Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Baccin SO Complete Hausa Novel by M Shakur

Author :  M SHAKUR Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 51

18K to 21K   out of 151.6K words

pharmacy gyadamai kai tayi saita wuce tafita shikuma saiya tsaya ya dauki folder nata yabude yana karanta condition dinta again for the second time tunda aka kawota, she s sick, she s traumatized, she s non verbal all 3, but this morning Mamanta bata yarda ya kwantar da itaba why in the evening Babanta yakawota dawasu kattai a daddaure? Her Mother doesn t look like wacce zatabar maza su kakkama mata yarinya haka, kaganta kasan she protects yarinyar nan with everything she got, did something happen to her Mom? Is that what triggers her? Saiyadanyi shiru yakalli karkashin gadon, he doesn t wants to think much, all that matters is his patient not her family, he will do everything he can to help her, she needs food if she s refusing to eat he needs to go for option B abata abinci ta drip cus she needs treatment this temperature and everything ya sauko kafin yafara treating underlining condition nata which is her mental issue.

Yana tsaye awajen nurse din tashigo da everything daya aika wani bell dake kusa dashi ya danna within seconds saiga wata babbar kosasshiyar katuwan mace sanye da uniform tace  Dr M which patient do you need help with? Naga you paged me ? Karkashin gadon ya nunamata dasauri tace  Ohhkay let s see what do we get here saita wuce taduka karkashin gadon tana kallon tray na abinci tace  laaaaaa bataci wannan abincin mai dadi ba Nurse dake tsaye gefenta tace  bataci ba Iyawo Iyawo tadauki plate din tamikama nurse din ta karba sannan takalli Amirah datake kara matsawa tana mannewa da bango Iyawo tamika hannunta tace  zo kinji we will take good care of you here don t be afraid uhnn Pretty girl tai maganan daidai tana daura hannunta kan cinyan Amirah, Amirah ta kurma ihu kaman wuta ya tabata.  Ahhhhhhhhhhhh! Marwan ya kallesu, ta wuntsila kafafunta takai hannunta zata cire hannun Iyawo, cikin asalin experience Iyawo takama hannu kawai tashi daya tajawo Amirah tana murmushi Amirah na kokawa da ita, Iyawo tadagata Amirah takara daburcewa tahau ihu sosai ihunta kaman zai fasa musu kunne tana kokawa gashi batada karfin ma, hakan yasa Marwan yajuyo yakallesu ahankali yanda Iyawo tadagata kaman yar baby tadaga, daurata tayi akan gado, tawani dirko daga gadon Iyawo zata kamata ga mamakinta kawai tai kan Marwan agigice zata fada jikinsa, baya yakoma dasauri Amirah tayo kansa zata shige jikinsa dawani irin sauri Marwan yakawo hannunsa gaba strictly yace  ke! Chak Amirah ta tsaya gabanta na faduwa saita koma gefensa ta tsaya dab dashi takai hannunta takama kasan rigan labcoat nashi tarike gam tana numfashi da sauri da sauri kaman kirjinta zai fito, daga Nurse har Iyawo suka kalli yanda tarike labcoat din Dr da yanda ta tsaya a gefensa looking petite.
Ahankali yashiga tafiya batare daya sa tasaki rigansa ba har zuwa wajen gadon tabiyosa gadon ya nuna mata yace  sit ahankali Amirah ta zauna tana rikeda labcoat dinshi sosai, cikeda lallabawa yace  bani hannunki ko kallonsa Amirah batayiba balle yasaran zata basa hannunsa, batare daya kalli su Iyawo ba yace  I need her hand matsowa Iyawo tayi wajen ihu tayi sosai Marwan yabata hannunsa daya saka gloves yace  give me ur hand then idan bakiso ta tabaki boye hannunta tayi abaya cus ta tsani anything allura hakan yasa Iyawo tazo wani tasowa Amirah tayi zata fado jikinsa dasauri yadan matsa baya Iyawo takamata wani irin ihu take tana kokawa zata fita daga jikinta, Iyawo tace  kina tsoron allura, hannun Dr ba zafi, tsaya amiki kihuta kema kiji sauki kinji yarinya gyaramai hannunta Iyawo tayi tace  you can do it now Dr takowa yayi yamatso this time bai kalli fuskanta ba dan baiso tabasa tausayi ahankali yasa alluran yadan kalli fuskanta tama rage shure kafa tagaji sosai kuma da alamu bataji zafi ba, sai ijiyan zuciya take gashin goshinta ya mammanne sabida zufa datayi daga dan kokawan datayi, dauke kansa Marwan yana setting drip din yayi yace  can you get her a cap for her hair, idan tai bacci change her to hospital uniform Iyawo tace  toh Doctor M within few minute ya gama fixing mata drip yasa allurai a ruwan duk Iyawo na rike da ita tadena ihu amman sai numfashi take sama sama tana wani irin ijiyan zuciya dake fitowa sosai irin na yanda yara suke, Marwan yace  kwantar da ita kwantar da ita Iyawo tayi Amirah ta kwanta lamooo idanunta na lumlumshewa, Iyawo tadan leka fuskanta tace  she s asleep lemme get her uniform da cap saita wuce tafita, ahankali yakai hannunsa saitin hancinta yana kallon agogon hannunsa yana noticing breath nata murya chan kasa yace  you need to calm down yayi maganan still hannunshi na wajen yanason nunfashinta ya daidaita, lumshe idanunta ruff tayi numfashin yakoma yana fita ahankali hakan yasa ya maida hannunsa yadauki folder nata yayi rubutu sannan yajuya yafita daga dakin yashiga another room, daya daga cikin ma aikatan dake aiki a wajen tace  don t tell me yanzu wannan ma da Babanta yakawota yagudu Dr M ne zai biya kudin? Dayan tace  shine mana, da a komar da patient gwara yacire kudi daga aljihunsa yabiya wlh bantaba ganin selfless Dr irinsa ba, yau shekaru kusan 20 ina aiki a asibiti duk sukai hmm suka wuce.

