Author : Ikilima Adam Category : African Stories & Novels
ita suna face din juna..
Babban rigar sa kodaddiya ya tattaro yana kuka tareda soma goge mata hawayen yace haba Khairi dîna yar Baban ta kiyi hakuri wallahi banson nisa dake ne shiyasa ga yayan ki Saifudeen baya zama gida kullum yana birni gun kai Albasa cikin kasuwar jahar Katsina....
Kara rusa wani uban kuka tayi cike da sakalci tace shikenan baffa ni kadai zanta zama Innaro tana cin zalina takarashe zancen tanama innaro gwalo batareda baffa ya gani ba....
Innaro Salati ta dauka tana yarfe hannun cike da takaicin su tace DUK abunda zakuyi saidai kuyi kuma ni wallahi baki isa kice sai Baffa ya sake ni ya auro wata eheee tana karkada kugu....
Malam Adamu yace ai mugun halin ku ke sakawa a sake ku inban da tsabar mugun ta yarinyar nan batada uwa fa rana daya uwar da kanin ta suka rasu .....
Sossai Baffa da Malam Adamu suka hau Innaro da fada sossai..
Itakuwa Khairi rarrashin ta sukayi..
Dakyar ta yarda zata zauna gidan dan taji Al'kawarin za'a tura ta makarantar boko Jan Zaki........
**************************************************
Wanene Baffa...
Baffa sunan sa Ibrahim Mohamed wanda yake cikin garin karamar hukumar Funtua Katsina State.....
A unguwar jabiri layin yan bokolo yake zaune inda anan ne gidan iyayen sa suke.....
Ya auri Matar sa ta Farko Amina wanda ta haifa masa yaya uku....
Saifudeen
Sultana
Ummul Khairi
Matarsa Amina yar garin Funtua ce itama iyayen ta suna zaune ne a unguwar mata....
Soyayya mai tsananin shakuwa Baffa yayi da matar sa wanda a lokacin iyayen ta bashi suke son ta aura ba kasantuwa talaka ne. beda komai Albasa yake talla...
Amina ta hadu da manyan masu Arziki kama Daga kan gwana 'attajirai biris taki yarda da kowa..
Baffa take so bata bukatar soyayyan kowani Attajiri...
Mahaifin ta yace tunda tace Mai tallan Albasa take so abata Amma da sharadi babu su babu ita..
Ya za'ayi duk dangin su babu wanda ya auri matsiyaci sai ita...
Hakanan dai akayi auren..
Tunda tace taji ta Amince
Tun daga wannan lokacin yan uwan ta suka cire hannu kan ta....
Bata isa ta tako kafarta tazo gidan iyayen ta ba...
Da tazo korar ta suke hakanan take hakura cikin kuka da bakin ciki
Take komawa gidan bukar su n'a Jan kasa.....
Baffa Sam baya son wulakancin da ake mata in taje gidan nasu shiyasa ya haramta mata zuwa gidan nasu....
Haka sukayi ta rayuwa cikin tsananin talauci wataran a wuni da yunwa
Har Allah ya arzuta su da yaya uku...
Washe garin ranar da ta haifi yar ta na ukun Aranar ne baffa ya dauko ta zekai ta Asibiti dan ayiwa yarinyar Allurar rigakafi ...
Suka hadu da wasu yan yan iska mutane su Shidda sai fadi suke ita ce...
Daya n'a cikin su yace yau shekara 13 kenan kullum sai mun zo unguwar nan.
Anya kuwa itace matar da muke bibiya kamar n'a miji take goyo
kaga nasan yanzu dan nata ya girma zekai shekaru 12 yanzu fa yake ma yan uwan sa misali.
dayan yace Alkur'an itace kuka sani Ko takara wani haihuwa ne awannan kauyen
Kuma wallahi mungaji dazuwa unguwar nan shekara shabiyu kenan kila wani auren takara nidai koba ita bace to suna mugun kama.
me kuke jira ne...maza ku harbe ta wallahi itace Ko mun huta shekara da shekaru muna abu daya..
Cikin tsananin tashin hankali Amina take kallon su bakin ta na rawa tace wallahi tallahi bansan wacce kuke nema ba.
Bani bace kama ce...
Dan Allah kumun rai karku kashe ni
Kunga mijina Na Nan auren saurayi da budurwa mukayi, cikin gigita take magana tana kokarin ajiye jaririyar ta a kasa.
Baffa be Ankara sai jiya yi sun harbawa matar tasa Alburushi daya akan ciki daya akan Fuska....
