Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RAI DAYA Inkiya JAN ZAKI by Ikilima Adam

Author :  Ikilima Adam Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 13

30K to 33K   out of 36.3K words

tana nan haryanzu.

Eh tana nan haryanzu mana tabashi amsa tace kai nake sauraro ?

Shiru yayi kamar me nazarin wani Abu yace ki shirya karfe goma , inason kidawo gida kafun ayi sallah juma'a zanyi wa drever magana da zaran kinshirya..
Cikeda Murna tace Allah yamaka Albarka Dana .
Tashi yayi dan agajiye yake yace zamu shiga daga ciki Mamy dan Allah banson akawo abinci har sai na tashi daga barci .
.cikin gamsuwa da hakan tace babu matsala , sossai yake Lura da Nusaiba yanda ta rame dan kwana biyun nan yanason yazauna da ita yaji damuwar ta ,Amma kuma yau gajiya ta masa yawa.
Dan zuwa dare zekoma cen gidan su khairi .

Yana ficewa yabar Salim akun sa,sauka daga kan kafadar sa yayi yadawo kan Mamy yace .
Mamy Aliyu fa yana fama da Ciwon zuciya

Daga Mamy Har Salim da Nusaiba zazzare idanu ,suka soma yi .
Kallon akun tayi tace ya Akai kasan da haka.

Shiru yayi yana kalle kalle kada Aliyu yafito yaji Abunda yake fade .
Mamy nima waya naji yanayi yana fadin in yatafi Amerika zega likitan sa .

Innalillahi wa'innalairajun sukayi ta maimaita wa .
Mamy ta fashe da kuka tace haba Aliyu ina uwarka har kanada sirrin dazaka boye mun.

In wani Abu yasameka bazan gafartawa kaina ba .
Aliyu Banda Miji Amma ka zamemin garkuwa .
Salim da idanun sa yaciko da kwalla yace Mamy meye mafita ne .
Tunda nake dashi ban taba ganin yasha magani ba hakan yana nuni da be damu da lafiyar sa ba.
Amma kibari yau yana fita Zan binciki dakin sa ,inhar akwai maganin dayake Sha Zan dauko in nuna miki muyi masa yan dabaru daze ringa Sha.

Mamy cikin gamsuwa da bayanan sa , tace dan Allah kayi kokarin haka .
Nikam bazan nuna masa nasan komai ba , harsai kadubo mun shedar da Zan kamashi da hujja.


Kashe gari.


Babban rana ce mai cike da dumbun tarihi arayuwar Baffa wacce beso tazo masa ahaka.
Sossai Gidan Baffa yacika da dumbun jamaa ana ta girke girke dangin mummy duk sun Zo.

Sultana kuwa tazo da makwafta ta harda kawaye.
Sossai cikin gidan ake ta hada hadan , Dora girki .

Akramakallahu tun safe yatafi Makaranta sai kusan karfe daya yadawo gida inda yaci karo da Baffa da Saifudeen ahanya.
Cike da mamaki yake kallon su kana ganin su kasan basa cikin hayyacin su.
Baffa yace yawwa gashi nan ya iso

Karasowa sukayi kusa dashi tareda kama masa hannu shida Saifudeen suka jashi gefe daya.

Cike da Mamaki yake kallon su ,sai ganin Baffa yayi yana zubda hawaye Masu zafi daga cikin zuciyar shi.

Yace Akramakallahu dan Girman Allah da kaunar ka da manzon Allah .
Kataimake mu , dan Allah kashiga gasar nan ,mun San kana shiga zakaci dan kacewa Saifudeen ka iya buga kwallon kafa.

Cikin tsananin Tashin hankali Akramakallahu ke kallon su yace me kuke nufi idan Har nashiga gasar .
Saifudeen yace inason abuga kwallo kafa dakai na auren Khairi wlh nasan zakaci tunda yan garin nan bawani iyawa sukayi ba , durkushewa kasa yayi tareda rike kafafun sa ,yace koba dan ni ba ,kayi dan Baffa da baya barcin kirki .
Dago Saifudeen yayi yace kuna nufin inhar naci Gasar aura min khairi za'ayi aini ban shirya aure ba , Banda sadaki.

Baffa yace wallahi inada shi Zan baka , banason khairi ta samu mijin banza a wannan gasar ba Abunda ba mijin kirki ake samu ba .

In andaura ko zuwa dare ne , kana iya sakin ta .
Kaga dai burina yacika kuma Gasar baza'a maimaita shi ba sai wani shekara.
Ajiyar zuciya mai karfi Akramakallahu yasauke yace na amince Baffa karka damu zanshiga Gasar nan kodan in taimake ka.
Tunda Kuma Kun taimaka min.
Fuskar su , cike da faraa baffa yace Allah Yasa kagama da duniya lafiya nagode InshAllah zakayi nasara arayuwar ka.

