Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RAI DAYA Inkiya JAN ZAKI by Ikilima Adam

Author :  Ikilima Adam Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 13

12K to 15K   out of 36.3K words

Ajin headmaster.
Ganin office din arufe yayi matukar bashi mamaki gashi har time ya gota.

Sauran Ajin yakebi bayan daya yana dubawa yaga ,malamai wajen uku duk basa nan.
Kai tsaye Ajin su Khairi yashiga inda nan ne wajen zaman sa.
Nan ma malamin turancin nasu be iso ba..

Ganin time yatafi yasashi Kallon daliban cikin nutsuwa yafara magana .
Yace daman malaman Makarantar nan basa zuwa kan lokaci ne ?

Sakina ce ta amsa masa cikin yauki tace eh Akramakallahu basa zuwa dawuri ,wani lokacin ma sai suyi kwana ki basu Zo ba.
OK yafurta tareda mata Izinin ta zauna .

Sakina sai kallon khairi take tana hararan ta.
Caraf suka hada Idanu da Khairi takara banka mata wani hararan.

Rike da baki Khairi take fadin oh ni wannan matar Me na tsare mata ne.
Najwa ta kalla tace kee! Kin Lura da kallon da waccen banzar ke mana kuwa.

Najwa tace eh ina kule da ita barta duk tsiyar ta akwai Na gaba da ita ,kamata yayi mu gyara mata zama tasan , bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane.
Suka karashe zancen akan yanda zasu fara saita Sakina.

Akramakallahu daura su yayi akan karatun turanci inda mamaki yacika daliban ,dan yanda yake fiddo kalmomi turanci a bakin sa ,zakayi tunani a kasar su America ne .

Yana cikin basu lecture ,malamin su na turanci ya iso ,hakan yasa malamin cike da mamaki yake kallon Akramakallahu dake basu darasin da ba nashi ba.

Musabaha sukayi , murmushi Akramakallahu yayi yace wai naga baka iso dawuri ba , shiyasa nake koya musu turanci kafun kazo ,time din karatuna beyi ba.

Malamin yace babu matsala yana tsotsa keya ,na dan je wani wurin ne shiyasa.

Sakina Ganin Akramakallahu yafita ,ranta yayi mugun baci tashi tayi dan bin bayan sa.

Cikin hanzari take tafiya tana kokarin barin Ajin ,malamin turancin nasu cikin tsawa yace kee Sakina ina zakije ne.

Turo baki tayi gaba tace inazuwa uzuri gareni bata jira cewar shi ba ta fice ,ganin saurin nata yayi yawa yayi tunanin ko bahaya zatayi shiyasa bekara fadin komai ba.

Koda ta baro Ajin leke leke ta fara inda zata hango shi.
Hango shi tayi daga cen nesa Alamun ,yana waya ne ,ya bata baya.

Ahankali take taku tana doso inda yake.
Shikuwa wayar sa ce tafara kunna danja Alamun akwai Abu abayan sa.

Azabure ya waigo cike da tsananin Mamaki yayi tozali da Sakina da take shirin.........





Taku har kullum kyauta daga Allah ce
🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜

*JAN ZAKI*🐆





*DAGA MARUBUCIYAR :*


*KAIKAJAWA KANKA*


*KANWATA*


*RAYUWAR MA'AURATA*


Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI*



*Paid book ne*


Normal group 500


Special group 1k


Acct nomba

*3115484026 ikilima Adam first bank*

Ko Katin MTN

Kan wanna layin

09069080725

Banason VTU






0️⃣5️⃣



Yace yanzu ba lokacin wannan tambayar bane..

Murmushi Malamin turancin nasu yayi yana kallon J A dashi din ma shiyake kallo .

Yace kwarai kuwa Akramakallahu ' murmushi yayi yana kallon Khairi da damuwa ya bayyana a fuskar ta ..

Yace karki damu daliba ta gobe InshAllah Zan amsa miki inban manta ba..
Ficewa yayi daga Ajin hakan Yasa Khairi komawa ta zauna cike da takaici J A. .

J A nashigowa gabadaya class din suka Mike dan gaishe sa Banda khairi da ta cikam fam saura kiris ta fashe...

Da Mamaki yake kallon cikin sanyin Muryan sa da Sam babu hayaniya yace Baiwar Allah lafiya kike zaune bayan kowa ya tashi...

Gabadaya daliban Maida kallon su sukayi akan ta...
Najwa tabata tayi da kafafun su dake hade akasa tana Mata nuni ta tashi itakuwa Fir taki tashi....

A J bawa dalibai damar zama yayi yana mai satar kallon ta cike da mamakin tsaurin idanun ta......


