BACCIN SO BY M SHAKUR

Author :  M SHAKUR Category :  African Stories & Novels

Chapter   12 / 51

33K to 36K   out of 151.6K words

 stop fighting my nurses they re all here to take of you, yanzu za a miki wanka kisa kaya then I will come back muyi maganan Kaganta this time bazakace da ita ake magana ba daidai Umma ta shigo wata yar dattijuwa ce sanye da uniform na ma aikata tace  sannu Dr M Gyadamata kai yayi yace  yauwa Umma, please ki taimaka mata tai wanka ta chanza kayan nan Umma tace  tom shikenan yammata tashi muje sai kawai Amirah ta sauko daga gadon ahankali har lokacin hannunta na baki tana cin kumba ga fitsari duk a wandonta tasauke kanta kasa kaman tanadan jin kunya tafiya agabansa ahaka, juyawa Marwan yayi yafita daga dakin batare daya karaba jikinta second look ba cus uniform din sundan kama jikinta shape nata yafito sosai hips dinta da boobs nata, yace  Baaba adinga samata uniform dasuka danfi wannan girma part of job nasu is protecting features na patients nasu ta yanda suransu bazai wani fito sosai dahar zaisa wani patient ko Dr ko worker yaganka yayi sha awanka ba,

Wucewa yayi yashiga duba other patients nasa, bayi suka shiga Baaba tahada mata ruwan wanka tace  yauwa zo ayi wankan toh make mata wuya Amirah tayi saita shiga tafiya ahankali ta duka ta rungume buket din irin kaman kunya takeji, Umma tace  ohh kunya akeji to maza yi wankan, ni bari na gyara gadon fita Umma tayi hakan yasa Amirah tacire kaya ahankali tashiga watsa ruwan ta shafa sabulu batason soso dama gamawa tayi tadaura towel tafito taga Umma ta ijiye mata uniform tace  masha Allah angama ka kaya saka daukan kayan Amirah tayi saita kara juyawa takoma bayi tasa kayan tafito tazauna abakin gado tana murza hannunta a cinya Baaba takawo wani black cap tace  a sa wannan ko takawo tasa mata black cap din aka ta tattare gashinta tasa aciki ahankali sannan tawuce tafita dan dago kanta Amirah tayi tawuce kofa chan sai gasa yazo wajen yarataya sthethoscope a wuyansa hannunsa daya rike da folder da iPad dayan hannun rike da wani small bottle of water da karamin container da kwayoyin magunguna guda biyu rak keciki, ahankali yabude kofan yana kallon gadon baiganta akai ba, lurada mutum dayayi a gefen kofan yasa yajuyo da kansa yakalli gefen kofan tsaye yaganta kanta akasa tana wasa da yatsunta, tundaga kai yake kallonta an samata hula black, zuwa uniform na jikinta yanzu that are a bit free compare to na dazu kafanta ba takalmi ba safa haka take taka tiles din, sosai tashiga murza hannayenta sai kuma tadaga hannu daya takai tasa fingers nata a baki bata dago kanta ba dake kasa, ahankali Marwan yamaida kofan yarufe calmly yace  jeki zauna juyawa tayi tawuce taje ta zauna abakin gadon like a very obidient girl saiya taho wajen yajawo wata kujera yazauna yana facing nata saiya ijiye bottle of water da container na maganin daidai anyi knocking Umma ce takawo tray na breakfast da akama patients yau tea ne da bread da egg abincin is not bad for government hospital o, hannu yasa ya karba da kansa ya kalli abincin saiya bata yace  take this kin cire hannunta daga baki Amirah tayi takima kallonsa sai cin yatsu datakeyi tana wasa da kafafunta, he knows bazataci ba bataso, saiya juya yaba Baaba yace  Baaba akwai flask na abinci a office dina za adan taimakamin dashi Umma tace  toh Dr tawuce tafita. Ahankali Marwan yasa hannu a aljihun lab coat nasa saiya ciro leda na new dogon black socks mai dan kauri yabude yacire safan tareda mikemata yace  take put this on a kafanki, always wear sock daga yanzu left hand nata wanda shine akan cinyanta takai tamikamai still bata kallesa ba, Marwan yace  no bani hannun dama not left cire hannunta tayi daga bakin tamikamai duk saliva a jiki, tsare hannun yayi da idanu saiya saka hannunsa a aljihun yaciro handkerchief dinsa, ahankali batare da skin na hannunsa yataba fatar hannunta ba yashiga share mata yawun daga hannunta, gently Amirah tadago kanta tadan kallesa da fararen manya manyan idanunta, kawai Ammi ta tuna anytime taba Ammi hannu idan akwai datti ko ruwa ko kasa ko yawu a hannunta sai Ammi tafara sa tsuma ko wani abu ta share hannun tass kafin tabata abinda zata bata, sosai take kallonsa especially glasses dake idanunsa, da lips dinsa dasuke pink yirrr ga kamshi mai bala in dadi dayakeyi dake kwantar mata da hankali.