Sossai yaji dadin kalaman sa , cike da Jin dadi yace muje ko .

**********************

Drever ne yashigo da Mamy cikin unguwar yan bokolo inda ta iske dukan garin duk ya hargitse ana ta saurin za'a je gasa bayan an idar da sallah juma'a.

Mai gari duk kowa ya isa Filin gasar .

Itakuwa Mamy sauka tayi daga cikin Motar tana sanye cikin doguwar Riga ba , fuskar ta dauke da Nikaf tafiya take cikin hanzarin ta .
Harta karaso daidai inda ake wannan Gasar rasa wanda zatayiwa tambaya tayi kasantuwa kowa hankalin nakan wasan da za'a fara.


Khairi cikin shigar ta , na Alfarma Mummy ta shirya ta , tsaf tareda yi Mata makeup sossai tayi kyau tana baza kamshi.
Yadiko na zaune gefen ta. Tace oh khairi ko waye angon namu da zamu aura ne.

Murmushi kwance akan Fuskar khairi tace ina Zan sani kibari su dawo su bamu labari ko.
Sultana dake tausayin kanwar ta , tace eh lallai Khairi kin girma murna ma kike .
Shiru khairi tayi tace Afuwan antina.
Sultana tace bakomai tareda
Daukar wayar ta , tayi tareda daukan ta Selfi tayi musu itada Najwa .
Yadiko ma tace da ita za'a dau hoton .
Dole yasa Sultana daukar ta hoto tareda Amarya .

Sultana tace khairi zaki ajiye Makarantar ne tunda zaki daura aure.
Zazzare idanu khairi tayi tace A'a bazan daina ba .

Kullum sai mun tafi ko Sultana tana mai Kallon ta.
Sultana da duk jikin ta yake a mace tace hakane InshAllah indai muna kusa.

********************

Saifudeen kayan kwallo yaba Akramakallahu yasa ajikin sa.
Suka rakasa wajen gasar daman anyi na sauran na Khairi kadai yarage .
Jiran isowar Akramakallahu yasa kowa yayi cirko cirko yana kallon ta inda zefito.

Gabakidaya wajen yadauki shewa yayinda yashigo Filin gasar hakan yasa ,mai gabatarwa yace ga dayan ya iso maza ku matsa baya abada fili ayi agama muje massalaci wajen daurin aure .

Mamy cikin zazzare idanu tace wannan kamar Aliyu kokarin shiga taron take , Masu tsaron wajen sukace baiwar Allah Ina zakije ne ?
Mata basa zuwa wajen dan Allah koma baya yanzu za'a gama ,idan angama kina iya ganin Wanda kike nema.
Komawa da baya tayi tana zazzare idanu ,soma kiran sunan sa tayi tana Aliyu Amma ina bayajin ta.

Dan hankalin yayi yayi nisa akan kwallon da suke bugawa.

Baffa da Saifudeen da Malam Adamu da wasu jamaa sai adua suke Allah yaba Akramakallahu nasara.

Ganin wasan yayi nisa babu Wanda ya jefa ball cikin raga yasa hankalin baffa yatashi.
Kokan su rufe baki sukaga ansaka ball din cikin raga wani ihu jama'ar wajen suka dauka suna Fadin .

J A Akramakallahu yaci gasar auren Ummulkhairi.
Cikin Razani Mamy take kallon andaga Aliyu Jan zaki sama .
Bakin ta na rawa tana kokarin karasowa wajen sa.

Taji an rike mata hannu a razane ta juyo tayi tozali da.............



Taku Har kullum kyauta daga Allah
*RAI DAYA* 🦜

*JAN ZAKI*🐆



*Saura page daya ingama free page Ku hanzarta kada ayi tafiyar babu ku*

*Paid book*

Domin karin bayani Ku tuntubi akan wannan number

09069080725


Akwai Group Dina Facebook mai suna .
( Kyauta daga Allah novel's)
Kuyi following Dina.





1️⃣4️⃣



Kamar dangin Margayya Amina , Baffa yace sune kam harda Mahaifin ta.
Sake da baki suke kallon su Har suka rufe motar su.
Kowannen na sanye cikin babban gezner milk color fuskokin su sanye da gilashi.
Wani kallo suke bin unguwar da dashi suna yatsine fuska , sannan suka dawo da kallon su akan gidan Baffa tareda Jan dokon tsuki.

