Author : Ikilima Adam Category : African Stories & Novels
wallahi dan matsiyata ne kuma wallahi karatun Addini kadai yake koya mana Amma bakaga iyayi ba kyawun sa kadai ya taimake sa.
Alhaji KAMAL yace to yayi kadan zesan yataboni ya tafka babban kuskure wallahi.
Dawo da kallon kan Sumayya yayi wacce tayi mutuwar tsaye.
Yace lafiya kuka tunda kika shigo na ganki sai aslow?
Cikin raunin Murya tace Daddy ga email din Jan zaki nasamo tareda mika masa .
Yana karba yashiga warware wa cikin tsananin Mamaki yace wannan yaso yayi kama da email din Muhammad marigayi .
Sumayya tace kwarai Kuwa banbancin sunan JAN ZAKI da akasa kadai ne.
Wani uban zufa ne ya keto masa yace karki damu anjima zamuyi magana .
Bata labarin Koran da akayi wa Sakina yayi.
Sumayya tace wani mahaukacin malami ne lallai yakira ruwa .
Daddy yace kwarai kuwa Kaga dan Iska wai Mahaifin ta yake son gani da kansa.
Gobe zantura drever na yaje shida Sakina wallahi yana hanata zaman Aji zega yanda zanyi dashi cikin tsananin bacin rai yake magana.
Sakina tace nidai banson a kore shi please dan wallahi na Kamu da son sa.
Zazzare idanu Daddy da Sumayya sukayi suna fadin soyayya fa kikace lallai yarinyar nan meye hadin ki da talaka .
Mummy dake shigowa falon tace ai suma talakawan mutane ne ,ai babu Wanda yazo duniya da Arziki .
Daddy rasa amsar daze bata yasashi yin dogon tsaki tareda barin dakin .
Itama Sumayya kai tsaye dakin ta ,ta nufa dan daukan laptop dinta zata saka Email din Jan zaki tareda tura masa Sako .
Mummy kallon Sakina tayi tace haba yata meyasa kuka raina talakawa ne dan hakkin daka raina shike tsole maka idanu .
Sakina turo baki tayi gaba cikin shagwaba tace mummy ai malamin ne bashida mutunci .
******************
Baffa agajiye yakaraso gida Sallama dauke Abakin sa.
Khairi najin Muryan sa aguje tafito daga dakin nata ,be Ankara ba saiji yayi tayi masa wawan runguma tana murmushi oyoyo Baffa kaganka kuwa Baffa wallahi kayi kyau kayi haske da kiba .
Sossai ya Dara yana mai shafa kanta yace Alhamdulillah nayi tozali da yar auta na .
Innaro tana dakin ta ,tana zuba magani cikin abinci khairi dan yau shine karo na biyu da Khairi zataci abincin nan ,duk da taji Muryan baffa fadi take azuciyar ta Allah Yasa tayi nasara ayau sannan tayi nasara ana ukun daya rage .
Ajiye kwanun tayi tareda fitowa tsakar gidan lale lale marhaba da maigida na dafatan ka iso lafiya.
Jakar kayan sa dake ajiye ta dauka tayi ciki dashi.
Shiko Baffa dakyar ya samu ya banbare Khairi daga jikin sa yana Fadin bara inje inyi wanka ko saimuci abinci tare.
Zazzare idanu Innaro tayi jin Furucin sa .
Caraf ta karbi zancen habawa aini da Khairi zamu ci Abinci kaikuma kaci naka.
Murmushi yayi yana mai Kallon khairi da tayi kasa da kanta .
Kai tsaye bandaki yashiga dan yin wanka kokan yafito Innaro ta mikawa Khairi abinci tana mai fadin yata maza muci abincin nan dauko spoon biyu tayi kamar da gaske ci zatayi hakan yasa Khairi tasoma ci .
Tana ganin khairi taci kusan rabin kwanun azuciyar ta sai fadin Alhamdulillah take afili kuma tace sauran Nawa ne Khairi maza kije ki share dakin baffa Sam na mance yau zedawo .
**********************
Kashe gari
Motocine sunkai goma suka paka daidai kofar Makarantar Jan zaki.
Ahankali mutanen dake cikin jerin motocin suke fitowa kowannen su sanye cikin bakaken kaya suite .
Basu tsaya bata lokaci ba kai tsaye suka cusa Kansu cikin Makarantar.
Office din headmaster suka nufa .
Iske shi sukayi zaune tareda drever su Sakina akan Koran da Akramakallahu yayi mata.
Cikin tsananin Tashin hankali yake bin kowanne su da kallo .
Sake da baki yace bayin Allah daga Ina haka?
