Author : Ikilima Adam Category : African Stories & Novels
su da adua.
Tafiya suke Khairi ta juyo tana kallon Najwa tace Kinga wanna dan iskan wai mu zegayawa wannan banzan daya zageni rannan a Makabarta gidan sa yake kinji Rainin wayau fa.
Najwa tabe baki tayi ,tace aidaga ji karya ne Amma shawaran da Zan baki , Khairi ki ajiye makaman ki mutanan nan fa ,Masu Arziki ne koda kin hadu dashi na tabbatar babu abunda za ki iya masa bodyguard din sa kad'ai sun ishe ki .
Zazzare idanu Khairi tayi tana nazarin Kalaman ta ,cikin takaici take maimaita sunada Arziki ,fuskantar Najwa tayi cikin dan bacin rai ,tace waike me kike d'auki masu Kud'i ne suna iya taka kowa ,suna iya cin mutunci kowa a zauna lafiya?, buga hannun tayi a kirjin ta ,da karfi har tanajin sautin karar buguwar cikin kankanin lokaci launin idanun ta suka canza zuwa ja ,tace wallahi Najwa wannan mutumin ko Dangote ne uban sa Alkur'an saina Rama ni za'a nunawa Arziki Zan nuna masa ko a talakawan akwai isassu
Ganin ta fusata sossai Yasa Najwa dafata cikin Muryan rarrashi tace haba Khairi na ,da wasa nake miki har kin dau zafi
Harara khairi ta watsa Mata cikin fushi tace wallahi kinban haushi gaba tayi Najwa nabiye da ita abaya cikin hanzari suke tafiya babu Wanda kewa dan uwan sa Magana.
**********************
Wani babban maaikata an rubuta *KAMAL ENTERTAINMENT* da manyan bak'i a kasar rubutun sun rubuta welcome .
Babban gate ne nahango wasu dattawa su uku sun tsaya , dai-dai kofar shiga suna tsayawa wajen kofar ta bud'e kanta .
Suka shige daga ciki.
Mai Gadi da su bodyguard cike da girmamawa suka fara barka da zuwa sir.
Fuskokin su d'auke da Murmushi suka amsa da yawwa Banda mutum daya acikin su.
Wanda shine ogan nasu.
Haraban gidan suke bi da kallo babban waje ne cike yake shuke shuken furanni da tsuntsaye dake ta shawagi awajen .
Cigaba da takun su sukayi tareda isa daga cikin Maaikatan.
Wani office suka shige da Alamu daki ne ,na meeting .
Alhaji KAMAL Wanda tun zuwan su yake cikin tsananin bacin rai ,samun wuri ya yi ya zauna hakan yasa dukan su kowannen su ya zauna .
Cikin daga Murya yace waiku dan Allah wani yaro ne wannan *JAN ZAKI* na Dad'e da Fad'in kuyi iya kokarin Ku ganin munyi tozali dashi Amma ace kowannen Ku yakasa .
Biyun dake zaune Kansu aduke suna sauraren yanda yake magana cikin Fushi da kunan rai.
Alhaji Lurwanu Murya a tausashe yace ,wallahi tallahi ranka yadade sanin kanka ne ,mun kai shekara Ashirin zuwa sama muna maka duk Abunda ka samu .
Wannan yaron wallahi munyi iya yin mu dan mugano daga ina yake fitowa Abunda ze baka haushi shine ,yana Neman ya karya duk wani kudurin mu akan takaran da muke nema excellent .
Alhaji Garba dake , murmushi ,yace haba Alhaji KAMAL kwantar da hankalin ka ,abu nafarko da zamu fara shine mu nemi gidan jaridar da suke saka bayanan sa gidan Redio,sannan mu samu wayanda ake ba kwangilar gine ginen sa...
Alhaji KAMAL kallon sa yake yana goge zufan da ya karyo masa ,hade dayin Murmushi yace Amma kai kanka yana ja wallahi ai shiyasa idan dabara ta kare min dole nake nemo Ku kaida Lurwanu ,kuma wallahi nayi naam da shawaran ka .
Yanzu gayamana yanda za'ai mukai ga matakin nasara.
Alhaji Garba dake kallon Shugaban nasu yace kasan dawa za'ai amfani cikin wasan nan kuwa ..
Girgiza kai dukan su ,sukayi cikin kosawa dajin zancen nasa.
Ni aganina Asa Sumayya tabi diddigin wannan yaron zazzare idanu dukan su sukayi Alh KAMAL ransa matukar a bace yacxe kako San me kake fad'e kuwa Sumayya Yata ce fa?