Alhaji Abdul Aziz cikin bacin rai yace ace shekara da shekaru gida yana nan ayanda yake babu sauyi Allah ya wadaran naka ya lalace .

Daga Baffa Har Malam Adamu kallon sa ,suke ganin sun karaso wajen nasu yasa Baffa yin Murmushin yake yace ranka yadade yau kune agarin namu .

Bismillah yace yana mai nuna musu gidan.

Kwabe baki sukayi dukan su , sukace ina gidan yake da zamu shiga nan ma , ya isa cewar Alhaji Abdul Aziz.

Baffa yace Bismillah ina sauraren Ku ?
Alhaji Abdul Aziz yace kasan dai Abunda yakawo mu , be wuce na Yaya , Ummulkhairi muke son dauka tareda Saifudeen ita zamu sanyan ta a Makaranta.
Shikuma waje zefita taredani kan harkan kasuwanci na.
Wannan shi yakawo mu , dan haka kashiga ka fito mana da Ummulkhairi Akira Saifudeen .

Sannan Ita Sultana a nuna mana gidan Mijin nata ,mu biya muga lafiyar ta.

Tunda yafara magana Baffa dukar dakai yayi kasa yana kukan zuci.
Jin yayi shiru ne yasa shi Fadin , Agaskiyar magana bazan taba baku yata ko Dana ba.

Saidai kuyi hakuri dan yaran suna dauke da jinina ,bazeyu Ku dauke su ba.
Malam Adamu yace gaskiya ne bayin Allah , gaskiya bazamu iya baku yaya ba.

Cikin tsananin bacin Rai Alhaji Abdul Aziz ke magana shida kannen sa.
Suka ce karfa Ku raina mana wayau dan kunga muna lallaba Ku .
To wallahi idan baku bada su ta lalama ba ,Zaku bayar ta tsiya.

Fitowar khairi yasa su , hankalin su yakoma kanta tana sanye cikin Wata Riga da zani kodaddiyar Atamfa .
Karaso gaban Baffa tayi tace Baffa na lafiya na gansu cikin Tsananin Tashin hankali.

Baffa yace Khairi kiji bayin Allah nan dangin Mahaifiyar ki ,nasan kin gane su ,wai sunzo su tafi dake.

Kan ubancen Khairi ta Furta tareda fuskantar kakan nata tace , wallahi babu inda zanje , meye hadani daku ,takamar Ku Arziki ,mu kuma takamar mu Allah.

Alhaji Abdul Aziz yace Haba Ummulkhairi nifa Na haifi uwar ki Amma kike fada mana haka , nan fa kakannin ki ne.

Khairi cikin kwabe baki tace Ai uwata kuka haifa bani ba.
Kuma data haifeni anan gidan ta haifan , kuma anan aka raineni nidai bazan taba binku ba takarashe zancen tana mai kama hannun Baffa da Malam Adamu tace muje ko .

Duk Abunda akeyi akan kunne Innaro dan ta labe zaure tana saurare.
Motar su take bi da kallo tace ikon Allah kenan , Mahaifiyar Amina iyayen ta , Masu Arziki ne.

Ganin khairi sunfice tareda Malam Adamu , sunbar bakin nan tsaye yasa ta fito Sadaf Sadaf
Ganin suna shirin shiga motar su , cikin bacin rai .

Ku dakata Bayin Allah tafada tana mai karasowa wajen su .

Kallon ta suke harta karaso , cike da ladabi ta gaishe su ta sanar musu matsayin ta awajen khairi.

In bazaku damu ba , zanyi iya kokarina inga na kawo muku khairi Har gida tareda Saifudeen Amma Ku gayamun me Zan samu idan nayi haka.

Wani uban kallo suke jifan ta dashi dukan su , Alhaji Abdul Aziz yace matsiyaciya mayun kudi ,kotu ce zata karban mun su bake ba.

Cikin kannensa wani yace please kabari muyi yanda tace mana , nasan ko dubu hamsin ka bata zance yakare.
Kallon Innaro sukayi da tayi sake da baki yace , bamu lambar wayar ki ,in bukatan haka yataso Zan kira ki.

Cike da Murna Ta karanto masa number ta ,tareda tsayawa tana jiran me zasu ce , ganin taki wucewa ne yasa Musa daukan dubu Biyar daga Aljihun rigar sa yabata , cike da murna ta karba tana farin ciki.

Ganin suna shirin tada mota tace wallahi Khairi bataci tana koshi gidan nan , meze hana kodan taliya Ku bada kudi asiye aringa dafa mata kafun , Allah yadawo muku da ita.