Wajajen magrib Marwan yafito daga office nasa yadauro alwala, idan yatafi sallan magrib baya dawowa, ward yashigo direct 441 yashiga yana bude kofa ahankali, night nurse yagani tanama drip da ke shiga jikinta next injection daya rubuta amata at that time, an chanza mata kaya zuwa blue uniform dinsu wanda yake riga da wando an dan rufa mata bargo sannan an saka mata wani dark blue hula daya zauna akanta yayi kyau, kallo daya yama fuskanta hakan nan kawai yasami kansa da cire idanunsa daga kanta da sauri, ya makala sthethoscope a kunnensa yana duba pulse nata sannan yakalli nurse din, yace  I will be going home now be checking on her after every 30min, if anything come up akirani dasauri tace  yess Dr, saida safe baicemata anything ba yajuya haryakai kofa ya tsaya saiya juyo yadan kalleta sannan ya kalli nurse yace  get blanket from my office cover her dasauri nurse din tace  yes sir yajuya yafita tabisa da kallo tama mamakin meya sami dan karamin zanin gadon da aka rufa mata dayace adauko bargo daga office nashi, are they related? Saikuma ta kauda tambayar tawuce tafito he never lock office nasa hakan yasa ta shiga wani bargo mai kyau da taushe na Hermes ne akan kujeran sa sai ta dauka tafito daga office din.
EPISODE 9??



Masallacin yashiga yabi jam i akayi magrib sannan yafito yashiga mota, yadanyi jimmm kafin yakunna motan yaja, baya wani gudu sosai, tsayawa yayi wajen fruits yasaya dayawa kwallo kwallo aka lodamai a booth sannan yaja motan, koda yakai unguwansu it s already isha i time, ya tsaya yayi sannan yadawo yaja motan yayi horn aka budemai gate ya shiga ciki, parking yayi gateman din yazo wajen motan da sauri kafin yabude yarigasa bude masa yace  sannu da zuwa Dakta murmushi kadan yamasa, Musa yace  Dr kaga kaman dan kankare naso yakamani hannun sai zugi yakemin mezansha ? Anatse Marwan yakalli dan yatsun dayake nuna masa daya kumbura sai yace  kanada ciwo haka tun safe maisa baka sanar dani ba ? Cikeda fara a yace  banso na dameka ne Dakta, dan karamin ciwo haka sainaita raki kaman mace Marwan yasake kallon hannun again saiya koma mota yadauko wani karamin box yabude, wani katin magani yabasa yace  kasha biyu yanzu biyu da safe, idan baiyi sauki ba zan tafi dakai hospital gobe, and kaje ka kwanta don t work again murmushi sosai Musa Allah yasani yana son bawan Allahn nan Marwan yace  nagode Dakta juyawa yayi zaitafi Marwan yawuce a natse yabude booth din bayan motan yashiga ciro fruits din zai dauka kaman ance mai hadin yajuyo dasauri yataho yace  laaa bari na tayaka Dr wani kallo Marwan yamasa yace  wuce kaje ka kwanta kahuta baiyi musu ba yawuce yana murmushi sosai, babu wani ma aikaci da bayason Dr agidan nan, da kansa yadauki all the fruits yawuce babban dankararen flat na gidan yabude kofa ahankali tareda sallama, Mami ne kadai a falon da waya a kunnenta tana magana ganinsa yashigo Niki Niki da kaya saita zare wayan daga kunnenta tace  why are you carrying all of this ? Baice komiba yawuce kitchen ya ijiye yafito Mami tace  ina Musa ? Ahankali yace  I told him to rest yanada Wicklow a hannun zama yayi kusada Mami saiya dauki plate na abincin daya gani agabanta wanda salad ne yarage da chicken yashiga ci, Mami tace  ga abinci a dinning why are you eating wannan dayayi sanyi cikin yar karaman murya yace  i am very hungry Mami tsaresa da idanu Mami tayi yanda yakecin salad din ahankali, ijiye plate yayi bayan ya cinye zai tashi tace  badai bazakaci abinci ba ? Dan yatsine fuska yayi ahankali yace  lemme shower first zan sauko nabaki magani yayi maganan yana kallon kafanta daya koma normal saiya wuce stairs Mami tabisa da kallo, sama yawuce ahankali yake tafiya kana gani kasan yadan gaji sai kawai ta maida wayan kunnenta tana sauke ijiyan zuciya daga ta dayan bangaren muryan wata tace  Menene Yaya Mami? Naji kina ijiyan zuciya ? Ahankali tace  Marwan ne, he bearly have time for kansa all he does is take care of others, hospital, hospital, hospital, he doesn t do any other thing, baya hutawa, bayama tunanin aure Nafisa Nafisa tace  to ba idan mun faramai maganan aure kice kaza kaza kaza ba, yaki yayi aure sai kallonsa kike & &