Kwarai kuwa nasan Yar ka ce dole Saida mace a wannan zaman ,kuma macen ma irin yar ka.
Tanada ilimi sossai ta fanni lauya tunda shi take karan ta , koka mance pratical da akai na lauyoyi itace tazo a na daya.
Gabadaya dakin saida yadau shiru babu abunda kake ji sai bugawan zuciyoyin su da sanyin Ac
Alhaji KAMAL cire gilashin dake Fuskar sa ya yi yana kallon su , cikin yarda da zancen yace Garba ka kawo shawara mai kyau Wanda dukan mu kwakwalwar mu , ta toshe indai Sumayya ce magana takare zamu zauna da ita ,nan dai suka shiga tsare-tsaren yanda Sumayya zata fara aikin da zasu sanya ta..
************************
Khairi da Najwa zaune gaban akwatin redio suna sauraren bayanan Jan ZAKI akan kula da tarbiyyan yara Matasa musamman yan mata .
Jin haka Yasa Sultana murmusawa tace laa yau Jan ZAKI fadakarwar sa akan irin Ku ne Khairi.
Najwa da Khairi kallon Juna sukayi , suna jinjina yanda yake magana cikin Muryan sa mai dankaren dad'i mai jan hankalin mai sauraron sa.
Najwa tace khairi ya naga duk kin wani nutsu kamar ba ke ba..
Jiki Asanyaye tace wallahi Khairi maganganun sa ,sun matukar tasiri wajen shiga jiki na ,aduk Sanda zanji Muryan Jan ZAKI nan ji nake kamar wani bangare na jiki na ne juyowa tayi tana fuskantar Najwa had'e da ajiye redio akasa takara da cewa wallahi Najwa ina kaunar mai Fad'in gaskiya cike da kamala ,dama ace Jan ZAKI dan gidan mu ne dayaga biyayya dan ban gajiyawa wajen sauraren sa, ba kamar Yaya saifudeen ba shi kullum fad'a takarashe zancen cikin kasalalliyar murya.
Najwa tace lallai Khairi kin yaba da hankalin Jan ZAKI ban taba jin kinyi yabo ba sai yau ,kinsan ko a Masu kud'in akwai masu tsoron Allah da bin umarnin sa ,saidai lamarin Jan ZAKI yana matukar bani tsoro yan jaridar ya sukeyi wajen samo rahotannin sa bayan baya zuwa saidai su samu faifan audio na Muryan sa.
Khairi tace shiya baiwa kansa sani , nasan yanada dalilin sa, Kinga tashi muje gida kada Yaya saifudeen yazo Bai same mu ba kin San halin sa.
Dakyar sukaci abincin gidan Sultana dan sossai Khairi ke tsoron yayan nasu shi Sam baya mata da sauki .
Sultana ganin basu da nutsuwa yasa ta rike hannun Khairi cikin sanyin Murya tace inkinje Ku gayawa Yaya saifudeen yakamata muje gidan iyayen Mahaifiyar mu .
Hada rai Khairi tayi sossai ,tace haba taya zamuje gidan da baa kaunar Baffa Alkur'an bazan je ba ,kuma din wallahi bakuda zuciya ne bakwa kishin baffa cikin bacin rai take fada ko sallama batayi wa Sultana ba tawuce fuuuu kamar iska .
Najwa Ganin fitan Khairi yasata fadin ,anti Sultana Saida Safe aguje tabi bayan Khairi.
Itako Sultana sossai tazama kamar Gunki a tsaye tana nazarin yanayin khairi Anya batada Aljanu kuwa .
Takai minti Ashirin tsaye tanata sake-sake daga karshe barin wani tunani tayi tareda shiga band'aki dan dauro Alwala.
*************************
Dai-dai shiga gidan khairi tajiyo Muryan Innaro tana ba Yaya saifudeen labarin tun safe suka bar gida ,batareda sun Fad'i inda zasu je ba..
Sossai jikin Khairi yad'au rawa ,tana k'ok'arin juyawa dan tayi gidan Mommyn Najwa taji an.....................
