Author : Ikilima Adam Category : African Stories & Novels
ya rungumi Sumayya ba yana murmushi mai sauti ,yata Allah yamiki Albarka yanzu naji zancen ki fadamun Nawa kike bukata na kudi daga millions goma zuwa sama.
A'a Daddy karka damu inada kud'i a acct Dina dazaran sun kare Zan maka magana.
Mummy ce ta iso Falon ta iske yanda suke magana cike da nishadi .
Tace Wai me kuke tattaunawa ne haka ne.
Daddy ne yakatse ta da Fad'in muna hira ne tsakanin uba da 'yar sa dan haka banson gulma yafada tareda fita daga Falon domin zuwa aikin sa.
Itakuwa Sumayya kallon mummy tayi tace bawani Abu bane ke kinsan Daddy beda burin daya wuce ya gano wanene Jan ZAKI , ni zanshige insamu inyi wanka takarashe zancen tareda barin Falon tayi sashin ta.
Mummy rike da baki tace oh ni Rahila wannan wace irin sawa kai Aiki ne ,ina ruwan su da damuwa akan Wanda ma besan sunayi ba .
*********
Anas , kwance karin ruwan da aka sa masa yakare ,kwance yake yana mai kokarin bud'e idanun sa ,yaga fuskar Khairi na masa gizo a jikin kanwar sa dake shigowa dakin ,razanannen k'ara ya saki yana Fad'in wayyo Inna gata nan tashigo , arude Inna ta kalli kofar dakin gani Rayya ce kanwar sa ,tace kai Anas bud'e idanun ka ,wannan ai Rayya ce ko mafarki kake ne.
Sannu a hankali ya sake bud'e idanun sa yaga lallai Rayya ce ahankali ya fara sauke ajiyar zuciya.
Rayya datayi mutuwar tsaye tace Yaya lafiya kuwa kake ihu dan ka ganni .
Kallon Inna ya yi yace yakamata ace mun tafi gida nikam na samu ,sauki nan da kwana uku muna Aiki babba .
Sallamar babban manager na Asibitin ne yasa su maida kallon su akan sa.
Gaishe su yayi cike da ladabi yana sanye cikin fararen kaya nasu na likitoci.
Kallon Anas ya yi yace Shugaban wannan Asibitin yaturo Sako ta email yace yana maka yajiki Allah yakara sauki .
Sannan yasa adauko million 5 abaka kudin jinya ,kuma gasu nan a hannuna Mika masa ya yi ,cike da mutuntawa.
Wani shock sossai Anas yashiga akan wannan kud'in ,cikin mamaki yace ya Akai JAN ZAKI yasan Banda lafiya ,shida baa ganin sa ,bama ganin sa ya akayi yasan da zamana .
Make Kafada manager ya yi yace wannan be zama lallai insan Amsar su ba.
Abu daya nasani shine duk wani ma'aikacin sa yasan da zaman sa ,koka mance kana cikin wayanda suke fita da motocin sa aduk karshen Wata.
Anas yace kwarai muna fita da motocin sa aduk karshen Wata ,tareda ma'aikatar sa , sai dai wani Wanda yake zama cikin mu amatsayin oga wallahi yacika miskillanci ,ta dalilin sa ne wannan abun yafaru dani .
Nan yaba manager labarin komai .
Jinjina Al'amarin Manager ya yi kai Anas shi wannan Shugaban naku ya sunan sa .
Sunan sa Aliyu Shima Jan ZAKI ne yaturo shi badai iko ba ,kuma munyi musan gidan sa ,yace muna a Makabarta ne.
Gabadaya dakin zazzare idanu sukayi , manager jin zancen yafi karfin sa yace Kaga nina tafi , babu dole sai mun San inda Jan ZAKI yake ,tunda yana mana Adalci iyakar mu ,mu rike masa Amana kada mu yarda mu fallasa sirrin sa awani wajen.
Gyada kai Anas ya yi cikin yarda da zancen nasa .
Shiko Manager fita ya yi.
Manager na fita Inna ta dawo da kallon akan Anas tace haba meya kaika fad'a da mace kila ma ba mutum bace dan Allah kafita harkan ta.
Rayya tace kwarai kuwa Yaya wai kai haryanzu baka daina sa'insa da mata ba .
Wani wawan kallo ya yi Mata mai cike da kishiga taitayin ki , maida kallon sa ya yi akan Inna yace InshAllah daga yanzu ban kara bin ta kanta , kuma wannan kud'in Inna ki ajiye awajen ki .