One of daily routine nasa is inhar yadawo before yaje dakinsa saiya shiga dakin kannensa spend time with them cus he s always busy but yadawo dole saiya basu time, he s their uncle, dudda they re just 16 but he respect privacy nasu, knocking yayi kafin yagama knocking din har an bude kofa, daki ne mai kyau da gadaje biyu masu kyau hadaddu, Faiza ce tabude tana sanye da yar rigan bacci data saukan mata har knee kalaba ne akanta tai wani tsalle ganinsa tareda hugging nasa tace  Uncle M welcome, ya clinic yau bayanta yashafa yace  it s okay where s Farida ?  She s in the restroom sakinshi tayi tajawo kofan yawuce yana bin dresses daya gani akan gadonsu da kallo yace  who bought this dresses? Murmushi tayi tace  Mami ne takawo mana tsaraba daidai Farida na bude bayi tafito daga ita saidan towel pink ta taho da gudu tai hugging dinsa tace  Uncle M kadawo, kaga Faiza has been troubling me ko? Daman nace saina gayamaka hannunsa Marwan yakai yana share mata kumfan dake kunnenta, Faiza tace  learn how to bath first kafin kidinga kai kar&  Wani kallo Marwan yamata hakan yasa ta hadiye tai shiru kawai Faiza fa fashe da kuka abinma dariya yaso bashi but yahadiye cus yana dariyan kukan zai karu, Faiza akwai saurin kuka tace  kaga wai ban iya wanka ba ko she always bully me Uncle Marwan shafa bayanta yayi sounding very caring yace  don t mind her, kin iya wanka kumfa a kunne even me it happens to me sometimes so don t cry because of that yakalli Farida dake murmushi yace  stop teasing your sister okay Gyadamai kai tayi tace  to nima hug me hannu yamika mata saitazo dukansu yayi hugging nasu yace  did anything happen today a school ko Islamiyya? Farida tace  no, revision kawai muke next week Monday zamu fara WAEC, Islamiyya kuma yau anje hutu next week zamu koma atare sukece  how is hospital today ? Dan shiru yayi kaman mai tunani, atare dukansu suka turasa kan gadonsu ya zauna, Faiza ta dauko chair ta zauna agabansa Farida kuma na nanike dashi suna kallonsa sukace what happen today? Lumshe idanu kadan yayi saiya bude ya kallesu yanda suke kallonsa yace  we got a new patient today sai yayi shiru, ahankali yace  she s just like Farida yasake shiru yace  she s gentle, super fragile morethan Farida and she s also so a small girl, she s my first small patient since when I came back to Nigeria, she s none verbal, I have no clue on how to go about her treatment, do you guys have an idea for me future Doctors? Duk shiru sukayi sai Farida dake rungume dashi ta tashi tace  Uncle kaga in public I hardly speak I only talk at home, mutane na cewa wai bana magana, you see I have two uncle you and Uncle Sam but I hardly talk to Uncle Sam cus he doesn t play with us, my point is idan I see someone that genuinely care for me, he s thoughtful and he s intentional about me just like the way you are very caring I will talk to you Dasauri Faiza tace  you re right Farida, Uncle M kaga naturally you re caring haka Allah ya yika, I think if you continue like that with her maybe she will open her mouth and talk to you, she will trust you, then you can help her get better, don t just study her study everything that she does read her like a book remember uncle this is statement naka kace mana shine first rule na idan kanaso kazama psychiatrist Murmushi yayi kadan yana kallonsu he loves them morethan anything a duniyan nan, saiya mike strictly yana kallon Farida yace  wuce kije kisa kaya anjima kihana mutane bacci da tari mikewa tayi tana murmushi, yaba Faiza hannu yace  goodnight highfive tabashi tace  gud night BUM,best Uncle M Farida