Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RAI DAYA Inkiya JAN ZAKI by Ikilima Adam

Author :  Ikilima Adam Category :  African Stories & Novels

Chapter   1 / 13

1 to 3K   out of 36.3K words

🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜

*JAN ZAKI*🐆





*DAGA MARUBUCIYAR :*


*KAIKAJAWA KANKA*


*KANWATA*


*RAYUWAR MA'AURATA*


Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI*



*Paid book ne*


Normal group 500


Special group 1k


Acct nomba

*3115484026 ikilima Adam first bank*

Ko Katin MTN

Kan wanna layin

09069080725

Banason VTU




0️⃣2️⃣



Tana kokarin cin kwalar rigar Mahaifin baffa 'tuni Yan gidan suka tattashi suna fadin subuhannallah baiwar Allah kinada hankali kuwa wannann sa'ar Mahaifin ki ne..

Yayar Margayya mai suna Sadiya tana hura hanci tace kutumar bura uban sa'an Mahaifina sun Mika *KANWATA* GA Yan mafiya shine zasu fake da kashe ta akayi shegu taron Mayu kawai..

Dakyar Malam Adamu ya kwaci Mahaifin Baffa hannun Sadiya ...
Sauran dake cin bala'i suka ce wallahi sai munyi shari'a daku kujira kuga meze faru daku..

Kuka sossai Mahaifin baffa sukayi shida Mahaifiyar sa Yadiko suka ce daman auren yayan masu kudi akwai wulakanci.....

Malam Adamu da autar su Baffa mai suna Lami tace Ah Ah wallahi kowa yasan Amina mutumiyar arziki ce kuma yar gidan Arziki ce iyayen ta Nada tarin dukiya Amma ta zabi auren yaya Sulaiman kuma zamantakewar su bata taba masa gori ko gajiyawa da talaucin sa ba......

Kowa gidan suka ce tabbas Amina ya ce Allah yana fidda rayayye acikin matacce.....

Bayan kwana biyu baffa yadan samu lafiya har anbasu sallama sun dawo gida..
Yazama kamar wani wawa be magana abinci ma sai an matsa masa yake ci..

Suna zaune aka kawo musu sammaci daga kotu.
Daga dangin Amina..

Shari'a akayi sossai Baffa yace bashine yakashe matar sa ba kazafi suke masa....
Kasantuwa talakawa ne Saida baffa yayi Wata shidda gidan yari...

Sannan suka samu kudin daukan lauya har aka sake wani zaman a kotu..

Inda sukayi nasara akayi belin din sa...

Dangin Amina sun nemi abasu yaran baffa yace har Abada jinin sa ba zasu zauna da masu zuciyar kafurci ba...
Duk da hk Yan uwan Amina sunci Alwashin zasu kwashe yaran su fitar dasu karatu America .

Mahaifan Amina sossai sukayi nadaman korar ta da suke yi intazo gidan .
Sun zabi mata hakane Dan tagaji ta kashe auren tadawo gare su.
suyi mata aure gidan Hutu kasantuwa yar Hutu ce yarinya mai tarin ilimin zamanii Dana Addini....



***************"**********"""""""""""""""



Cigaban labari......



Yau takama Monday tunda ummulkhairi tasan makarantar boko Baffa zekai ta jiya batayi barcin kirki ba har wasu mafarkai taringayi gata acikin makarantar ...
Tana horan dalibai .

Nan da nan tafito cikin shigar Atamfa ,man Vaseline kadai ta shafa tareda dauko wani yar gyalenta yar shara shara mai Arha ta yafa...

Madubi ta dauko tafito kofar dakin ta tana kallon kanta acikin madubin ita kadai take dariyar ta...
Cikin washe baki tace Alkur'an nayi kyau yau bakin ciki ze kashe Innaro yayi daidai da fitowar Innaro DAGA bandaki sake da baki take kallon Ummulkhairi da duk hankalin ta yatafi akan wanna madubi da take kallo taji an wabce madubin DAGA hannun ta...
Cike da Masifa ta dago kai zatayi Fada...
Innaro ta galla Mata harara cikin Jin haushi tace zaaje yawon iskanci ko....

