Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RAI DAYA Inkiya JAN ZAKI by Ikilima Adam

Author :  Ikilima Adam Category :  African Stories & Novels

Chapter   8 / 13

21K to 24K   out of 36.3K words

bin wannan hanyar ki dawo muyi gida .

Naga saura kwana biyar karki damu ranar da makaman yakin mu zamu taso ,da wannan kalamin ne , taja hankalin Khairi har ta amince su tafi gida .




Innaro zaune adakin ta sai safa da marwa take ita kadai ganin babu mafita ne yasa ta dau wayar ta ,takira Kawar ta ,bugu daya aka daga dagacen bangaren cikin dariya da shewa tace shegiyar mata sai yau kike nema na.

Tsuki Innaro taja tana mai fadin kedai wallahi kin bani bazaki bari a gaisa ba.

Kwabe baki Biba Kawar ta tayi tace am sorry yakike Safara'u kwana dayawa , bayan sun gaisa ne ,takara da cewa ina wannan nusarin mijin naki da wannan yar tashi sangartaciyya ?

Humm Innaro tayi tace ai shegu duk suna nan lafiya ,wannan yarinyar nan inhar banyi hankali ba wallahi saita sa an koreni agidan ,dan Allah ki koma gun Malam shehu ki fadamai Abunda nake bukata Kinga munyi nasarar yin Aiki har aka aurar da Sultana ,itama Khairi takai Aure dan Allah kice masa ayi Abunda za'ayi yarinya da kanta ,tace aure takeso .

yau befi saura Wata daya
Ayi wasan kwallo na aure da ake bugawa duk shekara.
Duk yanda za'ai dan Allah ayi inason Khairi ta bude bakin ta ,tace asaka Sunan ta a wannan gasar .

Bushewa da dariyar keta Biba tayi tace shegiya Safara'u kanki yanaja kinsan nama mance gasar nan ta kusa naso in saka yata Amma tunda kinzo da bukata sai asaka shegiyar Yarinyar nan kowa ma yahuta.

Sanyayyan Numfashi Innaro tayi wlh sai yanzu naji hankali na yakwanta ace yara su hanaka jin dadin aure , kinsan Baffa indai Khairi na gidan wayyo bazan taba yin haske a idanun sa ba.

Da khairi tabar gidan sannan zandawo da sababbin abubuwa agidan kedai kwantar da hankalin koda matsiyaci Amma dai ina hango wasu abubuwa tare dashi.
Jin takun tafiya yasa Innaro fadin Biba sai anjima zamuyi waya tareda fitowa tsakar gidan .

Kallon su tayi itada Najwa cike da Farin ciki tace yar Baba har andawo ..
Sake da baki suke kallon sabon salo , khairi ce ta amsa da mun dawo akwai abunci ne dan yunwa nikeji.

Haba yayana ya zaai ina uwar taku abinci saikun nema ,aikunwuce haka awajena nida Zan aurar daku inkun kara girma.

Zazzare idanu khairi da Najwa sukayi kusan tare suka furta aure kuma suna zazzare idanu ,ai wallahi ba yanzu ba.

Innaro cike da Salo tace Aina sani yayana
azuciyar ta sai fadi take wayyo khairi harkin ban tausayi ashekarun ki akai ki dakin Miji bansan me zaki tsinana ba.

Sallamar Saifudeen ne da Akramakallahu ne yajawo hankalin su akan sa.
Arazane Khairi ke kallon sa agidan su shikuwa kauda kai gefe yayi .

Muryan su taji suna gaida Innaro inda ita kuwa sai washe baki take , tace Dana Saif na Allah Ina kasamo wannan farin yaro mai zubin larabawa .

Saifudeen murmushi yayi yace uhmm abokina ne kuma bako ne sai ranar asabar zeringa tafiya garin su ,shike koyar dasu Khairi fanni Adinni .

Allahu Akbar Innaro ta Furta tace kenan adakin ka ze sauka ,ganin zata cika su da surutu Saif ya katse zancen eh daki daya zamu zauna tareda kama hannun Akramakallahu suka wuce dakin sa dake zaure .

Khairi da Najwa cike da mamaki suke kallon Al'ajabi suka hada baki wajen fadin oh ni Yaya saif haryanzu Ashe be bar kwashe kwashe ba .

Caraf Kalaman su yafada kunne Akramakallahu da Saif kallon Juna sukayi tareda yin Murmushi dan ya dauke su yara be sasu ajerin Masu hankali ba.

