BACCIN SO BY M SHAKUR

Author :  M SHAKUR Category :  African Stories & Novels

Chapter   20 / 51

57K to 60K   out of 151.6K words

Dasauri Saleem yace  why? Wani kallo Marwan yamai sai yadan shafa kansa yace  dazu i was so angry saisa banma tsaya neman CD ba Bantaba yin abu babu protection ba sai yau, ai Dr na yamin all tests I m clear baka gani ba idanun Marwan nakan titi yace  nagani Wayan Abba ne yashigo wayan Marwan hakan yasa yadaga yace  gani nan dashi Abba, zamuje hospital but zamuzo gida daganan Abba yace  to toh saikunzo suna kaiwa asibiti Marwan yayi parking Saleem yafito shima yafito sai suka shiga hospital din office dinsa suka wuce ahankali Marwan yace  go and shower Saleem baiyi musu ba yawuce yashiga bayin Marwan yazauna kan desk nasa yayi shiru kagansa saiya baka tausayi kasan karfin hali kawai yakeyi yazauna yayi shiru kawai, yana wajen Saleem yafito daure da towel saiya bude drawer yaciro another kaya yasaka tsaf ya shinfida dadduma yayi salla yana idarwa yamike yakalli Marwan dake rubuce rubuce yace  na idar muje karasa rubutun Marwan yayi saiya mike tsaye rikeda wani new big drawing book, da wani jar da pencils da crayons da eraser ke ciki suka wuce Marwan na gaba Saleem na binsa abaya, ahankali Marwan yabude dakin da Amirah ke ciki batadade da tashi daga bacci ba tana zaune akan gado duk ta damu sabida yanda bataga Marwan ba tun safe Umma takawo mata abinci kadan taci nurse ce adakin tagama duba vitals dinta tana rubuce rubuce jin an bude kofan dasauri Nurse din ta juyo itama Amirah tadan dago kanta hada idanu sukayi itada Marwan to his biggest suprise saiyaga ta turo baki tareda sauke kanta tamaida kasa yakarasa shigowa Saleem na shigowa Nurse tace  barka da zuwa Dr gyadamata kai yayi yamika hannu takarbi record na Amirah Saleem na shigowa dakin Nurse tabi Saleem da kallo dan bata sanshi ba he s so handsome kaman Dr, duba chats din yayi saiya bata yace  you can go tace  okay Dr Saka sthethoscope yayi a kunne ya tsaya gaban Amirah yana ijiye drawing board da pencils tin a gefenta, ahankali yace  how are you? Bakinta kawai yayi motsi kadan alamun fine maganan ma bai fitoba, hannunta ya kalla yace  give me ur hands hannunsa takawo zata basa saitaga alamun inuwan mutum na tafiya wanda ba Dr ba saita mika hannunta instead of tabashi saita rike gefen labcoat dinsa ta sauke kanta kasa sosai, Marwan dake lurada ita yadake yana danne zuciyansa sosai yace  this is my brother sunansa Saleem saiya juyo yace  Saleem come zuwa Saleem yafarayi wajen gadon Amirah takara rirrike lab coat din Marwan, daidai Saleem ya iso wajen kaman dodone yazo wajen sai kawai unexpectedly tai hugging Marwan daga zaunen datake tana manna fuskanta awajen kirjinsa da six packs din cikinsa, takai dayan hannunta tana kama dayan bangaren labcoat dinsa batare data bama Saleem ko one single look ba, sosai gaban Marwan yake bugawa sabida yanda tai hugging nasa so tight, wani abu Saleem yaji yazomai wuya ganin yanda Amirah ta rungume Marwan gabaki daya kirjinta na manne ajikinsa amman kuma sai yakore abun dayakeji cus yasan waye kaninsa Marwan ba dan iska bane, kuma the way Marwan is principled he doesn t look like wanda will ever develop feelings for any patient nasa, itama Amirah wani iri taji data shiga jikin Dr, she s always doing this to Ammi and Miemie idan Ammi bata wajen amman batajin komi, but jikin Dr yau saitaji wani iri, saitaji wani dumi dawani comfort dawani irin sanyi da dadi, ga kanshi dayakeyi dataji kaman yana sata sakejin bacci, tadauka she will feel normal yanda takeji ajikin _u Ammi idan ta boye ajikinsu amman bataji hakan ba, wani kalan nishi tayi ajikin Marwan cus what she s feeling is so strange, all this happens in few seconds, strictlymuryan Marwan sounding a bit harsh yace  cikani ahankali Amirah tasaki labcoat dinsa tana fitowa daga jikinsa saita koma kanta akasa still takai hannayenta biyu zatasa abaki Marwan yace  noo dakatawa tayi bata sakaba, yadanyi jimm, Saleem da jikinsa har rawa yake yataba Marwan alamun Marwan yasa tamai magana, dan ijiyan zuciya Marwan yasauke, ahankali yace  akwai abinda yake miki ciwo yau? Gyadamai kai tayi alamun eh, murya chan kasa yace  mene? Shiru tayi batai magana ba, saiya tsare fuskanta da kallo saiyaga second pimple yafito mata a kumatu this time, saiya dauke kai yace  baki gaida Brother na ba Saleem dauke kanta tayi gabaki daya yanzu tana kallon gefe tana wasa da hannunta, Saleem saya kasa daurewa saiya duka gaban gadon ta side din data maida fuskanta cikin sanyin murya yace  Hi My Amirahhhh! wani abu Marwan yaji yatabamai zuciya kaman numfashi sa zai fita dauke fuskanta Amirah tayi daga side din dayake da Saleem yazo tamaida fuskanta dayan side din tana wasa da yatsunta kaganta zaka rantse batasan Saleem na wajen ba, Saleem yasake zagayowa yace  my name is Saleem will you be my friend tsare Amirah Marwan yayi da idanu datay1 kaman bada ita ake magana ba ga Saleem na duke akasa, strictly yace  baki iya gaisuwa ba ahankali fuskanta na kallon nowhere exactly cikin yar sanyin muryan tace  uhn& .ina yini!
Ya Rabbi she actually talks like baby Saleem dafa kirjinsa yayi yace  Wayyoo Allah na Marwan sonta zai kasheni! Hawaye Marwan yaji kaman yana taruwan mai a idanu dasauri yajuya yace  let s go dago kanta Amirah tayi takalli Marwan daya juya saita yunkuro zata tashi kasawa tayi Marwan na kallonta ta gefen idanu Saleem yace  bye see you tomorrow Amirah data kasa tashi tabisu da kallo bataso Marwan yatafi ko kadan kawai saitaji ruwa yana taruwa a idanunta, now this is the thing part of kalan ciwonta shine bata kuka, cus kuka shima is emotions which batada shi ko ace bata iya displaying ba, dadi ko rashin dadi, bakin ciki damuwa ko fariciki baka are something da baka gani a fuskanta, ko ciwo take saidai kaga zufa ba hawaye ba but kawai saitaji ruwa yataru a idanunta ahankali takai hannu ta taba idanunta daidai lokacin hawayen ya fito daga idanunta yazuba hannu tasa ta goge takai hannunta ta shafa cikinta dake mata ciwo sosai, saida sukakai office nasa suka shiga Marwan a natse yace  I have to see a patients kafin mutafi ina zuwa Saleem dake tsananin farin ciki yace okay.

