Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TUBALIN TOKA Farashin Zuciya by BADIAT IBRAHIM

Author :  BADIAT IBRAHIM Category :  African Stories & Novels

Chapter   1 / 14

1 to 3K   out of 42K words

ο»Ώ[3/14, 3:48 PM] Mmn Areef: πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸ’€πŸ’€πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸ’€

*ΒΆTUBALIN*ΒΆ
βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†
*ΒΆTOKAΒΆ*
βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†
*¢BY BADIAT IBRAHIM*¢✍🏻


*BISMILLAHIL RAHMA NUN RAHEEM✍🏻*

_Allah yanafeni nai dawowa dawata tsarabarku dan farantawa samaπŸ’ƒπŸΌ_

*wannan littafi Nawa mesuna TUBALIN TOKA true life story ne,' abune wanda yazama tamkar ruwan dare gama gari,"*

_harga Allah banyishi dancin zarafin wani ko wataba, aa nayine danya zama ishara gamasu irin sabi'un_

_dan Allah karku fassara littafinnan dawata manufa tadaban nidai Ina kokarin aika sakone Allah kuma yasa mu amfana daga cikin littafin yakuma zama darasi ga masu aikata hakan_

_gargadi banyarda wani kowata yaimun amfani da ko wanne siga nacikin labarina ba yin hakan kuskurene babba akiyaye,'"_

*ya rabbi nayi rokonka ka haska kirjina kasanya hasken mutunta abaki, kayarda Wanda duk ya saurari sakona, yakaru dashi ya Allah*"

*"Kamar yadda nasoma littafin asa'a Allah yasa nagama asana"a Ameen*

*page________1_5✍🏻*


*¢SHIMFIDA🌫✍🏻¢*





*"MEEMAR!* ce alab'e a toilet dinta tana waya da kawarta, *ZEEBA* ahankali take maganar dankar mijinta dake cikin dakin yana shiryawa danzuwa makaranta koyarda yara yajiyota,'"

*"ZEEBA* tace ___"haba *MEEMAR* meyasane ke tsoronki yayi yawa! Aikezakisa harsai *Mahbub* yagane bakida gaskia ma,'

*"MEEMAR* tasakeyin kasa da voice dinta tace, __"bahaka bane Kawata, dole inji tsoro domun abunda zan aikata hadari gareshi sosai, in asirina ya tonu for example *Mahbub* yakira Anty sadeeya awaya tacemai banzoba what did u except?,"

*"ZEEBA* wacce tagama kula tace __"tayaya ma asirinki zaitonu?, amma shikenan tunda bazakijeba zankira shi *Hafeez* insanar masa kinfasa saiya sanarda mutumin dazakije wajan nasa,' sai insa *Hafeez* yahada connection din da lailah, dan inada appointment da wani babban mutumene nima kuma goben a Abuja dani zanje,'"
"Sai shegen tsoron *Mahbub* shibazai iya tsinana miki komaiba, to inama yagansu teacher harwani sana'ane yau watan malaman makarantar gwamnati Nawa babu albashi,"?

*"MEEMAR* tace __"to *ZEEBA* zanidin Allah yakaimu goben zantafi dan wlh inada bukatar kudin sabida rashin lafiyar Ummu,'"

__"yauwa kekefa dama *Hafeez* yafadamun cewar direban dazaizo ya daukeki yauzai shigo gari yakwana a hotel gobe kuwuce,: ke gashi *Hafeez* yace gayan yahadu kuma saurayine mejida kanshi sai Kudi,' a america yakefa dazama tareda iyayanshi dan mahaifinsa yaji kudi shima kanshi gudi gareshi sosai,' shima mitting ne kawai zaikawoshi Abuja, goben zanbi motarku kawai tunda nima abujan nanufa,'"

"Kamun *MEEMAR* tace wani Abu kawai taji *Mahbub* yabude kofar toilet din dasauri tasauke wayar a kunnenta tareda boyewa duktagama tsorata tanata zare idanu,'"

"Kallonta *Mahbub* yayi tadanyi murmushin yake kawai,'"

__*"MEEMAR* kinsanfa kenake jira kince zan saukeki a gidansu Ummu, karkisani latti fa dalibai suita jirana jarabawa sukeyi,'"