Inna fashewa da kuka tayi tace Anas wallahi Jan ZAKI Alkhairi ne a tattare da rayuwar mu ,shine mutum na farko da yacire mu daga kunci zuwa hasken Rayuwa in kaci Amanar sa bazan taba yafe maka ba.
Anas yace InshAllah hakan bazata faru ba Inna ta .
Likita ne yashigo yaduba jikin nasa yaga dasauki,takardan sallama yabasu ,cike da Jin dajin dad'i suka fara had'a inasu-inasu zasu fice gida.
***********************
Innaro cikin hanzarin ta ,tabar gidan dan taje gun malamin ta ,koda ta iso hanya cin karo tayi da J A da Saifudeen ,ganin su yasa ta canza hanya babu bata lokaci tayi hanyar daze sadata da gidan wannan malamin nata .
Tafiya tayi mai dan tsayi ,kafun tafara waige-waige tana duba lungu da Sako ganin babu me ganin ta yasa kai tsaye tayi cikin gidan nan.
Sallama dauke Abakin ta ,tashiga Malam shehu cikin sakin fuska yace lale da Safara'u sai yau ake ganin ki?
Amsa masa tayi da eh kasan mijina akwai sa'ido wallahi fita ,tana min wuya tunda Na aure shi tareda samun wuri ta zauna .
Hakane gaskiya kibarshi zamuyi maganin sa .
Meke tafe dake yafada yana mai Kallon fuskar ta .
Malam Shehu gaskiya kana mun Aiki yanaci yanda nake so kuma bukata ta ,tana biya sai dai wannan karan sonake wannan kwailan amata aure ,danaso tabi duniya Amma sainayi tunani kada Alhakin ya yi yawa gwamma a samu ko me gyaran takalmi ne ,ya aure ta .
Watau akwai wani gasa da za'ai na kwallon kafa .
Wanda akeyi duk shekara na yan mata Biyar Wanda Allah yaba rabo yaci gasar a kwallon kafa shi za'a Yarinyar farko .
Hakanan za'a wuni buga kwallon nan Har aba duka yan mata Biyar din nan.
Kasan Mijina Baffa baze taba yarda yasaka sunan yarsa ba Khairi dan yace wannan tallan kai ne .
Kuma fadi yake Allah ya tsari zuri'ar da shiga wannan gasar cewar shi ai tallan kai ,saikace an rasa mijin aure .
Dariya Malam shehu yayi yace Safara'u idan harna fahimce ce ,kinason in miki Aiki akan khairi wacce da kanta zata kekashe idanun ta ,tace asaka ta cikin yan mata Biyar da Mai gari yake aurar dasu a shekara.
Kwarai kuwa ,haka nakeso ,inason inhar baffa ya matsa mata akan ta janye ,ta saka masa Kukan wallahi saide ayi rai a mutu .
Karki damu bakida matsala ,wani kwarya yabude agaban tareda had'a ransa yafara karanto adu'oi Masu zafi na lakanin Asiri ,dago kai ya yi ya kalle ta tareda mika mata wani garin magani.
Yace wannan maganin saifa kin kula acikin abincin ta za ki ,saka mata.
Misali yau inkin sa mata taci sai bayan kwana uku ki sake saka Mata.
Duk bayan kwana uku haka za kiyi Kinga kenan nan da kwana tara kingama amfani dashi.
Ki saka idanu kiyi kallo tareda bushewa da dariya wallahi za kiyi mamaki amma fa ki tabbatar taci dan inhar ta tsallake daya bata ci ba Aiki ya lalace.
Innaro tace haba ai hakan baze faru ba ,cike da Jin dad'i ta bashi kud'i tareda barin wajen sa.
****************
Khairi da Najwa suna zaune cikin Ajin nasu inda malamin turancin nasu yake koyar dasu cike bayan yagama musu lecture yanuna yau baze Jima ba yanada uzuri .
Amma hankalin sa yana kan Khairi ,kallon ta ya yi yace Ummulkhairi Sulaiman tashi inason insan ko kina fahimtar karatun da ake koya muku duk da Ku baki ne .
Khairi cike da Jin dad'i tamike tsaye.
Kallon ta yake tareda binda da wani mayataccen kallo ya yi Mata tambaya daya shafi karatun sa.
Zazzare idanu khairi tasoma tareda ciza labban ta .
Sakina dake zaune murmushi tayi ganin yau za'a kure Khairi.
Mamaki ne yakamasu ganin khairi ta bada amsa dai-dai babu tangarda hatta Najwa tacika da mamaki .