Cike da Jin kunya Saif yace please kayi hakuri da Abunda kaji yara ne .
Hannun ya masa cikin nuna halin ko inkula da lamarin su Yace nima inada kanne irin su marasa ji.
Nuna masa wajen kwamciyar su yayi Wata katuwar katifa .

Sossai Akramakallahu ya yaba da tsaftan Saifudeen dan dakin agyare yake komai normal.

Kashe gari


Sakina cike da bacin rai tafito dakin ta ,tana sanye cikin kayan Makarantar su.

Abban su dake tsaye yana mai kare mata kallo yace haba daughter tun jiya naga baki walwala waya tabamun ke.

Kuka ta saki cike da shagwaba tace wallahi Daddy wasu yaran Ajin mu ne ,su biyu suke tsokana ta kuma ban musu komai ba , please daddy inason kasa akore su daga Makarantar nan hakan zesa inji dadi.

Mummy ta dake sauraron su ta haba Sakina wani irin a kore su , Makarantar ta uban ki ce .
Ran daddy Sakina yakai kololuwa wajen baci ,yace waike meyasa bakida zuciya ne ace ana zaluntar yar ki Amma kina Neman ki hana adauki mata ki akai why yafada cikin tsawa .

Mummy cikin sassaita nutsuwar ta tace ba haka bane Amma ka sani suma wayancen din Yaya ne kuma abun soyuwar iyayen su , balaifi sukayiwa Allah ba yabarsu a talakawa ba .
Tunda Sakina take zuwa Makaranta ni bandaji karatu Abakin ta ba.
Saidai inji ta samu sakamako me na tabbatar ba kokarin ne ya bata ba ,haba kudaiji tsoron Allah takarashe zancen tareda barin dakin.

Sakina da daddy kallon ta suke suna jinjina kalaman ta .
Maida kallon yayi akan Sakina yace karki damu da ita daughter ,gayamin sunan yaran nan wallahi Zan nuna wa iyayen su ba'a tabani a kwana lafiya ni Alhaji KAMAL dan natura ki Makarantar JAN ZAKI akwai dalilin yin haka karki damu ,kwananan nan Zan fitar dake waje karatu.

Sakina hada rai tayi cike da fargaba tace haba Dad's waje kuma ,cike da razani kada a rabata da ganin Akramakallahu dan tayi mugun kamuwa da son sa komai zata iyayi .

Please Dad's karka canza mun Makaranta kabarni anan kaidai kasa akori wannan yaran shine bukata ta.

Wata matashiyar budurwa wacce bazata wuce shekara Ashirin da Biyar bace tashigo Falon hannun ta dauke da wani basketball tana sanye cikin Riga da wandon kwallo .

Good morning Dad tafurta tareda karasowa gaban sa ,cikin tsokana tace Sak yadai naganki kamar wacce ke shirin kuka .
Daddy ne yabata labarin Abunda akayi wa Sakina ,jinjina lamarin tayi cikin nuna lallai yakamata a dau mataki akan su.
Sakina nawuce wa dan drever na zaman jiran ta .
A harabar gidan nasu.

Daddy kallon matashiyar budurwa yar sa yayi mai suna Sumayya Yace daughter yawwa Zo mu dan zauna muyi magana kullum inason inyi magana dake Amma wani uzurin naki saiya hana.

Samun wuri sukayi suka zauna ,cike da son jin Abunda ze Fada ta tattara nutsuwar ta ,tace Daddy inajinka ,tareda daura kafar ta daya kan center table tsakiyar dakin.

Sumayya yakira sunan ta ,cikin cool voice din sa.
Inason zaki mun Aiki akan JAN ZAKI

Firgit ta dago kai ta kalle shi cikin zazzare idanu bakin ta ,na rawa tace Daddy banji Abunda kake fada ba kodai kunne na ,ne ke min gizo da kalaman ka.

Girgiza kai yayi yace A'a Sumayya Abunda na fada hakan yake akan sa nakeson son ki mun Aiki ko baki bane yafada cikin daga Murya alamun so yake ya fusata.

Zumbur ta Mike tsaye rike da kugun ta tace Daddy kasan.............






Taku Har kullum kyauta daga Allah.


Ikilima Adam
09069080725
*🦜RAI DAYA*


*JAN ZAKI*🐆




Ikilima Adam( kyauta daga Allah)

Paid book.

09069080725



1️⃣1️⃣



Ganin ogan nasu na fitowa daga cikin Motar ,yasata hanzartawa ta isa gaban sa , cikin tsananin b'acin rai da suka had'e mata ga na kora da akayi musu daga Makaranta , ga bak'in cikin sa da ta Dade dashi.
Kasa hada idanu tayi dashi dan kwarjini ya yi Mata , cikin karfin Hali .