Alhaji Abdul Aziz akaro na biyu kenan daya kalle ta , tareda nazarin kalaman ta , Gefen sa ya kalla ya zaro bandir din kudi ,Wanda akallah zasu kai Dubu dari yace Amshi wannan kudin duk kayan abinci da kika San anaci kisiya ki ajiye , kije gidan Gona kisai kaji guda goma ayanka mata , sauran kudin su Juice da kayan abinci dafatan kin gane ko.
Gyada masa kai tayi alamun gamsuwa hakan yasa , taringa musu adua Allah yatsare cike da Jin dadi .
Kasa komawa gida tayi harsai da taga tafiyar su , sannan ta daka uban tsalle tayi cikin gida .

Zazzare idanu tasoma tace laaa yau nice da bandir din kudi na dubu dari , ga kuma Dubu Biyar cen wayyo dadi.
Tsaki tayi data tuno da Baffa tace ana maganar Arziki wake ta tsiya .


Khairi Har wajen gonar Baffa tajasu suka tafi , dukan su babu Wanda ya musa mata , kallon kasan wajen tayi , tace Baffa ga ramin da aka binne mahaifiyata cen , kullum kana hanani zuwa wajen dan Allah kabarni inje koda Adua ne inmata takarashe zancen cikin raunin Murya.

Daga Baffa Har Malam Adamu Saida kuka ya kwace musu , rungume ta sukayi ,suna fadin haba Yi hakuri Khairin mu , kibari zuwa gaba in kinyi aure mijin ki yaringa wakiltan ki ,kuma adua duk inda kake yana bin mamaci.

Khairi dake kuka tace Baffa , dagaske wancen mutumin da muka bari kofar Gidan ka , shiya haifi mahaifiyata .

Gyada mata kai sukayi tareda bata amsar shine Mahaifin ta .
Sabon kuka ya kwace mata tace Baffa inason ka fiye dasu bansan kowa ba sai kai , dan haka babu mai raba mu nidakai.

Baffa Sha fuskar ta yayi yace Khairi ai nan gaba aure zakiyi Kinga dole kibar gida ki koma gidan mijin ki.
Zazzare idanu khairi tayi tace aure kuma A'a baffa banason jin wanna zancen .
Damar na kawo Ku nan ne saboda naga mutanen cen suna son su tada maka hankali abanza akan Abunda bazeyu ba.


Su Alhaji Abdul Aziz daidai suna kokarin hawa kan titi ya hango Sultana ta fito daga wani gida hannun ta rike da ruwa alamun zata zubar ne .
Cak ya Saida tukin yace dan Allah Ku dubamin wa nake hangowa cen kamar Sultana.

Dukan su suka amsa da itace wallahi.
Tsaki yayi yace wannan matsiyacin ya gama damu wallahi ,kuka ya kwace mishi yace yanzu diyar Amina ce cen take wahala ina hango ta.

Dukan su shiru sukayi suna jin zafin Abunda suka gani.
Kanin sa Musa yace Alhaji kasan me ze faru ne , yace A'a saika fada tunda Kaga gidan Sultana muje kawai zanyi nazari akai , maganar kotu mu ajiye ta agefe saboda Kaga yaran nan sun girma ana iya zaman kotun suce wajen Mahaifin su ,zasu zauna .

Wannan karfi da karfi ne zamu hada wajen cimma burin mu .
Kaban Sati daya inyi tunanin Mafita , ana samun solution komai zezo karshe.
Karma mu tsaya bare ta tsorata da ganin mu.

*********************

Su Baffa suna dawo wa gida yayi daidai da zuwan Akramakallahu , cike da Ladabi ya gaishe da Baffa shida Malam Adamu.

Baffa yace ko kaine bakon da Saifudeen yace mun , kuna kwana tare .
Bashi Amsa yayi da shine .
Malam Adamu cikin Sauri yace Baffa bara inje cen cikin gari indawo daga haka yafice .
Baffa na masa Allah yatsare ya Amsa da Ameen.

Khairi da tun zuwan Akramakallahu idanun ta ke akan sa tace sannu da zuwa Akramakallahu . I
Kasamu labarin ansauke headmaster ansaka sabo.
Cikin mamaki yake zazzare mata idanu yace dagaske kuwa KANWATA?

Eh wallahi dazun Kawar Ajin mu keban labari Kaga gobe dani za'a je Makarantar InshAllah.

Murmushi yayi saida kuncin sa ya lotsa yace Allah yakaimu khairi.

Baffa ne ya kalle sa yace Amshi makullin dakin naku ko ,maza kaje kayi wanka kahuta .
Nasan ka kwaso rana .
Godiya yayiwa Baffa hakan yasa yashige daga cikin gidan.