Waike ubanki baze miki aure bane .
Yafi ki zauna ki takura Mata da miji ki Hana su zaman lafiya......

Kan ubancen cewar khairi..
Madubina kika kwace sannan kika hada da Zagi harda min gori...

Kuka ta fashe dashi tanata shure shure wayyo Allah Baffa shikenan anmun gori ...
Tareda daura hannu akai..

Afirgice Baffa yafito daga dakin hannun sa dauke da rigar da yake shirin sakawa...
Bakin sa Na rawa yace khairi wacece tamiki gori keda gidan uban ki.....

Nuna Innaro tayi da yatsa tana shure shuren tace ba gatanan ba ...
Har da cemin wai Na Hana Mata da miji sakewa.....

Innaro hararan su take tace nafada saime karya nayi meye ya Hana kahada khairi itada Sultana kai musu aure ai duk girman su DAYA ........

Baffa cikin kunan RAI yace wallahi Safara'u ki fita hanyar yata Ina ruwanki da ita ..
Yarinyar nan ba akan ki take ba wallahi akan ta saiki bar gidan nan bafa tsoro bane shiru shiru Na daga miki kafa ne Dan mutane su rage surutun Ina sakin Mata saboda khairi......
Inkika kaini bango babu Abunda baze faru ba ...
Innaro jikin ta yayi mugun sanyi Dan duk auren da takeyi saboda rashin haihuwa Ake sakin ta...

Shikuma bedamu da haihuwar ba. .
Yi hakuri maigida bazan sake ba Amma kaja Mata kunne tasani zaman Uwar ta nake....

Khairi buga kafa tayi kasa tace kutmlesinan ashema zaman uwa ta...
Baki isa ba ...

Cike da rarrashi baffa yatada khairi daga zaunen
Madubin ta .
Ta nuna masa hannun Innaro ..
Amso Mata yayi ya Mika Mata cike da kwantar da Murya yace kiyi hakuri yau makarantar Jan ZAKI ze dauki manyan dalibai.

Murmushi tayi Saida kuncin ta ya lotsa tana fari da idanu tace Baffa kasan me yace Aa saikin Fada khairi Naa.....

Tsaki Innaro taja tawuce tabarsu Dan bata iya kallon iya shegen Khairi.....


Khairi Tace Baffa wai Makarantar in munje secondary za'a sani ko university....ne tayi tambaya iya gaskiyar ta..

Sossai Baffa ya Dara yace keko khairi yanzu ZAKI Fara karatun fa..

Sunce zasu Amshe Ku Aji shida primary keda Najwa....
Baffa uhmm yau Innaje Ajin nan hatta Malamin saiya jinjina dan har shi Zan koyar....

Sake da baki Baffa ke kallon ta babu daman yace Aa ba haka bane.
Yanzu ta tada bori..

Murmushi yayi yace Kwarai kuwa ai kece ZAKI Koya masa...
Basu bata lokaci ba wajen yin break koko da kosai .
Saida ya tabbatar ta koshi yaja hannun ta suka fice.....

Kai tsaye gidan Najwa yatura ta dan kiranta su Tafi...
Koda taje iske Najwa tayi har ta shirya...
Cike da ladabi ta gaida Rashida Mahaifiyar Najwa.....

Mommy Najwa tace yata har kin iso zauna kiyi break ...

Aa nakoshi Mommy Kallon ta tamaida akan Najwa dake kokarin zura takalmi a kafar ta...

Tace muje danyi Sauri Baffa Na waje Na jiran mu.....
Babu bata lokaci sukayi was Mommy sallama itako da adua tabi su cike da tausayin Khairi harda guntun hawayen ta...
Tace khairi naso Abban naki yabarni inci gaba da rainon ki bayan na yaye ki...