Rai ab'ace tace rannan kace mun stupid girl to kaikuma hauka boy , kace mun mental problems to kaine kwakwalwa problem dan na tabbata kwakwalwar taka ba a dai-dai suke ba , shiyasa kake zagin yayan mutane get out tafada jibe shi mutum Shiba kowa ba ,ya tara samudawa yana jawo dashi in katashi zuwa lahira mun gani ko zakuyi kwanciyar kabarin tare dasu nusarin namiji taja tsaki tana mai buga masa uban harara .

Ogan nasu tunda tafara zazzaga masa ruwan Masifa babu abunda yake kallo sai bakin ta , ganin takai karshen zancen ta .

Yakara takun tafiyar sa izuwa gare ta had'e da shan kunu yace yau kin tabbatar mun dake Stupid girl ce mara hankali inbanda dabbanci an gayamiki ana wasa da Rayuwa ne to bari kiji in gayamaki daga rana ita yau , idan nakara cin karo dake kan Titin nan Zan dauke ki inkai ki gidan zooo inba Kura suyi fata-fata da namar jikin ki yakarashe zancen yana bin ta da kallon kishiga taitayin ki.

Tsit kake jin khairi takasa koda kwakwaran motsi arude take kallon sa , tace eh lallai yau na tabbatar da maganar Najwa akan gargadin da ta data janye maganar daukar fansa .
Ganin tayi shiru ne Banda hawaye babu abunda ke kwaranya daga idanun ta .
Yasa shi Fad'in dan Allah malama bamu hanya
In kunne yaji jiki ya tsira.
Yaja karamin tsuki.

tareda juyawa yayi cikin jerin Motocin.

Najwa dake gefe tana kallon Abunda yafaru zuwa tayi tarikota dakyar tana Fad'in khairi kinban mamaki ya za'ai bakin ki ya mutu gaban wannan mutumin .

Anas ne yakaraso gaban Khairi yana dariya yace yammata hiiiii yana kashe mata idanu , yakika ga wasan yanzu kin tabbatar sahun giwa ya take na rakumi ko?

Khairi da idanu kawai tabishi dan tarasa dalilin dayasa takasa jaa da wannan mutumin , ta tabbatar idan Anas ne da tuni ta dau mugun mataki akan sa.
Tsuki taja hade da hararan sa tace Inka isa karama Marin danayi maka rannan agaban su..
Gabakidaya magoya bayan Aliyu dake tsaye Har shi kansa JAN ZAKI duk da yana cikin Motar be hanashi jin Furucin ta ba.
Kasa daurewa yayi hakan yasa yafito daga motar karo na biyu cike da kasaita yake tafiya harya iso gaban Anas yana mai masa kallo mai Alaman tambaya .
Yace wai kana nufin ,Saida kabiyo wannan yarinyar dan daukar fansa ne.

Zazzare idanu Anas yasoma cikin rawar Murya zece A'a .
Najwa tace karya yake be kamaceka ba inace biyo mu kayi rannan Har yar uwata ta hukunta ka takarashe zancen tana mai buga masa harara cikin tsawa.

Aliyu JAN ZAKI sossai Anas ya yi matukar bashi mamaki Afili kuma kallon sa ya yi yace maza kashiga mota ,yana girgiza kai Alamun akwai Abunda ya Sosa masa rai acikin jawabin Najwa.

Yaran sa dake wajen kowanne su yana sake sake akan hukunci da ogan su ze dauka akan Anas .
Khairi rike da baki take kallon yanda motocin nasu suka kunna wuta zasu bar wajen .
Kamar ance mata waigo aikuwa tana juyawa taga Yaya saifudeen ne .
Kuka ta fashe dashi , cikin kidimewa yace lafiya meya faru Khairi na.
Nuna masa motar su Aliyu tayi da hannun ta dake shirin hawa kan titi.

Dakata yafad'a atsawace ahakan yasa motocin suka dakata cak .

Kallon khairi ya yi yace me sukayi miki ne?
Cikin kuka tashiga bashi labarin Abunda yafaru Abu daya taboye masa shine bibiyar sa da suke tayi Har yau din nan da suka same shi.

Saifudeen isa ya yi wajen motocin yana kallon kowani mota baki wul yace ina ogan naku yake cikin bacin rai.