Fitowa Marwan yayi yawuce kofa Amirah taji ana budewa hakan yasa ta kalli kofan goshinta na hada zuwa tanaso ta tashi zaune takasa, maida kofan yayi yarufe saiya tako zuwa gadon hannunshi zube a aljihun lab coat ya kalleta yana kallon yanda goshinta ke zufa, gently yace  meke miki ciwo ? Bakinta ne yayi motsi muryanta yafito kadan.  Cikina! Strictly yace  mesa dana tambayeki dazu baki fadamin ba? Shiru tayi taki magana, gently Marwan yace  ba magana nake miki ba ?  I don t like wanchan baice komiba yagane Saleem take nufi, matsowa dab da ita yayi yana kallon kwayan idanunta dayaga kaman tai kuka, bugawa kirjin Amirah yafarayi sosai tana kallonsa tanajin tafiyan some cold butterflies in her stomach, bata taba ganin mutum mai kyan this Dr ba arayuwanta she s still feeling kaman tai hugging nasa, batasan meya faruba amman ahankali da yar baby voice tace  Yaya Marwan! yanda takira sunansa shi kansa Marwan saida kirjinsa yabuga baitaba sanin sunansa nada dadi hakaba sai yau, amman sai bai nuna mata ba ya tsareta da idanu yadake his heart beating so fast yace  na am Ameenah! Batasan mema zatace ba but kawai she s feeling wired, having some creepy feelings ajikinta data rasa na menene, sai kallonsa datake da idanunta dasukemai walkiya a idanu sabida haske ga ruwa na cikasu lips dinta na rawa rawa, da murya yar karama yana kallonta har lokacin kaman yana magana da baby yace  talk I m waiting magana Amirah tashiga kokarin yi amman saita kasa batasan mezatace ba, batasan meya sameta ba wani karfi yazo mata kawai saita yunkuro kadan and just hug him passionately then abinda takeji saiya kara tasomata kawai tasakinmai kuka da she can t describe na menene exactly.