Nan take ta yanke jiki ta fadi daman koda suka fito sai Fadi take Baffa nifa yau wallahi inajin kamar mummunar Al'amari zefaru dani...
Yace mata ah Ah babu komai Adu'a itace maganin musiba...
Ganin Amina tana kalmar shahada rike da hannun Baffa dake kuka iya karfin sa jaririyar sai tsala ihu take.... Bebi ta kan ta ba.
Cikin muryan wanda rai ke d'af da barin jikin nata
Tace Baffa ga Ummul Khairi nan karike ta Amana dan Allah karka bari tayi maraici..
Tana gama fadin haka tayi kalmar shahada nan da nan rai yayi halin sa..
Ganin ta mutu ne suka d'au hoton Jinin jikin nata...
Basu tsaya wata wata ba suka haye mashinan su guda uku Kowanne su ya goya dan uwan sa abaya......
Baffa Innaliahi wa'inna yake Furtawa cikin kuka da tashin Hankali
ya mugun fita hayyacin sa yana Girgiza ta yana Ihu wayyo Jama'a kuzo ku taimakeni Wayyo ! Wayyo ina jama'a suke yana ihu cikin tsarkewan murya bakin sa na rawa yana Girgiza ta sai Fadi Aminatu dan Allah ki Bude Idanun ki...
Dan Allah karki mutu Wayyo Amina n'amiki Mafarkin Jin dadi da Arziki anan gaba zaki tafi ki barni.....
Inkika tafi waze raini Ummul Khairi.
Kan kace me wajen gabadaya makil da jama'a kowa nata sallallami suna ihun nan da nan suka hau koke koke......
Wata makociyar Amina kuma Aminiyar ta mai suna Rashida cikin kuka take Girgiza Amina datake kwance fuskar wasai cike da Annuri kamar zata budi baki tayi magana gawar ta.
Ganin Aminan bata Ko numfashi yasa ta rufe mata idanu nan take wajen kowa yanata fadin ALLAHU Akbar wannan wani irin zalunci ne...
A iya sanin mu Amina bata fada kowa nata ne...
Wasu Azzalumai ne suka kashe ta me tayi musu ne....
Babu bata lokaci jami'ar tsaro suka iso wajen sossai suka tsora ta ganin wannan matar yanda akayi mata kisan gilla.
Aune aune suka shigayi suka gama d'ube duben su awaje kallon su suka maida akan Baffa dake kokarin fita hayyacin Alamun ze sume....
Basuyi wata wata ba suka dauke sa cikin gaggawa kai tsaye Asibiti suka nufa dashi inda Likitoci Gêneral hospital Funtua suka raja'a akan sa.....
Itakuwa makociyar Amina daukan Jaririyar tayi takai gidan nasu inda taci gaba da basu nono ita da yar ta datake goyo...
Mahaifan Amina labari yaje musu akan Mutuwar yar su '' sossai sukayi sansani suka nufi gidan Baffa koda suka isa wayam babu kowa agidan ..
Cikin tashin hankali suka nemi a nuna musu gidan Iyayen Baffa...
Awulakance suka Shiga gidan ganin gidan duk laka ne ruwa cike à tsakar gidan bangon gidan da yayi bakin kirin gawayi suke kallo cike da mugun tsana suka karaso gidan nasu....
Mahaifin Baffa yana kuka zaune shida yan uwan sa duk sun jejeru suna kwasar gaisuwa....
Firgit suka tashi ganin d'angin Amina sun shigo da ruwan bala'i sai Fadi suke dangi matsiyata wallahi sai munyi shari'a daku yar ta mu kuka kashe mana...
Sossai babban yayar Amina ke kuka tana kokarin cin kwalar rigar........
Taku Har Kullum KYAUTA Daga Allah..
Karku Manta Paid book...
Free Page guda goma kacal zan baku...
Barkan mu da Sallah Allah ya maimaita mana...
Allah yajikan iyayen mu da kakannin mu da dukan musulman duniya Ameen ya Allah
🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜
*JAN ZAKI*🐆
*DAGA MARUBUCIYAR :*
*KAIKAJAWA KANKA*
*KANWATA*
*RAYUWAR MA'AURATA*
Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI*
*Paid book ne*
Normal group 300
Special group 500
Acct nomba
*3115484026 ikilima Adam first bank*
Ko Katin MTN
Kan wanna layin
09069080725
Banason VTU
0️⃣4️⃣
Har ogan nasu cikin isa yafito suka bashi hanya
Taku yake kamar beson taka kasa.
dukar da kai dukan yaran sa sukayi alamun girmamawa .