__"toh ganinan fitowa amma sainadan hada kayan *tasmeena* ajaka zataje gidansu Ummu Hutu tundadai sunsamu Hutu, danni hazanyi tafiya da yarinyaba,"

*"Mahbub* yace __"to kifito da sauri dan Allah,'"

"Kofar yarufe mata wata ajjiyar zuchiya tasauke tareda fitowa dasauri,' tasoma hadama *tasmeena* kayanta ajaka dayake dama sunakan gadone,' tayafa matafi tace,'"

__"yallab'ai Na kammala muje,' karasowa yayi ya rungumeta tareda shafa bayanta dagota yayi tareda bata peak akumatu,'"

__"kinga kyanki kuwa? Woow kinyi Kyau sosai,'"

"Murmushi taimasa tace __"akoda yaushe innayi kwalliya saika yabeni mijina,'"

__"uhm gaskia nafada sabida kedin me kyauce inkikayi kwalliya kuma saiki dad's susutani,''

"Dariya sukayi tareda fitowa daga dakin zuwa falo,"

"Diyarsuce *tasmeena* wacce akalla bata wuce shekara ukuba tana zaune tanata wasanta da bebian roba tana hango mommy,nta tataso aguje tareda d'afe mommynta,'"

__"mommy dani zakije wajan Ummu ko?,'

__"ehmana mamana zakijema ummuna Hutu banda rigima Anty *zabrena* batasan b'arna kuma tace kinfiye rigima,'"

"Dariya sukayi dukkansu abbanta yasureta suka fita hannu yabama *tasmeena* suka tafa,'"

"Ajjiyar xuchiya *MEEMAR* tasauke taredabin bayansu takulle dakinta tafita agidan,' samunsu tayi harsunhau mashin din *roba_roba* ,'"

"Murmushi *Mahbub* yaimata yace __"to bismillah madam hau mutafi ko,'"

"Karasowa tayi gabanshi taredasa hannu tana kyaramai zaman hularsa tace,'"

__"kanaso acemun ban'iya yima hadadden mijina kwalliya ba ko? Kaikaga yanda kasaka hular kuwa,'"

"Danewa mashin din tayi yaja suka wuce __" ba dole kiganni hakaba inata zuba sauri zuwa makaranta kar students dina surigani zuwa gashi yau last peppar dinsu zasu zana, kuma kekika tsayar dani ai,'"

"Sunkarasa kofar gidan *tasmeena* ta sakko mommynta Tamika mata jakar kayanta ,'"

__"oya kishiga gida kijirani,' aguje tazura tanata doki,'"

*"Abbanta* yace __"aa bazakiyima daddy ba bye ba sabida kinaso kiga Ummu da Anty *zabreena* ko(,"

"Dariya tasaka tana dagama dadynta hannu harta shige,' ahankali *MEEMAR* tasauka dagakan mashin din tatsaya agabanshi,'"__"yaya akayi *MEEMAR* Dina?

___"meza'a dafa for dinnie?'"

__"uhmm to duk abunda yasamu gadai Dari biyar dinnan, sai maganar zuwanki gobe Gombe zandan nema indanyi fafutukar Na Mota insha Allah,'"
"Kigaida Ummu innadawo daukarki zanshiga,'"

"Murmushi kawai tayi ta amshi kudin tace __"adawo lfy Allah yatsare,'"

__"Ameen inasan adda'arnan dakikemun kullum inzan fita nagode,' love u saina dawo,'"

"Mashin dinshi yaja tanata dagamai hannu haryayi nisa juyawa tayi tashiga gidan iyayan nata da sallama,'"

*love u oll*
[3/14, 3:48 PM] Mmn Areef: πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸ’€πŸ’€πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸ’€

*ΒΆTUBALIN*ΒΆ
βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†
*ΒΆTOKAΒΆ*
βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†
*¢BY BADIAT IBRAHIM ¢✍🏻*

*page__________ 6_10✍🏻*








" Ummu tana zaune tanashan maganin bature Na ciwon kodarta yayinda *zabreena* take tsugunne tana wankema ummu kayan sawanta ,'"

*"tasmeena* ce tashigo aguje tadane jikin Anty *zabreena* kanwar mahaifiyarta'"

