Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bariki (auren Soja) Compelet Complete Hausa Novel by Nil

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   22 / 37

63K to 66K   out of 109.1K words

bayan ta mata fadan rashin zuwa gidan nata ta fada mata, "Aunty nasan bazaki Barni intafi ba shiyasa kawai kuma raina ya 'b'aci yanzu inda gaske ne cikin nashi takeda shi ya zanyi? "Ba gaskiya bane baban Auwal yayi bincike yagano cewar ba gaskiya bane zuby ce ta aiko ta don ta bata zamanku kuma tayi nasara don haka ki shirya next time kiyi maganin Abin karki bari su sami nasara akanki anzo mishi da cikin karya bakisan dame za azomishi wani karon ba kuma,




Ganin kiran shi da ya shigo tace "Aunty yana kirana, "kidauka ni bari inje wurin nawa mijin, picking tayi bayan ya katse ya kuma kira tayi Mai shiru "Ajiyar zuciya ya sauke tareda cewa "baby meyasa zaki nemi bani horo mai tsanani,? Kinsan bazan iya dauka ba shine kike son bani wahala why zaki gujeni a lokacin da nafi bukatar ki? Kinsan jikina yasaba da naki why zaki tafi Kibarni akan Abinda ni nasan sharri ne maniyyina bai taba ratsa mutuncin kowace mace ba sai ke don't you understand your husband is a virgin like you, kece kika bareni nima a Leda baby believe me,




Shiru tayi Mai batareda ta bashi Amsa ba "Fatima please gobe da safe zanzo inganki don Allah kifito inganki kafin inje aiki ni yau bansan yazanyi bacci ba ma batareda keba, inada tafiya jibi zuwa birnin gwari ki bari gobe inganki, please " saikazo tafada tareda kashe kiran, yasamu y'ar natsuwa da yaji sautin ta karasa gidan shi a ranar bai iya runtsawq ba sai juyi kawai yakeyi "zuby ta cuceshi ta hana mai farin cikin shi na dare daya da yafi na dare dubu tsawo a gurin shi,




Itama Yasmin haka ta kwana juyi don tasaba da jin hannun shi akoda yaushe cikin jikinta yana ya mutsata a sati dayan nan tasaba dashi ya mugun yiwa jikinta illa ya mata mugun sabo, tuni tafara mishi tana juyi tunowa da irin dad in da yake jiyar da ita MA namiji ne da ake kirada namijin Zuma ya iya tafiyarda Rayuwar mace a ko ina dare da rana dole mata su makale mishi yanada qualities da yawa da sukadai sun isa su ruda mace basai anje gado ba,



Kusan Karfe biyu ya kirata tayi zurfi cikin tunanin shi taji karar wayar shi dauka tayi ba bata lokaci ta saka a kunnen ta cikin yin kasa da murya tace "lfy bakayi bacci ba? "Tanbaya ta kikeyi baby? Ke me yahanaki bacci? Kin jamun damuwa baby bazan boye miki ba meyasa zaki bani irin wannan wahalar? I can't sleep today meyasa zaki nisanceni bayan kinsan jikina yasaba da naki hannu na suna kwadayin taba nonuwanki baby miyauna na missing naki why zaki wahalar dani "mika tayi a hankali domin saida tsigar jikinta ya tashi magan ganunshi suntaba ta ya iya rudata da kalaman shi,


Mika yayi Shima "baby kinsa kaya yau? "Um tace kawai don yagama kasheta da dirty talk dinshi "wane iri kikasa? "Zani kawai na daura zafi nakeji, ta tafada cikeda fisgo magana "kidaina daura Zani akan kirji karki zubarmin dasu, "Ahhh baby jibi zanyi tafiya gashi hajiya ta hana ni dawo dake wai sai Anyi biki kuma jibi zamuje birnin gwari yanzu sai nadawo za ayi bikin mu kitare kenan? "Gsky zan wahala da yawa kuma hajiya ta yi fushi da sai na daukeki mungudu Allah,


"Ina zaka kaini? Can zamuje tare " tab wurin barayin? "Ba muna tareba noting will happen mijin ki nq nan , har saida Asuba tayi sukayi sallama domin yin salla tareda fada mata zai zo ta fadawa mama zaisha kokon ta da kosai, tace tom, taji dad in yanda hajiya ta saka baki a lamarin da yanzu ya sungumeta ya gudu again,



Karfe goma tayiwa baban zango a gidan domin tattauna biki "to yanzu me za a siya Saude? Ya tanbayi mama "Aa ai maganar kuce ko ka nemi hindatu itace uwar ya, to nidai. ga kudin nan asan nayi yarinya dai dole mufitar da ita kunya, baba ya zubawa tulin kudin da ya juyesu cikin gari yayi zafi ya zaro idanu "ina kasamu kudi mamuda? "Ai jiya muna gama magana dakai na kira dillalai mukayi cinikin filayen nan da na wurin gwaggon mu da kuma na wurinka muka kammala komai tunda safe kudi suka shigo hannu na don haka musan nayi ayi a wuce wurin,