Tass Marwan ya goge mata hannun saiya saka safan akai tareda dago kansa karaf hada ido yayi da Amirah dasauri Amirah ta maida kanta kasa abin yadan basa mamaki ganin takallesa, bude safan tayi saita shiga sawa a birkice wajen diddige na saman kafa instead of yazauna a kasa zata saka dayan, cikin tattausan murya Marwan yace  wait! Tsayawa Amirah tayi batare data kallesa ba, hannunsa biyu yakai kan kafan data saka safan, ahankali yakama fatar safan without touching her sai yayi adjusting ya daidaita safan, kaman yana magana da Baby sabida how soft he s da ita yace  jashi sama toh ahankali Amirah taja safan sama, Marwan yace  sa dayan saka dayan tayi same way, yasake gyara mata saiya koma yazauna yabude file nata sai yayi rubutu awani fresh paper, saiya dago yakallate tamaida hannunta baki, a hankali yace  I will ask you some questions inhar kin bani amsa kinyi duk abinda nace baki mana rashin ji ba zan kawo miki Ammi gobe kin yarda zakiyi ? Gydamai kai tayi tana cin hannu tana kallon waje daya, gently yace  stop eating your fingers ciro da hannun tayi daga baki ta ijiye akan cinyanta, saita shiga ninninke yatsun nata all together Marwan na kallonta saiyayi rubutu ahankali yace  kinsan sunanki ? Gyadamai kai tayi, his eyes fixed on her yace  gayamin sunanki naji dan bata lokaci tayi kaman mai tunani idan zatai magana murya chan kasa that s very tiny and slow suna kiran term din a psychiatrict world da bedroom voice idan baka natsu bama bazakaji me zatace ba, murya very very kasa Amirah tace  A& ..mirah! .
EPISODE 1?? 5??