Amma Kash baffa be yarda ba ...
Cike da kewar su tashiga fiddo kwanukan wanke wanke............


Tafiya sukayi mai dan nisa kafun su Iso Makarantar.....

Najwa itada Khairi Saida suka kalli Juna suka Dara.. .

Waoh Najwa ta furta tace wanna makarantar saikace ginin Ajanna...

Khairi Tace uhmm ai Makarantar Jan ZAKI ne dole ya hadu..
Matashi ne ko tsoho ne babu Wanda yasani haka naji ana firan sa gidan rediyo.....

Ginin Baffa yayi gaba suka take masa baya...

Office din headmaster suka nufa.
Daman yasan da zuwan su sake da Baki yake kallon Khairi subuhannallah ya Furta acikin zuciyar sa...

Yace wanna yarinyar Anya bil'adama ce kuwa irin wanna uban kyau haka ...
Ga yar Uwar ta duk da bata kaita ba...
Amma itama akwai kyawun halitta...
Shagala da kallon nasu yayi...
Wanda Yasa khairi ta tsargu shiko Baffa murmushi yake yayi yace Bawan Allah kayi shiru inata magana ...

Sau uku ya maimaita maganarr besan yanayi ba....
Khairi daukan takalmin kafar tayi ta kwada Masa Mari dashi.

Afirgice yadawo hankalin sa rike da kuncin sa yana Jin zafin Marin..
Yace haba baiwar Allah kina da hankali kuwa Ina shugabar makaranta ki mareni......

Cikin Fada tace an mareka din ya za'a yi ka tsura min idanu kai maye ne??

Baffa cikin ban hakuri yace Yallabai kayi hakuri dan Allah .
Bazata sake ba..

Maida kallon sa akan khairi yayi yace yata baa zagin malami ko dukan sa suma kamar iyayen ki ne....

Najwa tace Yi hakuri Malam bazata sake ba...

Headmaster murmushi yayi yace azuciyar sa dan ta burgeni ne Zan hakura da Wata gaja ce tamin haka korar ku Zan yi wallahi..

Maida kallon sa yayi akan Baffa yace karka damu yawuce Biro yadauka yasoma rubuce rubuce takardun dake gaban sa...
Dago kansa yayi tareda kallon Khairi yace ya sunanki....

Itako turo baki gaba tayi Wanda Yasa yaji kamar ya kwana yana kallon bakin ....

Suna Na Ummulkhairi Sulaiman tafada cike da gadara...

Itako Najwa yana tambayar ta bata tsaya Wata Wata ba tafada masa sunan ta Najwa Adam....
Nan da nan Baffa yayi Abunda yadace yatafi yabar su......

Khairi zaune suke office din sa .
Suna jiran ya gama yayi musu jagora zuwa Ajin nasu.......... .

Shiko kyalesu yayi yana ci gaba da Ayyukan sa....
Sallamar da akayi ne yasashi daga kai daga rubutun da yake yi

Wani Matashi yaron yagani Fari sol Ajin Karshe.....

Tafiyarsa ma abun kallo ce ...
Headmaster dake kallon kyakyawan Matashi yace azuciyar sa yau dai ranar kyakyawawa ne....

Kallon sa ya maida akan Matashin yace Bawan Allah daga Ina haka..

Sai asannan ne Khairi da Najwa suka dago kai suna kallon sa...
Waouh Najwa ta furta tana mai kare masa kallo ta kasan idanu.....
Yana sanye cikin jallabiya Fari , kyakyawa ne Ajin karshe yanada yalwatacen saje a fuskar shi.....
Badan sunji yayi Hausa ba zasu iya rantsewa baya ji tsaf kama yake da larabawa jajayen labban sa take kallo da zararan idanun sa mai cike da kwarjini..

Kallon sa ya maida kan headmaster tareda Mika masa takardun hannun sa....

Cikin hanzari ya Amsa ya soma warwarewa .