Malamin kallo yake yace Amma fa kinyi mugun k'ok'ari , murmushi tayi tana maganar zuci luhmm inbanda Akramakallahu yana gidan mu taya Zan iya .
Afili kuma fad'i tayi inaywan nazarin karatuttukan da ake koya mana ne .
Sakina dafe da kanta tace Kash Amma wannan yarinya abun nata gaba yake inna sake zata wuce ni a komi gwamma insan abunyi .
Malamin bada Umarni yayi akan su tafawa Khairi kowa Saida ya yi Banda sakina .
Bayan sun tashi daga Ajin ne dan yau Akramakallahu be Zo mamaki ne yacika dalibai dan tunda yake zuwa baya fashi .
Direban gidan su Sakina ne yazo hannun sa ,rike da takarda Wanda ke dauke da sunan Ummulkhairi Sulaiman
Da Najwa ADAM.
Har office d'in headmaster yaje ya Mika masa wanna takardan.
Yana karba yace Yallabai wannan takardan fa.
Drever yace bude ka gani mana .
Warware takardan ya yi yaga ansa Sako daga Alhaji Kamal .
Yana son akori Ummulkhairi da Najwa.
Sossai headmaster yashiga tashin hankali ,shida yake shirin yaje ya nuna mata yana son ta .
Za'a wani ce a kore su.
Maido da kallon sa akan drever Sakina da Har ya juya yace dakata dan Allah cikin bacin rai.
Wannan takardan na menene yana masa nuni da takardan.
Drever yace nikaina bansan meye aciki ba , Sako aka ban kana iya kiran Alhaji ai kanada number sa Sakai ya yi yafice daga Makaranta tareda d'aukan Sakina a motar .
Shiko headmaster sossai yashiga tashin hankali dan yasan a dokar Makarantar ba'a kora Saida Izinin Jan ZAKI dakuma sa hannun sa.
Kiran Alhaji Kamal ya yi akan maganar cike da damuwa
Alh Kamal yace haba headmaster ya zakace kana tsoro kaine ke fad'a Aji kuma JAN ZAKI besan komai akan Abunda ke gudana ba.
Millions Biyar Zan baka nidai kacika mun burina a goben nan.
Katse wayar ya yi bejira cewar headmaster ba.
Shiko headmaster rana zafi inuwa kuna ,wani bangaren kud'in da akai masa tayi ne yafara tunani akai ,sossai kan sa ya kulle rike da kugun sa.
Najwa da Khairi ahanyar ta komawa gida suna hiran gobe InshAllah karshen Wata dan haka da shirin su .
Zasu je wannan titin da ba kyale shi zasuyi ba.
Direct gidan Mahaifiyar Baffa Yadiko suka nufa .
Bakin su dauke da sallama suka shigo.
Yadiko tana ganin su , ta fadada Fara'ar ta ,tace yau wace rana ce Khairi nake gani.
Murmushi kwance akan fuskokin su ,suka karasa ciki tareda samun wuri suka zauna.
Khairi Tace Yadiko tunda bakya nemana yau nazo dakaina.
Wai me kika dafa ne tafada tareda shiga kitchen din yadiko tana dube-dube.
Yadiko rike da baki tace abunci mijina kika dauko khairi tana kwabe baki.
Khairi Tace kwarai kuwa nashi zanci ,ya za'ai be bani naci ba Amma kullum saiya baki .
Najwa Ganin dagaske Abinci khairi zata ci yasata zuwa wanke hannun ta suka fara ci.
Yadiko tace wayyo Allah Ashe baku canza halin Ku ba daga zuwan Ku ,Har Kun dauke abinci Malam.
Khairi dake santin shinkafa da wake da mai da yaji tace au haba Ashe abinci Malam ne ,Miko mana yankanken salad din nan mu zuba aciki .
Kuma kiyi maza ki dafa mishi wani ko Alkur'an ya kwana da yunwa ina ruwana ni Ummulkhairi idan yakwana beci ba.
Sake da baki Yadiko ke kallon ta ,tace lallai yarinya kince wani Abu .
To maza kuci kuzo kumun jajjagen kayan Miya in dafa masa koda taliya takarashe zancen tareda shiga kitchen din.
********************
Innaro cikin hanzarin ta ta kamalla girkin ta abinci khairi harda nama ta saka Mata me uban yawa.
Saifudeen da Akramakallahu kuwa .
Kai musu abincin nasu tayi Har dakin nasu .
Kasantuwa yau Saif da Akramakallahu yawo kawai suka tafi cikin gari .
Sai kallon agogon hannun ta take ya Akai haryanzu khairi basu dawo ba ganin laasar ta kusa .
