Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RAI DAYA Inkiya JAN ZAKI by Ikilima Adam

Author :  Ikilima Adam Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 13

15K to 18K   out of 36.3K words

tayi tace Zaku Zo gida na sauraren wannan shirin na JAN ZAKI .
Khairi tsalle ta daka awajen tace laa kice yau ma laraba ana sakawa aikuwa zamu Zo da Najwa da takai ruwa gida zaki ganmu.

Murmushi Sultana tayi tana kallon Najwa dake son yin magana Ganin su Baffa yasa tayi shiru.
Najwa tace to Antin mu sai kingan mu.

Sultana tace to kannena tareda barin wajen dan zuwa daura girkin rana.

tsallaka titi tayi kasantuwa gidan ta a titi yake tareda dagawa su Baffa hannu ,suma hannu suka daga mata suna murmushi.

Baffa cikin sa'a ya samu motar daze kaishi babban tasha ,yahau motar tareda rike hannun Khairi yana Mata adua da mata nasiha akan tazauna waje daya yanzu duniyar nan annoba tayi yawa .
Tace InshAllah zata kiyaye .
Sossai sukayi sallama tana kuka motar ta tashi .
Shiko Malam Adamu sai Allah yatsare yake ta Furtawa yana daga masa hannu kallon Najwa da Khairi yayi yace kunga ni Gaba nayi dan haka kuyi maza ku wuce gida .
Yafice yabar su nan tsaye.

Kokarin juyawa suke Khairi ta hango wannan Motar datake mafarkin haduwa dasu dan daukar fansa, ta tahowa aguje kamar zata tashi sama.

Cikin hanzarin su suka matsa daga gefen titin tareda fadawa kan Juna suna fadin subuhannallah cikin tsananin Tashin hankali.

Ji suke kiiiiii motar taja wani wawan birki.
daidai wajen su..
Cikin Razani Khairi ke kallon motar yayin da taga ana kokarin bude motar idanun ta yayi tozali da ...................




Oh Masu Karatu kodawa Khairi tayi tozali ne .
Kudai Ku biyomu acikin daddan labarin nan *RAI DAYA* karku Manta paid book ne.


*Ku biya Ku karanta cikin salama dan ankusa gama Free page*

*09069080725* ko @⁨+229 53 72 61 62⁩
*🦜 RAI DAYA*🦜


*JAN ZAKI 🐆*

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*









*DAGA MARUBUCIYAR :*


*KAIKAJAWA KANKA*


*KANWATA*


*RAYUWAR MA'AURATA*


Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI*



*Paid book ne*


Normal group 500


Special group 1k


Acct nomba

*3115484026 ikilima Adam first bank*

Ko Katin MTN

Kan wanna layin

09069080725

Banason VTU


1️⃣0️⃣


Taji Muryan khairi da Najwa suna fadin Assalam Alaikum.

Amsa musu tayi da fara'arta Wanda daga khairi Har Najwa Saida sukayi shock mamaki ne ya kamasu ba kadan ba .
Khairi dake da baki tace Innaro inawuni ya gida , Najwa ma gaishe tayi kowannen su , cikin tsananin Mamaki .

Haba Khairi sai yanzu kuka dawo , Ku daina dare please Yaya na.
Kama hannun Khairi tayi cike da nuna damuwa tace yata yau ina kuka tsaya ne.
Najwa ce tabata Amsa da wajen Yadiko mukaje kinsan gidan wannan tsohuwar ba'a zuwa a fito da wuri .
Murmushi Innaro tayi tace hakane dafatan Yadiko tana lafiya nima zuwa gobe nakeson zuwa gidan nasu.

Khairi kallon Najwa tayi tace muje in rakaki kada mummy tayi miki fada ko tana mai kokarin Jan hannun Najwa.
Innaro tace please khairi inkinje kada ki Dade wallahi duk duniya yanzu babu wacce nakeji da kauna irin ki .

Kallon juna khairi da Najwa sukayi hakan yasa ta amsa da saina dawo suka fice daga gidan.

Itakuwa Innaro cikin tsananin Mamaki tace wannan yarinyar ya zanyi da ita karfa taje ta cika cikin ta agidan Rashida dan nasan bazata kyalesu ba.

Khairi suna isa gidan suka Iske Malam Adamu zaune sai fada yake yana Fadin ze dauki mataki akan su ace tun fitar su zuwa Makaranta babu Wanda ya dawo gida Har dare.
Mummy tace nasan dai baze wuce gidan Sultana sukaje ba ko gidan Yadiko basuda gidan dayawuce nan .
Sallamar su ya katse firan da suke .
Mummy ranta abace tace isassu sai yanzu kuka dawo ne tabbatu tana doso inda suke.
Malam Adamu yataso cikin tsananin bacin rai yace dan iyayen Ku ban hanaku yawo ,Ku bakwa iya Fadin zakuje wani wurin saidai kuyi gaban kan Ku , sossai yaringa musu fada kamar ze zane su.

