Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RAI DAYA Inkiya JAN ZAKI by Ikilima Adam

Author :  Ikilima Adam Category :  African Stories & Novels

Chapter   12 / 13

33K to 36K   out of 36.3K words

ce.

Wani mummunar Faduwar gaba ta doki zuciyar Akramakallahu ya maimaita kalaman sa yace Amaryan JAN ZAKI fa kace.
Daman tasan shi ne , saifudeen yace A'a zolayarta nake kasan batada Aiki sai sauraren Redio saboda shi .

Khairi ganin be amsa mata sallama ba yasa tashigo tareda ajiye kwanun abincin ko kallon inda yake batayi ba , tafice.

Akramakallahu dake kallon Fitan khairi yace ai duk wannan Abunda takeyi kuruciya ce .
Kuma a maganar ta datayi rannan cewa tayi batasan meye so ba.
Daga haka sukaci gaba da hirar su , cike da burgewa.


Kashe gari


Tun karfe bakwai Safe duka gidan suna karyawa sukaji Muryan dan Sako daga mai gari yana shela.

Yana fadin yaku jama'ar gari mai gari ya gaishe Ku ya kuma ya gaishe Ku.
Yace a sanar daku nan da sati uku ranar juma'a akwai gasar aure .

Duk wacce taga yarta batayi saurin samun Miji ba ,tana iya kai sunan ta.
Yan mata Biyar kacal ake bukata , Mai gari yayi Alkawarin daukan nauyin kayan auren su .

Khairi dake shan shayi azabure ta tashi kamar an mata joni da wutar lantarki , tace Baffa inason aure inaso asa sunana acikin jerin sunayen matan da za'a gudanar da gasar domin samun zakaran dazeci gasar ya aure su.

Cikin zazzare idanu Baffa da Innaro sukace Khairi kinkosan me kike fade kuwa?

Kwarai kuwa nasani tafurta cike da isa nace aure nakeso kuna min tambaya bayan kunji Abunda na fada.
Akramakallahu dake dakin yana shirin fitowa , zancen nasu yasashi karasowa cikin Gidan.

Cikin Kuka Baffa yace haba Khairi dan Allah ki rufa min Asiri inma auren kike so Zan miki Amma ba cikin gasa ba.

Khairi da zuciyar ta ke tafasa tace Baffa wallahi tallahi a gasa nakeson asaka aure Na.
Kuma babu fashi inhar ka hanani wallahi Zan kashe kaina takarashe zancen tana sakin kuka mai cin rai.

Zazzare idanu Akramakallahu yayi yace Khairi Mahaifin ki , kike gayawa aure kike so babu kunya , kuma har kina fadin a gasa kike so a saka auren naki.

Murmushi tayi mai ciwo tana kallon shi , tace Akramakallahu aure fa nace inaso ba cewa nayi zanbi duniya ba ,innayi laifi anan wajen awajen Allah Banda laifi .

Baffa cikin tsawa yace Khairi bazan saka sunan ki acikin wannan gasar ba .
Ki fiddo Miji ko waye shi Zan aura miki koda kuwa ayau ne .
Banda tallan kai Khairi.
Na rokeki .

Akramakallahu mutuwar tsaye yayi yace Khairi ba magana ake miki ba.
Tsuki taja tana kallon Akramakallahu tace aisai kuyita yi nina gama Nawa zancen , kafun na wuce Makaranta yanzu zanbiya gidan mai gari in sanar masa da bukata ta.

Zazzare idanu suka soma dukan su .
Akramakallahu yace Amma .......

Dakata tace mishi ta hanyar daga masa hannu tace Inaruwan ka ne .

Daman nasan babu ruwana da harkan ki.
Amma Saifudeen yazama jinina dan haka dole inji haushin Abunda kike shirin aikatawa na gangancin.

Dan tsabar bakin ciki Baffa fita daga gidan yayi zuciyar sa , na tafarfasa yana Fadin Khairi yaushe ki ka canza bansani ba , khairi sakayyar da zaki mun kenan tafiya yake kamar wani zautacce shikadai ahanya .

Akramakallahu kallon Khairi yayi yace muje Makaranta ko indan antashi saikije gidan mai garin ki sanar masa ko yabata amsa cikin jin haushin ta.

Gyada masa kai tayi alamun gamsuwa da bayanan sa .
Suna fita sukaci karo da Najwa tare suka wuce .

Innaro zazzare idanu tasoma tace nashiga uku , kenan magani yakama khairi meye mafita ne ko komawa zanyi gidan Malam ince masa a karya inzeyu da wannan tunanin ta zura hijabin ta.