__"wanake gani kamar my daughter *tasmeena* kece?,'"

"Kanta tadaga tana dariya Ummu tace,' __"zomana takwarata,'"

"Aguje takarasa wajan Ummu suna dariya *MEEMAR* ce tashigo da sallama,'" tareda karasawa kusada Ummu tazauna,'"

__"yayadai jikin Ummu da sauki ko?,'"

__"toh balaifi *MEEMAR* inadanjin dadin maganin balaifi,' yamai GIDAN naki?,'"

*MEEMAR* tace __"yace ingaidaki intataso makaranta zaizo yadubaki Ummu sannu,'"

*"zabreena* ce takaraso da ruwa akofi tace __"ga ruwa Anty, kinsan kuwa dama nace Dana gama wankinnan zanje muyi sallama dake inroka kikawomun *tasmeena* taimana Hutu,'"

__"basaima kin rikaba wannan fitinanniyar yarinyar gatanan aibazanyi tafiya ma da'itaba tafiyar ta sassafece fa,'"

"Ummu tace __"amma bakince wajan kanwar Babar Baban yarinyarnan zakijeba mezaihana kitafi da yarinyarnan sabida Allah fa *MEEMAR*?",

"kamun *MEEMAR* tace wani Abu wayarta tashiga kara number kawarta *zeeba* tagani hakanne yasa tatashi dawuri tareda kulewa uwar dakin Ummu,'"

__*"zeeba* yaya akayine dazu muna waya Mahbub yakatsemu?,'"

*"zeeba* tace __"yanzunnan mukayi waya da *hafeez* yake shaidamun direban yakaraso harma yakaishi hotel din dazai sauka," *MEEMAR* kishirya da sassafe goben muwuce danshi Wanda zakije wajan nashi da rana jirginsu zai sauka shine yace kekifito da sassafe,'"

___"badamuwa *zeeba* gidanki zanzo muwuce aiko?,'"

__"aa abban rumaisa yana gida muhadu kawai a amadu bello way zamuhadu dasu *hafeez* da direban saimu wuce,'" amma kizo gidana yanzu kikarasa shan ragowar magungunanki kuma zamushiga market siyayyan kananan kaya kitaho kawai,'"

__"shikenan dama ina GIDAN Ummu bani minty goma zanzo",

*"zeeba* tace __"saikin karaso Kawata",'

*"MEEMAR* takashe wayar tareda fitowa tasamu Ummu sunacin abinci itada *tasmeena* __"Ummu zanje kasuwa indawo zanje siyo tsarabar tafiya,'"

"Ummu tace __"to shikenan saikin dawo kikawo mana tsaraba nida *takwarata,* ko *tasmeena*?,'" daga kanta tayi kawai,'"

"Tazari Jakarta tafita adaidaita sahu tatara tareda fadamai inda zataje tashiga suka wuce,'"

__"amma Malam saba'infa zanbiya gaskia danba Dari nasaba zuwaba,'"

"Me adaidaita sahu yace __"Tabb ai hajia inaga kindan kwan biyune bakijeba ammma ina yafi saba'in maifa kwana biyunnan wuyama yake,'"

__"to badamuwa muje din yazanyi,'"

"Suna tafe sunadan tab'a hira harsuka karaso daidai kofar gidansu *zeeba*",

__"kagama anan zan sauka yayi,'" tsayawa yayi ta sauka tareda mikamai gudar Dari tawuce kaitsaye zuwa cikin gidansu *zeeba* gidane irin Na hayarnan katoto Wanda kowa da shashenshi baruwan kowa da kowa,'"

"Kaitsaye tawuce shashen *zeeba* da sallama tashiga cikin falon wasu hadaddun 'yanmata tagani azaune suna kallo su uku,'"

__"sannunkufa *zeeba* tana cikine?,'"

"Daya daga cikin 'yanmatan tace __"kishiga tana ciki sannu da zuwa,'" wucewa tayi uwar dakar *zeeba* samunta tayi tana waya tanata dariya, *MEEMAR* tasamu waje tazauna tana kallon kawarta *zeeba*

__"aa Alajina aikanunamun kafisan matarka tunda kadauketa kuka tafi Dubai Alhalin inada raina yaya bazanyima kukaba, uhm kasanfa inaji dakai,'"