Ganin An Rubuta sakone daga JAN ZAKI...kuma ga sa hannun sa nan akai

Haka Yasa shi gyara zaman sa dakyau...

Bakin sa Na rawa yace Naga takardan yana magana ne akan kaine mai Koya musu karatun Addini acikin makarantar...

Saida Aji shidda ne basuda Malamin Addini....
Matashin Saurayin kayataccen Murmushi yayi dan tunda yashigo dakin kallo DAYA yayi wa khairi da Najwa ya dauke idanun sa....
Yana tabe baki..

Zazzakar Muryan sa mai dauke da sirriku ne sukaji yana Fadin ai babu matsala yafada cike da gamsuwa....

Good Ya furta tareda tambayar sa sunan sa.....
Shiru yayi kamar ne nazari...
Sannan yace J A Mohamed......
Headmaster ganin bako ne daga Jan ZAKI yace..
Yawwa Mohamed muje in kaika Ajin naku...
Kallon sa ya maida akan khairi da kanta yake aduke tun zuwan J A taji wani muguwar Faduwar gaba.....

Jiki Asanyaye suka tashi tareda bin bayan nasa

J A na bayan headmaster yana karewa Makarantar kallon tsafta sossai yakasa cire idanun sa akan dalibai dake ta safa da marwa acikin makarantar......

Koda suka isa Ajin dalibai da suka gauraye Ajin da surutu kowa yayi tsit ganin headmaster.....

Aladabce suka tashi domin gaishe shi hannu yayi musu alamun kowa ya zauna......

Kowannen su zama sukayi idanun su nakan J A dake tsaye rike da takardu hannayen sa....

Khairi kallon Najwa tayi suna magana kasa kasa tace kinga nan ne Ajin Na mu...
Najwa cikin yin kasa da murya tace shine Allah Yasa mu iya bokon nan mu ma.....ehee kinsan lauya muke son karanta.

Gyaran Murya headmaster yayi yace ywwa wanna dakuke gani ya nuna J A Muhammad shine Malamin daze ringa koyar daku Addini daga gobe zefara koya muku...... InshAllah.

Bagabadaya class cikin ladabi sukace barka da zuwa Malam Muhammad.
Kayataccen Murmushi yayi yana kallon su cike da kulawa
Yace dafatan Na same Ku lafiya suna Na Muhammad Amma anfi kirana da J A..
Ina fatan Zaku bani hadin kai domin koyar daku Abunda Allah yace da manzon sa .

Gabadaya Ajin suka dauka da InshAllah Malam J A ..

Headmaster dake Murmushin amsar da suka bashi .
Kallon sa ya maida akan Khairi da Najwa da suke kus kus..

Yace ywwa ga sabbin dalibai nan hannun sa Yasa ya nuna Wata daliba dake rubutu mai suna Sakina yace tashi tsaye...

Hakan Yasa ta ajiye Abunda take ta tashi ..

Kinga baki ne yaran nan dan Allah ki ringa dan koya musu Naga alamun kan su naja bazaa Sha wahala ba ashekarun su nan Ajin shine daidai dasu inhar sun maida hankali .

Sakina kallo daya tayiwa khairi ta razana da mugun kyawun ta wani mugun yawu ta hadiye tace InshAllah Zan koya musu..

Nuna musu wajen zaman nasu akayi ...
Khairi cikin hanzari taje tazauna tana zazzare idanu dan atarihin RAYUWAR ta wanna shine karo na farko data shigo cikin Alumma da sunan karatu har ita Najwa din...
Bayan sun zauna kowacce daliba ta maida hankalin ta akan nazarin da suke Amma dukan su hankalin su nakan J A dake tsaye hannayen sa goye a kirjin sa...

Kallo daya yayi wa khairi ya dauke idanun sa ..
Yana gama magana da headmaster tare suka bar Ajin.......

Koda ya Fita wajen makarantar kara juyowa yayi yana karewa Makarantar kallo Na tsafta..