Taku har kullum kyauta daga Allah
Karku Manta paid book ne
Ki biya ki karanta cikin salama
🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜
*JAN ZAKI*🐆
*DAGA MARUBUCIYAR :*
*KAIKAJAWA KANKA*
*KANWATA*
*RAYUWAR MA'AURATA*
Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI*
*Paid book ne*
Normal group 500
Special group 1k
Acct nomba
*3115484026 ikilima Adam first bank*
Ko Katin MTN
Kan wanna layin
09069080725
Banason VTU
0️⃣7️⃣
Taji an fiskota a zafafe cikin tsananin bacin rai yace ,tundazu nasan kina labe nan wajen ,watau ita Najwa guduwa tayi ko har gida zanje in same ta.
Ke zakakura shine zaki gudu kije cen ko .
Cikin tsananin Tashin hankali khairi ke kallon sa nan da nan idanun ta suka kawo ruwa ,tace wallahi Yaya ba tun safe na bar gidan nan inbaka yarda ba, ka kira Baffa tunda sanda mukayi masa rakiya Innaro bata gidan nan taje barka haihuwar dangin tsiyan ta takarashe zancen tareda banka mata muguwar harara.
Innaro dake sauraren su ta buge da salati tana yarfe hannu, cikin kuka tace kaji Abunda ta fada ko wai dangin tsiya?
Saif tsawa ya dakawa Khairi yace Amma yau Na tabbatar bakida kunya koba komi ai Innaro Uwar ki ce ,kuma matar baban ki kuma a haife ta haife ki.
Turo baki Khairi tayi gaba tace ni wallahi bata haife ni ba ,matar da bata Sona tana min sharri.
Kuma wallahi ka bugeni akan ta sai Allah ya.....
Rufe mata baki yayi tareda cika ta ,dan bayason ta karasa fadin Abunda tayi Niyar fadi.
Dawo da kallon yayi akan Innaro dake kuka yace Innaro kiyi hakuri Khairi yarinya ce karama sossai yayi ta rarrashin Innaro har ta sauko Amma aranra tana kudurin inda tana auran Baffa saitayi sanadin da Khairi zata bar gidan.
Itako Khairi Fada yashiga mata tareda bata Umarnin taba Innaro hakuri , Sam taki bata hakuri tace badai Innaro ba tunda bata kaunar ta itako bazata bata hakuri ba koda kuwa ze kashe ta ne.
Ganin da gaske take ne yasa shi fadin shige daga ciki kiyi wanka ,kizo inbaki tsaraban Dana kawo miki harda Fara , wani uban tsalle khairi ta yi tace Allah Yaya dagaske kazo min da farar nan mai mugun dadi Na garin nan ,gyada mata kai yayi Alamun eh.
Innaro ganin bata ita suke ba taja tsaki tawuce tana magana kasa _kasa tace ai wayannan mutanen akwai mugun son kai jifa yanda ya zaburo kamar Wanda ze Mata hukunci gaskiya Amma gashi ya buge da rarrashi .
**************************
Anas yana isa Asibitin Jan ZAKI likitoci sukayi caa akan sa , sossai yake ihu yana Fadin dan Allah Ku dubamin Fuska radadi nakeji ,wayyo kaina ze fashe Ku agaje ni yakarashe zancen yana sakin Kukan radadin Azaban Ciwon da yake ji.
Likitoci ganin halin dayake ciki yasa basu tsaya Wata Wata ba sukai masa Alluran barci , ganin yayi barci ne suka shiga duba fuskar sa , sossai shatin hannu suke gani cike da mamaki suke kallon junan su .
Cikin Abunda befi minti goma ba sukai masa Alluran daze taimaka masa akan kashe radadi da Ciwon kan dayace yana damun sa.
***********
Sultana shiru take tunda su Khairi suka barta ,tana Fadin oh Allah jamaa wai wanna yarinyar kodai magani zanje nema nata ne kullum yarinya sai sangarcewa take tana girma Amma kuma takasa hankali ,mijin ta yashigo yanata kwada sallama bama tasan yanayi ba.
Yana shigowa dakin kallon ta yake yanda ta zabga uban tagumi , hannun ta yakama firgit ta dawo hayyacin ta , Murmushin yake tayi tace sannu da zuwa maigida na .
Yawwa ya Furta tareda samun waje ya zauna kusa da ita hannun ta , yakama ya hade da nashi hakan yasa ta dago kai tana kallon yanda hannayen su, suke tsarke cikin Juna yace haba Sultana tunanin me kikeyi ne ,karfa ki manta na ce miki in kinada damuwa ki sanar min nine abokin shawaran ki.