"Daga cikin wayar yace ___"come on *zeeba* Darling wlh kinfita sau dubu neza'ayi da saude?, ladanfa nomace wlh matsawa tayi dole dole sai taje, kekuma danace kishirya kitawo saikikacemun mijinki nagari shiyasa amma ina roko ayafemun uhm,'"

*zeeba* tace __"aishekenan Alhaji Na Allah dai yadawomun dakai lfy kabari muyi waya to anjima aminiyata ce tazo nabarta azaune,'"

__"toh toh gimbiya sarautar mata saimunyi waya take care,'

"Bakinta tatab'e tareda kashe wayarta dariya tasakama *MEEMAR* suka tafa,'"

__"aa Kawata wannan kashe murya aisaiki susutashi,'"

*zeeba* tace __"kedai bari manyannan saida haka inba hakaba bamecin kudadensu wlh saida dabara,' toyaya akayine ya shirye shiryen tafiya,'"?

__"uhm munatayi Kawata wanne magani zansha kuma bayan Wanda nadingasha harfa ciwon Mara nadingayi sabida karfinsa wlh dan gaskia mekyaune nikaina inajin sauyi ajikina,' Kawata wasu tsula tsulan kyawawan 'yanmata nagani afalanki suna zaune suwaye?,'"

__"hahaha Kawata bakida dama harsuka kaiki Kyau?, wlh *hafeez* ne yazo ya ajjiyemunsu yaje yakamama direbanda zaitafi damu hotel sukuma 'Yan matannan Gombe sukayi zasuje ganin wasu 'Yan majalisu,' biyun 'yanmatane dayar kuma Matar aurece yaranta biyu,'"

__"ikon Allah kawata ashe abunda akeyi agari kenan ba 'Yan matanba ma matan auranba kowa Ron's?,'"

__"zauna nan kekinayin Abu tamkar baki tab'a zaman class ba saikiga macce mijintama baida aiki amma ita tana hawa manyan kaya mafi yawanci wannan hanyar sukebi wata kiganta jazur kamar tsada taji kayan kudi wlh inkikaga mijinta almajirima yafishi,'"

*"MEEMAR* tace ohh mazajan mu abun tausayi *zeeba*'"

"Zabura *zeeba* tayi tace __"inji ubanwa mazajan mu abun tausayine. *MEEMAR* inmafa bacci kikeyi u have to wakeup and Shane ur eyes,' kekikasan abunda suke aikatawa insun fitanne,' ke rayuwa sirrice kawai,' ga maganin shanye mutafi kasuwa,'"

"Karb'a *MEEMAR* tayi tareda kafa kanta tashanye sannan suka fito,'"

__"ammm Hafsat idan *hafeez* yazo kicemai munfita kasuwa da *MEEMAR* kukullemun kofar kawai makullin yana jiki natafi da 'ya'yan makullin,'"

__"shikenan anty munfa gode sosai,' wucewa sukayi tareda ficewa sai kasuwa,'*

*love u oll*
[3/14, 3:48 PM] Mmn Areef: πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸ’€πŸ’€πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸ’€

*ΒΆTUBALIN*ΒΆ
βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†
*ΒΆTOKAΒΆ*
βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†
*¢BY BADIAT IBRAHIM ¢✍🏻*

*page_______11_15✍🏻*






"Wani hadadden *boutique* suka shiga Wanda *zeeba* take siyan kananan kaya hadaddu,'"

__"barka da shigowa hajia bismillah ga waje kuzauna,'"

"Zama sukayi __"barka da kasuwa Malam Isa ya kasuwar dai?,'"

__"toh hajia saidai godiya kawai meza'a Baku nasha fanta ko coke?,'"

__"uhmm banu fanta din dai me sanyi,'". Aguje yafita yasiyo musu sannan yadawo ,' yashiga tsab'o musu hadaddun kananan kaya sunfi kala ashirin ko wanne da mahadinsa,'"

__"inaga iyakar asalin masu tsadar kenan designa ne kayan hajia,'"

__"toh babazai gagaraba ,' tasoma daga kayan tana yabawa dan sunhadu sosai yahada colour's masu Kyau matchwat colour's,'"

__"toh Malam Isa fadi farashinsu muji amma kafinnan kayan bacci mukeso hadaddu kamar guda biyar zaka karb'o mana awajan makocinka,'"