Koda Khairi suka isa Makarantar iske sabon headmaster sukayi inda ya gabatar musu da kansa.
Cike da Jin dadi khairi tace yanzu kam mun huta da barazanar kora.

Akramakallahu sossai Abunda yafaru agidan su khairi ya hanashi sakat ,hango fuskar Baffa yakeyi a idanun sa , asanda yake kuka.
Kallon khairi yayi tareda hada rai yana mai hararan ta ,kasan idanu.

Mamaki ne yakamashi ganin shigowar Sakina .
Tana sanye cikin kayan Makarantar sai wani hararan sa take tana tauna cingam.

Cikin tsawa yace keee! dakata daga ina haka?

Shiru tayi ta Gaza magana hakan yasa yakara fadin ki fitar min daga Aji naceee.

Tsintar Muryan Mahaifin ta , yayi yana karasowa Ajin cike da izza su uku tareda wasu yace .
Nine nan Mahaifin ta Alhaji KAMAL nace tazo tashiga Aji tunda bana ubanka bane .


Akramakallahu cikin zazzare idanu yace .....



Saura page daya in gama free Ku hanzarta kada ayi babu Ku.



Taku Har kullum kyauta daga Allah
*RAI DAYA*🦜

*JAN ZAKI*🐆




Mallakar

Ikilima Adam ( kyauta daga Allah)

09069080725

*Paid book*


*Saura page biyu ingama free dan Allah duk wacce ta siye littafina dan Allah karki fitar min dashi da zaran nagama free.*

*Dakuma wayanda suke da burin siya dan su fitar na roke Ku inkun San fitar dashi zakuyi to dan Allah basai kinsiya ba , kibarni da abuna .*




1️⃣3️⃣



Daga Aliyu Jan zaki munzo ne domin ,mu isar da sakon sa , izuwa gare ka ,kuma yace kaduba emails dinka zakaga Abu daya da irin Wanda mukazo dashi .

Nan da nan headmaster ya rikice ,cikin Razani yace wani Sako kenan?

Mika masa takarda sukayi tareda yin tsaye cirko cirko suna kallon sa yana karantawa wani uban zufa na karyo masa.

Dago kai yayi cikin inda_inda yace bangane ansauke ni daga Aiki ba laifin me na aika ta ?

Dukan su make Kafada sukayi sukace bamu zakayi wa wannan tambayar ba.
Kaduba emails dinka koma menene ta cen zakaji dalilin haka.

Nuno wani daga cikin su sukayi wani Salihin bawan Allah ,sukace wannan shine zai maye gurbin ka .
Kallon agogon hannun su ,sukayi sukace Awa daya muka baka ka tattara duk wani Abu dakasan nakane kafice ,gobe InshAllah zamu Zo maka da Albashin ka .
Har gidan ka.

Drever Sakina sake da baki yake kallon Ikon Allah dan ma , ya mance Abunda yakawo shi.

Headmaster yace haba bayin Allah karku mun haka wannan aikin dashi na dogara dashi nake daukan dawainiyar iyayena da duk Abunda ya shafeni dashi na Gina gidana ya kuke son inyi idan Har narasa Aiki na.

Cikin su wani yace bakin da Allah yatsaga baya hanashi abinci ,karka bata mana lokaci ,kuma da kake complain ,mu ba laifin mu bane daga Me Makarantar ne shiyasan me aka fada masa game da kai naga makarantun sa dayawa a fadin Nigeria kaine mutum na biyu daya sallama.

Cikin Tashin hankali headmaster ke tattara takardun da duk Abunda ya shafe sa.
Yana gama hada su yace , nagama hada komi Nawa.
Daya daga cikin su yace Miko mana takardun mugani dan kada asamu matsala ka dauki Abunda ba naka ba.

Suna karban takardun hannun sa , mamaki ne yakama su ganin check din kudi daga Alhaji Kamal .
Sauran file suke bi suna dubawa sukaga harda hoton Khairi tana cikin dalibai ya dauke ta batareda ta sani ba ,haka hoton ya nuna.
Zare hoton sukayi daga ciki ,tareda fadin wanna hoton dalibar Makarantar nan kuma da dukan Alama batasan ka dauka ba .
Dan haka wannan hoton Har wajen Jan zaki ze isa InshAllah ta email Zan tura masa.
Arazane headmaster ke kallon su yace wannan ai cin Fuska ne ,Kun koreni inaruwan Ku dashiga personnel problem Dina.

