Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Baccin SO Complete Hausa Novel by M Shakur

Author :  M SHAKUR Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 51

42K to 45K   out of 151.6K words

Ya Fadila, kap gabaki dayansu suna kama, kana ganinsu kasan yayyinsa ne especially Fadila wanda ita Marwan kebi tabasa 2yrs, ita ke rike da cake da akwai candles na 34yrs ajiki, suka hau waka.  Happy birthday to you, Happy Birthday to you Happy birthday, happy birthday to Marwan, happy birthday kid bro kansa yadan shafakai cikeda takaici zai juya Ya Fadila tace  zai gudu dasauri Ya Ammah tazo ta jawosa tace  zan cimaka mutunci fa Marwan kaman zaiyi kuka yadan kalli Mami dake dariya na manya tana kallonsu yace  Mami Mami tace  don t call me, kasan how long they ve been planning this? Kowacce tazo gidan nan sabida kai kana wani Mami awajen, menene problem dinka da birthday naka ? Ya Maryam tace  zaunar dashi Ya Ammah ya hura candles nasa zaunar dashi Ya Ammah tayi tana karban folder hannunsa da labcoat, tace  Faiza take this folder to your Uncle s room dasauri Faiza ta amsa tawuce sama, Ya Fadila takawo cake din tana murmushi sosai tace  Happy Birthday Kiddo wani kallo yamata yace  waye Kiddo ? Ya Maryam wacce Fadila ke bi tace  kahura candle kadena wahalar damu Mami ya kalla gyadamai kai tayi alamun yayi, baiyi musu ba, ahankali ya hura candle din, sukahau tafi, Ya Fadila ta lakato icing sugar ta shafa masa a fuska tana dariya, Marwan yace  Mami zuwa wajen Mami tayi kaman zata mata fada sai itama ta lakata ta shafa mai a kumatu tace  happy birthday Son, Allah maka albarka saita mannamai kiss a goshi, lumshe idanu yayi, Ya Ammah ta rungumesa tace  I love my only brother Ya Maryam itama ta zauna tace  I love him even more, Faiza kumana hoto dasauri Marwan ya yunkura zai tashi suka rikesa, Ya Fadila tace  Wlh saika dauki hoto yahade fuska twins na dariya suka mummusu hotuna,
Ya Ammah takama fuskansa tace  smile dan Baby this is what you get idan all yayyinka mata ne kaman zaiyi kuka yamike zai wuce Fadila tai hugging nashi tace  tsaya kaji ina zaka sabida kai aka hada meeting dinnan fa dan tsayawa yayi ya kalleta yace  meeting na mene ? Mami ganin yagaji and tasan bazasu barsa yahuta ba tace  sai gobe za ayi go and get changed yanzu ka sauko let s do dinner dan kallonsu yayi duk suna kallonsa, understanding mata is so hard yakasa gane anything, sai kawai yajuya yana magana kasa kasa yace  why do i have to be their younger brother not elder please, i hate this! Ya Maryam tace  Allah ne yakeso yakama ka kuma ba yanda zakayi bai kara magana ba yawuce abinsa.
Ya Ammah wacce kebin Mami tace  but how s the girl like Mami? Duk Mami suke cemata kap dinsu, Ya Maryam tace  banson yarinya mara tarbiya fa wacce zatazo tarabamu da kanninmu, we raised kaninmu together zumuncin mu is thriving so she has to be good and from a good home ahankali Mami tace  kawai namai sha awabta ne, tanada hankali sosai, ga kirki, she called me jiya taji ya kafan nawa, kawai ni namai kwadayin yarinyar sabida nasan baida budurwa, kuma naga itama sai Satan kallonsa take, zanso ahada bikinsa dana Saleem suyi aure, he s 34 why is he still single yakamata yanada yara by now Ya Ammah tace  ai haka likitoci suke wlh idan bamu tsaya akansa ba auren ma bazaiyi ba dayayi aure zaiyi gwara yaje yakaro course kan wani abu daban karatun likitoci baya taba karewa fa aduniya duk sukai dariya, Fadila tamike tace  lemme go and bring him down .