Bismillahi rahmani rahim ya rubuta jikin Allo da harshen larabci...

Kowa Class din nutsuwa sukayi ana kallon yanda hannayen ke rubutu cike da kwarewa da nutsuwa yana kai Ayar rubutun nasa yadawo da kallon sa akan Dalibai tareda ajiye alif din kan kujerar mazaunin malami.....

Yafara da Fadin kamar yanda kuka gani a rubuce inason Zan fara da koya muku baki ta yanda zakufi saurin fahimtar karatun da ake ..

Sanna duk ranar jumaa waazi Zan ringa muku .
Zandai tsara jadawalin karattuka Na gare Ku...

Gaban Allo yakoma yace ko akwai Wanda ze karanta min Abunda narubuta musamman Ku yan Aji shidda ne nasan Kun sani ko Kun taba karanta a wanna makarantar....

Gabadaya class din rau rau da idanu suke kallon sa..
Dan su ba'a taba koya musu baki ba ..
Saidai a koya musu surori..

Khairi ce ta Mike cikin nutsuwa dan sossai rubutun sa yaja hankalin ta musamman ita maabociya son karatun islamiyya ce...


Akramakallahu Zan iya karantawa..
Bismillahi yafada cikin son gano ainihin gaskiyar ta...

Alif ba'un ta'un. Ta karanto masa har karshen su....

A J sossai yayi mamakin ganin yarinyar da rawan kai yayi Mata yawa har ta iya rike Baki akan ta...

MashAllah yafurta tareda ba kowa daman ya taba Mata...
Kowa Saida yayi tabi Banda Sakina da wani zuciya ta dibe ta..

Tashi tayi tace Akramakallahu ai bansan fassaran karatun bane Amma tabbas muna ji ana karanta mana .
A Makarantar islamiyya...

A J kallon ta yake yace yakamata ace kin San shi arubuce sannan ki haddace shi...
Sannan asannan Makarantar nan yakamata ace kin San shi inhar karatun akeyi .

Sossai taji kunyar Amsar daya bata Wanda shi yafada ne iya gaskiyar sa.
Samun wuri tayi tazauna tana hararan Khairi wacce batasan ma tanayi ba..

Kusan Awa biyu yadauka yana koya musu baki.
All class din sossai suke gane karatun nasa dan yanayi ne yanda kowa ze fahimta...

Koda ya tashe su tsaida Khairi da Najwa yayi ...
Su biyun...

Khairi da haryanzu take cike da takaicin amsar da ya hana malamin turanci ya basu ta tsaya cike da kosawa.....

Kallon Najwa yayi yace Na fahimci Ku baki ne kamar ni...
Kuma da dukan Alamu Baku taba yin bokon ba..
In bazaku damu ba zanringa dan koyar daku karatun bokon har Ku iya yana mai tsare Khairi dayaga ta soma dan murmushi..

Khairi cike da Murna ta dafa Najwa tace dan Allah da gaske Akramakallahu zaka ringa koya mana....
Papper dake cikin jakarta ta dauko tace yawwa Najwa karanta mishi Abunda ke ciki dan na mance yanda ake fadi...

Najwa Na karban Papper ta karanto masa ..
Zazzare idanu yayi cikin firgita yana mai Kallon su Yace ke Khairi kirasa Abunda zaki fara koyon karatun boko dashi sai wayannan kalmomin...

Khairi cike da Neman Agaji tace karka damu Akramakallahu nidai ka gayamin matar baba Na ta Fada mun jiya Amma dayake tanada yar Hali shiyasa banyarda da zancen nata dari bisa dari ba

A J tana kai karshen zancen nata yace .

Stupid girl zagine
Shima mental problems haka yake Amma shi yana nufin kamar mai tabuwar hankali ..

Rau rau da idanu take kallon sa kamar zatayi kuka sai ta dan ciza labban ta .
Tana mai jin radadi da kuna cikin zuciyar ta..

Kallo daya yamata ya fahimci yanda Kalmar ta tsaga bango da duk wani huda Na jikin ta...

Be Ankara ba sai yaga hawaye na kwaranya daga idanun ta Shar Shar kamar anbude famfo

Agigice Najwa ta dafata tana mai Fadin subuhannallah haba Khairi meye zaki dau zafi dan wani Wanda besan darajan kan sa ba ya zageki..
Inace mun ce zamu dau fansa ko kin manta shawaran da Innaro ta bamu .
Shawara ce mai kyau in mukayi amfani da ita....