Daya daga cikin su ,yace mu ma'aikata ne , daga Aliyu Jan zaki munzo da...............
Taku Har kullum kyauta daga Allah
Karku Manta paid book ne .
Saura page uku agama free page.
09069080725
*RAI DAYA*🦜
*JAN ZAKI*🐆
Mallakar
Marubuciyar
KAIKAJAWA KANKA
KANWATA
RAYUWAR MA'AURATA sabon Salo
*Last Free page*
Daga wannan na gama na bati duk me bukata ya tuntubi lamba kamar haka.
09069080725
*Duk Wanda zesiye* *littafin nan dan yafitar na roke shi Dan Allah yamin** *magana in dawo masa da kudin sa , ko kuma yake da niyar siya to kada yasiya inhar ze fitar*
Kudin karatu ne, ba kudin mallaka ba
Karku mun Abunda kukayi a littafin KANWATA please dan Girman Allah na roke Ku.
1️⃣5️⃣
Cikin zazzare idanu yace bawan Allah lafiya kuwa nan fa Makaranta ce wajen koya tarbiyya , ya zakazo kana Aikata badala gaban dalibai .
Caraf idanun su ,suka tsarke cikin juna ,wani muguwar Faduwar gaba Akramakallahu yaji zuciyar sa tanayi gab gab gab da karfi.
Alhaji KAMAL cikin Razani yake kallon Akramakallahu ,
Muhammad yafurta ,sannan yafara girgiza kai , yace A'a mafarki nake .
Akramakallahu cikin around jarumta yace bakayi karya ba , yar taka ce tagayamaka sunana ko.
Ba wannan ba , Makarantar nan dauka na Aiki akayi ,kuma Shugabar Makarantar yaban daman in dauki doka a hannuna .
Amatsayin ka na Mahaifin ta , kamata yayi kazo cikin salama sai mu sasanta ta koma Aji ,Amma tunda kazo da rigima daga kai Har yar taka kada inkara tozali da kafafun naku a wannan Makarantar , nasan Kanada tarin tambayoyi sokake kaji uban wa ya bani wannan ikon ko.
Uhmmmm Allah shike bada dama da iko ba mutum ba dan haka get out yafada a tsawace Saida jijiyoyin kansa suka mimmike .
Alhaji KAMAL da magoya bayan sa , sossai suka rude da lamarin Akramakallahu.
Alhaji KAMAL sassaita nutsuwar sa yayi yace kasan dan matsiyata beyi iya samun wuri ba.
Jibi suturar dayake jikin ka ,kaikasan talauci be goge ba ajikin ka .
Wallahi tallahi indai ni uban Sakina ne Zan nuna maka izzata yakarashe zancen yana fadin kee Sakina Zo muje .
Makarantar nan na yayan talakawa ne .
Kin wani damu kanki akan matsiyatan malamai .
Abokan tafiyar sa , da mamaki suke kallon tsaurin idanun Akramakallahu.
Kasaitaccen murmushi Akramakallahu yayi yana kallon yanda yaja hannu yar sa itakuwa tana turjewa batasan tafiya .
Hankalin sa yadawo akan Dalibai da kowannen su , yayi cirko suna kallon Abunda ke wakana kwabe baki sukayi .
Kowacce da Abunda take fadi akan Sakina da Mahaifin ta.
*****************
Sallamar Innaro ne yasa Malam amsa mata , Bismillah yace ..
Hakan yasa tashiga tareda samun wuri ta zauna.
Cikin tsananin damuwa suka gaisa tace Malam nayi amfani da maganin da kabani wallahi yaci dan ga Yarinya nan ta bushe idanun ta , tace auren Gasa take so.
Yanzu kuma wani tunanin nayi Wanda abaya banyi shi ba .
Nan tabashi labarin dangin Mahaifiyar ta Masu Arziki ne ,da kuma dalilin dayasa tazo , tanason ya taimaka a warware sihirin daya kama khairi.
Malam kallon ta yake yace Safara'u tun ran Gini tun ran zane ,wannan sihirin ba yanda za'ai a warware shi dan wallahi yakamata kenan saidai kawai Ku zuba idanu kuyi kallo.
Nan da nan wani uban zufa yafara sassafo wa Innaro cike da damuwa tace wallahi da nasan jikar Masu Arziki ce bazan mata wannan Asirin ba , saidai in samu hanyar da Zan ringa tatsar dangin su .
Malam yace Saidai idan tayi auren za'a iya raba auren , tadawo gida.
Ko kuma ana daurawa da awa daya ko biyu asa mijin ya sake ta ,Yana sakin ta asirin ze warware jikin ta.
