alamu maganar Innaro gaskiya ce kin Kamu da son Jan zaki .

Idanun Khairi ne yacika da kwalla nan da nan suka ciko da kwalla tace Akramakallahu gaskiya na fada bansan meye so ba.
Nidai na tsinci kaina da son jin fadakarwar sa .
Koda ma ze ganni nasan ko kallon inda nake bazeyi ba.
Murmushi Akramakallahu yayi yace to saboda me baze kalleki ba kina kyakyawar mace ?

Saboda ni ba Ajin sa bace nidai Abar ma zancen nan kawai tafada tareda tashi tabar wajen.
Akramakallahu da Saifudeen dariya sukayi kusan a tare.


Saifudeen yace yarinyar nan tana bala'in kaunar duk Abunda ya shafi Jan zaki ,kuruciya ke dawainiya da ita.

Innaro ce ta kalle su tace aiko Jan zaki yamata nisa wane mutum inji mutuwa yanzu haka yana tareda manyan Mata Masu Aji da kudi me zeyi da Wata khairi ita kanta tasan tatsuniya takeyi .

Saifudeen yace Innaro bafa cewa tayi tana son Jan zaki ba , cewa tayi tana kaunar fadakarwar da yake yawan yi yakamata ki gane .
Daman meye ze hada Khairi da Jan ZAKI ko baki fada ba , nasan mu talakawa ne dan haka ki gyara kalaman ki yakarashe zancen yana mai Kallon Akramakallahu yace muje ko?
Akramakallahu yace Yaya saifudeen yi hakuri rashin fahimta ne shiyasa tayi maka wannan zargin.

Innaro dake sake da baki ganin ran Saif ya baci tace haba Dana da wasa nake Allah ya huci zuciyan maza.

Basu bi ta kanta ba suka fice daga gidan .
Itako Khairi shiga daki tayi tana tunanin makomar ta inhar bazata koma Makarantar Jan ZAKI ba.


Har bakin titi Akramakallahu ya rako Saifudeen tareda masa Alkawarin InshAllah su Khairi zasu koma Makaranta kada ya damu .
Hango Sultana tana doso inda suke ne yasa Saifudeen kallon Akramakallahu yace kaga ga kanwata nan Sultana zuwa .
Fuskokin su cike da faraa suka ce Mata barka da zuwa.

Da yawwa ta amsa musu tace Yaya saifudeen Har zaka wuce ne ?
Eh Zan tafi Sultana nayi rana yau .
Nuna mata Akramakallahu yayi yace wannan shine malamin su Khairi a makaranta .

Kallon sa tayi tareda gaishe shi cike da ladabi
Ya Amsa Mata gaisuwar fuska a sake yana mai yaba hankalin ta .
Yaga tsantsar kamanni dasuke itada Khairi da dukan Alamu bazata wuce shekaru shabakwai ba.

Saifudeen yace Sultana Allah yayi zamu hadu Kinga sauri nake saide ki karasa gida please kije kiga kanwar ki.

Allah yatsare ta fada tareda wuce su cikin jin dadi tace na tafi byeee tana mai daga masa hannu shima hannu yake daga mata .
Akramakallahu sun dade suna fira akan titin kafun ya samu motar daze kaishi tasha.

********************


Babban gidan redio mai suna *kukan kurciya* wacce tayi zarra acikin garin Katsina .

Wata katuwar mota ce tayi parking daidai bakin gate din.
Mai gadi najin horn a hanzarce yabude gate .

Kai tsaye wannan Motar mai kirar Mercedes kai tsaye tashiga farfajiyar wannan gidan redio.

Jamaa dake kai kawo wajen kowa ya zuba idanu yaga waye wannan ko wacece zata shigo .
Ahankali ta kashe wutar motar tareda bude motar tafito .
Sanye take da Riga da wando irin exgytien marron color tayi rollin din gashin kanta da ribom ,tareda dan karamin gyale marron color , idanun ta dauke da bakin glass .
Takalmin ta mai tsini ne yaja hankalin mutanen wajen dake kallon tana rufe motar ta .
Suka hada baki wajen fadin MashAllah wannan yarinyar ta hadu ta ko ina.