Da ace Ammi zataga Amirah na kuka datai mamaki cus rabon dataga Amirah na kuka tun shekarun yarinta little girl, you know mutumin da bai iya fitar da emotions ba duk randa emotions din zai fara zuwa mai rasa yanda zaiyi yake da how to properly display the exact emotion dayakeji, yanda kirjin Marwan ke bugawa kaman zai fito sabida yanda Amirah ta kankamesa tana kuka she could hear it da ace zata tsagaita kukan, wani irin kuka mai pericing zuciya dayake so gentle so light so low yet ashagwabe and heart melting takemai, he s trying his best yaturata tafita daga jikinsa amman yakasa, da kyar ya iya tattaro the little words dake bakinsa, asanyaye yace  why are you crying like this, kinaso ki kasheni ne? Girgizamai kai tayi tana jikinsa still ta rikesa, ahankali tace  to sakeni saiki fadamin menene makemai kafada Amirah tayi ashagwabe no dan bataso yaje ko ina, batason ya saketa, batason tabar jikinsa, bataso tadenajin kamshin turarensa, batason tadenajin dadin voice nasa dakeda taushi, yakuma ke cika da lalama.


He has little self control idan yanason mutum, he just realize that, cus Amirah na neman jefasa wani yanayi, da kyar yace  Ameenahhh! Wani sanyi Amirah taji aranta saita sake kankamesa sosai nipples dinta nawani kalan tashi yanajinsu akirjinsa sosai danta manne sa sosai ta kwakumesa da kyau, rawa jikinsa yafara, Amirah batada hankali nor wayau, is very wrong of him yabiye mata or entertain such innocent abu datakeyi, ahankali yace  tsaya toh mugani Amirah Ammi saiya shiga cirota daga jikinsa batai musuba sabida cikin lallashi yamata maganan, saita fito idanunta sunyi kananu, kallo daya yamata yadauke kai sabida the way her nipples were pointing out kaman an chokalo tsinke, jikinta yasaki batamasan meka faruwa ba kawai kallonsa take innocently, takai duka hannayenta tasa abaki tana kallonsa she knows absolutely nothing!
Idan mutum baida karfin Imani he will take advantage of her innocence cus ita kanta batasan metake ba ko meke damunta ba, ko meke faruwa ajikinta ba, bargonsa yadauka saiya daura saman jikinta from shoulder to shoulder har lokacin yana kokarin dawo da kansa daidai his body is still shivering falling madly in love with Amirah more and more dudda yayi alkwarin cewa zaiyi BACCIN SO.
EPISODE 2?? 9??