Wai ma ina Saifudeen yake ne dan Har yasamuku idanu yau beje Makarantar naku bane.

Dukan su dukar da kai kasa sukayi cikin Muryan su dake nuna nama sukace Malam kayi hakuri bazamu sake ba InshAllah.

Mummy tace to ina Kuka tafi kuka zauna Najwa ce tabata Amsa da gidan Yadiko suka je.

Samun wuri sukayi suka zazzauna ,ganin duk jikin su a sanyaye yake yasa Mummy fadin maza kuyi sallah kuzo kuci abinci .

Babu bata lokaci suka tashi don dauro Alwala.

Wayar Malam Adamu ne yasoma ring yana dubawa yaga Baffa ne ,cikin hanzari ya daga wayar sallama dauke a bakin sa hade da gaisuwa.
Dagacen bangaren Baffa ya Amsa masa da lafiya Lau Alhamdulillah.
Daman zuwa nan da jibi Zan dawo InshAllah.
Kuma wallahi nasamu cigaba sossai dan Har shago nasamu acikin kasuwar kaga mun samu wajen fakewa.

Malam Adamu MashAllah yafurta yana washe baki yace kace harka tabude Allah yakaro Arziki da daukaka.
Kace Saifudeen ze zama dan gari yahuta da tallah.

Kwarai kuwa yahuta cewar Baffa , yawwa ina yayan ka suke ne ?
Murmushi yayi yana kallon su , yace Sallah suke yau gidan Yadiko suka wuni .

Baffa yace lallai Yadiko tasha Aiki ,in sun idar please ka hadani da Khairi in danjin Muryan ta, yakarashe zancen cikin kankantar da Muryan nasa.

Malam Adamu dariya yayi yasan dalilin kiran sa kenan .
Daga haka sukayi sallama.

Mummy kallon Malam Adamu tayi tace Baffa yasa Khairi aransa kuma dashi bata jin magana Allah dai yashirya su.

Da Ameen suka amsa .
Su Khairi na idar da sallah abinci ,suka soma ci .

Suna cikin ci ne suka jiyo Muryan Innaro tana kwada sallama.

Mummy da Malam ne suka amsa mata Sallamar ta cike da mamaki suke kallon ta ,dan suna iya rantsewa tunda Baffa ya auro ta , yau shine karo na farko data shigo gidan.

Mummy tace lale lale yau wa nake gani kamar Innaro , cikin sakin Fuska tace nice dakaina tareda gaishe su cike da ladabin dole .

Malam Adam fita daga gidan yayi dan zuwa massalaci dan sai an idar da sallah Isha'i ze dawo gida.
Yana fita Innaro tace haba Khairi gidan yamin zafi ni kadai ga wayata cajin ya dauke.
Mummy tace abinci suka tsaya ci kibari tasha ruwa sai Ku tafi .
Wani katutun bakin cikine ya tokare zuciyar Innaro nan take taji zuciyar ta ,na tsanan ta bugawa .

Abinci ta maimaita cikin sanyin Murya .
Khairi ta amsa da eh abinci nagama ci tareda saka hijab din ta.
Tace muje ko tana mai Kallon Innaro dake bin ta da kallo cike da mamaki.

Ganin Mummy na kallon su yasata Fadin Saida safe , khairi muje tafada tana kokarin rike mata hannu.
Hakan datayi ba karamin dadi yayiwa Mummy ba dan azaton ta Innaro tafara damuwa da damuwar khairi.
Suna ficewa daga gidan Mummy ta kalli Najwa dake kokarin gyara inda suka bata ,tace Najwa Kinga Innaro tasoma canja halin ta ko.

Najwa tace eh nima haka muka Lura yau da muka dawo daga gidan Yadiko kamar ta hadiye khairi dan so.

Sossai Mummy ta daga hannun sama ,tace ya Allah Ina mai godiya agareka daka nuna mun Wannan rana ya Allah kasa ta daure ko yarinyar nan ta samu sukuni wannan cutar Ciwon zuciyar nan ya ragu ajikin ta .

******************

Suna isa gida Innaro takai khairi dakin ta tareda ajiye mata kwanun abinci agaban ta ,tace haba yata be kamata ace inada rai ba kina cin Abinci wani gida ba.