Innaro cike da gamsuwa tace tayarda ta da hakan .
***********************
Baffa zaune kofar Gidan nasu yana waya da Saifudeen akan yakamata su dau hutun Wata daya basuje kasuwa ba.
Saifudeen yace Baffa yanaga yau sai ahankali gayamin yakai Mahaifina wani Abun na damun ka ne?
Cikin Damuwa Baffa yashiga bashi labarin Abunda ke Faruwa .
Zumbur Saifudeen yatashi daga zaunen dayake yana maimaita auren Gasa tareda daura hannun sa akai yana salati .yace
Baffa InshAllah gobe Zan dawo gida tunda kace mu dan huta .
Baffa inhar nazo karka hanani hukunta Khairi wannan wace irin yarinya ce , wacce batasan kunya ba.
Jiki Asanyaye Baffa yace kana ganin Khairi zataji tsoron ka ta janye ?
Kwarai kuwa InshAllah haka nake tunani .
Allah yakawo ka lafiya Dana kafun kataho ka sanarwa makota , zamu dau Hutu na wani lokaci .
InshAllah Baffa bakada matsala.
*********************
Tsohon headmaster yayi shigar shi ta Alfarma tareda daukan motar haya zuwa gidan Alhaji KAMAL.
Koda ya isa ya iske shi a farfajiyar gidan zaune tareda manyan abokan sa ,suna shawara akan Akramakallahu.
Sallama dauke Abakin sa yakaraso , su kuwa cike da faraa suka tarbe shi tareda yin musabaha ,samun wuri yayi yazauna kusa dasu cikin damuwa ya sanar musu Koran da Jan zaki ya masa akan wannan yar matsiyatan.
Alhaji KAMAL yace yanzu kana nufin shi Jan zaki duk Abunda akeyi a makarantar sa yana samun labari kenan , shege saidai baze fitoba burin sa kullum yayi ta jefa mana harsashi .
Headmaster samun wuri yayi yazauna yace ranka yadade wallahi korata yayi ,kuma yarinyar nan inason na wulakanta ta .
Ita da Alhlin ta .
Alhaji Garba dake sauraren sa yace to me zaka mata ne ya tsaresa da idanu cikin tsananin tsoron Furucin sa.
Headmaster yace wallahi Fyade Zan mata kawai shine illah da Zan mata da baze taba goguwa a cikin zuciyar ta ba.
Dukan su suka sheke da dariya Banda Alhaji Garba daya hada rai .
Yace Ku tsaya wannan maganar ba abun dariya bace , kunsan me ake nufi da fyade kuwa.
Nasan cikin mu babu Wanda yake son ayiwa yayan sa , sai nake ganin wannan ba ita bace mafita ba.
Alhaji KAMAL Kamal yace to menene mafitar ?
Nidai Abunda nake gani shine kawai Ya aure ta sannan ya mata duk wani wulakanci hakan zefi , tunda iyayen ta talakawa ne bazasu hana shi ba.
. sossai sukayi Naam da shawaran sa .
Headmaster yace Alhaji daman nazo na Amshi cikon kudi na , gobe zanyi tafiya sati biyu zanyi indawo Dana dawo kai tsaye gidan su Yarinyar zanje Neman aure .
Alhaji KAMAL yace bani account number in saka maka kudin , sannan Inka dawo kazo muyi shawara akan shegen malamin nan dan wallahi bazan kyaleshi ba , dan banza ni zegayawa bakar magana .
Cigaba da tattaunawa sukayi akan yanda Sumayya zataci gaba da bibiyar Jan Zaki da kalaman soyayya.
***********
Akramakallahu sallama yayiwa Baffa akan zeje yadawo tareda barin su .
Tafiya yake cikin hanzarin sa harya kawo bakin titi.
Yakai kusan mintina bakwai tsaye yana kalle kalle gefen sa hagu da Dama.
Sannan yaciro tsadaddan Wayar kiran iPhone tareda danna number yayi dialling.
Buga daya suka daga , cikin Muryan sa mai dauke da sirrika yace Harna iso kuna ina ?cikin Fada yake magana
Bejira cewar su ba ya katse wayar yana mai cigaba da kallon agogon hannun sa.
Abunda befi minti Biyar ba saiga motocin sun iso tareda parking daidai inda suka gansa.
Cikin Yaran sa yace ranka yadade dan Allah kayi hakuri bamu san kataho ba .
Beko kalle su ba yasakai yashige motar da dan uwan sa yake ciki.
Yana shiga suka rufe motar gam .
Adu'oi yafara karantowa yana kallon Salim dake bin sa da kallo alamun tarin tambaya.