EPISODE 1?? 9??





Sama Ya Fadila tawuce knocking dakinsa tayi batare data bude ta shiga ba, he might be kanninsu but all of them even Mami wacce take matsayin mamansa da mamansu duka respect him, sabida Marwan nada natsuwa, da hankali, they all play and crack jokes but they respect his privacy sosai, sake knocking tayi tace  idan bakace na shigo ba Allah zan shigo abu&  bude kofan Marwan yayi yana sanye da 3qauater wando na common flag dawani dari green sleeve daya kamasa hakan yasa muscles dinsa suka bayyana na hannunsa a mummurde yama baza kamshi da farin glasses din a idanunsa yahade fuska sosai itama Fadila tahade fuska tana kallonsa tace  wai sabida kaga kafimu girma shine you are feeling kaman kaine babba hararanta yayi kawai yajuya baiyi magana ba, shigowa dakin tayi tanabin ko ina da kallo dakinsa kamshi sosai everywhere looks clean tawuce bakin gadonsa ta zauna shikuma tana kallon wani English novel dake wajen babba masu irin thousand plus pages dinan mai suna love wreck, tadauka tabude tana murmushi tace  you book warm Marwan ya wuce closet nasa dan Saleem ya hargitsamai kaya aikin yakeyi, ahankali Fadila tamaida novel din ta ijiye tanabin ko ina da kallo tace  Doc kasan mene ? Shiru yamata still hakan yasa tamike tashigo closet din ta tsaye gefensa tana kallon yanda yake arranging kayansa tace  Mami wants that girl for you dan tsayawa yayi chak saiya juyo ya kalleta looking very confuse yace  which girl? Ya Fadila tace  wacce ta taimaketa a airport dan gajeren tsaki yayi yajuya yacigaba da abinda yakeyi bai magana ba, sai Fadila tazo gaban closet din ta tsaya gabansa tana kallonsa sosai, ahankali yace  what? Hannu tasa ta karbi hannunsa tarike cikeda dan damuwa tace  Marwannnnnn dan rage murya tayi tace  please get married kaji kodan hankalin mu ya kwanta gabaki daya, kagama school you are doing well for yourself, to what is stopping you from getting married? Kobakayi dan mu ba do it for Mami kaji, you know batason takuraka tana sonka da yawa amman batada burin daya wuce kai aure kasami yarinya daga gidan arziki ka aura kaji shiru yayi baice komiba, Fadila tace  Kanada anyone yet dakakeso tunda bakason wacce Mami keso ? Ahankali yawuce yana tattara kayan laundry kaman bazaiyi magana ba yace  I don t know dasauri Ya Fadila tace  I don t know? What does I don t know mean? Is that a yes ko no saitai shiru kaman mai tunani saita zaro idanu tace  akwai wacce kakeso amman baka riga kafada mata ba kenan Marwan is that abinda kake nufi ? Wucewa yayi yashiga restroom abinsa Fadila tai wani tsalle tace  yesss, yessss saita wuce tabar closet din dasauri tasauka kasa.
Around 9 ya sauko yau duk agaidan Mami yau yayyinsa suka kwana, kitchen yawuce yasami Mami na bama Faiza cereal tace  morning Best Uncle kanta yashafa yace  how are you tace  fine ta karbi cereal tafita yace  Mami ina kwana Mami tace  nace maka we have meeting yau ina zaka kuma ? Ahankali yace  I have patients now anjima idan zaku fara calll me zan dawo dan jim Mami tayi saita gyadamai kai tace  muje kai breakfast toh dasauri yace  Mami nadawo zanyi I don t want to eat this early, or pack for me yayi magana tuna Amirah dayayi& ..