Cikin su wani yace wannan ba personnel problem dinka bane , hakkin mu ne ,mu kare mutunci kowace daliba a makarantar nan.
Saida suka tabbatar yafita da Abunda yake nashi sannan suka rufe office din.

Sauran Ajin suka nufa ,tareda nuna musu sabon headmaster din su daze ringa kula da su.

Dalibai sossai sukayi farin ciki da Faruwan hakan dan ya takura musu da yawan tsanani ga shegen son mata.
Sabon headmaster mai Suna Sagir , murmushi yayi yana kallon yanda dalibai ke karatu cike da nutsuwa.


Headmaster na isa gida kwalban giya ya jera agaban sa ,yana Sha idanun sa ,sun kada jajir kamar gauta yana Sha yana tuna Abunda akayi masa a makarantar tareda daukan Alwashin duk inda Khairi take saiya nemo ta ,yanada tabbacin daga sune wannan matsalar yafito .

Kamar shi Muktar za'a kora a Makaranta , to babu hukunci daya dace da Khairi illah ya mata fyade , wani shu'umin murmushi yayi yana Fadin idan na miki fyade Ummulkhairi dole ne , iyayen ki , su nemi rufa asiri dan kada arasa me auren ki.
Kafun na aure ki saina wulakantaki Ummulkhairi keda iyayen ki ,yakarashe zancen nasa cikin Muryan maye.

Mahaifiyar sa ce tashigo dakin aguje tace kai Muktar lafiya kake kuwa Naga kanata surutai .
Dago rinannun idanun sa yayi yana kallon Mahaifiyar sa tareda buga kirji yace kamar ni ,za'a sauke daga aiki akan mace , yarinyar ma yar matsiyata.

Cikin tsananin Tashin hankali mamar sa ta daura hannu akai tace mun shiga uku ,Muktar haryanzu baka canza Hali ba , kaiko Meka Aikata ne haka ne ,nasan ruwa baya tsami banza idanun ta shar da hawaye tace Dan nan ka tona Mana Asiri , dan Allah kanemi hanyar da zakabi asamu amaidaka bakin aikin ka cikin rikicewa take magana.
Shiko dayake abuge kasa amsa mata yayi yana kallon ta da idanun maye .


****************


Koda aka tashi Makaranta cike da Farin ciki ,Wata daliba mai suna Aisha ta ringa Neman gidan su khairi Har aka nuna mata.

Tsaye take bakin kofar Gidan taci karo da Baffa yafito daga gidan Alamun a hanzarce yake .
Gaishe sa tayi cike da ladabi tace dan Allah nan ne gidan Ummulkhairi Sulaiman ?

Murmushi Baffa yayi dan idan aka danganta sunan khairi da nashi jin sa yake a shauki.

Eh nan ne gidan su yabata amsa cikin sakin fuska kina iya shiga da ciki zaki same ta daga haka yasa kai yawuce.

Itakuwa kai tsaye gidan tashiga bakin ta dauke da sallama, sake da baki Khairi ke kallon ta , tace laaa Aysha wai kece nan agidan mu ,dan Allah waya kwatanta miki wannan gidan namu .

Aysha cike da Jin dadi tace garin masoyi baya nisa da tambaya har aka nuna mun gidan naku .
Sossai Aysha ke kallon gidan su khairi ji tayi duk ta bata tausayi dan dagani talakawa ne futuk .

Dakin khairi suka shiga tareda samun waje suka zauna ,suna tattauna yaushe gamo
Aysha tace Albishirin ki?

Khairi Tace goro tana mai Kallon ta ,bata labarin korar da akayi wa headmaster tayi.
Wani uban tsalle khairi tayi hade da ihu.

hakan yasa Innaro dake barci ta farka tana tsuki marasa adadi , cikin bacin rai tace shegiyar Yarinyar nan yau da bataje Makaranta ba , zata hanani sakewa hade da Jan tsuki taja filo ta daura kanta tareda cigaba da barcin ta.

Khairi Tace Alhamdulillah kai naji dadin wannan bayanan naki ,kice gobe ina iya zuwa Aji.
Tambayar ta , tayi yau Akramakallahu yazo ne?

Aysha tace gaskiya yau bezo ba dan jiya dayazo Sakina ta masa rashin kunya , korar ta yayi yace takawo Mahaifin ta , kila bacin ran ne yahanshi zuwa .

Khairi Tace me Sakinan ta masa cikin zazzare idanu .
Bata amsa tayi akan Abunda yafaru jiya .
Sossai Khairi ta jinjina Al'amarin tace lallai yarinyar nan ba yar gidan tarbiyya bace.
Aysha tace aikuwa dai ta hadu da daidai su , ba takamar su Arziki ba .