Karasowa yayi daidai inda khairi take tun daga kasa har sama yake bin ta da kallo tareda kau da kansa gefe daya ya maida kallon sa akan Najwa data zuba masa idanu .
Karamin tsaki yayi yanda bazasu iya jiyo sa ba.
Wanda aka mara yake kallo rike da kuncin sa yana shirin ramawa .
Hannun ya daga masa Alamun kada yayi mari.
Hakan Yasa cikin kunan rai ya tsaya cak kamar an dasa shi...
Itakuwa Khairi sai hura hanci take tana Fadin Aida ka barshi ya Rama Dana nuna muku karamin hauka banza dakiki ni akuya ce ko kaza da kake shirin buge ni da Mota..
Takamar Ku kudi ko .
Mu kuma takamar mu Allah ehee
Najwa tace wlh babu kodaya yar uwata Zo mu tafi dan Allah jibi kallon da suke jifan mu dashi....
Muryan ogan nasu sukaji yana Fadin dan Allah kuyi hakuri akasi aka samu...
Sossai Muryan nasa ya doki kunnuwan su dan babu Wanda yayi zaton zeyi magana hatta yaran sa...
Yarinyar dake cikin daya daga cikin jerin motocin ne tafito ranta abace.
Tace haba Yaya Aliyu hakurin me zaka bata itace fa tayi laifi .
Kutumar bura uban cen khairi ta Furta tareda bude baki tace yau Naga Wata yar iska me shigar banza watau ga awaki ko a buge mu dan .....
Saurin katse khairi yayi ta hanyar daka Mata tsawa Wanda Yasa ita da khairi hantar cikin su ya kada..
Yace stupid girl kinada mental problems ne yanda yayi magana cikin daga Murya gabadaya wajen kowa yayi tsit yarinyar data fito daga jerin motocin cikin hanzari ta koma motar ganin yanda yake a zuciye....
Itakuwa Khairi kuka ta saka tace Najwa dauko biro da papper nasan kin iya rubutu dan Allah rubuta mun Kalmar stupid girl din nan daya furta da kuma Mental problem..
Wallahi Nasan muguwar Kalma ce Alkur'an bazan bari ba .
Yasani ya ciwo bashi da baze iya biya ba..
Ganin yana kokarin komawa motar tasa tasha gaban sa..
Cikin tsiwa da fushi tace wallahi Zan nuna maka ba kai kadai ne kayi boko ba ...
Sossai kalaman ta suka kara bashi takaici kyaleta yayi batareda ya Amsa Mata ba..
Yashige mota abun sa..
Nan da nan duka sauran yaran sa duk suka shige motocin...
Wanda khairi ta Mara yanata Ayyanawa Aran sa saiya dawo ya zane ta .
Dan bata mari banza ba...
Motocin su nabarin wajen Khairi Tace yawwa Miko min takardan nan in boye ta...
Najwa Mika Mata takardan tayi tareda jero Mata sannu.
Tace badai kiji ciwo ba ko?
Khairi Tace aa banji ciwo ba kawaide Faduwar danayi ne naji azaba danaje gida Na gasa wajen ya wadatar..
Takarashe zancen tana kokarin saka papper acikin jakar ta...
Basu bata lokaci ba wajen barin titin kai tsaye gida suka nufa...
Daidai kofar gidan su khairi sukaga Baffa da Malam Adamu suna Alwala alamun sallah magrib ce zasu yi...
Kallo daya Baffa yayi wa khairi ya fadada Murmushin sa cikin zolaya yace yar auta ta yar Makaranta sai yanzu muke ganin Ku..
Ganin bata Murmushi yasashi Fadin subuhannallah yana mai Kallon Najwa da tayi shiru kamar ruwa ya cita...
Malam Adamu cikin halin damuwa yace khairi meya faru ne yar autan mu..
Kuka ta fashe da Wanda Yasa dukan su mikewa tsaye sukayo kanta hannun ta suka kamo tareda zaunar da ita tsakiyar su..
Baffa yace Najwa gayamana Abunda ke Faruwa dan maganar da yake daga ji yanayin Muryan sa ta canza ..
Najwa cikin sanyin Murya tashiga basu labarin Abunda yafaru harda kalamin daya batawa Khairi rai...
Baffa da Malam Adamu suka hada baki wajen Fadin muga papper ..
Mika musu tayi tana kakalo kukan shagwaba tace Alkur'an Baffa wanna mutumin saina Rama nasan mugun Zagi yamin da turan ci....
Baffa karban Papper yayi shida Malam Adamu . suka shiga warware wa duk da rubutun Najwa babu kwarewa aciki Amma tsaf ake iya karanta rubutun nata daya fito daga gabas yayi arewa...