Salim yace Haidar Amma ba inda zakaje da wannan kayan na jikin ka ,habawa saikace an tsintoka a rami.
Akramakallahu tsaki yayi yace a kabari aka hakoni.
Maza akaini gidana na JRA zanje nayi wanka na shirya yajikin Nuriyat ne ?
Gaskiya Nuriyat taji sauki tunda likitoci sukayi ta bata kulawa harma ta warware fa.
OK naji dadin hakan , ni Kaga kadaina samun idanu kasan me yaban mamaki ne?
Salim yace saika fada inajin ka.
Wallahi yarinya Dana ke kwana gidan su ce ,ta feshe idanun ta wai aure take so ,nifa bantaba ganin fitsararriya irin ta ba.
Salim yace Toka aure mana yana mai Kallon yanayin sa.
Sossai Akramakallahu yahada rai yasha kunu yace kasan maganar banzan ce banso me zanyi da wannan kwailan , wacce take saka iyayen ta kuka .
Ni Mahaifin ta ne abun tausayi dan inta nine , su barta mana tayi auren shasha yarinya kawai.
Salim dake kallon reaction din sa yace kaiko yada daukan zafi haka , kodan yayan ta abokin ka ne?
Shirune yabiyo baya ya jingina jikin sa da kujerar motar yana mai lumshe idanun sa.
Salim ganin Miskillanci yatashi yasa shi fadin mutum sai iyayi kadauko fira mai dadi kana bani daga bisani ka kyaleni ina magana ni kadai nifa tsiyata dakai kenan kasani ko in auri Yarinyar ne.
Akramakallahu ko kallon sa beyi ba bare yasa ran ze bashi amsa .
******************
Kwanci tashi asaran mai rai gashi Har lokaci yazo gobe ne za'ayi gasar .
Mai shela daga gidan mai gari yakara fitowa yana shela.
Jamaa gari mai gari yace a sanar muku gobe ne za'ayi gasar bayan anyi sallah juma'a Allah yaba mai rabo sa'a
Duk matasa dasukaji harda khairi aci kowannen su sai fadi yake gaskiya ba za'ayi babu shi ba , yarinya mai kyau da haduwa bazasu bar banza ta fadi ba.
Khairi cike da Murna gobe za'ayi gasar Najwa ta kalle ta cikin kuka tace haba Khairi bazaki janye ba kowa yamiki magana kinki sauraren su.
Khairi cike da raunin ta ,tace wallahi inajin zafin ganin Baffa da Yaya saifudeen da Sultana suna cikin damuwa saboda ni , Amma wallahi nakasa gane dalilin dayasa na bijire musu wlh Najwa inajin zafin hakan acikin raina.
Mummy ce ta taho wajen nasu duk firan dasuke yi akan kunnen ta .
Cikin kuka tace khairi nice Na shayar dake inma bakiji maganar kowa ba aikin ji tawa ko.
Tashi Khairi tayi tace wallahi Mummy bansan me Ma'anar aure ba , bansan yanda ake zaman gidan Miji ba .
Kawai na tsinci kaina da son auren ne ,dan Allah ki yafemun kada kiyi kuka dani Uwata .
Rungume Mummy tayi sukaci gaba da rera kuka .
Itakuwa Najwa hannu ta daura akai tana fadin shikenan tawa ta kare khairi bazan iya Rayuwa babu ke ,nono daya muka Sha , bansan Waze aure ki anan garin yake kokuwa wani wurin Allah masani .
Khairi sakin mummy tayi ta dawo ta rungume Najwa cikin kuka tace kuyafe ni dan Allah.
Wallahi bansan meyasa na Aikata haka ba.
Malam Adamu ne yashigo yana kallon yanda suke kuka zuciyar sa ta karye jikin sa yayi sanyi yana fadin oh Allah ka kawo mana agajin wannan musiba .
Cen bangaren Innaro sossai tashiga damuwa ganin yanda Baffa ya rame duk yafita hayyacin sa .
Kudi yafiddo akalla zasu kai Dubu dari yakirawo Saifudeen yace gashi kaje kasuwa kasiyewa Ummulkhairi tukwane da dinkakkun Shadda kala biyu da takalmi da jaka Wanda zata sanya agobe.
Sannan yakara bashi Wata dubu hamsin yace wannan kuma Shadda zaka siyo mana nida Malam Adamu Wanda zamu sanya wajen daurin aure.
Kowannen mu shaddar dubu goma zakasai mana kasa Amana dinki a kasuwa ,sauran kudin kayi cefane abinci da za'a dafa gobe .