Wuraren 10 yakai asibitin parking yayi yafito as usual yana tafiya a nutse dayake yau Friday, wani soft yadi ne ajikinsa dark blue anyi wani simple karamin aiki a wuyan Ya Rabbi yayi wani irin kyau kaman ango, baisa hulaba gashin kansa sun kwanta suna kyalli glasses na idanunsa sunmai kyau, hardly yake rike kulan amman yau yadauki kulan abincin da Mami tasamai da kansa yawuce ciki yana shiga reception yaga Ammi zaune da hijabi har kasa tareda wata yarinya da kusan kansu daya da Amirah zamatafi Amirah kiba saidai Amirah tafisu haske sosai but suna kama tana sanye da black hijab, yana ganinta yagane itane Miemie da Amirah ta rubuta, tunda ya shigo reception din Miemie takafesa da idanu tunda take arayuwanta bata taba ganin namiji kyakkyawa dan gayu irinsa ba ba lab coat ajikinsa so he doesn t look like a Dr, yana shigowa reception din yadauki kamshi, kallo daya yama Ammi yaganeta batama ganesa ba saiya taho wajen kai tsaye alamun mutum na zuwa towards them yasa Ammi tadago kai itama bata ganesa ba danba lab coat a idanunsa amman glasses na idanunsa yasa tadan dauki fuskan tamike da sauri tace  Doctor ina kwanan mu anatse Marwan yace  Assalamu Alaykum, ina kwana Ammi ahankali Ammi tace  lafiya lau ta taba Miemie dake kallonsa tace  baki iya gaisuwa ba dasauri Miemie tace  ina kwana Gyadamata kai yayi batare daya amsa koya kalleta ba yajuya yace  let s go dasauri Ammi tace  to suka bisa abaya har zuwa office nasa Ammi sai kallon wajen take yanda wajen yakeda kyau kaman ba a Nigeria ba ga patients da uniform suna breakfast mai kyau shayi da bread da egg, ga ma aikata ana kula dasu, suna ganin Marwan suka fara ihu.  Dr M good morning hannu yadaga musu yace  morning friends yabude office ya shiga yace  bismillah shigowa su Ammi sukayi suka yanuna musu couch Ammi gabanta faduwa kawai yake ta kosa taga Amirah, labcoat dake hanger Marwan yadauka yasaka tareda daukan sthethoscope nasa yace  bari nakawota Ammi tace  tom yawuce yafita Miemie tabisa da kallo Ammi ta daka mata duka tace  baki taba ganin likita namiji bane kike binsa da idanu haka dasauri Miemie tace  Ammi wlh bantaba ganin Dr dan gayu kyakkyawa kaman balarabe ga charisma irinsa ba, Ammi inama ya auri ya Amirah, yaransu will be very fine Baki Ammi tabude tana kallon Miemie, sai kawai takai hannu ta dan bugi bakinta tace  shirmammiya yimin shiru Miemie tadan turo baki bata kara magana ba.