Wani babban shagon me Saida kayan provision taje ta saiwa khairi lemun kwalba hade da ice cream mai dan Karen sanyi .
Komawa gida tayi ,tadau abinci khairi takai dakin ta.
Lemun ma da ice cream duka ajiye mata su tayi.
Zaune take sai kallon agogon hannun ta ,take shiru kake ji Har magrib.
Tana kokarin shiga daki da dauko buta kansatuwa ankira sallah .
taji Muryan khairi da Najwa suna...........
Taku Har kullum kyauta daga Allah
Free page yakusa karewa Ku hanzarta kubiya dan kucigaba da samun littafin .
🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜
*JAN ZAKI*🐆
*DAGA MARUBUCIYAR :*
*KAIKAJAWA KANKA*
*KANWATA*
*RAYUWAR MA'AURATA*
Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI*
*Paid book ne*
Normal group 300
Special group 500
Acct nomba
*3115484026 ikilima Adam first bank*
Ko Katin MTN
Kan wanna layin
09069080725
Banason VTU
0️⃣8️⃣
Yayi tozali da Sakina da take shirin dafa bayan sa.
Cikin hanzarin sa yabuge hannun ta kafun yakai jikin sa , tareda bin ta da mugun kallo mai cike da mekike nema dani.
Cikin rawar Murya da kunyar da ya lullube ta , tace Akramakallahu kayi hakuri ,wani kwaro ne na hango ,nazo inbige maka shi ,bata karasa fadin Abunda takeda Niya ba ,ya daka mata uban tsawa ,Wanda Yasa ta razana kadan ya rage bata saki Fitsari ajikin ta ba.
Keeee yafurta cikin kakkausar Murya , wallahi nakara ganin wannan gangancin akaina ,Zan mugun daukan mataki akan ki banason iskanci ,ko na miki kalan yan iska ne .
Sakina cike da tsoro kada hankalin mutane yadawo akan su ,tabar wajen cikin Sauri Sauri , bin bayan ta yayi da kallo yana buga uban tsuki akai akai ,tareda kunna hasken wayar sa ,yacigaba da wayar sa ,murya cen kasa kasa.
Bayan Malamin turanci yagama musu lecture, Akramakallahu yashiga Ajin ,suna hada idanu da Sakina ya dauke kai ,ita kuwa sossai tasha jinin jikin ta ,tana gudun kada ya fallasa Abunda yafaru .
Kallon Dalibai yayi yace yau ba ranar waazi bace Amma zanyi mana waazi game da rayuwar student a school.
Nan da nan hantar cikin Sakina ya kada cike da tsoro kada yakawo misali akan ta ,yasa tafara tunanin Mafita Kota fita ne koko dai taboye kanta .
Najwa da Khairi hankalin su tsab yana kan Sakina Dan su Lura akwai Abunda ke damun ta ,tun shigowar Akramakallahu.
Shikuwa Sam hankalin sa baya kanta bare yasan da halin da take ciki.
Tsintar Muryan sa sukayi yana Fadin , a fadin duniyar da muke ciki , Makaranta tana cikin Abunda ake gyara tarbiyya kuma tana cikin hanyar gurbata tarbiyya ,sai Kaga yarinya a makaranta Amma tasan namiji , ko kuma ka samu malami yana amfani da ita dan yabata maki.
So yakamata kowace daliba acikin Ku ,ta maida hankalin ta akan Abunda ya taramu ,Ku rufawa iyayen Ku Asiri da suka turo Ku ,dan Ku samu ilimi mai amfani.
Tunda yafara magana kan Sakina a duke yake.
Yana gama musu nasiha ya maida hankalin sa akan agogon dake makale hannun sa .
Ganin Time ya kusa ne yasa shi fadin akwai Mai tambaya acikin Ku ne?
Tsit kake ji Ajin ,Lura da Khairi yayi bakin ta na motsi alamun tana son yin magana.
Khairi ta daga Hannu tace inada tambaya.
Bismillahi yafurta yana mai Kallon ta , idanun su ,suka tsarke cikin Juna ,nan take zuciyoyin su , suka harba , Akramakallahu Subuhannallah ya Furta acikin zuciyar sa.
Itakuwa Khairi hannun tasa ta dafa wajen saitin zuciyar ta ,tana jin yanda yake mugun tsananin bugawa .
Akramakallahu dauke idanun sa yayi akan Khairi tareda bata daman tayi magana dan yau karo na Farko da sukayi kallon kallo shida ita.