Itakuwa Khairi kai tsaye gidan Su Najwa ta nufa.
Tana isa gidan ta iske ta zaune tana tankaden garin tuwo , mummy bata nan.

Samun wuri tayi tazauna kusa da ita fuskar ta cike da Annuri , Najwa tace Khairi ai mungode wa Allah da zamu koma makaranta wannan dan iskan yaso ya datse mana.
Jin Khairi tayi shiru ne Alamun tayi zurfi a tunani tace keee khairi lafiya me kike tunani ne.
Bakomai ta bata amsa .
.
Wallahi Najwa inajin wani bakon Al'amari a tattare dani .
Najwa tace kamar me kenan yar uwa gayamin tana fuskantar ta.

Yau kwana uku kenan Dana soma jin ina shaawan wani Abu Amma haryanzu ban tabbatar da komene ba .

Murmushi Najwa tayi tace kila yanayin Rayuwa ne.
Bara indauko mana redio mana .
Tana kunnawa yayi daidai da ansaka fadakarwar JAN ZAKI.

Tsuki Khairi tayi duk da tanajin dadin haka tace su kullum suke saka bayanan sa ne.

Najwa tace inaga maimaici ne tunda magana yake Amma illan cin Amana da zanba cikin aminci .
Kasa kunne sukayi suna sauraro.
Khairi Tace kinsan me wallahi Muryan Jan zaki yana mun kama da Muryan Dana tabaki ji a kunne na .

Najwa tace nima haka nake yawan tunani Amma aikin San ana kamanni a murya .
Cigaba da sauraren Redio sukayi.

Jin Muryan Innaro tana kwada mata kira ne yasata amsa mata tareda tashi tace Najwa bara inje inga Me matar nan take so ne.

Gyada mata kai tayi tareda fadin saikin dawo tawan.
Khairi na isa gida iske Innaro tayi rike da kwanun abincin data zubawa maganin karshe tace , zonan yata yau fa baki wani ci Abinci ba.

Samun wuri Khairi tayi tazauna tace wallahi kamar kinsan yunwa ne fal aciki na.

Innaro shiga daki tayi wayar ta na ring .
Itakuwa Khairi abinci ta soma ci , cikin hanzarin dan yau basu karya da abun kirki ba.

Innaro waya take da Kawar ta Tana bata labarin dangin uwar khairi.

Kawarta tace gaskiya Safara'u ke Shu'uma ce ta karshe .
Innaro tace kedai bari angayamiki ana wasa da Masu gidan rana ne.

Dagacen bangaren tace Kinga maganar kiyiwa khairi Asiri dan tabar gidan be taso ba.
In ma baki bata na karshe ba to karki bata ai hanya ce ta samun kudi tazo miki .
Kiyi ta tasar dangin ta Masu Arziki nan ,kan kice me kema kinzama hajiya..
Salati Innaro ta dauka tace wallahi nabata abincin karshen inazuwa tafada tareda katse wayar koda tafito aguje ,iske Khairi tayi harta gama cin abincin ruwa take Sha.
Bakin ta na rawa tace khairi Har kin cinye ne .

Cike da mamaki khairi ke kallon ta , tace ai cemin kikayi Nawa ne lafiya kuwa ta tambaya cikin son jin zancen?

Cikin Tashin hankali Innaro tace ai nayi tunanin tare zamu ci ne .
Bakomai anjima zanje gidan mu ,insaida wani Abu na cikin kayana inyo mana cefanen kayan abinci .

Khairi Tace ai Baffa yace babu kyau mutum ya dauki abun amfanin sa ya siyar .
Innaro tace karki damu sonake mu ma , mu soma cin dadi kamar kowa Har nama Zan ringa soya mana na kaji.

Khairi cike da Jin dadi tace wayyo Dadi !

Akramakallahu fa yazo cewar khairi ya kamata akai masa abinci .
Innaro tace ayya bansani bara indauko Wanda na rage kije ki kai Masa.

Komawa dakin tayi zuciyar ta na kunan abincin da Khairi taci .
Tana nazarin ya zatayi ne , batason khairi ta tafi ?

Akramakallahu zaune shikadai adakin yana waya da Saifudeen akan yayi kewar sa yakamata ace sun dawo gida.
Yaji Sallamar Khairi hannun ta rike da kwanun abinci.

Saifudeen yace kamar Muryan khairi nake ji .

Amsa masa yayi da itace .
Murmushi saifudeen yayi yace kace Amaryan JAN ZAKI

11 / 13