Ahankali yabude kofan dakin Amirah na zaune bakin gado an gyara dakin tsaf Umma na tareda ita tayi wanka ta chanza uniform Umma na bata abincin data kawo mata taki karba yana bude kofa Amirah tajuyo da sauri ta kallesa sabida kamshin dataji, yana sanye da lab coat baisa botura ba kana ganin blue yadi dake jikinsa wani irin sanyi Amirah taji da batasan sanda tadaga hannunta takai baki ba tana bitting nails nata kafafunta farare tasss dan ba a Riga an maida mata black sock dinba, Umma tace  barka da zuwa Doctor karasowa wajen yayi anatse yace  sannu da aiki Umma Umma tace  takicin abincin hannunsa yamika yadauki chat na Amirah yana dubawa dan yaga abubuwan da nurses sukai logging in yace  barta zaki iya tafiya wucewa Umma tayi ta bar dakik yana tsaye wajen yana duba chat nata Amirah da hannunta ke baki tasake dago kanta kaman yar Baby ta kallesa wlh yamata kyau genunaa da sajensa akwance suna shinning yana kamshi sosai wani irin haske taji azuciyanta tareda sanyi juyowa Marwan yayi yadaura kwayan idanunsa cikin nata wani kalan kwarewa tayi da tari sabida tsabagen sanyin dataji sabida yanda ya kalleta cire idanunta tayi tana tarin maida folder yayi yarufe saiya taho ya tsaya gaban gadon daidai tarin na tsayawa hannunsa yasa yadauki black sock dinta dake gefen gadon batare daya kalleta ba yace  baki iya gaisuwa ba sai kallon mutane dayan hannunta takai tasa abakin tahada duka biyun ko tadanji dama daman abinda takeji cikin yar karaman very tiny bedroom voice din tace  ina kwana  how are you Ameenah? Ya amsa da very husky manly voice yana kallon fuskanta ganin wani katon pimple guda daya daya fito mata a kumatu wanda babushi jiya yana gani yasan kuma na menene, shiru tayi takasa magana, saiya sa mata safa a kafa without touching her skin juyowa tayi ta kallesa dukawa yayi saiya dauki canvas nata ya zazzage datti dake ciki yashiga samata yana kulle igiyan yasa mata Second one din saiya mike yakalleta dasauri tadena kallonsa yace  kinaso kiga Ammin ki? Dasauri tajuyo ta kallesa lumshe idanu yayi yabude yace  let s go dasauri tawani sauko daga gadon jikinta har wani tsuma yake dudda fuskanta is normal ba farin ciki nor bakin ciki saiya juya yayi gaba tabisa da sauri yabude kofa yajuyo yana jiranta danya lura bata iya tafiya da sauri ba ficewa tayi yafito yarufe kofan yawuce tana biye dashi har zuwa office nasa, bude kofan yayi Ammi tamike dasauri hakama Miemie Marwan ya matsa yana kallon Amirah yamata alamu data shiga dawani irin sauri ta shiga ganin Ammin wani tsuma jikinta yafara kaman tai shekara bataga Mamanta ba kawai saita wani irin kwasa da gudu tai wani tsalle kaman yarinya tawani rungume Ammi ta kankame Ammi gamgam tana manna fuskanta sosai a kirjin Ammi kaman zatasha nono, batace anything but kalan hugging Mamanta datayi says morethan enough, she misses mahaifiyarta, kankameta Ammi tayi idanunta na ciko da hawaye sosai duk yanda Ammi taso kartai kuka amman takasa sai hawaye tana shafa bayanta tace  Amirahhhhh Miemie ta share hawaye tana kallonsu she s so happy taga sister ta, Marwan yadade yana kallonsu dazai shigo office dinne amman saiya maida musu kofan yarufe yawuce they need the time.
EPISODE 2?? 0??