Ajiyar zuciya ta sauke tace yi hakuri maigida ,bawata matsala bace daya wuce kanwar Khairi, nashiga damuwa nan tashiga bashi labarin Abunda yafaru ,jinjina Al'amarin yayi yace inbanda abun ki Sultana ita Khairi kishin Baffa take karkiga laifin ta yarinyar ce bansan ya akai ba takeda zafin rai saidai mu rakata da adua Amma sainake ganin harda kuruciya zata bari ne, da kalamai Masu dadi yaringa kwantar wa Sultana hankali ,harta saki jikin ta ,tace gobe InshAllah zanje gida inga Yaya saifudeen , mijin nata yace Allah yakaimu ahaka dai suka zauna itada Mijin nata suna Firan su cike da ban shaawa.
*********************
Tafiya yake shi kadai cikin jeji yanayi yana waige waige , laptop a hannun sa ,dakuma Wata tsuntsuwar Aku akan kafadar sa .
Akun ne yayi masa rada a kunne yace Yallabai ka canza wannan hanyar ,muyi gabas .
Aikuwa babu musu ya canza hanya cikin hanzarin sa saidai yayi tafiya mai dan tsawo kafun ya iso daidai wani rami mai uban zurfi ganin ya tsaya awajen ne ,na tsaya kallon me yake shirin yi .
Akun dake kafadar sa sai kalle kalle yake gabas da arewa ,kudu ,Yamma , sannan yace Yallabai bismillah .
Jin Furucin sa yasashi dago wani murfin karfe tareda taka wani matakala dake cikin ramin yashiga cikin wannan ramin yana shiga yasa hannayen sa yarufe.
Ni kaina Ikilima Adam zazzare Idanu nayi dan abun yayi matukar bani mamaki matuka .
Daga cikin rami Wata duniya ce na hango babban gida ne sossai cike da ma'aikata da security ,ganin isowar sa ne yasa duk sukayi caa akan sa suna fadin welcome sir ,daga musu hannu yayi yana tafiya cikin Sauri saurin sa, akun na kafadar sa.
Kokan yakai hannun sa wajen bude kofar , da kanta tabude kanta ,babu bata lokaci Yasa kai tareda isa babban Falon nasu , Mama ta taso tace haba Aliyu yau akayi kayi dare ne kuma kafita kai kadai wallahi hankalina ya tashi gashi kai baka fita da waya.
. kallon ta yake cikin marairace Fuska tareda samun wuri ya zauna kusa da ita , wash ya Furta cikin kasalalliyar Muryan sa mai nuna zallan gajiya yace Am sorry ,Mamy na wallahi yau ayyukan ne ,sun min yawa kuma kinsan gobe Zan fita da safe gun karamin Aiki na.
Isowar Nusaiba ne yasasu dago kai suna kallon ta ,fuskar ta dauke da Murmushi tace Yaya na barka da zuwa .
Dakyar ya Amsa mata da yawwa tareda maida kallon sa akan Mamy yace ni zanshiga daga ciki , please kada akawo mun abinci na koshi yayi maganar kamar Wanda ke shirin kuka.
Akun nasa ya kalla dake makale a kafadar sa yace dan Lele ka sauko mana , gobe mun hadu da safe InshAllah be gama rufe baki ba akun yayi fuffuke ya sauko kan center table tsakiyar daki.
Akun ya kalli Mamy yace wash Ku kale ogana yagaji ,dani zakuyi firan .
Aliyu
Saida Safe yafurtawa Mamy batareda ya kalli , Nusaiba ba data kafe sa da idanu ba.
Cikin hanzarin sa yabi corridor dake sadashi da dakin nasa.
Yana isa dakin fadawa bandaki yayi kai tsaye tareda yin wanka da ruwan dumi yana wanka yana tunanin wannan labarin dayaji akan wannan yaron nasa da yaji ance Wata ce ta mare shi yana kwance Asibiti ana kara masa ruwa
So yake yagano wacece wannan kuma meye alakar su ,kuma shi meyake kallo da har mace zata fi karfin sa ,taron dangi sukayi masa ne .
.rasa mai bashi Amsa yashi hanzarta fitowa , tawul din sa mai taushi kamar auduga ya dauko yafara goge jikin nasa .
Kayan barci ya saka tareda hawa kan gadon sa , yayi tareda bude system din sa dan ganin Abunda ke Faruwa a labaran duniya.