Stupid Girl Mental problem Baffa suka furta kusan tare ..
Khairi kada kai tayi tace eh haka naji yafada shiyasa nasa ta rubuta kada in manta...
Please baffa da Malam Adamu nasan duk kunyi boko kunsan maanar hakan ..
Daga Baffa har Malam Adamun sun rasa yanda zasuyi su gayamata dan sunsan kuwa tanajin maanar hakan ankira ruwa....
Baffa ne ya saisaita nutsuwar sa yace khairi Na karki manta malamin Ku yana muku nasiha akan in wani ya zage ka baka Rama ba..
Kansa ya zaga narokeki daughter kiyi hakuri yar auta ta.....
Sake hada rai tayi tana kokarin fashewa da kuka tace yanzu bazaku gayamin me Maanar wannan Kalmar ba...
Malam Adamu katseta yayi da Fadin yata ai yanzu so muke ki gano da kanki tunda kin zama yar boko kedai kibar Sauri..
Sossai suka shiga lallabata akan ta manta wannan zancen ..
Itakuwa sarai tagane wayau suka Mata ..
Wayance musu tayi tareda fadin yawu ce..
Karban Papper tayi tace Baffa zanje dashi saboda in ringa koyon hada kalmomi..
Baffa da Malam Adamu kallon Juna sukayi
lta kan ta Najwa dake gefe zaune cikin sanyin jiki ta mike tareda fadin Khairi muje ko...
Bakin su dauke da sallama suka shiga gidan..
Iske innaro sukayi tana goge kafafun ta da sukayi Faso..
Kallo daya tayi musu ta. Bushe da dariya dan duk firan da suke awaje ta labe zaure tana sauraren su....
Ajiye dutsen gogan kafar tayi tareda Mike wa tsaye tace khairi..
Sai yanzu aka dawo daga zuwa Makaranta sai dare .
Khairi ranta abace yake shiyasa bata tanka mata ba
Najwa tace innaro munje gidan Anty Sultana ne ..
Innaro zazzare idanu tayi tace haba shiyasa Kuka Dade duk gidan da akwai maiko maiko nan ake ganin Ku sarakan kwadayi....
Khairi sossai takara harzuka tace eh gwamma mu gidan Antin mu ne mukaje kwadayin
Ke kuma yawon karere kikeyi kina fadin ana barin ki da yunwa bayan karya kike wallahi Baffa yana kashe dukiyar sa akan ki....
Innaro kada kai tayi tace ikon Allah mai karfi Na bara...
Shi uban naki har wani dukiya gare shi Banda wahala...
Be Tara komai ba..
Gidan da muke ciki da bashi yaita biya har yazama nashi ..
Khairi kara fusata tayi tanabin ta da mugun kallo tace ai gwamma shi yaci bashin yasai gida ..
Kekuwa gidan iyayen ki Na haya ne kuma....
Saurin katse ta Najwa tayi tace yi hakuri Khairi kidaina biyewa Innaro kema kinsan ba kaunar mu take ba ..ayanda tayi furucin Innaro sossai jikin ta yayi sanyi...
Cikin duniyanci irin nata tace nasan Papper ne hannun Ku kunason sanin meye aciki...
Dasauri khairi da Najwa suka maida kallosu akan ta dan Sam sun manta tsohuwar malamar Makaranta ce.....
Cikin hanzari Khairi taje gun Innaro dan ta mance fadan da suke tace..
Dan Allah Innaro gayamin fassaran wannan kalmomin Fiddo Papper tayi tana warware wa tareda Mika Mata...
Innaro Na karba ta karanta ta bushe da dariya tace lallai Khairi ko wanene wlh ya gama dake kyakyawa mace kamar ki ze zaga da kalmar stupid girl..
Harda karawa da Mental problem...
Kallon Juna khairi da Najwa sukayi tareda Furta ki gayamana me hakan yake nufi dan Allah ....
Innaro tace yana nufin wawiyar yaringa mai tabun hankali ..
. sossai suka razana dan tunda ta taso babu Wanda ya taba zagin ta da kalma mai kamanceceniya da wanna sai shi...
Najwa dafa Khairi tayi cikin rarrashi tace Baki ji Abunda Baffa ya fada bane..
Kansa ya zaga tunda baki Rama ba.....
Khairi Banda tafasa babu abunda zuciyar ta takeyi aguje tayi dakin nata...
Tahau gado tareda rushewa da uban kuka mai cin rai...
Innaro da Najwa tare suka shigo dakin sossai Innaro ke mamakin zallan shagwaban Khairi saboda an zage ta take wannan sakarcin laifin Baffa ne tafada cikin zuciyar ta.....