Jin haka Yasa ,Aliyu yabude glass din motar sa yana mai Kallon sa.

zazzare idanu Saifudeen ya yi yace kamar nasan fuskar nan.
Ganin Aliyu yahada rai yasashi Fad'in bawan Allah me KANWATA tayi muku ,kuji tsoron Allah Arziki ba wayau bane .
Bazeyu Ku cutar da marainiyar Allah ba .
Akan kuna takama da Arziki yakarashe zancen cikin raunin Murya .

Aliyu Saida yashiga shock sossai jin Furucin maraici hakan yasa shi fitowa daga motar nasa shi kadai hannu ya bashi sukayi musabaha.

Saifudeen jin taushin hannun sa ya yi yawa yace azuciyar sa uhmm to ansaba kwana Ac ko ina Ac dole jiki ya yi taushi .
Maganar Aliyu ne yadawo da hankalin sa kusa .
Nan yashiga bashi labarin abunda yafaru tareda bashi hakuri ,nuna masa ya yi yaji haushin Abunda khairi tayi ya za'ai tayi wasa da rayuwar ta harda hawa kan titi akan wani shirmen ta *RAI DAYA* ne daga shi babu Kari dan Allah kaja mata kunnen sossai na Lura yarinya ce yakarashe zancen tareda shigewa motar ,basu bata lokaci ba suka bar wajen cikin hanzari.
Saifudeen tsaye ya yi yana kallon motocin nasu Har suka bace masa da gani .

Karasowa wajen khairi ya yi wacce take jiran taji meze fad'a sai dai ji tayi ya wanke ta da wawan mari ze kara mata ne.
Mijin Sultana ya yi maza yarike masa hannu.
Cikin Fushi yace Khairi wai yaushe zakiyi hankali ne ,jibi bawan Allah nan duk da mutum ne mai Arziki Amma yanada hankali da tunani , dan yace miki stupid girl beyi karya ba ,me ce ce ke inba haka ba .
Da rayuwar ki kike wasa khairi , ki kashe kanki abanza kisa hawan jini Yakama Baffa.

Sossai Khairi ke kuka Har cikin zuciyar ta bawai Marin takewa kuka ba , kuskuren data Aikata wajen tsayuwar titin.

Mijin Sultana hakuri yaringa ba Saifudeen ,dakyar ya hak'ura tareda kama hannun Khairi da Najwa yaringa fisgan su kamar yasamu yayan sa.

Shiko Isma'il kai tsaye gida yashiga yaba Sultana labarin abunda yafaru kuka ta saki tana salati tace khairi dan Allah ki rufa mana Asiri .
Mijin nata yace tunda gobe Baffa zedawo Yakama kije ki mata fad'a sossai .

*****************

Suna isa gidan sossai yashiga musu Nasiha khairi da Najwa yana nuna musu muhimmanci hak'uri da Rayuwa .
Jiki Asanyaye Khairi tace InshAllah Yaya bazan kara sa'insa da wani ko Wata ba.
Murmushi ya yi yana mai Kallon kyakyawar fuskar ta yace koke fa.
Najwa tashi tayi zata wuce gida tareda yiwa Khairi sallama.
Innaro da sallama tashigo hannun ta dauke da kayan cefane.

Gabanta yayi mummunar Faduwa a zaton ta ko khairi taba Yaya saifudeen labarin kan tilasta mata taci abinci ne.

Saifudeen ne ya katse mata tunani ta hanyar Fad'i Innaro harkin dawo Kinga Khairi Fad'a nake mata.

Ajiyar zuciya Innaro ta sauke tareda zazzare idanu tace Saifudeen meyafaru ?

Yana bata labari tashiga sallallami tana yarfe hannu rike da baki tace Khairi karki sake gangancin wasa da rayuwar ki kinji 'yata .
Cikin kissa da iya taku taringa bawa Khairi shawara akan ta daina fad'a da Masu Arziki dan ko kotu akaje baza'a iya shari'a dasu ba.
Saifudeen yace Innaro maganar ki dutse .

Khairi tace Yaya saifudeen ga wannan takardan tareda mika masa , yana karba yashiga warware wa.

Kallon sa take yanda yake bin rubutun dake cikin takardan yana kai karshe wani zufa ne ya keto masa .
Cikin tsananin bacin rai yace Khairi yaushe zakiyi hankali ne meya kaiki marin Shugaban Makaranta.

Cikin kuka khairi tace wallahi ba yau akayi ba nan tashiga bashi labarin tun farkon zuwan su kuma da dalilin mugun kallon dayake jifan ta dashi ne.

