Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RAI DAYA Inkiya JAN ZAKI by Ikilima Adam

Author :  Ikilima Adam Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 13

6K to 9K   out of 36.3K words

malamin nasu ne....

Khairi da Najwa suna kallon yanda yake musu darasi har lokacin tashin nashi yayi .....
Malamin kallon Khairi yake dan ta tafi da imanin sa....

Sakina tana lure dashi hakan Yasa duk ta tsane su batasan uban dayasa aka kawo su Ajin ta ba...
Malamin Na kokarin fita daga Ajin yaji Muryan Khairi tana Fadin dan Allah inada tambaya....

Kowa Class din maida kallon su sukayi akan su dan so suke suji me zata fada...
Sallamar J A ne Alamun time din karatun sa yayi ...
Yaji tana Fadin dan Allah Malam meye Ma'anar Stupid girl da Mental problem..

A J zazzare idanu yayi duk bashi take Mata tambayar ba yace................



*Karku Manta Paid book ne*

*Da Free yakare littafin zekoma 1k special group*

*Normal kuma 500*



*Taku Har Kullum kyauta daga Allah*
🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜

*JAN ZAKI*🐆





*DAGA MARUBUCIYAR :*


*KAIKAJAWA KANKA*


*KANWATA*


*RAYUWAR MA'AURATA*


Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI*



*Paid book ne*


Normal group 500


Special group 1k


Acct nomba

*3115484026 ikilima Adam first bank*

Ko Katin MTN

Kan wanna layin

09069080725

Banason VTU





0️⃣3️⃣



Tareda Fiddo Biro da pepper samun bangon Makarantar yayi tareda makala pepper yanda ZAKI dadin rubutu yana gamawa ya nade papper cikin Aljihun sa yafice cikin hanzarin yana buga uban Sauri.....

**********************

Cikin Ajin kuwa Khairi sake da Baki take kallon malamin dake koyar dasu cike da kwarewa yake koyar dasu darasin mathematics ..

Najwa da khairi kallon Juna sukayi Sam basa fahimtar me yake fadi tunda da harshen turanci yake magana...

Amma duk Abunda Yake idanun sa nakan Khairi sossai taja hankalin sa .
Dan befiye wuce lokacin tashi ba Amma yau Saida dalibai sukayi masa 'tuni..

Karfe daya da kwata ya tashe su...
Najwa kallon Sakina tayi dake kokarin fita tace baiwar Allah kece wacce akace ZAKI ringa koya mana darasi...

Cak Sakina ta tsaya tareda waigowa 'tabe baki tayi tace eh nice wacce Zan ringa koya muku darasi Amma azuciyar ta sai fadi take zandai kara dulmiyar daku yanda bazaku ringa fahimtar komai ba....
Murmushi tayi tacigaba da Fadin Ku bari zuwa gobe Zan fara horar daku tana Murmushin keta .
Khairi daman Sam bata kwanta Mata arai ba ..
Tace Najwa muje dan Allah ya kike damun kanki akan sai ankoya mana kedai ki zuba idanu kigani duk wayanda muka samu anan zamu wuce su....
Jan hannun Najwa tayi da karfi tareda barin Ajin cikin kunan rai..

Sakina ikon Allah ta furta rike da bakin ta tace yau Naga mara kunyar yarinya kenan kyawun dan maciji ce batada Kirki.
InshAllah Ni Sakina Zan hanaku fahimtar komai masu fararen kafa takarashe zancen tana fita daga Ajin cike da mamakin Kalaman Khairi ...



**************************



sunkai su Ashirin zaune cikin office suna karanta sakonni cikin computer Wanda ya nuna Sako ne daga Jan ZAKI...

Babban cikin su Yace Kaga Abunda oga yafada kuwa...?
Sauran dake latse latsen keyboard sukace eh mun karanta sakonnin sa...

Toshi meyasa baze bayyana bane koda agare mu ne..
Babban cikin su Yace nasan yanada kwakwaran dalilin sa..
Amma duk da haka yakamata yazo mugan sa muga yanayin sa ......

Kuma kasan me yake bani mamaki kuwa..
Dayan dake zaune mai Suna Jafar yace saikun Fada....

Gabadaya be taba tozali da wani ma'aikacin sa ba...
Kullum sai bada umarni hatta kudade baya turo su ta bank cash yake ajiyewa Yasa aje adauka Anya kuwa mutum ne dayan yafada cike da nuna damuwa akan haka....