ta dawo da sauri tace  nima high-five yabata yace  rigimammiya yawuce yafita daga dakin abinsa yawuce karshen wajen akwai wani corridor nan yashiga saiga dakuna biyu tsayawa yayi yakalli second room din saiyadan sauke ijiyan zuciya yabude kofan yashiga dakine that s very simple yet very fine, Baban bed ne adakin sai shelf wanda medical books da Islamic books ne cike tam awajen maida kofan yayi yarufe, yakarasa yashiga closet nasa ahankali yasa hannu yazare glasses na idanunsa ya ijiye kan slap sannan yarage kayan jikinsa yadauki glasses din yamaida idanunsa saiya bude bathroom ya shiga akwai wani specific chamber dayake bayin next to wajen shower zare glasses din yayi ya ijiye kan chamber saiya shiga shower yayi wanka yafito yadauki glasses din yamaida yawuce yayi brush tareda dauro alwala yafito yashiga closet nasa ga karamin towel a hannunsa yana goge kansa tsayawa yayi sabida Amirah ne tafado ransa, did that man ohh father nata forcefully brought her to the hospital? What about the Mom? The girl isn t violent but why is she hitting her father? Maisa taji masa ciwo akai haka cus he saw it, He also saw kalan cizon data masa wanda it wasn t funny, how can a father zaisa wasu unknown kattin maza suyi man handling sick daughter ka haka da batada lafiya? How can a Dad brought his child to the hospital and left without paying a dime? No explanation? Bai damu da wani hali zata shiga ba? Baidamu da idan hospital din rejected her ba, He saw mutumin he looked into his eyes unlike mahaifiyar yarinyar there s no single affection or soyayya na yarinyar a idanunsa ba kaman mahaifiyarta ba da kallo daya yama matan yasa tana matukar kaunar yarinyar, the next question dayazo ransa is does the mom even knows cewa an dauki yarta? An kawota asibiti? Idan Maman tasan da zuwa asibiti he knows kotana ciwon kafafu zatai rarrafe tabiyosu akawo yarsu tare to the hospital something is fishy? Just today daya ga yarinya he knows she s not having wani autism dasuka lakaba mata, and he s sure he can help her to get better but the way yarinyar keson mahaifiyarta he can t do it alone, he needs the mother, family factors na yakara wan gani a mental condition mai kyau ko mara kyau, Babanta is a bad agent a mental condition nata but Mamanta is a very positive agent in her mental condition idan zaisa yarinyar nan ta warke he needs the Mom she s the first step na therapy yarinyar
Ijiyan zuciya ya sauke yana shafa mai wayansa ringing yahauyi screen din ya kalla Mami yagani hakan yasa ya dakatar da abinda yakeyi yadauki wayan kafin yayi magana tace  Marwan zo kasa maza Abban ku baida lafiya he just entered the house banso yaran su sani dasauri ya ijiye wayan da pajamas zaisa amman saiya dauki wata 3quater black yasaka dayar farar T-shirt mai kyau bai feda turare ba amman kamshi yake sosai yadauki wayansa yafito.


EPISODE =??



Dasauri gaske Marwan yayi stairs tundaga staircase ya hango Mami tareda wani dattijo daya manyanta sosai atleast zaikai 66yrs yana kwance flat akasa yana wani irin haki Mami ta rude, dawani irin gudu Marwan yayi wajen yace  what happened to him Mami? Yayi maganan yana tallabo Abba dasauri, Mami tace  wlh shigowansa kenan ransa abace nasan dai ya ambato Saleem saikawai yafadi saida na yayyafamai ruwa ma yafara numfashin nan ahankali yace  Mami bring first aid box wanda na ijiye a dakin Abba mikewa Mami tayi tace  toh, toh ahankali Marwan yace  Abba, Abba, calm down please nothing is going to happen to you kaji daidai nan Mami tadawo bude akwatin yayi da hannu daya yadauki wani allura yakama hannun

7 / 51