Saifudeen da idanun sa , suka kada yace Baffa saidai insiyo kayan Khairi da naku ,Amma cefane sai mata ,zankaiwa mummy kudin sai tayi.
Baffa yace hakane To ka kai mata kaji Dana .
*********************
Suna iso babban Falon nasu cikin tafiyar sa mai nuna ,kwarjinin sa.
Yakaraso Falon tareda samun wuri yazauna .
Kallon ma'aikatan da suka kewaye shi yayi , yace ina Nuriyat take .
Kokan yagama rufe baki yahangota tana saukowa daga kan matakalan tana sanye cikin bakar habaya tasha makeup hannun ta dauke da awarwao.
Kallo daya ya mata yadauke kai.
Koda ta iso Falon dukar dakai tayi cike da ladabi tace uban mu maganin kukan mu barka da iso wa.
Samun wuri tayi tazauna kujerar dake face din sa ,tace nasan kashiga damuwa akan rashin lafiya ta Amma Alhamdulillah na warke ta dalilin kulawan ka .
Allah yasaka maka da Alkhairi.
Magoya bayan sa ne ,suka amsa da Ameen , shikuwa cigaba da danne danne wayar sa ,yake .
Harta fidda ran zeyi magana saita ga yatashi tareda yi Mata kallo na wasu dakiku ,sannan yace yawwa Inason ki zauna cikin shiri kowani lokaci ,zakiji sakona .
Zazzare idanu tayi tace kana nufin ka Amince zaka aureni ne.
Kalaman ta , sun matukar girgiza shi yace Nuriyat yaushe muka fara wasa nidake da Har raini yashigo ciki.
Dukar da kanta kasa tayi tace Afuwan mistek aka samu .
Salim dake shigowa falon yace Nuriyat wai me yake burge mata ne akan wannan miskilin .
Kasa magana tayi ganin yana wajen , shikuwa be kalli inda Salim yake ba.
Yace idan kagama kazo mu tafi ko.
Salim bin bayan sa , yayi sukayi Wannan dakin sirri tare , tareda fita , ta bayan gida kai tsaye motar Taxi dinsu suka hau daze kaisu Har gida cen gidan su dake karkashin kasa.
*****************
Mamy zaune adakin ta itada Nusaiba suna hiran gobe ne zata fita zuwa cikin gari
Nusaiba tace mummy wallahi kibari in raka ki.
Mummy cike da tsoro tace rufan Asiri ni kaina ba karamin artabun muka Sha dashi ba , harya amince , yazo yaji dake zaaje cewa zeyi bazan fita ba .
Kinsan kuwa in yahana dole na hakura dan yafini gaskiya.
Nusaiba tace Allah yakaimu .
Wai yaushe ne zamu koma cikin gari da zama ne Mummy duk da dai anan din ma ,bamuda matsalar komai saidai bamu ganin mutane irin makwata ,kawaye duk babu su.
Murmushi Mamy tayi tace InshAllah wataran zakiyi su karki damu .
Aliyu Jan zaki , kusan atare suka iso wannan wajen jejin
Tareda shiga ramin suka rufe ta ciki.
Maaikatan na ganin su , suka fara barka da zuwa ranka yadade .
Daga musu hannu yake batareda ya tsaya ba.
Kai tsaye falon Mammy yanufa shida Salim , Aku na ganin sa aguje yayo kansa tareda hawa kan kafadar sa yace ranka yadade kana sane kuwa jibi ne zamuje kasar America kan harkokin computer da kake son bude kamfanin sa a Nigeria.
Dafa kai yayi yace oh My God wallahi gwamma daka tunanin dan Lele yafada yayin da yake doka sallama adakin Mamy .
Lalale lale marhaba da yayana cewar Mamy .
Cike da ladabi suka duka Har kasa shida Salim suka gaishe ta .
Nusaiba dake kallon yanda yakarayin kyau da haske ,tace gaishe su cike da ladabi amsa mata sukayi .
Samun wuri sukayi suka zazzauna inda kukun Aliyu yayi sallama hannun sa dauke da su lemun juice da cincin ya ajiye akan center table dake tsakiyar dakin.
Tareda jera musu kofuna gaban su , tsiyaya musu yayi cikin ban girma yace Yallabai ko akwai Abunda kake bukata ne ?
Daga masa hannu yayi alamun babu hakan yasa kukun nasa yafice daga dakin.
Mamy cike da Jin dadi take kallon su ,suna shan lemu tareda yin gyaran Murya tace Aliyu gobe da karfe Nawa Zan fita ne?
Dago kai yayi yana kallon ta ,dan shi Sam yama mance da zancen fitan ta.
Dafe kai yayi yace oh Ashe maganar fitan