Khairi Tace Allah ya kyauta taso muje wajen Najwa tafada tana mai daukan hijab din ta .

********************


Aliyu zaune afalon sa , laptop dinsa na gaban sa ,Alamu Aiki yakeyi Masu muhimmanci.
Kamar an tsukule shi yatuna rannan da yake jin barci akwai wani sako ta email din sa dabe duba ba.
Hakan yasa cikin hanzarin sa , yashiga email din sa.

Yayi daidai da Sumayya tana gaban laptop din ta itama tana rubuta Sako dazata tura masa.

Shiko Aliyu Jan zaki sakon email din sa yabude na wancen ranar yana karantawa .
Murmushi yayi saida kuncin sa ya lotsa yana mai kara karanta sakon Wanda ba komai bane aciki .
Wani bakon email me dauke da sunan Suyfan yana fadamai yasan inda yake kwana yayi hattara yasan da Wanda zeringa sa'insa ba irin su ba.

Yana kokarin fita daga email din yaci karo da sakon Sumayya.

Tsaki yayi dan cikin wayanda yake hulda dasu babu mata , me take nema yafada azuciyar sa .
Bude sakon ta yayi yaga Sako kamar haka.


Aliyu Jan zaki , sunana Sumayya KAMAL
Hakika na kasance daga cikin masoyan ka .
Yau kimanin shekaru Biyar kenan ina sauraron fadakarwar ka kuma sossai yake shiga jikina.
Allah ya jarabce ni da sonka akanka kowa ke kirana na zauce da Allah ka taimake ni ka fidda ni kunya koda lambar wayar ka ce .
Dan jamaa su sheda soyayyar da nake maka ,bata wasa bace.

Yana gama karanta sakon ta , tsaki yayi be mata reply ba.
Ya kashe laptop din .
Stupid girl ya furta a Fili .

Karar wayar sa ce yadawo da kallon sa akan sa , ganin anrubuta Salim
Daga wayar yayi tareda karata akunne .

Dagacen bangaren yace Haidar tundazu ina kofar dakin ka nayi knocking shiru baka bude ba haba meye haka ne yana magana cikin Fada.

Karamin tsuki yaja tareda tashi cikin tafiyar sa mai daukan hankali hannun rike da remote din TV .
Yana bude kofar ,Salim yashigo kamar ze bigeshi sai safa da marwa yake cikin dakin.
Akun🦜 Aliyu ne yashigo ahanzarce tareda hawa kan kafadar uban gidan sa.

Cikin Tsananin bacin rai Salim yace wai Haidar yaushe zaka ringa daukan magana ta ne.

Kullum ina nuna maka ka kiyayi wannan fadakarwar dakake yi labari yazo mun akan wayanda sukayi zaman meeting akan ka , suna son su San dalilin dayasa kake shiga harkan su .

Aliyu Jan zaki samun wuri yayi yazauna yana mai cigaba da sauraren Abunda Salim yake fade .

Cikin Muryan sa dake nuna bacin ransa yace suwaye sukayi meeting akaina ?

Bashi Amsa yayi nadaiji ance .
Alhaji KAMAL
Alhaji Garba
Alhaji Sufyan .

Jan zaki girgiza kansa yake cikin tsananin damuwa yace saboda ina fadakarwar ne yasa , suke nema na to su mun me?

Ran Salim ne yabashi yace Kash oh My god kai wallahi bansan meyasa baka daukan abubuwa serious ba kayi imagine fa ,ina maka maganar rayuwar ka ,kana nuna mun halin ko inkula akan haka why why cikin tsananin ihu hakan yasa Mamy taji sautin Muryan sa aguje, ta taho dakin cikin Rudewa take kallon Salim tace suwaye suke Neman suga bayan Dana idanun ta sun kada jajir.

Fada mata Sunayen yayi yace Mamy Banda Tabbas akan Neman da suke masa , Amma naji suna fadin suna bukatar suyi tozali dashi tareda hanashi wannan fadakarwar da yakeyi dan wannan yana kawo musu cikas acikin harkan su , ta kasuwanci da Siyasa.

Mamy sake da baki tace ikon Allah aikuwa Aliyu bazai taba daina fadakarwar nan ba .
Tunda yakeyi bantajin ya kama suna ba.
Akan me zasu tsargu dashi , ni bansa Aliyu fadakarwa ba dan yayi sa'insa da wani ba.