Afili kuma nuna tausayawa tayi tace khairi dole ne fa ..
Ki rama inhar Ummulkhairi Dana sani ce......
Tashi tayi tazauna da rinannun idanun ta da suka kada jajir.....
Tace Innaro zauna ki gayamin hanyar da zanbi in Rama ....
Bayan sun zauna dukan su ne tashiga musu bayanin dole ne wanna wurin hanyar sa ce.
Indai suna bibiyan wajen a time din da suka hadu lallai wataran zasu ganshi.....
Najwa ta yarda da shawaran Innaro tace Amma dan Allah karki gayawa su Baffa dan ze iya hana mu...
Innaro tace haba taya Zan gayamai nida nakeson inga ta rama...
Azuciyar ta sai fadi take uhmm angayamiki masu kudin birni sunada mutunci ne uban ki beda kudin daukan lauya yaro besan wuta ba saiya taka.
Saida sukayi Isha'i Khairi ta raka Najwa gidan nasu.
Nan ma kara samun waje sukayi suna ta bawa Maman Najwa labarin yanda Makarantar yake itako dariya take cike da so da kaunar su..
Tace Khairi ki kwana nan gidan mana ...
Zazzare idanu Khairi tayi tana rike Baki tace Mommy kema kinsan Baffa baze bari ba ...
Bayason ina nisa dashi ...
Mommy jigum tayi tace khairi in kikayi aure ya Baffa zeyi ne..
Cikin rashin kan gado irin nata da wauta tace aure fa kikace ai babu dalilin dazesa inyi aure Mommy muna nan tare daku nida Najwa gira ta daga wa Najwa tace koba haka bane..
Najwa tace kwarai kuwa Mommy muna nan daram daku ...
Murmushi tayi tana kallon nasu adua tayi musu tareda shafe musu jiki dashi..
Khairi ganin dare nayi yasata mikewa agajiye ta dau hanyar gidan nasu ...
Da yake Katanga ce ta raba gidan nasu ...
Iske Baffa tayi zaune yana fada da Innaro ...
Yana Fadin haba wai meyasa bakida tausayi ne Safara'u meye ribar ki .
Na fadawa Khairi gaskiyar Abunda aka rubuta ajikin papper ai dukan mu .
Mun sani nida Malam Adamu Amma muka lallabata ta....
Dan tabar zancen kinsani Na sani Ummulkhairi tana dauke da Ciwon zuciya ,bana son bacin ran ta ...
Allah shike rayawa Amma ban zaci Khairi zata rayu har zuwa wannan lokacin ba..
Ki kiyaye Na gayamiki in ba haka ba Zan sauwake miki in taimaki Wacce take da bukatar kulawa irin ta Mahaifiya ...
Cak Khairi ta tsaya daga inda ta labe domin sauraren su...
Wasu hawaye masu zafi ne suka shiga silalo Mata daga idanun ta zuwa kan fuskar ta....
Share hawayen nata tayi takarasa shigowa cikin gidan...
Baffa najin Sallamar ta ya katse firan da yake cike da kakalo Fara'ar dole..
Yace khairi Na Ashe zaki dawo ki kwana gida...
Jiki Asanyaye Tace Baffa aidole indawo kaima kasan bani iya kwana wani gidan in ba naka ba....
Kallon Innaro take da Alamun sossai jikin ta yake amace akan fadan da Baffa yayi Mata...
Saida Safe tace musu tayi dakin nata....
Sam bekawo Aran sa taji firan da sukayi ba ya zata gajiya ne yake dawainiya da ita......
**************************
Kashe Gari
Tunda sassafe suka shirya domin zuwa Makaranta...
Innaro da kanta tashiryawa Khairi brek dan tasoma tsorata da kalaman saki daga bakin Baffa....
Khairi
Koda tagama shiryawa cikin uniform din Makaranta blue black din wando da Farin Riga farin hijabi .
Sossai sukayi kyau da shigar itada Najwa..
Basu tsaya Wata Wata ba.
Suka kama hanyar su tazuwa Makarantar JAN ZAKI....
Sossai suke shan tafiya akasa kasantuwa akwai dan nisa...
Khairi cikin gajiya take kallon Najwa tace kinga daga yau aringa bamu kudi muna hawa mashin dan ni nasoma gajiya....
Najwa tace au nifa bana ganin nisa wajen kece dai shagwababbiya bakyason motsa jiki...
Khairi Murmushi ta sakar Mata tace naji tunda shedar da zaki min kenan..
Koda suka iso Ajin yayi daidai da shigar