A office Marwan yasami Saleem dake zaune sai murmushi yake shi kadai Marwan ya dauke kai yace  let s go tare suka fito suka shiga mota zuwa gida, a compound suka tarar da Abba shi kadai tsaye Marwan ya tsare Abba da idanu duk yayi zuruu saiya kalli Saleem dake murmushi abinsa yace  can you give this man peace of mind Saleem? Karka manta yanada yara, idan kai baka bukatansa y ayansa needs him da matansa stop troubling him Saleem dan kallon Abba Saleem yayi dake tahowa wajen yayi, yatabe baki yace  ya nemamin aure yaga idan zan karabi takansa yana maganan ya bude mota yafito Abba yakara saurin tafiya yana nuna kansa yace  ni kake cema zaka kawomin yaran karuwai Saleem yayo kansa da zafi kaman zai dakesa, Marwan daya fito saiya tare gaban Abba tareda rikesa yace  Abba dan Allah no, Saleem ba yaro bane and kai hannu ko daga murya will not change anything, babu amfanin kullum kaita fada da dan uwanka ana jinku Saleem yataho yana dan sosa kai yakalli Abba dake kallonsa yana huci yadan dauke kai, yace  sorry Yaya amman nidai kawai kanemamin auren Ameenatu, gobe zan fara zuwa office a company and join the legal team, I m making you one last final promise cewa bazan kara troubling nakaba, I will be responsible da aiki da komi just handle aurena kaji Yays yadan kannema Abba idanu cikeda shedanci, Abba dake kallonsa yace  nika maida dan iska ko Saleem ? Saleem yawuce abinsa yace  a a amman dai kai Yayan dan iska ne Saleem yayi wucewan sa Abba yabisa da kallo idanunsa sunyi ja, Saleem was never like this before tunda yafara shaye shaye yazama dan iska, kuma mara kunya wanda baya ganin kowa da gashi, Abba zaiyi magana Marwan calmly yace  Abba let him be, karka biye masa kaji, kayakuri, Allah ya shiryar dashi tsayawa Abba yayi saiya tsare Marwan da idanu yana kallonsa cikeda tsantsan kauna dakuma so ahankali yace  nagode ko Marwan, Allah yamaka albarka ahankali yace  Ameen Abba yace  Wife tacemin dazu kadawo kanka na ciwo ya kan yanzu ? Ahankali yace  yadena Abba Abba yace  Masha Allah tom muje ciki wucewa ciki sukayi Saleem yasamu tareda Mami a dinning tana basa abinci yana bama Mami labarin Amirah Mami na sauraronsa, everything yafadama Mami daga yanda yaganta rannan bayan ya ari motanta yaje office waje???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n Marwan yabata abinci down to details na abinda yafaru yau da all history Amirah daya karanta a file dinta abun yama Marwan ciwo patient history is confidential akanme zai bada labari Abba zama yayi a falo yasa glasses yana bude wata jarida Marwan yayi hanyar staircase zaiyi sama Mami tace  hala wani laifin abincin yamaka Saleem dakecin abinci abinsa yace  Mami ai wannan bana jin zai so abinci fa , common let s eat, Mami s food is delicious Mami ya kalla ahankali yace  lemme shower zan sauko nasha tea bata cemai komiba tadauke kai yawuce ahankali su Faiza yafara shiga yaduba sannan yafito yashiga dakinsa, ya watsa ruwa yafito yana saka kayan bacci yaji sallaman Mami, dasauri yakarasa saka pajamas yafito yazo wajen kofa yabude Mami ne rikeda tray na abinci, hannu yasa dasauri yakarba yace  Mami why are you stressing yourself zan sauko ai tsaresa da idanu Mami tayi dan harya fada mata, ciki yashiga saita biyosa tamaida kofan tarufe, Marwan ya ijiye tray kan desk nasa yajuyo yakalli Mami data zauna akan kujeran wajen tana kallonsa saitace  what was our agreement tun kana yaro? Shine zaka dena zurfin ciki, komeke damunka you will tell me right? Kanada wata uwa aduniya ne sama da ni Marwan? Girgizama Mami kai yayi alamun no, asanyaye Mami tace  to meka damunka harka fada haka? I could clearly see it, idan kowa zai kalleka bazai gane damuwanka ba ni dazaran na kalleka nake ganewa, What is it Marwan? Shiru yayi shi baijin zai taba iya bude baki yafadama Mami abin nan ba, sauke kansa kasa yayi Mami na kallonsa, chan tace  wacece Aminah dinnan patient dinka da Saleem ke maganan ta? Dan dagokai yayi ya kalli Mami ta tsaresa da idanu kaman tana shirin ganosa, saiya maida kansa kasa, ahankali Mami tace  shikenan ka nunamin iyakata ai tamike zata wuce hannunta Marwan yarike Mami ta dakata ta tsaya tana kallonsa, ga magana abakinsa amman yakasa fadi, hannunta ta karbe daga hannunsa kawai tawuce tabude kofa tafita Marwan yayi shiru yakalli abincin datakawomai, shayi kawai yadauka saiya koma gado yazauna yana sauke ijiyan zuciya idanunsa sun kada sunyi ja.
EPISODE 3?? 0??