Babban nasu yace Mutum ne mana Ku daina damun kan Ku tunda dai yana biyan kowa to meye matsalar Ku ....
Hakadai sukaci gaba da amsa sakonnin jan ZAKI

Jan ZAKI yana musu bayani akan Babban hospital da yake son abude agarin Funtua cikin gari Asai Filin cikin gaggawa Awa Ashirin da hudu ya basu
Su kai masa takardun inda suke aje masa Sako yagani ya tabbatar da komai kuma yasa hannu akai...
Sannan Asibitin Wata biyu kacal yake son agama ginin Katafaren Asibiti mai Suna hospital jan ZAKI.....
Sossai suka shiga shirin aiwatar da Abunda Yasa su........

**************************



Wayyo Mama yanzu fa Na kwanta cike da shagwaba yake magana...
Sake da Baki take kallon sa tace haba Aliyu saika kulle kanka adaki kai kadai ..
Ko abincin rana bakaci ba..
Yamutsa fuska yayi yace oh Mama wai ......
Katse shi tayi tana Fadin please Dana tashi Kaci abincin nan so kake inshiga damuwa ne tafada cike da nuna raunin ta...

Dago jajayen idanun sa Masu kwarjini yayi yasauke su akan ta...
Cikin kwantar da Murya yace yi hakuri Mama.
Na tashi tunda haka kike so...
Kama hannun nata yayi cikin nasa ahaka har suka karaso falo suka zauna diner table ...
Plate din Abincin ta jawo gaban sa tana diban abincin cikin spoon tana bashi abaki...

Kwabe fuska yayi yana cin Abinci kamar yana tauna magani.
Kadan yaci cikin Muryan shagwaba yace Mama jibi cikina nakoshi ...

Murmushi tayi tace kokaifa duk da bamai yawa Kaci ba Amma ka rage mun damuwa....

Nusaiba ce ta iso Falon cike da kulawa take kallon Aliyu dake shan lemun kwali ...

Inawuni Yaya ta Furta tareda neman waje ta zauna tana masa kallon Kirilla...
Murmushi Mama ta sakar Mata tace yata kinga sai yanzu yafito danma nice Na fiddo shi dole barci ze koma.

Nusaiba zare idanu tayi tace haba Yaya sai kayita. Fama da computer 24hrs in rasa me kake shukawa .
Duk maganar da take kamar besan da ita..
Kallo daya yayi Mata yadauke idanun sa....

Yace yawwa kishirya bayan laasar zamu fita yakarashe zancen tareda barin Falon...

Wani uban tsalle Nusaiba tayi ta rungume Mama ta baya...

Mama kinajin wai tare zamu fita ..
Murmushi Mama tayi tace ke yar gata ce...
Yau dai nasan malamin naku me koyar dake Addini baze Zo ba ko..

Tabe baki tayi tace haba Mama ace mishi naje inga gari inbanda Makarantar boko babu indan kafafuna yake takawa yau babban rana ce awajena..

Mama tace Adawo lafiya nusy ta tana kokarin tattare kwanukan da suka ci Abinci .
Cikin hanzari Nusy ta Amshe hannun Mama takai kitchen bata tsaya Wata Wata ba...
Kai tsaye dakin nata taje daukan wanka dan tasan shi be jira ze iya wuce wa yabarta...

Koda Akayi Sallah Laasar fita yayi yakai kusan Awa daya sannan yadawo cikin dan saurin sa...

Kai tsaye dakin sa yanufa yakara daukar wanka tareda saka kanunan kayan sa...
Chemis da bakin wando jeans sossai shigar ta Amshe shi glass din sa ya saka yazo gaban mirror yana taje sumar kansa ..

Babu bata lokaci yadau abun bukatar sa yasauko ahankali yake taka matakalan step cike da nutsuwa ahankalin Sam yatafi awani tunani Na daban...

Koda ya iso Falon iske Nusaiba yayi harta shirya shi take jira dan harga Allah yama mance da ita zefita...

Kallon ta yake yace kekuma Ina zakije ne har da yafa gyale..

Sakaka sake da Baki take kallon sa tace Yaya kaine kace inshirya fa kuma yanzu kazo kana mun tambaya..

Dafe kansa yayi yace oh am sorry na mance ne muje ko yafada cike da kulawa......
Gaba tayi shiko kai tsaye sashin Mama ya nufa dan yi Mata sallama..

Koda ya isa kayataccen dakin Wanda ya tsaru iya tsaruwa kallo daya zaka yiwa dakin kasan an narka dukiya awajen musamman gadon da Mama ke zaune kai......
Wani ado irin Na lu'ulu ne kai kace da zinariya akai kayan cikin dakin har tsif din ta..
Lumshe idanun sa yayi sakamakon wani sirritance kamshi daya doki hancin sa.....