Ammi taciro Amirah daga jikinta da bataso ta barta taga yarinyar kaman ma takara kyau ne tana bin jikinta da kallo tundaga sama har kasa tace  Yammatan Ammi ta tsare Ammi Amirah tai da idanu tana kallonta batako kyafta idanu, Miemie tace  ni barakimin magana ba ko kallonta Amirah tajuyo tayi saita shige jikin Ammi dasauri tai lamo amman still tana kallon Miemie dake murmushi sosai, Ammi tacirota daga jikinta ta zaunar da ita cikeda kulawa irin na mahaifiya ta taba uniform din tace  wayake samiki kayan nan Amirah ? Ahankali tana kallon Ammi da yar karaman muryan tace  ni Ammi tace  an ina ? Ahankali tace  bayi Ammi tace  wanka fa waya miki ?ahankali tace  ni Ammi tace  da me da me nace babu kyau namiji ko mace su taba miki idan sun taba kiyi ihu ki gudu ko kiyi cizo sannan ki sanar dani ahankali Amirah ta nunama Ammi boobs da wajen fitsari, cikeda hikima Ammi tace  wata ko wani yataba? Girgixama Ammi kai tayi alamun a a, wani ijiyan zuciya Ammi tasauke tace  Alhamdulillah ,Alhamdulillah Ammi takai hannunta tadaura gefen fuskanta tana murmushi sosai hawaye naso su kara zuba amman ta tsaresu tace  bari Dr yazo saimu tafi gida ko sake hawa jikinta Amirah tayi ta kankame Ammi wlh kaganta zaka dauka nono zatasha she s super clingy to her Mom, Knocking kofan akayi Ammi na kokarin cireta taki fita daga jikinta tai lamo Marwan yabude kofa tashigo batare daya kallesu ba yamaida kofan yarufe Ammi tabisa da kallo kawai taji zuciyanta ya natsu da Dr ganin diyarta is fine babu wanda yayi kokarin cutar da ita a facility or take advantage of condition na yarta na rashin wayau da shirme haka, zama Marwan yayi ahankali Ammi tace  Doctor Marwan dan dago kansa Marwan yayi dan baitabama tunanin Ammi zata rike sunansa ba ko ta kirasa in full hakaba, baki Ammi tabude zatai magana but she s so emotional saitai shiru kafin tace sauke iniyan zuciya tace  this past kwanakin nan sune the saddest day of my life Ammi takai hannu ta sharce hawayen daya zubo mata hakan yasa Marwan yasauke kansa kasa Ammi tace  banda tunanin daya wuce is y ata fine? Taci abinci? Tana ina? Yana wajen wa? Yarinya na bata magana, what if wani ko wata take advantage of condition nata kaganta ba uhm ba uhmhum ba wayau ba& .. Ammi tai shiru sabida kuka dayake cinta, Ammi tasauke sauke ijiyan zuciya tace  naga diyata she is fine, healthy, babu abinda yasameta, she looks healthy than yanda takema a gidana, zzzabin yatafi nobody took advantage of her, she s well taken care of and it s all thank to you Dr Marwan, dan haka nagode nagode, Allah yayi Albarka sannan Allah yabiyaka nagode dakin duk akai shiru, ahankali Ammi tace  zan iya tafiya da ita ai ko Dr? Dan shiru yayi saiya dago kansa yakalli Ammi yace  before that akwai maganan danakeso muyi dake saiya mike yazagayo yayi wajen kofa yace  Maryam keda Amirah ku biyoni dasauri Miemie tamike tana mamakkin yanda yakirata cikeda izza kaman yana kiran kanwarsa, ahankali Ammi tadaga Amirah daga jikinta tace  bi Miemie kuje zamuyi magana da Doctor gani nan zuwa awani kalan shagwabe Amirah takara kwakwume Ammi, Marwan na kallonta kai tsaye yace  come with Maryam Amirah ba musu tasaki Ammi ta taso, saitazo sai yayi gaba wani room yabude kayan wasa ne adakin da tv saiya bude yace  ku zauna anan shiga sukayi yamaida kofan yarufe yawuce yakoma office din Ammi tabisa da kallo tace  ina fatan komi lafiya lau Dr ahankali yace  eh, sit here yanunama Ammi kujeran dake gaban table hakan yasa Ammi ta taso tazo wajen gaban tazauna Marwan yazauna yana bude locket saiya ciro zanen da Amirah tayi daya linke yamikama Ammi yace  Ameenah tai zanen nan ahankali Ammi tasa hannu ta karba saita shiga warwarewa batamasan Amirah tai zane ba Ammi ta zana tsafa akasa ga Daddy yana kaimata punches da duka dasauri Ammi tarufe zanen takalli Marwan dake kallonta tace  Dr Amirah tai zanen nan? Bata taba zane a agida ba banmasan ta iya Zane hakaba ahankali Marwan yace  kids like her nada talents da dama da bazama kasani ba sai randa zasuyi zakaita mamaki, and yara irinsu nada wani irin memory da basa mance abu, she might not be verbal

15 / 51