Hannun sa Yasa cikin Aljihun rigar sa .
Yana murmushi tareda Fiddo wani ...........


*Karku manta paid book ne*

*RAI DAYA*



*Taku har kullum kyauta daga Allah*


09069080725
🦜🦜 *RAI DAYA*🦜🦜

*JAN ZAKI*🐅




DAGA MARUBUCIYAR

Kaikajawa kanka

KANWATA


RAYUWAR MA'AURATA


Yanzu kuma gani dauke da sabon book dina
*RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI*🐅


*Paid book ne*

Vip 500

Spécial 1k

Àcct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ko Kuma Katin MTN ta wannan nombar 09069080725



Inayiwa Al'umma musulmi gabakidaya Barka da sallah Allah ya maimaita mana..

Da sunan Allah mai Rahama mai Jin kai nafara wannan littafin ya Allah ka haneni rubuta abunda ze gurbata tarbiyyan Al'umma kabani ladan fad'akarwa.
Ya Allah kasa yanda muka fara lafiya mu kare shi lafiya...
Ka karemu da yan hassada ka hanemu dayiwa wani hassada...
Ka azurtamu da halal ka hanemu da cin haram komin kankartar sa...
Ya Allah kasa muyi kyakkyawan karshe ka shirya mana zuri'ar mu.........
Kasa Albarka acikin neman mu....

Fitacciya Daga cikin kungiyar Jarumai writ associat

IKILIMA ADAM

(kyauta Daga Allah)


0️⃣1️⃣


........... ✍️

Wayyo Allah ! Wayyo !
Allah ! Ataimaka mun gudu take shararawa iya karfin ta cikin dajin Allah babyn dake bayan ta yanata rusa uban kuka Alamun ya jikata........


Mazan dake bin ta wajen su shidda n'a hango 'kowannen su rike da makamai, suna harba bindiga amma baya samun ta...
Sai kaucewa take.....

D'are ne sossai misalin karfe shabiyun d'are touchla ne hannun ta take haska gaban ta..
Su kuma suna rike da fitilar wayoyin su.....

A'cikin wannan yanayin ta buga uban tsalle ta fada wani kango mai cike da kayoyi yaron nata dan wata biyun dake kuka iya karfin sa muryan sa ta shake da gajiyawa da kukan da yake.
Allah yataimake ta barci barawo yayi awon gaba dashi.....

Su kuma wayanda suke bin sahun ta '' sai zagaye zagaye suke suna nishi sama sama...
Ogan tafiyar su cikin tashin hankali yace taya mukayi sake *RAI DAYA* ta gagare mu kamawa.....

Cikin su wani yana huci sama sama tareda haska tochla cikin ciyayin nan yace Mun shiga uku mun lalace in shugaba yasan Wannan matar ta kubuce mana bazamu ji da dadi ba....

Wayar babban nasu ne yasoma ring yana dubawa yaga shugaban nasu ne '' cikin tsananin fargaba da tashin hankali d'asuka bayyana a fuskar sa..

Yace Ranka ya dade wallahi gamu cikin jejin nan wallahi ta bace mana babu ita babu Alamun ta Ko kukan dan nata mun daina ji......
Dagacen bangaren cikin tsananin tashin hankali yana ciza labbansa ga wani uban Zufa ne t'a karyo masa nan da nan hantar cikin sa suka kada...

Na'urar dake gaban sa yasoma dandannawa yana zufa yace kash amma dai babu waya hannun ta..naso inyi trakin din layin nata insan inda tabuya....

Yaron nasa yace gaskiya oga tun agida tabar wayar nan..
Cikin tsawa Shugaban yace maza kuci gaba da neman ta 'tana cikin jejin nan ku haska wayoyin naku n'a tabbatar kukan dan nata zai sa kusan inda tabuya......