__"toh hajia nakine kona wannan hajiyar ne?,'"

__"ohh natane Malam Isa,'

__"to badamuwa, dasauri yafita danyaje yakawo musu *MEEMAR* tace,'"

__"Kawata kayanfa sunyi yawa tsada zasuyi sosai amma sunyi Kyau over,'"

__"Kawata bazai gagaraba kina dawowa zaki biya kudin keda zaki dawo a Hajiya,'". Dariya sukasa,'"

"Dawowa yayi da rigunan baccin,' __"gasu sunyi ko Hajiya?,'

"Karb'a tayi tana dubawa tace __"sunyi nawane kudin dukka harda Na kayan naka?,'"

__"toh hajia rigunan baccin dubu biyarne saikayan kuma dubu ashirin kinga Yakama ashirin da biyar,'"

*MEEMAR* tace __"wadannan 'Yan kayanne dubu ashirin Malam?,'"

__"hajia kenan duk inda kikasa kayannan sai yance kinsan kaya designa nefa hajia,'"

*"zeeba* tace __"rabu da'ita kaji Malam Isa ga kudinka,' tamikamai yakirga,'"

__"suncika hajia nagode,' aledar ashagon yasaka musu*MEEMAR* ta amsa suka fito kasuwa suka kutsa sukaita siye siye turarukane Maya mayaine dasu kayan makeup sannan suka shiga adaidaita sahu,'"

__"Kawata kudindafa aka kashe sunkusa dubu Dari har Nawa zansamone haka wai?,'"

*"zeeba* tace __"wayasan uban Kare?, nikaina bansan Nawa zaki dawo dashiba abunda nasani shine koda dubu Dari Nawa muka kashe zaki biya harki loda kudinki a account,'"

*"MEEMAR* tace __"kudin dayawane haka,'"

"Dariya *zeeba* tasaka tace __"aike metsadace zakizo kibani labarin yanda gayan zai haukace miki ya like miki Kawata,'.

"Adaidaita sahun yasauke *MEEMAR* daidai kofar gidansu Ummu tasauka,'"

__"toh Kawata saizuwa goben inmun hadu ko?,'"

__"eh Kawata karfe bakwaifa taimiki a amadu bello way plz,'"

"To kawai *MEEMAR* tace tareda shigewa GIDAN daidai ana kiran magrib,'"

___"yanzu dan Allah *MEEMAR* saiyanzu zaki dawo dayanzu kuma *Mahbub* yarigaki zuwafa kezakice kasuwane tunsafe sai yanzu?,:"

__"kai ummu siyayya nayifa kuma dayawa shiyasa ga kasuwa dab'ata lokaci ni gidama zantafi insamu indaura abinci,'"

__"aa *zabreena* tayi abinci daku gashican acikin kula saiku tafi dashi ai,'"

__"Allah sarki 'Yar kanwata aikuwa ta taimakeni sossi,' ina sukayine Ummu?,'"

__"sunje GIDAN Kawar *zabreena* din tuntuni,'"

"Sallamar *Mahbub* sukajiyo shigowa yayi tareda zubewa agaban Ummu yana gaisheta da fara'arta ta amsa yaimata yajikin,' sannsn *MEEMAR* tadauko kular tabama *mahbub* yaima Ummu sallama yafita,'"

__"kibamu wani Abu mana *MEEMAR* kinga kayan abincinmu yakusa karewa kuma babu kosisi wlh a hannuna,'"

__"to Ummu ga dubu ukunnan kuyi maneji kamun indawo kwana uku zanyi ai,' Ummu tasaka hannu ta amsa tana godiya *MEEMAR* taimata sallama tawuce.'"