Khairi dago kai tayi tana kallon ta tace wallahi Innaro Na koshi ne karki damu daga yau gida kadai Zan ringa ci tafada tana kokarin cire hijab dake jikin ta.

Marairaice Fuska Innaro tayi tana kallon Khairi tace dan Girman Allah kici abinci nan saboda ke nayi kuma harda nama da ice cream takarashe zancen tana mai bude mata ledan ice cream din.

Khairi Uwar kwadayi tace dan Allah kice harda nama ni yaushe rabona ,ma danaci nama tun a gidan Sultana.
Kwanun abinci ta jawo gaban ta .
Tareda daukar spoon zata soma ci tajiyo Muryan Yaya saifudeen shida Akramakallahu sun shigo gidan.

Kokarin tashi take Innaro tace dan Allah zauna mana Khairi na , ko kina tunanin Zan cutar dake ne.
Kada kai Khairi tayi tace A'a naga yaya saifudeen ne yashigo nakeson inje indawo kafun naci aitunda nawa ne zanci kada ki damu.

Innaro hada rai tayi cikin cool voice din ta ,tace khairi indai ni uwar ki ce maza ki zauna kici banason rashin biyayya tsakanina dake ki dauke ni kamar Mahaifiyar ki.
Tareda rushewa da kukan Munafunci wayyo khairi naso ace na iske Amina agidan nan yanda mutane ke bada sheda akan ta ,ana fadin mutumiyar Arziki ce .
Ina fatan nayi koyi da halayen ta.

Khairi mutuwar tsaye tayi hakan yasa ta nemi waje tazauna abinci ta bude tanakai lomar farko a bakin ta , taji wani irin juwa na diban ta , Cikin hanzari Innaro ta kama mata hannu ,cikin Damuwa tace khairi lafiya kuwa ?

Ganin yanda ta dafe kanta ,cikin karfin Hali Khairi tace babu komai kinsan nayi ciye ciye shiyasa kika ga ina kokarin Faduwa.
Abincin taci gaba daci tana santi ,nan da nan ta ture kwanun abinci takoma kan Ice cream din tana Sha cike da Jin dadi .
Innaro sossai taji dadin hakan barin dakin tayi tana fadin Alhamdulillah saura nan da kwana uku yarinya uhmm dafa kirjin ta ,tayi tace habawa khairi nawuce tunanin yarinya.

Akramakallahu ne yafito hannun rike da bakin leda Wanda kayan kala daya ke ciki.
Saifudeen cike da damuwa yace haba Akramakallahu yanzu baka bari sai jibi ba ,katafi gida ba.

Akramakallahu dake Murmushi yace yi hakuri gobe Zan dawo da Yamma InshAllah jibi zanje koyarwa makaranta yakarashe zancen tareda Nufo tsakar gidan.

Hango Innaro yayi cike da ladabi yagaishe ta tareda sheda mata yau zeje kauyen nasu sai gobe ze dawo.
Innaro sake da baki tace kaiko adaren uhmm saide muce Allah yakai ka lafiya.
Khairi ce tafito hannun ta dauke da roban ice cream .

Kallo daya ya mata ya kauda kansa gefe .
Khairi cike da Jin haushin halin ko inkula daya nuna mata ,tace uhmm wasu dai gasu nan baka gane Alkiblan su.

Daga Saifudeen Har Akramakallahu kallon ta sukayi , Akramakallahu yasan dashi take hakan yasa shi fadin KANWATA natafi Saida anjima .

Khairi samun kanta tayi dafadin Allah yatsare ,shiko Saifudeen kallon Innaro da Khairi yana mai fadin zanje in raka shi saina dawo.

Ficewa sukayi daga gidan kai tsaye hanya suka nufa .
Tafiya suke ahanya Saifudeen na bin sa abaya yace Kaga garin ya hade kamar hadari.

Akramakallahu juyowa yayi yana kallon sa hade dayin Murmushi yace Yaya saifudeen koma gida Zan karasa kaji InshAllah babu damuwa.
Saifudeen badan yaso ba yajuya zuwa gida.

Shiko Akramakallahu ganin Saif harya juya ,yasashi kara hanzarin tafiyar sa ,yanayi yana waige waige koda ya iso daidai fita kan Titin wayar ce yazaro daga Aljihun rigar ,cike da mamaki nake kallon iPhone 13 max hannun sa ban Ankara ba , naji yana Fadin na iso bakin titi.

Mamaki ne yakamani ganin ya kalli Wata bishiya dake bayan sa .
Tsalle yayi yabugi wani leda sai gata ta fado kasa.
Hannu yasa yadauki ledan nan ,warware ledan yayi ,saiga wasu kaya na Alfarma hade da agogo hannun sa .
Babu lokaci ya canza rigar jikin sa .
Takalmi ya saka cikin Abunda befi minti daya ba.