Fadarwar da yayi akan matasan yara yaga ansa agidan jarida , murmushi yayi saida kuncin sa ya lotsa ,tareda lumshe idanun sa ,yana mai cigaba da latsa keyboard din system din sa , yana gama duba labarai be wani tsaya wata Wata kai tsaye yashiga email din sa nan ma yaci karo da sakonni ratata ,binsu yake daki daki yana karantawa Amma babu Wanda yayi wa reply dan yana matukar jin kasala ajikin nasa ,wani Sako ne. Yagani na karshe kasan email din sa , da dukan Alamu sabon email ne kokarin dubawa yake yaji idanun na na masa dishi dishi ahaka har barci barawo yayi awon gaba da shi batareda ya duba ba.
Mamy da Nusaiba fira suke akan yakamata ace Aliyu yayi aure zaman ya isa hakanan , Nusaiba cikin yin kasa da murya tace Mamy ni gaskiya da dai da zaki hada aurena da Aliyu dakin taimaka min.
Firgit Mamy ke kallon ta ,tace Amma Nusaiba yau Na tabbatar bakida hankali kina mace Amma kece kike Neman a aure ki .
Kuma ba wannan ba ,inason Aliyu yayi aure Amma ki sani ba yanzu ba dan akwai wani babban Abunda nake son ganowa cikin yan kwanakin nan inhar Allah Yasa na gano abunnan ,zan duba ingani ko zaki iya auran sa ,inkuma yana da raayin auren ki , bismillah nikam saidai in biku da adua.
Sossai Jikin Nusaiba yayi sanyi tareda dukar da kanta kasa , cikin ban hakuri tace Mamy kamar ranki ya bace kiyi hakuri bazan sake ba .
Harta tashi zata fice ,Mamy ta dakatar da ita ta hanyar rike mata hannun ta tace dakata yata.
Cak ta tsaya tana rintse idanun ta , sauraren me zata ce takeyi.
Mamy tace wallahi ina kaunar ki Nusaiba , Amana kike a hannuna ,bazan taba cutar dake ba .
Aliyu fa tamkar yar Uwar sa ta jini ciki daya ,ya dauke ki Amma kinsan komai yana iya canzawa ikon Allah yawuce wasa inhar Allah ya karkato hankalin sa , Nina wa fatan Alkhairi Zan muku.
Please karkiyi fushi da kalamai na daughter.
Sossai jikin Nusaiba yayi sanyi tace InshAllah Mamy nabi shawarar ki tareda yin murmushi ta rungumi Mamy .
Ita ma Murmushin tayi mata tareda Fadin tashi ki kira mun yar Aikin nan Asabe ,tazo da daurawa Aliyu ko coffee ne , jin sa nake harda wani fadin kada akawo masa abinci bakiga ko tanka masa banyi ba takarashe zancen cikin kwaikwayon yanda yayi maganar.
Sossai Nusaiba ta Dara tace ainasan ba kyale shi zakiyi ba ,sa mishi idanu kikayi mutum sai shegen son rashin cin Abinci .
****************
Kashe Gari .
Yaya saifudeen, rike da hannun Khairi da Najwa ze kaisu makaranta .
Cikin hanzarin yake jansu , khairi tace haba Yaya kajamu a hankali mana saikace barayi .
Tsaki yayi yace nasan halin ku sai Kun tsaya tsokana kafun , kuje Makaranta dan haka bazan amince ba indai ina gari..
Har Makarantar yakai su ,Saida ya tabbatar sun shiga Aji sannan yadawo kofar Makarantar yana karanta sunan Makarantar Jan ZAKI.
Sallamar da akai abayan sa ne yasashi waigowa .
Hannu Muhammad J A yabashi sukayi musabaha.
Saifudeen yace inakwana kwana ?
Malam ya Amsa da lafiya Lau Alhamdulillah .
Saif kallon sa yake cikin farar jallabiya sanye da farin hular saka akan sa , yace sai anjima dama kannena nakawo Makaranta .
Amma kamar kaima malami ne a makarantar nan yafada tareda zuba masa idanu.
J A yace ya sunan kannnen naka ?
Saif yace Ummulkhairi Sulaiman da Najwa Adam.
Tunani yake kamar yasan Masu irin wanna sunan.
Yace kamar ajina suke ,Amma ban Dade da fara koyar dasu ba .
Saifudeen yace MashAllah ya sunan ka Mallam?
Jim yayi kamar me nazari tareda dago kansa ya kalli rubutun sunan Jan ZAKI dake rubuce a ajikin Makarantar ajiyar zuciya ya sauke.
Yace Sunana Muhammad A J.
MashAllah cewar saifudeen tareda yi masa sallama yabar wajen.
Ganin Saif harya wuce yasa Shima kai tsaye yayi cikin Makarantar be zarce ko ina ba sai