Duk Abunda suke fade zaune yake yana sauraren su kansa aduke zuciyar sa tana tafarfasa .
Dago jajayen idanun yayi dasu suka canza kala.
Yace Mamy wayannan sunayen daya ambata kamar na San su ko?

Mamy tace kwarai kuwa Amma saide bamuda tabbas akan haka.

Kallo Salim tayi cikin bada Umarni tace inason ka samo mini hotunan wayannan bayin Allah .

Salim yace InshAllah Mamy bakida matsala.

Kallon Haidar Mamy tayi tace Dana karka damu da Abunda suke tattauna mudai mun rike Allah , kuma shize cigaba da karemu da dukan sharri .

Daman inason Sanar dakai nan da Sati uku zanje Cikin gari Jabiri layin yan bokolo .

Cikin tsananin bacin rai yace me zakije yi Mamy ?
Gaskiya babu inda zakije yabata amsa adunkule.

Haba Aliyu ya zakace babu inda zani akwai wani bawan Allah da nake nema wallahi shekarun baya kana dan yaron ka lokacin naje bansamu ganin sa ba.

In banje ba Zan samu matsala acikin zuciyata ba.
Kuma bazan taba gafartawa kaina ba takarashe zancen cikin kukan dayake Neman kwace mata.

Aliyu Jan zaki shida Salim Har Akun🦜 kallon ta suke cike da tsananin mamakin furucin ta .

Gaskiya Mamy bazaki je
Kiyi hakuri yabata amsa .

Zazzare idanu tasoma tace to ubana ko kuma ince mijina Muhammad .
To wallahi sainaje sai lallabaka nake , kana wani tauyeni , shekaru Nawa nayi ban fita ba ,sai fitan da zanyi na yini daya shine ze kawo matsala.

Aliyu dake kallon ta cikin gajiyawa da yawan surutun da yayi yace Mamy da kika zauna shekara da shekaru aikin zauna cikin kariyar ubangiji , yanzu so kike ki lalata min duk wani shirina kiyi hakuri Mamy .

Ki gayamin sunan Wanda kike nema ko unguwar dayake .
Ni Zan Nemo sa.

Ran Mamy yakai kololuwa wajen baci tace Kasan Allah dakaina zanje ,Zan sanya nikaf InshAllah bazan baka matsala ba.

Shiru yayi na wasu dakiku sannan yace Allah yakaimu ya sa mu wuce lokacin da Ameen ta amsa .

Tace wai Aliyu meyasa bazaka tausayawa marainiyar Allah ba.
Nusaiba ta Dade tana sonka ina maka magiya dan Allah ka aure ta.

Cikin tsananin Tashin hankali da damuwar da sukayi masa yawa yace Mamy babu biyayya agun Aikata sabo agun abokin halitta ko wanene ni fa Nusaiba ina mata kallon ya ne bawai Kanwa ,mune fa muka Raine ta , sannan kuce na aure ta ,inyi amai in lashe kenan yafada cikin jin haushin zancen.

Salim yace haba Haidar ya zakace kayi amai ka lashe saikace kaine uban ta .
Dan ka raineta menene aciki ,kuma ina tabbacin lokacin da Nusaiba tazo hannun Mamy kaima kana karami , nasan kasan me ake kira Kalmar so inma baka sani ba ,kanaji agari .

Azuciye yatashi tsaye hade dayin tsawa Wanda Yasa daga Mamy Har Salim da akun dake kafadar sa fuffuke yayi yakoma kan Salim yana zazzare idanu.

Yace me ze hana kai ka aure ta ?

Nace mukuuuuu bazan auri Nusaiba ba ko bakwa fahimta ne , ban haifeta ba Amma ta zama kamar jini na ,abun kaunata ,Banda Kani ko Kanwa sai ita kadai inna aure ta , tazama mata ta , kallon da nake mata abaya duk ya kau.

Dan haka Ku bar zancen nan haka ya ishe ni wallahi .
Maganar aure anan gaba , babu shi .
Ni Aliyu Muhammad nace bazan yi aure ba.

Bazan yi aure ba.
Bazanyi aure ba.
Bazanyi aure ba
Har Abada yakarashe zancen tareda barin Falon yayi dakin sa , aguje tareda danna mata keyy

Wani uban kuka ya saki mai tsuma rai yana Fadin Ni Aliyu Muhammad , ya ilahi ka taimake ni , ya ubangiji na karka barni da iyawata ,ya Allah karka hanani ganin haske .

Kuka yake mai tsuma zuciya tareda bude drower din gadon sa.
Ya fiddo wani hoto mai dauke da hoton wani Da da dukan

12 / 13