Ganin shigowarsa Mama ta fadada Murmushin ta ..
Tace Dana har kafito ko...
Gyada mata kai yayi cike da kulawa hade da zallan shagwaba yace eh nafito kuma Sauri nake...

Saidai kwana biyun nan akwai aikin gaggawa daya taso mun kuma kullum Zan ringa fita Banda Asabar da lahadi...
Kallon agogon tsintsiyar hannun sa yayi yace mun tafi sai mun dawo ki mana adua .

Allah yakareku ta furta tana Murmushin dole...
Kuma Allah yataimake ka akan aikin da baa son insan Kona menene ta Fada cike da son tsokano shi ...


Murmushi yayi yafice yana girgiza kai koda yafito iske Nusaiba yayi duk ta kumbura kadan ya rage ta fashe dan takaicin barin ta da yayi ya Dade dakin Mama.

Nuna rashin damuwa da halin da take ciki yayi kai tsaye yayi hanyar fita ita kuwa cikin hanzarin ta .
Ta take masa baya......


**************************



Najwa da Khairi ahanyar su ta dawo gida daga Makarantar suka hadu da Sultana yayar Khairi kasantuwa tana auren wani dan kasuwa kuma gidan nata kan titi yake yasa basu wuce gida kai tsaye ba....

Suka bita gidan ta anan ne suka bata lokaci sossai..
Dan Sultana takira baffa ta gaya masa suna gidan ta agayawa Maman Najwa karta tada hankalin ta...

Baffa yace babu matsala tunda gida ne sai sun dawo din.


Khairi tabe baki tayi tana sauraren redio da Mijin Sultana ya kunna .....
Inda suka sanya voice din jawaban Jan ZAKI akan harkan kasuwanci da siyasa yake magana da yanda za'a kawo zaman lafiya acikin Al'umma

Sossai mijin Sultana ya maida hankalin sa yana jinjina kalaman Jan zakin..

Kallon Sultana yayi yace da ana samun matasa masu fadin gaskiya irin sa da anzauna lafiya da kuma an rage yawan talauci...

Yaron nan fa shekarun sa 25 kacal aduniya Amma yana ilimin da wayanda sukayi jika dashi basu dashi......
Murmushi Sultana tayi tana kallon Khairi da ta nutsu wajen sauraron redio tace....

My sister kema kinfara jin dadin jawaban dan ZAKI ne......
Duk ranar litinin karfe uku ake Sako voice din sa kiringa amsar Redio baffa kina saurare ZAKI Karu sossai..

Tabe baki tayi tace ina dadi awajen Wanda keda baki cakwai inkika bibiya maganar fatar baki ce.....

Sossai suka Dara har Mijin Sultana da Sultana da Najwa.......

Mijin Sultana yace KANWATA jan ZAKI da kike gani yatara yawan magauta saidai abun takaici shine har yanzu babu Wanda ya taba ganin fuskar sa....

Khairi karo na Farko da ta dago kai tana kallon Redio tace a ina suke samun sa suyi magana dashi??

Mijin Sultana Isma'il Yace
KANWATA an Dade ana saka voice din sa gidan Redio yanda labari yazo daga majiya mai karfi sunce turo voice din sa yakeyi ta account din sa Na Instagram da Facebook...

Khairi da Najwa suka hada baki wajen fadin ikon Allah ...

Nidai kam da Wata mai kudi ce Dana bayyana ma duniya fuskar sa mutum saikace mara gaskiya cewar khairi tana turo Baki....

Sultana tace waya sani ko haka dinne Amma kuma an shede shi da taimakon Alumma gidan marayu dari garesa a Nigeria shike daukan nauyin su in kin gansu wlh zaki dauka gaban iyayen su suka taso dan beyarda akai musu wani tallafi ba...

Jinjina kai Khairi sukayi itada Najwa..
Suka hada baki wajen Fadin Allah yataimaka.

Tashi sukayi cikin sakin Fuska Najwa tace to Antin mu zamu je gida....

Murmushi Sultana tayi tace haba khairi keda Najwa kubari in gama girki mana.....
Jin Abunda suke fade Yasa Ismail fadin kinga Sauri suke maza ki Diba musu duka Abunda kikasan ze isheshu dafa irin girkin da kike yi ki basu..
Dan nasan kannena din nan uhmm yan rigima ne.....
Dukan su dariya suka sa...
Khairi Tace Aa yaya Na yafe Na yau wlh be raina kaima kasan da muna bukata in zata kai nan da isha'i bata gama ba zamu jira ta, ta fadi zancen da shakiyan ci....