A J dake kallon su Murmushi yayi kamar zece wani Abu saiya fasa...
Kallon Najwa yayi yace itada wa sukayi Fada ne?
Sannan meye ya hada su

Najwa cike da takaicin Abunda yafaru a ranar ta ringa bashi labari tun daga Farko har karshe..

Mamaki ne yakamashi Matuka yace da kunyi hakuri da dai yafi Alkhairi.

Caraf Khairi ta karbi zancen tareda Fadin Allah ya kiyaye nayi hakuri wallahi in kere Na jawo zabo na yawo wataran zasu hadu ne.

Ai wannan *RAI DAYA* saina Rama Abunda yafada agaban wayanda yayi zagin saidai Ni ba diyar Sulaiman da Amina bace takarashe zancen tareda kama hannun Najwa zasu bar Ajin...

Najwa tace Akramakallahu InshAllah daga gobe zaka fara koya mana Amma dan Allah in dai agarin Na kake me ze hana muringa zuwa gidan naku koyon karatu...

A J zazzare idanu yayi yace ai gidan namu da nisa kedai anan Zan ringa koya muku inya muku..

Khairi data kosa subar Makarantar dan suje suyi check din titin ko Allah zesa su hadu wanna bawan Allah....
Tace babu damuwa Akramakallahu zaka ringa koya mana a Makarantar.
Barin sa sukayi cikin hanzari tsaye yake yana kallon fitar su .
Tsinkayo Muryan Sakina yayi tana magana cike da iyayi sai Fari take da idanu tana bankaro kirji dan ya tabbatar ta cika iya mace ..

Akramakallahu dan Allah in bazaka damu ba zanso karinga koyar dani ina biyan ka agidan mu..
Kallon ta yake yana nazartan Kalaman ta cikin kosawa yaje ai iya nan karatuna ya tsaya saidai kibiya in koya miki anan yakarashe zancen tareda barin ta anan tsaye rike da bakin ta tace ikon Allah.

Jibe shi talaka dashi Amma sa Girman kai rawanin ni badan kyawun ka wlh baka isa in tsaya kusa da mai kodadden Riga ba takarashe zancen tareda shiga Ajin dan dauko jakar ta.........


***********************



Mama zaune gefen sa tana kallon yanda yake lumshe idanun sa lokaci zuwa lokaci.....

Cikin halin Damuwa tace Haba Aliyu taya zaka sawa kanka damuwa tun jiya kaki Fadamun Abunda ke Faruwa...

Sallamar Nusaiba ne Yasa ta maida kallon nata akan ta ..
Fuskar ta dauke da Murmushi tace zonan daughter gayamin Abunda yafaru jiya kila kinsan wani Abun..

Shiru ne ya ratsa dakin dan sossai Nusaiba ke tsoron bawa Mama labari .
Abu karami ne yanzu ya hau ta da fada...

Mama tace shikenan dukan Ku Kun maidani Mara Amfani ko tun jiya..
Jin Muryan Mama ya canza Alamun bacin rai Yasa Nusaiba ta fara zayyano Mata Abunda yafaru daki daki... .

Salati Mama ta dauka tana yarfe hannun rike da bakin ta tace ikon Allah..
Kaiko Aliyu meye ya hadaka fada da mace..

Kalaman ta ne yasashi dan mikewa ya jingina da bangon dakin ..
Ahankali yake daga lallabansa cikin sakalci yace haba Mama wuce nan wallahi kawaide Na hadu da yaran kauyen nan ne wayanda basuda kan gado har hakuri fa Na bata .
Amma kamar nace cigaba .
Ko ba haka akayi ba yana mai Kallon Nusaiba.

Kada kai tayi tace kwarai kuwa Mama yarinyar ce kamar Wata tabbabiya...

Mama dake sauraren su Murmushi tayi maimakon suga nata ran ya bace..

Haba Aliyu be kamata kubiye Mata ba..
Maybe yarinyar ce tanaji da hayakin kuruciya ne...
Kaga Kalmar daka furta Mata ze zauna mata arai...

Tabe baki yayi yace yana jinjina zancen.

Kallon Nusaiba tayi cike da bada Umarni tace dan bamu waje Zan gana dashi.

Sanda Sanda Nusaiba ta fice tana girgiza kai dan atunanin ta fada zesha wajen Mama....

Nusaiba Na fita ta maida kallon ta akan sa..

Haba Aliyu kamance kaine Aliyu mai kokarin kare hakkin mutane..
Kaine Aliyu dake tausayin na kasa dashi..
Atarihin RAYUWAR ka wannan yarinyar itace farkon wacce kuka taba samun sabani please dan Allah irin haka kuringa kiyayewa Yaran naka kaja musu kunne dan sakacin su yakawo hakan..