Motoci shida ne sukayi parking bakin titin gabadayan su fitowa sukayi suna fadin barka da warhaka sir.
Be tanka ba yadoso inda suke cikin hanzari aka bude masa ,motar yashiga tareda rufewa.

Kallon juna suka shiga yi shida Aminin sa , Salim yace kai meyasa ka biyo su .

Salim yace dan inga gari mana kai kadai ne dan Adam yafada yana mai karewa wandon jikin sa kodadde kallo .

Ganin kallon da Salim ke jifan sa dashi yasashi hada RAI ,dan yasan yanzu yana iya jefo masa tambaya .

Salim numfashi ya fesar yace uhmm watau dai ba'a son inyi magana to yau miskillanci ya tashi kenan.
Jin be tanka masa ba yasashi yin shiru.
Babu bata lokaci motocin nasu ,suka bar unguwar.


************************


Kashe gari


Headmaster ko barcin kirki beyi ba adaren jiya sossai yashiga damuwa ta yanda ze bullowa lamarin .
Wata zuciyar na fadin kawai ka Amshi kudin inyaso saikaje ka auro khairi Kaga riba biyu kenan.
Murmushi yayi yana tunanin yanda ze basu takardan Koran kuma wani laifi zece sunyi .
Tunowa yayi da Khairi ta taba Marin sa ,farkon zuwan su Makarantar .
Girgiza kai yayi yana murmushi hannun sa goye a baya yace tabbas wannan kwakwaran hujja ce .

Yau kam tun dawuri Innaro ta hadawa Khairi brek itada Saifudeen .
Suna gama karyawa tashirya cikin kayan Makarantar ,yau kam harda fesa turare ajikin ta.

MashAllah Innaro ta Furta ,tace khairi wallahi kinyi kyau kinata baza kamshi.
Kasaitaccen murmushi tayi Saida kuncin ta ya lotsa tace nagode Innaro mun tafi sai mun dawo takarashe zancen tareda fita waje dan Saifudeen yana jiran ta .
Fitowar ta yayi daidai da Fitowar Najwa kusan atare suka dau hanya .
Saifudeen na bayan su ,sai fadi yake Ku hanzarta mu tafi banson kuyi latti.
Kwabe baki Khairi da Najwa sukayi suna fadin ikon Allah, wallahi inhar saif ze rakasu ba karamin wahala suke Sha ba.
Adua suke ya Allah Yasa goben tayi dawuri yawuce Baffa yazo .

Saifudeen jin suna kus kus yace gulmata kuke ne?
Najwa ta zazzare idanu tace gulmarka kuma kawai firan mu , muke fa.

OK to naji maza kuyi Sauri banson jin kus_kus din nan yafada iya gaskiyar sa.

Suna isa Makarantar daidai kofar shiga yatsaya tareda zaro naira dari daga Aljihun wandon sa , yabasu su biyun godiya sukayi masa tareda shiga Makarantar.

Shiko Saifudeen juyawa yayi yana mai adua Allah Yasa su ringa gane karatun su.
Koda Khairi suka shiga Aji ,sun iske yau Sakina sai dariya take musu daga ta kalle su sai fashe da mugun dariya tana rike ciki.
Wata yar ajin su mai suna Aysha ta kalli khairi cike da tausayawa dan Sakina ta basu labarin Koran da za'a musu ayau.
Cikin sanyin Murya tace dan Allah kuyi hakuri karka damu da Abunda take hassada gamai rabo taki ce.

Khairi da Najwa sunji dadin Furucin Aysha hakan yasa sukayi shiru basu ko damu da Abunda Sakina takeyi ba.

Malamin turanci nasu yana gama musu lecture yafice acewar sa yanzu lokacin Akramakallahu ne.
Sallamar headmaster yasa dukan dalibai tashi
dan gaishe sa , Banda Sakina dake zaune tana taunan cingam .

Headmaster hakan be damesa ba saima kallon Khairi da Najwa yayi yace kuzo Ku sameni a office
Daga haka yafice.

Khairi da Najwa kallon juna sukayi ,kowani dalibi dawo da kallon akan su ,sukayi suna tambayar ko sunyi laifi ne?

Khairi Tace gaskiya bamu sani ba saide munje .
Sakina dariya ta fashe dashi tace kila ma korar Ku zeyi karku ja mishi bakin jini .

Basu bi ta kanta ba tunda sun dauki shawaran Aysha .
Suna isa office din iske shi sukayi yana latse latse wayar shi.