Dukan su dariya suka sa..
Sultana dambun nama ta dauko ta cika musu Leda dashi tace to gashi nasan bakin nan naku Yasa ba da ciye ciye....
Cike da murna suka karba suna godiya

Sossai Isma'il yake son yawan jin Muryan khairi duk da kanwar Matar sa ce...
Amma yana hango wani sirritance Abu a tattare da ita shiyasa take kara shiga ransa yake Mata so Na tsakani da Allah kamar kanwar sa uwa daya uba daya .

Har bakin gate suka rakosu tareda musu bye bye....

Najwa kallon Khairi take da duk yanayin ta ya canza lokaci daya tunda akayi firan Jan ZAKI babu Abunda ya burge ta illa maganar marayu da akace yadau nauyin su fiyeda gidaje dari....


Daidai satin kan titi Najwa ta waigo tana kallon Khairi dake tsaye ta Lula duniyar tunani..

Keeee ta Furta da karfi sakamakon ganin wani mota kiris yayo kanta .....
Aguje taje ta Ture ta tafadi kan wasu dutsina yayi daidai da fakin wannan motocin da suka jeru..

Itakuwa Najwa cikin kuka tace azzalumai Zaku kashe min yar uwata ne kuma takama da Arziki takarashe zancen tana mai kokarin daga Khairi.

Daya daga cikin jerin motar yafito ransa abace yace haba baiwar Allah kune da laifi Amma kune da Zagi ....
Kanya gama rufe bakin sa....

Khairi dake jin jikin azababen Faduwar da tayi tamike cikin karfin Hali ta wanka masa mari ji kake tass...

Azabure dukan su wayanda ke cikin motar suka fara fiffitowa
Harda ogan nasu cikin....................


*Karku Manta Paid book ne.*
*Please in free yakare Na roke Ku karku fitar min da littafi masu son cigaban daga free yakare su shiga Arewa book din karatun ..*


*Taku har kullum kyauta daga Allah*
🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜

*JAN ZAKI*🐆





*DAGA MARUBUCIYAR :*


*KAIKAJAWA KANKA*


*KANWATA*


*RAYUWAR MA'AURATA*


Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI*



*Paid book ne*


Normal group 500


Special group 1k


Acct nomba

*3115484026 ikilima Adam first bank*

Ko Katin MTN

Kan wanna layin

09069080725

Banason VTU





0️⃣6️⃣




Idanun ta ya yi tozali da kafafun dake saukowa daga cikin Motar , kokarin Tashi sukeyi itada Najwa dan akan Juna suka Fad'i.

Sukaji Muryan sa yana Fad'in Ku yayan matsiyata ,Banda dabbanci irin naku titin na uban Ku ne Zaku ringa tsayawa.
Kuna shashanci?

Najwa da Khairi cikin tsananin Tashin hankali suke kallon sa yake doso inda suke cikin zafin nama tareda rufe motar nasa.

Cikin Isa da tafiyar takama yakaraso wajen.
Wani kallon mai cike da mugun tsana yake bin su dashi ,tareda maida kallon sa akan Khairi Idanun su suka tsarke cikin Juna , hada rai ya yi tamau fuskar sa tamau babu Annuri bare su sa ran tausayi a tattare dashi .
Tsawar daya dakawa Khairi ne ,yasa ta razana had'e da zazzare manyan idanun ta mai dauke da digon baki a aciki.

"keeee! ballagaza tun daga nesa kan titi na hango ki bayan nawuce Ku shine nayi reverse na dawo, cire gilashin dake Fuskar sa ya yi .
Dan su gane waye a gaban su.

Khairi da Najwa suka hada baki wajen Fadi kaine ?

Kwarai kuwa nine yabata amsa ,ai bazaki manta ni ba karuwa tunda hannun ki ya mari fuska ta.
Aranar kinci sa'ar mai gidan mu da wallahi bazaki kara gigicin mari wani ba .