Aliyu Haidar dake kallon Mahaifiyar sa cikin sanyin Murya yace InshAllah Mama Zan kiyaye.
Amma ni fa ba laifina bane yarinyar ce batada kunya ko na second daya.
kinga Agajiye Na dawo Zan dan kwanta kafun Anjima ko

To Dana Abun Alfaharina takarashe zancen tana kokarin barin dakin nasa daidai kofar fita juyowa tayi tana kallon sa tana girgiza kai shiko kallon yake yana lumshe idanun sa..


*********************


Khairi da Najwa kusan Awan su uku akan titi suna ta kallon titin ko zasu hango irin wayannan motocin na wanna ranar shiru kake ji...

Najwa Ganin Yamma tayi tace khairi mu hakura mana mu bari duk Ranar Monday mun ringa gadin hanyar ko nasan haka nasara ne tafada cike da gajiyawa dan batason Khairi ta fahimci ta gaji da gadin titi su ba sallah ba bare cin Abinci..

Kokarin tsallake Titi suke sukajiyo Muryan Mijin Sultana yana Fadin yan halak daga ina kuke ne..

Khairi Murmushin dole sukayi ita da Najwa suka hada baki wajen Fadin .

Kaga mun je gidan Wata Kawar mu ce yar ajin mu.
Ko gidan Anty Sultana bamu leka..
Dan Allah karka ce Mata ka ganmu kofar Gidan ta dan ranta ze baci ace muna kofar gidan nata bamu leko ba.

Karku damu cewar Mijin Sultana yana mai kare musu kallo harsuka fice cikin hanzarin su...
Girgiza kai yayi yashige gida Abinsa.




Baffa da Malam Adamu duk hankulan su yatashi akan rashin dawowar su dawuri .
Har sun kama hanya zasu Neman su.
Sukaci karo dasu cike da Razani suke kallon iyayen nasu..
Khairi Tace Baffa ina zakuje ne ?
Baffa cikin damuwa yace haba Khairi ai kunsan Neman Ku zamuje .
Ina kuka tsaya ne har wannan time din baku dawo ba cewar Malam Adamu cikin Fada dan yasan Baffa baya iya tsawata musu..

Najwa cikin tsoro tace Wata Kawar Ajin mu ce muka je dubata batada lafiya..
Kallon kwayar idanun ta yake tareda nazartan Kalaman ta.
Yace Najwa yaushe kika fara Karya ne?
Khairi caraf ta karbi zancen da fadin Malam aikuwa gidan Kawar mu ,mukaje Amma daga yau zamu kiyaye .
zamu sanar muku duk inda zamuje .
Murmushi Baffa yayi shi harga Allah beson bacin ran Khairi Amma kuma baya son hakan yazama silar gurbacewar tarbiyyar ta. shiyasa in Khairi tayi laifi cikin hikima yake ganar da ita kuren ta dayake akwai hankali irin ta manya to sam bata kara maimaita laifin da aka hane ta...

Kusan tare suka jiyo inda Khairi tayi gida itama Najwa tayi gidan nasu.
Tasha fada wajen Mommy sossai .

Khairi nashiga gida taci Karo da Innaro tana tuka tuwon gari da Alama talgi take...
Sannu da aiki ta furta mata tareda wuce ta..

Innaro dago kai tayi tana kallon shigewar ta daki..
Tabe baki tayi tace inbanda abun Baffa wannan ma takai ayi mata Aure yarinya saidai in dafa taci kuma bata aikin komai sai taga dama wannan shi ake kira so .
Ni kenan nazama baiwa kenan.
Cigaba da tukin tuwon tayi tana girgiza kai...


Khairi tana shiga dakin fiddo papper tayi cike da bakin cikin rashin samun sa da basuyi ba..
Tashi tayi tadauro Alwala tareda jero sallolin da ke kanta akan sallayar barci yayi awon gaba da ita .
Papper yana gefen nata.

Da sallama Baffa yashigo dakin nata yana kallon yanda ta buge kan dadduma gyara mata shimfida yayi .
Ahankali ya dago ta yadaura ta kan katifar ta..
Itakuwa dan bude idanun ta tayi tana ganin Baffa ne turo baki tayi takoma barcin nata..


**********************



Kashe Gari...


Yau babu Makaranta kasantuwa duk Makarantar Jan ZAKI ba'a zuwa Makaranta ranar laraba gwamnati tasan da wannan dokar nashi Amma haryanzu suna son suji dalilin sa .
suna da tarin tamboyoyi akan sa..
Amma haryanzu be amsa musu kodaya ba.