Dago kai yayi yana kallon. Su tareda hada rai tamau ,yace ke Ummulkhairi marin da kikamin rannan ban hakura ba .
Dan haka ga takardan Koran Ku nan nabaku ,kuje kunemi wani Makarantar Amma ba wannan ba.

Bakin Khairi na rawa tace kora fa kace Malam?
Daga mata gira yayi Alamun eh hakane.

Kan ubancen Khairi ta Furta tun ranar da hakan ta faru baka kore mu ba sai yau .
Najwa cikin bacin rai tace Amma kai headmaster munafuki ne wallahi .
Irinku karkashin wuta Zaku zauna.
Kuma Makarantar nan bana ubanka bane .
Wallahi saimunyi karar ka.
Headmaster kasa magana yayi yana Kallon su.
Azafafe Najwa ta kama hannun Khairi tace muje kyale banza kada ki tanka masa ai zamu koma gida ko.
Kuma Akramakallahu da Yamma yace zedawo saimu fada mishi Abunda ke Faruwa.
Khairi dan tsananin bacin rai kasa magana tayi dakyar ta Furta Najwa muje kan titi kinsan yau muke sa ran wannan mutumin zebi hanyar nan.
Shikuma headmaster kibarshi zeyi nadama zamu gani tsakanin mu dashi Waze bar Makarantar.

Cikin hanzarin suka iso kan titi saboda tsabar ranar da ake tsulawa nan da nan kishir ruwa ya kama su.
Hango mai tallan pure water sukayi tareda kiran sa .
Kowanne leda biyu biyu suka Sha suna maida numfashi .
Suna Sallamar me ruwan Khairi tace Allah yasa wannan mutumin ba karya yayi mana ba , bata gama rufe bakin ta ba.

Ta hango motocin nasu sun doso kai a aguje .
Cikin karfin Hali Khairi ta tsaya tsakiyar titin rike da kugun ta.

Motocin jikake kiiiiiiiiii sunja wani wawan birki dake nunin kadan ya rage na gaban ya buge ta .

Azafafe suka bude motocin su.
Cikin tsananin Tashin hankali ogan nasu yasa abude masa motar sa.

Khairi ganin ogan nasu na fitowa yasa ta cikin................




Taku Har kullum kyauta daga Allah
🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜

*JAN ZAKI*🐆





*DAGA MARUBUCIYAR :*


*KAIKAJAWA KANKA*


*KANWATA*


*RAYUWAR MA'AURATA*


Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI*



*Paid book ne*


Normal group 500


Special group 1k


Acct nomba

*3115484026 ikilima Adam first bank*

Ko Katin MTN

Kan wanna layin

09069080725

Banason VTU





0️⃣9️⃣


Daddy kasan akwai manyan kasa da suka kware a harkan computer Wanda a China sukayi karatun su ,ko su sun kasa sanin daga inda yake fitowa saini ,haba kaima kasan wahalar dani zakuyi akan Abunda babu nasara acikin sa.
Takarashe zancen tana mai kokarin barin d'akin .
Jin yariko hannun ta ne yasata dago kai ta kalle sa ,cikin marairace Fuska tace gaskiya Daddy bazan iya ba .

Sossai Daddy yaji ransa ya yi mugun baci ,nan da nan Muryan sa ta canza launi yace haba Sumayya ina Alfahari da tarin ilimin da Allah yabaki ,indai baki yi wani Abu akai ba , wallahi Zan rasa kujerar mulkina sonake in gana dashi in gayamasa bukatuna a gare shi ,kuma in masa gargadi yadaina tsoma bakin sa akan Abunda yashafi siyasa .
. sossai jikin Sumayya ya yi sanyi Allah yasani tana mugun kaunar Mahaifin ta ,kuma batason Abunda zeja ya rasa kujerar mulkin sa na senata yanzu takarar gwamna yake nema .

Karka damu Daddy yanzu na fahimce InshAllah zanyi kokarin yin iya kokarina ,kamar a gidan redio ,*Kukan kurciya* akafi saka jawaban sa.

Daddy yace kowace gidan Redio na Fad'in Nigeria duk suna sakawa narasa yanda akai maganar sa yake tasiri a zuciyoyin mutane .

Murmushi tayi tace karka damu bincike ne zefara ne akan gidan redio *Kukan kurciya* sannan Har Asibitin sa da makarantu zansa idanu akai kaidai barshi in kere Na jawo zabo na yawo wataran zasu hade ba takamar shi ,wayau ba ze hadu da wayanda suka kera shi.

Daddy besan sanda

6 / 13