Daman inason ka gayamin idan har wani ya cuceka koda da zagine ko duka ,da dai sauran su.
Kana son ka rama wani hanza zaka bi.
Gabadaya Glass rike da baki kowa ya juyo yana kallon ta.
Akramakallahu cikin Muryan sa dake nuni da babu wasa acikin sa yace inhar Cutar da akayi miki ,kina ganin bazaki iya yafewa ba ,toki rama daidai Abunda akai miki ko kibarwa Allah .
Mafi Alkhairi acikin mu shine Wanda yabarwa Allah dan yayi masa sakayya.
yakarashe zancen yana Fadin ina ganin lokaci yayi zamu tashi tareda sallamar dalibai .
Akramakallahu na fita kowace daliba tafara kokarin fita , gabadaya class din firan sa ake akan fadakarwar da yayi.
Najwa da Khairi daidai kusa da Sakina suka karaso ,cikin daga Murya khairi tace Kash Amma dai wasu matan basu da Aji wallahi sune ke barin ana muna kudin goro ace ba muda kamun kai.
Najwa tace kwarai kuwa ai haka suke da sunga na Miji kamar su cinye shi.
Wuce ta sukayi suna dariya rike da baki.
Sakina dago kai tayi tana kallon su ,rike da baki tace wayannan yaran dawa suke ne?
Rasa me bata amsa yasata bin sahun su ,har waje ta same , su tsaye suna fira.
Azafafe tazo wajen su , cikin karaji tace,wani dan iskan ne acikin Ku yake min habaici ?
Khairi dake bin ta da mugun kallo tace gani nan ,nice ko akwai Abunda zaki mun ne?
Kokarin kai hannu take dan kaiwa Khairi, Mari caraf taji an rike hannun ta.
Cikin tsananin Mamaki take kallon Yaya saifudeen da ransa yake a matukar bace ,yace wallahi koda wasa hannun ki ya taba fuskar yar auta na lahira saiya fiki jin dadi ,kuma taimakon ki ,nayi dan wacce kike shirin kaiwa mari ,ba zumar lasa bace , madaci ce yakarashe zancen tareda kama hannun Khairi da Najwa cikin zafin nama yabar school din dasu.
Mutuwar tsaye Sakina tayi ,cike da mamakin wayannan yaran da kuma kalaman Yaya saifudeen ,cikin kunan rai tayi hanyar gidan nasu, tana Ayyana aranta sai tayi karar su intaje gidan su.
*****************
Yaya saifudeen sunci rabin tafiya daga Makaranta zuwa gida.
Hango Akramakallahu yayi zaune gefe yana karantun Alkur'an mai girma.
Har sun wuce shi , Najwa tace laa Yaya ga Malamin mu nan mai koya mana karatun Addini .
Waigowa Saif yayi suka hada Idanu da Akramakallahu dake shirin rufe Alkur'an.
Saifudeen yace kamar dashi muka gaisa da safe , hannun yaba Akramakallahu sukayi musabaha , saif yace Malam kai dan garin nan ne yana mai tsare shi da idanu .
Dago kai yayi yana kallon su Khairi da Najwa karamin tsuki yaja ,yamaida kallon sa akan Saif tareda bashi Amsa ni bako ne .
Kuma dan Allah ko Zan samu daki haya agarin nan ?
Saif yace inhar bakada iyali inaga me ze hana ka sauka a muhallina .
Akramakallahu jinjina kalaman sa yayi yace haba kai daga ganin bako saikayi saurin yarda dashi .
Eh inada kyakyawar zato akan ka ,kaiba mutumin banza bane .
Kuma nasan bazaka taba iya kashe koda kiyashi ba.
Murmushi Akramakallahu yayi yace inagodiya Amma kabar ni indai kama hayar zefi,
Saif yace dan Girman Allah ka zauna taredani daman kadaici yana damu na ni kadai adakin.
Dan Jimm Akramakallahu yayi yana mai satar kallon su Khairi da suke tabe baki akan firan nasu.
Na'amince ya Furta Allah yasa Alkhairi acikin zaman da zamuyi .
Saidai baka gayamin sunan ka ba.
Bashi Amsa yayi da Saifudeen Sulaiman .
Khairi ce ta katse firan nasu da Fadin , Yaya kabari zamuyi gaba har Ku gama tattaunawa.
Daga musu kai yayi Alamun gamsuwa.
Hakan yasa suka wuce suka bar Saif da Akramakallahu tsaye suna tattaunawa.
Bakin Titi suka nufa ,Najwa tace khairi kinsa wannan yaron nan yace ,sai karshen Wata yake