She speaks very low with a very gentle tone da zaka dauka a year old baby ne tai magana, muryanta bala in dadi, soft charming and adorable da baby yanda zatai magana da zuciyanka bazai amsa ba, sosai Marwan ke kallonta tai maganan tana wasu wired wasanni da yatsunta bazama kace itane tai magana ba, kaman badaga bakinta maganan yafito ba, rubutu yayi yacigaba da kallon gesture datake making, calmly yace  Amirah sunanki but rannan Ammin ki tafadamin asalin sunanki, kinsan asalin Sunanki? Shima magana yake mata calmly and very gentle baiso yadaurama kanta abubuwa dayawa, gyadamai kai Amirah tayi alamun eh batare data kallesa ba, Marwan daya kafeta da idanu bayako kyaftawa yace  gayamin, menene asalin sunanki wannan karan maganan ma fitowa yayi daga bakinta like whispering, kaman irin tafadi ma mutum magana a kunne dinnan, tace  Ameenatu! Wlh bugawa kirjin Marwan yayi dum! Dan shiru yayi ya lumshe idanu kadan taredakai hannunsa yadaura kan goshinsa sannan yazare tareda bude idanun, why is he feeling like this towards this patient? Yasake dago idanunsa yadaura akan fuskanta yana kallonta, wasa take da hannayenta tanadan motsi da kafafunta suma, dakewa Marwan yayi ya danne duk wani abu da zuciyansa kemai yace  dake da waye da waye agidanku ? Tafin hannunta daya shiga zufa ta share a cinyanta saita daga duka hannunta biyu zatakai baki saita tuna abinda yace dazu yahanata wasa da yatsunta tashiga yi saita kalli gefe kaman bada ita akai magana ba, chan da yar kankanuwan muryan tace  Ammi, Miemie da Amirah ne agidan muuu taja muu din like a baby tai shiru sai kawai this time takai hannun nata baki tafara ci tana kallon gefe, Marwan ya tsaya yana kallonta kirjinsa na bugawa dum dum dum yana maimaita kalan sigan yanda tajero sunansu Ammi, Miemie da Amirah ne agidan mu, irin yanda yara ke gayamaka waya da waye gidansu dinnan sai Marwan yayi circling Babanta cus bata ambato mahaifinta ba, daidai lokacin akai knocking akan shigo Baaba ce da flask dayace takawo mai tace  gashi Dr nuna mata inda ya ijiye ruwa da magani yayi saita wuce ta ijiye tajuya tafita, sai yadauki wani empty blank paper yarubuta Ameena boldly saiya daga paper yabata yace  take hannunta datake wasa dashi tazare zata bashi na haggu batare data juyoba saita basa na dama yasa mata takardan ta amshi paper tana kallo yace  mena rubuta anan? He wants to know idan ta iya karatu koda kadan ne, ahankali Amirah tace  Ameenah murmushi Marwan yayi yace  good job Ameenah wani sanyi taji a zuciyanta kaman an goga da kankara yanda yace good job Ameenah, saiya mikamata hannu alamun tabasa yace  kawo basa tayi ahankali tana kallon agogon hannunsa, saiyasa hannunsa a aljihu yaciro chocolate na cabry diary milk yamika mata yace  that s all for today take your reward chocholate din ta kalla sai dawani irin sauri tasa hannu ta amshe, zata bude yace  wait, wait kisha magani kici abinci then chocholate maganin yakawo yana bude ruwa, yawanci su ne suka ba patient magani da kansu a gidan mahaukata wannan ka ida ne dan patients akwai wayau basashan magani, gently Marwan yace  haaaa kin bude baki Amirah tayi dan batason magani ko kadan takai hannuwanta biyu tadaura akan fuskanta tarufe, abin yaso basa dariya, saiya mika mata hannu yace  bani chocholate dina tunda bazaki sha magani ba dasauri tacire hannayenta dake kan fuskanta da chocholate din ke jiki taboye chocholate din abayanta tana makemai kafada batare data kallesa ba, Marwan yamata wani kallon mamaki da ace this girl is very fine kalan tsiwan dazatayi ko, ataushashe kaman mai lallashinta yace  okay tunda bakiso na amsa chocolate din open your mouth kisha magani, ko bakiso nakawo miki Ammi ? Ahankali tabude baki jin maganan Ammi, dan bugawa zuciyansa yayi sabida yanda tabudemai bakinta that is very clean, hakoranta yan kananu with her very pinkish lips and tongue, maganin guda biyu yasamata abaki tareda samata ruwa ta zuka ta hadiye tana lumshe idanu tai ahhhh, ahankali yace  karkimin amai yadan kalleta to be honest bata iya expressing happiness ko