"Mashin din tahau suna murmushi yace __"sorry kinata jirana ko? Wlh kuma wayata ba kati shiyasa bankiraba nadanje kasuwa nayi aikine nasamo miki kudin motarki,'"

"Tashafa bayanshi tareda kwanciya abayan nashi tace __"nima nayi tunanin hakan shiyasa banma kirakaba,'"

__"irin wannan muryar aisaikisa mufada katuwar kwata ina tuki kinamun shagwaba harda kwanciya abayana,?'"

"Dariya sukayi dukkansu sunata hira harsuka Isa gida,' gaba wuta,' ga wayarta takusan mutuwa,'"

"Ahaka suka shiga dakin lanta *mahubu* ya kunna sannan itakuma tashiga kicin tadauramai ruwan wanka a risho sannan tadawo tahau cinyarsa,'"

"Dasauri tatoshe hancinta tana tsokanarshi __"uhm warin zufa kaketayi,'" matsowa yayi yaciji kumatunta yace,'"

__"zan kamaki zaki Sani ai bani abinci inci kamun ruwan yayi wlh tunsafe banci abinciba,:'

"Dasauri taje tazubomai jalob din shinkaface taji kifi soyayya Asama takawomai tareda jawomai table ruwa tadauko ta ajjiyemai,'"

"Daki tanufa tareda kullewa tadauko akwatin da *zeeba* tabata tajera kananan kayannan tareda rigunan baccin dadai d'an abunda zata bukata, kayan makeup din tazubasu a hand back dinta sannan tafito tajuyemai ruwan wankan takaimai,'"

__"yallab'ai ruwan yayi kaje kayi,' dasauri yamike tareda hadata da jikinshi yace,'

__"wai haryanzu baki gama perioud dinbane? Kishinki dukya damenifa gashi zakiyi tafiya kibarni yazanyi kenan?,'"

__"nima inada bukatar ka ai but wannan karon nima ina mamakin period din yanatamun wasa fa,'"

"Sauke kanta tayi kasa tana zare idanu dan karya takemai ba period dinda takeyi,' wucewa yayi yayo wankansa tareda fitowa itama tayi wankan Tahauro gadan,'"

__"ga kudin motar dubu ukune da Dari biyar zaimiki ko,?' Hannu tasa ta amsa tace,'"

__"yayimun yallab'ai nagode bacci zanyi dan gobe sassafe zanwuce insauka da wuri,'"

"Shiga tayi jikinshi ahankali yadinga shafata harsukayi bacci,'"

*Allah yayi dare gari yawaye*β˜€


*love u oll*
[3/14, 3:48 PM] Mmn Areef: πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸ’€πŸ’€πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ
πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸ’€πŸ’€πŸ’€
πŸ’€

*ΒΆTUBALIN*ΒΆ
βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†
*ΒΆTOKAΒΆ*
βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†
*¢BY BADIAT IBRAHIM ¢✍🏻*

*page______16_20✍🏻*





*"MEEMAR* tunda tatashi tayi sallar asuba tayo wankanta zama tayi tatsara kwalliya tagani tafada sannan tasaka wata doguwar Riga 'Yar kanti blue taimata Kyau sosai mayafi tadauko pink tareda takalmi da jaka pink,' tadanyi murmushi tareda kara janbaki a bakinta,'"

"Matsowa tayi gaban gadan tasoma dan bubbugawa ahankali yabude idanunshi yace,''

__"kaddai kicemun harkin gama sai tafiya?,'"

__"yes yallab'ai nagama nafiso insauka ido naganin ido shiyasa,' banyifa breakfast ba saidai kasiyo waina agidan Umma me waina,'"

"Mikewa yayi tareda sumbatar Lip's dinta __"jirani inyi wanka inkaiki mana tasha,'"

__"aa kakoma kayi baccinka wlh nayafe zantafi kagaji surutun 'Yan makaranta ma ya'isheka,' take care of ur self plz,'"

"Sumbatarta yasakeyi yace __"nagode dakika fahimceni shikenan Allah yakiyaye kicema Anty sadeeya ina gaisheta sosai zamuta waya inajin inda kike, kikulafa sosai,'"

"Rungumeshi tayi tareda bashi peak akumatu taja akwatinta tawuce tana dan murmushi bayanta yabi da kallo yana murmushi Yakoma Gado sai bacci,'"

"Tana fita tasamu abun hawa tahau yakaita amadu bello way tunkamun tasakko tahango *zeeba* atsaye abakin wata tsukekiyar Mota kirar 4matic,' ta sallami me keken tanufo *zeeba*,'"

__"Kawata yazaki kashe wayarki kuma.,'"

"Akwatinta *hafeez* ya amsa yasaka abayan both sannan suka shiga motar su biyu abaya sai *hafeez* da direba agaba,'" direba yaja motar suka wuce,'"

__"kedai

1 / 14