Kan ubancen Khairi ta Furta tareda tashi tsaye tana jijjiga cikin ruwan bala'i tace watau sai yanzu na gane ka, kace kazo ka rama Marin danai maka ne raggon namiji dakai nusari yau ka tabbatar mun dakai sakarai ne.
Inace ......Najwa ta rufe mata baki cikin tsananin tsoro dan yanda taga idanun sa sun kada tasan kiris yake jira ya yi kasa-kasa da Khairi.
A hasale Khairi ta buge hannun Najwa daya rufe mata baki tana huci sama-sama kamar zakanya tace waike Najwa akan wannan banzan zaki rufe mun baki.
Sake hada rai tayi tacigaba da Fad'in Abunda take niyar fada.
Inace agaban ayarin ka na mareka ,ai kamata ya yi inzaka rama ka rama agaban su , dan su sheda Amma kazo kai kadai kenan ,kana tada kura bayan yaki .
Dan Allah Malam matsa kabamu waje ,nazata wani isasshe ne ,ni wallahi kamun kadan a fada uban gidan naka Wanda ya zageni ,shi kawai nake nema wallahi dan beci abanza ba...

Mutuwar tsaye Anas ya yi idanun sa sun kad'a jajir kokarin kaiwa Khairi ,naushi yake ,kafun hannun sa yakai kanta ,ji ya yi caraf ta kama hannun sa ,be Ankara ba sai jiyayi ta wanke sa da Wasu lafiyayyun Maruka Masu hasarin gaske .
Nan take yaji cen kasan kunnen sa jin sa ya dauke .
Arazane yake kallon ta dan ya tabbatar da gaske ita din ce , ganin yanda ta canza kamar ba mace ba tana kokarin Murda masa hannun sa data rike .

Yaji Najwa Na Fad'in dan Girman Allah Khairi karki Aikata kefa kika ce kin daina ,inkikayi haka kin saba Alkawari narokeki dan Girman manzon Allah , Albarkacin maman mu dake kwance kasa.
Sossai jikin ta yadau rawa ,
Idanun Khairi ne suka kawo ruwa nan da nan ta saki hannun nasa daya gama masa sanyi duk yanda yaso ya kwace ya kasa.

Tana sakin sa
Hannun nasa yake bi da kallo yanda yasha damka ,kallon ta yake tana kakkabe kasar daya bata musu jiki itada Yar Uwar ta .
Jiyayi Khairi na fadin wallahi da kin barni da shi dayau yazama nakasasshe tareda kama hannun Najwa zasu bar wajen .
Har sun kama hanya zasu wuce shi .

Khairi tayi return ganin tahowan ta yasa shi yafara Neman hanyar guduwa zuwa motar sa.

Dakata ta Furta a tsawace hakan yasa ya tsaya cak batareda ya waigo ba.

Inason ka gayamin inane Zan samu uban gidan naka dan wlh saina Rama Abunda yamun ko ana ha maza ha mata, kuma wallahi baka ban amsa ba baka isa kabar wajen nan ba in kace karya ne bismillahi tai masa nuni da hannu.

Batareda ya kalle ta ba yace ni kaina bansan daga inda yake fitowa ba ma'ana bansan gidan nasu ba Amma kamar naji yace a Makabarta ne .

Zazzare idanu Khairi da Najwa sukayi suna buga Salati , Khairi sossai jikin ta yadau rawa cikin tattaro nutsuwar ta tace karka raina mana hankali kasan me ake kira da Makabarta ta kuwa ?

Shiko ya kosa ya bar wajen dan Marin datayi masa yasa kansa na tsananin ciwo kamar zata tsage dan radad'i.

Eh nasani shine Amsar daya bata yana k'ok'arin shiga motarsa ,tsintar Muryan ta ya yi tana Fad'in in ma ka boye mun ai zamu hadu ne .
Ka gayamin da wani lokaci yake bin wannan titin.

Cikin Muryan sa mai cike da takaici yace Sau daya yake bin wannan titin kuma duk karshen Wata ne .
Bejira cewar ta ba yashige mota ,be tsaya Wata-Wata ba yatada motar tareda barin unguwar cikin zalama direct hospital Jan ZAKI ya nufa .

Tuki yake hankalin sa atashe , dan tunda yake arayuwar sa be taba cin karo da Yarinyar mai tsaurin Ido kamar ta.
Tafiya yake Amma yana tunanin hanyar ramuwa dan wannan RAI DAYA bazata gagare shi daukar fansa ba .


Khairi da Najwa nan da nan suka bar wajen tareda zuwa sola suka dibo ruwa a jarka koda suka isa gidan su Najwa basu ,bata lokaci ba suka bar gidan.

Mommy ta dan so tagane akwai damuwa tattare dasu kasantuwa , khairi bata ba ta damar tayi musu tambaya ba. Ce Mata sukayi,Sultana ce tace suzo su tayata Aiki.
Sunsan Mommy bata iya hanawa , Adawo lafiya ta Furta tareda bin

3 / 13