sadness ko tsana ba, she hates magani tasha taji ba dadi but fuskanta is just d way it is, rufe goran ruwan yayi yace  open your mouth nagani cus you patient are kinda sneaky now adays bude bakinta tayi ya kalla saiya wuce wajen warmer da Mami tabasa abinci saiya bude, chips ne da eggs da pepped chicken and plantain saiyasaka spoon yazo wajen yabata yace  ea& . Kafin yama karasa magana yaga takawo hannunta takarbi kulan hannunta nataba nasa takarba da sauri tadaura akan cinyanta saitasa hannu tafara cin chips din da egg da plantain, tsayawa Marwan yayi yana kallonta saiya sa hannu yadauki bottle water din yabude yazo wajen ya ijiye mata a gefenta, sai kawai yadena kallonta yabude folder yashiga rubuce rubuce saiya rufe yasake kallonta she s still eating comfortably kaman batasan da mutum awajen ba, sai yadan sauke ijiyan zuciya since she s eating today unlike jiya, and yau she s not running temperature, yajuya zaiyi kofa dawani irin sauri Amirah tamike tabiyosa hannunta daya rikeda chocholate dinta dayan rike da kulan abinci gabanta na faduwa hankalinta natashi bataso yabar inda take, dakatawa Marwan yayi ya tsaya jin tabiyosa yajuyo da sauri yakalleta tana tsaya dab dashi kanta akasa ga kulan a hannunta da chocholate, kaman zata shiga jikinsa ayanda take dab dashi yayi dan jim saiya juya yawuce yace  muje kici abinci juyawa tayi itama sum sum yanuna mata gadon taje ta zauna tasake tacigaba da cin abincin yana tsaye yana kallonta, she has a very very good appetite dudda bada sauri takecin abincin ba but she s eating well, tagama takama naman duk tanaci, abinma dariya yaso basa saiya dauke kai yaciro wayansa yana dannawa dan ita kawai yake jira, kadan tarage a abincin tadauki ruwan tasha ta ijiye saiya dago kansa yakalleta ganin tagama kanta akasa saiya maida wayansa aljihu ya matso dab da gadon yasa hannu yadauki gora sai yarufe ya ijiye a gefe yadauki flask din yakalli dan naman karamin data rage, saiya sa hannu yashiga picking abincin data zuzzubar a gadon, ahankali Amirah tadan dago idanunta ta kallesa yana wani irin sanyi takaraji acikin zuciyanta kaman an zuba kankara, rufe flask din yayi ya ijiye ya kalleta hada idanu sukayi dasauri Amirah tadauke kai, baice mata komiba yawuce wajen bayi dasauri tamike tabiyosa yana bude kofa tabisa yajuyo ya kalleta saiya kunna tap yace  come wash your hand bude tap yayi saitazo tasa hannunta akasa tana wanke hannunta saita bude baki hakoranta suka fito tai wani clapping hannunta under the running tap ruwan yawani tawarwatsa har fuskan Marwan ya tsareta da idanu ahankali yace  wasa da ruwa nace kiyi dasauri tajuyo ta kallesa sai takai hannun data wanke zatasa abaki yace  don t, clean your mouth goge bakinta tayi, yace  wash your hand again wanke hannun tayi, saiya bude kofa yace  let s go ahankali tafita yafito shima, wani takalmi canvas ne wanda shine general shoes dasuke bama patient nasu fari ya dauko a drawer dakin, sa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?iya duka ahankali gabanta agaban gadon, Amirah ta kallesa, bude takalmin yayi yace  put your leg sa kafanta Amirah tayi saiya samata takalmi da kyau ya kulle igiyan sai kallonsa take kanta trying to put things together, he s just like Ammi, he is her second Ammi sabida yanda yake kula da ita, same thing da dayan kafan yayi ya kulle, yakalli hulanta ya zauna akanta sosai, yace  let s go saukowa tayi yadan tsaya ya kalleta fully kayan looks free ajikinta sai yajuya kawai yawuce yayi kofa tana biye da shi abaya suka fito, lobby yakaita yau drawing a painting ake koya musu, chair yanuna mata yace  sit zama tayi Malaman na kallonsu da other patients, Malaman takawo mata new board da pen ta ijiye tace  here you go anatse Marwan yace  I want you to draw anything dakika tuna, stay here I will come back anjima kadan karki biyoni yafada strictly saiya juya binsa Amirah tayi da kallo zuciyanta yashiga rawa sosai har saida tadaina ganinsa sai kawai takifa kanta a table din tai lamo kaman marainiya tareda lumshe idanu.
EPISODE 1?? 6??