Baffa tsaf yashirya yau zetafi Birni kai Doya inya tafi saiyakai Sati be dawo ba.
Sossai Khairi ke kuka cikin Muryan lallashi Baffa yace kiyi hakuri yar auta ta inazuwa cen yayan ki zezo gida Shima yayi sati aibaki da matsala bakwabe Fuska tayi tasan yayan nata beda sauki duk da yana mugun son ta fiye da kima Amma beson sakarci..

Sallamar Sultana ne yadawo da hankalin su akanta hannun ta rike da bakin leda bakin dauke da Murmushi take kallon Baffa cike da ladabi ta gaishe shi ya Amsa Mata cikin faraa tareda dafata .

Khairi Tace Antina duk larabar duniya saikin zo dole saikin ma Baffa sallama ko yayan mu.
Murmushi ta sakar Mata tareda maida kallon nata akan Baffa hannun sa tarike tana matso yar kwalla tace Baffa na.
Ya Amsa da na'am Sultana yana kallon yanda yanayin ta ya canza lokaci daya..

Baffa banason kana gilan doya daga Funtua zuwa kasuwar Sheme kai inkaje saikayi sati baka dawo ba.
Hannun sa tarike tareda saka masa kudade Wanda akalla zasu kai Dubu hamsin tasa cikin hannun sa .
Yakai Mahaifina wanna kudin dan Allah karka dawo mun dashi kamar yanda ka saba .
Banason kaje Birnin Baffa kayi zaman ka.
Kaja jari anan garin ko dan shago kabude ina Sanaa agida Zan dauki nauyin wani Abu na cikin gidan nan, takarashe zancen cikin raunin Muryan wacce take gab da sakin kuka..

Ganin hawaye sun fara kwaranya daga idanun ta ne.
Yasa Baffa gigicewa dan kwata kwata baya son Kukan yaran sa.
Cikin tsarkewan murya
Yace Sultana Zan Amshi kudin dan in Faranta miki rai Amma wanna yazamo shine na farko Dana karshe banaso ki kara kawo mun ko sisi ki barni in nema dakaina InshAllah Allah yana tare da me nema wanna kudin Zan dan siyewa Khairi kaya irin naku na mata ina tara mata koda auren nata yazo kada inji kunya kamar yanda nakusa jin kunya a auren ki ...
Kuma maganar shago Sultana Abar shi ,babu sana'ar da banyi ba Amma a banza ne jarin karewa yakeyi yakarashe zancen yana mai matso kwalla a idanun sa tareda Dan bubbuga bayan Sultana data dawo kalan tausayi, wahalar da maihaifin ta yakeyi yayi yawa.

Sossai jikin Khairi yayi mugun sanyin gabadaya Baffa yagama bata tausayi .
Rungume shi tayi tana Fadin InshAllah Baffa ni Khairi Zan sanya ka kaji dadi kasamu Hutu wataran saidai kabada Umarni amaka batareda ka motsa ba.
Murmushi yayi shida Sultana suna kallon zancen nata a shirme .
Baffa da Sultana suka hada baki wajen Fadi Allah yacika miki burin ki yar Auta.
Sossai ta Dara sai da dimple din ta ya lotsa zararan idanun ta, ta sauke akan Baffa murmushi tayi tareda daukar masa jakar sa tayi gaba .

Har waje suka rako sa kasantuwa Innaro bata gidan taje barkan haihuwar kanwar ta.....

Suna barin kofar Gidan sukaci karo da Malam Adamu da Najwa zata sola debo ruwa hannun ta dauke da karamar jarkar lita goma.

Ganin su Baffa yasa sukayo wajen su ,Malam Adamu yace ah tafiya dai ta tashi yau tun dawuri zaka je kenan yana mai zuba masa idanu tareda basa hannu sukayi musabaha ,gaisawa sukayi cike da dattako irin nasu na manya.

Baffa cikin yanayin sa da yayan sa suka gama kashe masa jiki yace .
Kwarai kuwa sonake Innaje Dana yadawo gida dawuri tun gari beyi duhu ba.

Ana fama da kidnapped a Nigeria ,local government nan barnar tafi yawa.

Malam Adamu ya jinjina zancen nasa yace wanna zancen gaskiya ne kayi tunani me kyau.

Dukan su rakiya sukayi masa har bakin Titi .
Tsaye suke bakin titin suna jiran abun hawa daze kaishi tasha...

Sultana sossai tayiwa baffa sallama hade da aduar Allah ya tsare cike da zallan kewa sukayi sallama ,
kallon Khairi da Najwa

5 / 13