Cike da takama da izzar ta , ta iso inda taga jamaa .
Zazzakar Muryan ta sukaji tana fadin barkan Ku da warhaka dan Allah inason ganin manager din gidan redio nan.

Daya daga cikin yace gaskiya hajiya indai besan da zuwan ki ba.
Ganin sa kai tsaye yana wahala .
Hada rai tayi cikin tsananin bacin rai tace kako san dawa kake magana kuwa.
To kaje ka gaya masa diyar Alhaj Kamal ce kana Fadin haka yasan ko wacece cikin bacin rai take magana.
Angama ranki yadade bara muje mu fada masa.
Koda ya iso office din knocking yayi aka bashi damar shigowa.
Yana shigowa ya sanar masa da wacce ke Neman sa.
Manager cike da mamaki yace diyar Alh Kamal anan wajen .
OK jeka shigo da ita yafada cike da tunani me tazo nema.
Koda suka iso da ita samun kujerar dake face da nashi tayi tazauna tana mai Kallon sa.
Tareda cire madubin tace
Ranka yadade barka da Aiki nasan ka kosa kaji meyakawo ni wajen ka.

Gyada mata kai yayi yace ina sauraron ki tareda bata duk hankalin sa.

Cike da wayau da kissa tace Gidan redio Zan bude Nawa nakaina sainake ganin babu fadakarwa dake Jan hankalin Al'umma sama Dana Jan zaki.

In bazaka damu ba zanso Ku sanar dani ta wani hanya kuke bi wajen samun bayanan sa ko ince fadakarwar sa.

Ajiyar zuciya mai karfi Manager ya sauke yana mai Kallon ta , yana murmushi yace gaskiya tunda muke samun bayanai akan jan zaki babu takamaimai waje daya da zamu ce nan ne kadai ake ajiye Mp3.
Tunda kina bukata kibari da mun samu sai mu baki kema ki saka hakan zefi sauki .

No nidai Ku gayamin ta hanyar dakuke bi nima basai na jira Ku ba.

Manager dago kai yayi yana kallon ta yace.

Sako ne yake zuwa mana ta email akan Jan zaki ya aiko da Mp3 waje kaza .
Mu kuma Zuwa muke mu dauka damun kawo sai mu daura duniya taji Kinga yanda muke samu kuma duk gidan redio dake fadin kasar nigeria haka sukeyi wajen samun jawaban sa.
Tunda kince zaki bude gidan redio ne .
Dakin bude kibamu tallah nasan zeji da kunne sa.
Ze saki a layin wayanda ze ringa turowa wannan faifan audio .

Zazzare idanu tayi tace uhmm Kaga ni Zan tafi kabani Email din sa.
Dauko papper yayi kusa dashi tareda rubuta mata .
Jan ZAKI 111 @ gmail.com

Cikin tsananin Tashin hankali take kallon email din ,dauka tayi tareda da saka shi a jakar ta .
Godiya ta masa sannan tabar office kai tsaye gida ta nufa cikin hanzarin ta kamar zata tashi sama dan sauri.

Shiko Manager tana fita ajiyar zuciya ya sauke yace uhmm wannan yarinyar akwai makirci waini zatayiwa wayau .

To Ni babu ruwana da fallasa sirrin mutum mai Amana .


Koda Sumayya ta isa gidan bata gama daidai ta parking din motar ta ba.
Tafito tayi gidan gadan gadan
Mai gadi na gaishe ta bama tasan yanayi ba.

Kai tsaye babban Falon nasu ta isa , cike da mamaki take kallon Abban su yana magana cikin bacin rai da Sakina.
Yace wani dan Iska ne zece dole sai Mahaifin ki yazo zaki koma Makarantar waye uban shi.
Sakina tace

9 / 13