Itakuwa tana cikin wannan kango sai zazzare idanu take' nishi take fitarwa à hankali tareda toshe bakin nata......à hankali taleko kai ba abunda kake gani sai fararen Idanun ta cikin wannan uban duhun take dan lekawa taga Ko sun tafi ne....
Ganin suna d'af da ita ya sata kara cusa kanta cikin kango innaliahi wa'inna ilairajun kadai take maimatawa à zuciyar ta tareda kankame yaron dake sauke ajiyar zuciya akai akai......



Ihu mai firgitarwa sukaji Daga Sama wanda alamu sun nuna kura ce...
Ta nufo su Gadan Gadan suna ganin tahowar kuran nan habawa suka ari n'a kare gudu suke tsulawa shima Kuran iya karfin nasa yake bin su.....

Suna gudu iya gudu har suka isa kan tsakiyar jeji wannan kuran sai haushi take ta samu nama....

Itakuwa ganin Kura be tsaya ba hakan yasa tasa taci gaba da gudun nata uban kaya suna hannun ta ' wanda sune suke bata matukar wahalar gaske....



**************************************************


Bayan shekara Ashirin da biyar 25 yrs........




Baffa ne zaune kofar gidan nasa zaune yana shawarar yanda zekoma birni dan soma kasuwancin nasa.....

Abokin sa malam Adamu ne zaune kusa dashi suna zantawa...
Yace baffa kaiko inka je birni wa da wa kasani ne....
Baffa dariya yayi irin tasu ta manya yace ah lallai Adamu kace wani abu ' ina ruwana da sanin wani abirnin nida doya zan ringa kaiwa...

Kaga Ummulkhairi so nake in sata boko..
Kuma d'ana bincika bokon ance wai tayi girma tunda yanzu shekarun 13 aduniya shiyasa za'a sata aji shidda din frimari school...
Kuma nayi magana da wani malamin dake kula da makaranta sunce su kansu basu taba ganin wanda ya gina makarantar ba komai nasa umarni ne koda ya siya filin ance wasu ne yaturo suma din wayanda yaturo din basu taba ganin sa ba....

Rike da baki Malam Adamu yace ikon Allah yau nakejin sabon Al'amari to taya haka zata kasance ne....
Wai ma ya sunan wanda keda makarantar ne yajefo masa tambaya.....

Baffa yace Karma sunce *JAN ZAKI*

Kai kai wai daman wannan shahararren makarantar n'a Jan zaki ne..
Habawa shiyasa makarantar tacika haduwa da tsaruwa wallahi ashe ba banza ba...
Kuma makaranta ga mugun Arha kamar ta gwanati cewar Malam Adamu......

Ance wannan makaranta shine n'a talatin daya bude À Nigeria kuma dukan su irin gini daya ne ansa Jan zaki........

Ihun Ummul Khairi sukajiyo innaro n'a bugun ta...

Baffa ce ya la kamar muryan ummu '' malam Adamu yace ita ce mana..
Babu bata lokaci sukayi cikin gidan koda suka isa gidan iske Innaro sukayi sai dukan ummul Khairi take babu sassauci.....

Baffa cike dajin zafin wannan bugun yace ke Safara'u ki sakar mun ya nace...
Saboda baki san zafin haihuwa ba shine zakiyi ta dukan marainiyar Allah......

Kuka sossai Innaro ta fashe dashi tana salati tace yau Baffa ni zakawa gorin haihuwa...

Malam Adamu cikin takaici yace dole ya miki gorin haihuwa mana jibi har waje akejin karar bugun da kike mata Saboda kin samu jaka Ko ?
Wai shin ma laifin me tayi miki ne....

Kallon su suka maida Akan ummul Khairi dake rusa uban kuka iya karfin ta...tana shure shure akasa cikin kukan shagwaba ganin baffa tace wallahi Baffa saika auro wata matar in bahaka ba ni ka kaini gun d'angin uwata sossai take ihu tana shure shure....

Babba durkushewa yayi ya Dago Daga zaune tareda mikar da

1 / 13