**
Wuraren 1:30PM Saleem yashiga bude idanu shima sabida knocking kofan dakin da Mami tazo tanayi da kanta ne,  Saleem maza atashi lokacin sallan zuhur yayi da kyar kaman zaiyi ihu ya juya, sai kawai Mami tashigo dakin labulen windows daki tabude dakin yayi haske abinda baiso kenan yabude idanu yatashi zaune kaman zai mata kuka yace  Mamsssss dakuwa Mami tamai tace  wuce kaje kayi salla Saleem kafito ina jiranka magana zamuyi dan kallonta yayi kadan saiya tashi ahankali yawuce bayi Mami tawuce tafita daga dakin.
Wanka yayi yafito da gangan yakara shiga closet na Marwan yanabin kananun kayansa da kallo, they re to decent for his liking hakanan dai yazaro wani Zara jean blue da farin shirt na H&M yasaka, yadauki p-cap yarike a hannu yafito yana baza kamshi saiya shimfida dadduma yayi salla yawuce gadon yadauki wayansa yana dubawa miss calls ne dayawa kuma duk na abokan sa ne, message din David yaduba a watsapp yace  Johnson street yasan abinda abin ke nufi hakan yasa yawuce yafita daga dakin tundaga staircase yake kwalama Mami kira.  Mams, Mams Mami dake kitchen tare da masu aiki tace  oh ni jama a Saleem gani nan fa fitowa tayi daga kitchen takallesa tace  zokai breakfast baiyi musu ba yawuce yazauna kan dinning wayansa na ringing yasa a kunne yana magana Mami na zubamasa abinci, fried rice tasamai da tea da kaji sauke wayan yayi daga kunnensa yace  you are the best cook Mams zuwa bayansa Mami tayi kai tsaye yaji hannunta akan kunnuwansa dasauri yakalleta Mami tahararesa tace  kace wani abu wlh saina rankwashi kanka bani dan kunnen nan, ko su Faiza naba suna sawa zaka sami lada, these don t belong a kunnenka eh Saleem yanajin nauyin Mami sosai sama da yayan nasa ma, cire an kunnayen tayi takai hannunta ta kwance sarkan shima ta cire kaman zaiyi kuka yace  Mamssssss zama kusada shi tayi ta tsaresa da kallo tace  Saleem! Kin magana yayi yaturo baki yana jan abincinsa yafara ci, Mami ta tsaresa da kallo, tace  Saleem wai bakaga mutuwa ake ba yau mune gobe bamu bane, menene amfanin muna sabama Allah da gangan with the little time we have left? Kayi islamiyya kayi boko, d same school dakayi shi Marwan yayi, amman baka aiki da abinda aka koyar daku a islamiyya, we all love you so much we want the best for you mesa kake haka ? Muryan Mami yadanyi sanyi, saiyadan kalleta yace  Mami don t do the sad voice here please just tell me mekikeso ? Shiru Mami tayi tana nazarinsa, all magananganunn data gamayi ko tabasa basuyi ba wlh kawai dan muryan data chanza ne bai so Abinci ma yakeci abinsa, ahankali Mami tace  aure nakeso kayi Saleem! Ruwa yakai bakinsa amman saida ya kware yahau tari yana buga kirjinsa yakalli Mami yace  wait wat? Mams mene? Aure? Me? Ya yunkura zai mike Mami takamasa ta zaunar tace  zauna ban gama magana dakai ba kaman zaiyi kuka mata dan jiransa ake yace  Mamii please jirana akeyi fa Mami tace  fitanma saina hanaka dasauri yace 

12 / 51