Ajiyar zuciya ya sauke yace wallahi tallahi be isa shidin banza akwai Abunda yake nufi dake Khairi kuma wlh zesan ya taboni badan antashi ba yanzu da munje Amma kijira Akramakallahu yadawo yace yau zedawo zamu San abunyi shidin banza .

Murmushi khairi tayi Saida kuncin ta ya lotsa .
Tace Yaya na wallahi nima dai nasan da Wata akasa .

*********************


Motocin nasu kai tsaye wani kerarareen gida a JRA suka faka Horne suke ta zubawa ,ahanzarce manyan bodyguard suka fiffito tareda wangale musu gate .

Basu bata lokaci ba wajen kusa hancin motocin su a wannan farfajiyar gidan Wanda kana masa kallo daya kasan a narkan kudi ,dukiya ta zauna .

Yanayin tsarin gidan da shuke shuken furanni da yawan ma'aikata dake kai komo cikin gidan.
Kokan su fito daga cikin motocin gabakidaya maaikatan gidan sun jejjeru kowanne su hannun rike da flawa suna Fad'in barka da zuwa sir ogan mu mai Adalci .
Uba goya marayu , maganin kukan mu.
Ahanzarce aka bud'e masa kofar yafito daga cikin Motar .

Kallo daya ya musu daga mazan Har matan harya sa kai zefice saiya dawo da baya .
Ahankali yake bud'e lallabansa yace Ina Nuriyat take ne ?

Kowanne zazzare idanu suka shigayi.
Cikin su Wata tace tana dakin batada lafiya uban Marayu.
Ya sallam ya Furta acikin zuciyar sa.
Tareda cigaba da tafiyar sa .
Magoya bayan sa suna bin bayan sa.

Wow nace lokacin da shiga wannan babban Falon ta Alfarma hatta TV plasma a kewaye shi da ado yalwatacce mai dauke da sunan JAN ZAKI.

Kujerun dakin nasa duk inda ake Neman kallo toya kare awajen hade carpet dake malale tsakiyar dakin mai zubin dawisu komai na cikin dakin Hash color ne.

Anas yau shine karo na Farko daya shigo wannan Falon zallan mamaki ne yakamashi ganin anrubuta JAN ZAKI ..
Arazane yake kallon ogan nasu yana maimaita Jan ZAKI rasa me bashi amsa yayi hakan yasashi Fad'in Yallabai kozan iya tafiya .
Cike da tsoron kada ya yi masa Magana akan Abunda Najwa ta fad'a masa.

Hannu ya masa Alamun yatafi .
Ajiyar zuciya ya sauke had'e da Fad'in Alhamdulillah.
be tsaya Wata Wata ba yafita zuwa farfajiyar gidan.

Cikin Maaikatan dake zarya wajen yakira mutum daya cikin su.
Yace dan Allah wannan bawan Allah shine JAN ZAKI?

Murmushi wanda yakira ya yi yace mu kanmu bamuda masaniya Amma dai naji ance wai Jan ZAKI uban gidan sa ne.
Kaga dole ne ya yi amfani da sunan sa acikin gidan nan shida , ba'a anan yake kwana ba yana gama uzurin sa zamu nemeshi mu rasa .
Da yadauki akun nan nasa mai shegen surutu .

Ajiyar zuciya Anas ya sauke yace nidai na fara zargin kamar shine JAN ZAKI fa.

Bawan Allah yace kai muma haka muke zargi saboda halayen sa daya da Jan ZAKI duk da bamu taba zama dashi ba.

Bodyguard dake kai komowa sukaga firan Anas da wannan mutumin ya yi yawa .
Taka musu birki sukayi ta hanyar Fad'in doka be baka damar ka Fad'i wani Abu daga cikin gidan nan ba dan haka akiyaye.

Hak'uri suka shiga bashi tareda barin wajen shiko Anas kai tsaye waje ya yi dan taran napep zuwa gida.


JAN ZAKI kallon lemukan da ake jera masa agaban sa ya yi , beyi aune ba saiga akun nasa ya iso wajen tareda hawa kan kafadar sa.

Kallon akun ya yi yace dan gata sai yanzu kasan na dawo ko?
Akun yace A'a inacen ina kallon cikin unguwar ne Uban marayu.

Rada yamasa akunne yace kana iya shan lemun nan uban mu.
.Babu bata lokaci yadauki kofun dake dauke lemun exotic ya kurba ahankali tareda ajiyewa .

Yana tashi magoya bayan sa zasu

8 / 13