Wuraren 8 bayan sallan isha i wayan Miemie yashiga ringing tana tsakar gida tareda Mustapa da Bashir yaran Baffa dasuke kansu daya da Miemie suna hira, macen Baffa daya kuma she s only 5 tana wajen su Ammi dake tareda Baffa, tafito da gudu takawo ma Miemie wayan tace  ana kiranki Mustapa yace  ango ango ke kiranta hararanshi tayi saita tashi taje kitchen tadauki wayan tamaki magana, murmushi Ya Umar yayi yace  kicema Baffa ina waje katse wayan tayi saita fito, Baffa da Ammi da Lami duka suna dakin saita fito tashiga dakin akunyace tace  Baffa wai gashi nan awaje Baffa yayi murmushi yace  to acemai ya shigo Mamama Maryama gyadamai kai tayi tawuce tafita saitaje wajensu Mustapa tace  Baffa yace kushigo dashi dasauri Musty yamike daga kan tabarma yana kakkabe riga yace angama saiyayi zaure itakuma Miemie tawuce dakin Ammi da gudu tana zaune adakin taji an shigo dasu yana gaisawa dasu yaran, falon Abba aka shigar da Umar inda Baffa ne awajen kawai da Lami Ammi bata wajen sabida alkunya, zama Umar yayi kansa akasa bayan sun gama gaisawa Abba yayi gyaran murya yace  ammm to Masha Allah Umari, daman dalilin dayasa na kiraka shine duba da kaddaran data faru ysakanin iyayen matarka dole nakiraka anan naji menene plan dinka Maryama dai tazama matarka, na farko dai zamuso kadan bamu lokaci kafin ta tare tunda auren yazo haka bagatatan bamu gana yan shirye shirye a bangarenmu ba wanda zamuso muyi yanzu kafin ta tare amman fa idan ka yarda kenan tunda kaine mai gidan yanzu Baffa yayi shiru cikeda natsuwa da kamala da girmamawa Umar yace  ammm Baffa eh ba matsala nima a bangarena gidan danake ginawa wanda ashi zata zauna ciki ban karasaba, zai daukeni sati hudu zuwa sati biyar na gama, so tarewanta zai zamana nan da wata daya da sati daya gyadakai Abba yayi yace  masha Allah lokacin ya ishemu, ina muku fatan alkhairi yakalli Lami yace  kiramin Maryama batai musu ba ta tashi tafita tashiga dakinta inda Miemie na zaune tana wasa da Asiya dan mazan harsun fice su Mustapha sai anjima za a gansu tace  tashi sa mayafi Baffanki na kiranki a falonsa na zaure gyadama Lami kai tayi tamike tadauki maroon hijabinta tasaka tafito zuwa zauren sallama tayi kanta akasa, Baffa yace  bismillah shigo Maryama shiga ciki tayi tasamu gefe daya ta zauna, Baffa yace  ga mijinki nan Maryama kisani cewa hakki ke akanki kimai biyayya shine jagoranki ayanzu sannan aljannan ki na tafin kafansa, banso naji ance

20 / 51