"Amma dai mamuda kagama dani ni nafada maka inason sayarda filina filin da zaiyi miliyan uku kasayar kuma namu na wurin gwaggon mu da yayi miliyan da rabi nawa kasayarda su duka? Yanzu kai yazaka dauki gadon mu nidakai kasa a kasuwa su sauran yarafa ga ismail gasu hajara duk suna cikin gadon mu sai a kashe su akan mutum guda,


"Yaya nidai na siyar kuma filinka tsakani da Allah nawa ka sayeshi? Lokacin can"dubu Dari biyar da hamsin' " to ka godewa Allah ansiya miliyan daya kaci ribar hudu da biyar sai na wurin gwaggon mu Dari tara kaga nawa kenan, kace fa bakada kudi me kakeson muyi munada kadara basai tamana rana ba, don haka gado da kujeru Y'an yayi nake so a sakawa y'ata, mama daki ta shiga tana dariyar wa innan Y'an Uwa biyu da kullum dramar su bata karewa tana mutunta mamuda kodan zumuncin shi da fadar gaskiya yi yake da zuciya daya ba algus a zuciyar bawan Allah, su biyu kadai Amma sunada fahimtar junan su,



Yasmin ma tanajin su tayi dariya tareda kara kaunar kanin mahaifin nata nan ya kara jin kunyar rashin Auren jinin shi da basuyi ba ga matar shi ma dai dai da halinshi itakam sai godiya, ita ta fito sanye cikin doguwar Riga baka mai stone tana sheki ta yafa karamin gyalenta ta tsuguna tareda gaishe da baban zango yace 'Allah ya miki Albarka mamana ina soja? Dukar da kanta kawai tayi takasa Amsawa saboda kunya, ta hado mai kari don tasan idan yazo gidan to sai ya ci Karin mama yake tafiya,




Karfe goma sha daya MA ya iso tareda Ahmed suka shigo wannan karon suka zauna a kaci gaba da hirar Rayuwa kafin suyi maganar da ta kawo baban " to yanzu mudai mun shirya zuwa sati mai zuwa sai ayi bikin tarewar ko me kuka ce? "Eh gaskiya naso da yau ta koma ne don zanyi tafiya gobe, yafada musu kuma bazasu dawoba sai karshen wata,, baba yace to in haka ne sai a bari idan kadawo sai Ayi bikin ta tare zsifi cikin natsuwa, ba haka yasoba gsky Amma yazaiyi hajiya ko yau saida ta gargadeshi da zancen tsaurin idon nan na rashin kunya, dole ya hakura tareda fada musu za akawo lefe jibi,



Wayar shi ya ciro tareda tura mata text "baby kina ina? Ta bashi Amsa da "dakina kawai, ya mike yana sosa keya ya nufi kofar dakin "Ahmad kamar ya nutse kasa gaskiya Oga karshen rashin kunya ne, shikuwa gaskiya ya matsu ya ganta he can't take it anymore, ta mugun firgita jin sallamar shi a kofar dakin ta zabura cikeda tsoro "na shiga uku wani irin kallo yake kare mata tundaga kasa har sama cikeda kewar ganin ta na kwana daya ya nufeta cikin sauri kafin tace wani Abu ya rungume ta tareda hade bakinsu wuri daya ya kuma tura hannun shi ta saman kirjinta,



"Ahh yaja mugun numfashi tareda wani irin gurnanin fitina "babyyyy yaja sunan bayan ya cire bakinshi da a nata "ya zanyi am in need very badly touch me and feel my body is getting hotter, am going tomorrow gashi wai tarewarki sai nadawo bazan iyaba baby Allah I can't, tausayinshi taji duk da irin shigoma matan da yayi ta raba jikinsu tareda ciro hannun shi a jikinta tace "me yasa ka shigo? "You are my wife now I have the right, shiru tayi tareda cewa "bari inkawo ma breakfast din ko Kayi? "No bring it, to kafito waje mana, "no ki kalli jikina inna fita su baba zasu gani yafada tareda nuna mata wandonshi tayi saurin fita tana jinjina Rayuwar MA,



Baba shiru kawai yayi daga baya ma mikewa yayi yace "muje ko mamuda muga baba liman don dole mu nemi shawarr shi, don bayason ganin wata rashin kunyar sukabar Ahmed dake rikeda yaron shi yana mishi wasa don ya gujesu yazama Dan gidan mama, daga karshe ma fitar su sukayi ya sakashi a mota yace muje insiya maka sweet,


Zubewa MA yayi akan katifar ta tareda sauke gurnani yana danne marar shi cikeda tsananin feelings ina he can't bazai yarda ba gaskiya,

Koda ta fito duk sun fice mama dama baccin ta takoma yi batama san shigowar su ba, saida ta kawomai komai yana kife yana jin marar shi ta mugun daurewa saida ta Ajiye tayi Mai magana "gashi nakawo, juyowa yayi idanun shi gaba daya sun kankance ya kalleta cikeda fitina "ina Ahmad? Baya nan yafita, ta bashi Amsa "su baba fa? Suma bangansu ba, "mama bata gidan ne? "Bacci takeyi tundazu, good ya fada tareda mikewa yana hada hanya ta zuba mai ido tareda binshi da kallon me zaiyi, ganin ya garkame mata kofa yasa ta zaro idanun ta "Meye haka kakeyi Meye na kulle min kofa? Idan wani yayi tunanin wani Abu mike... Maganar ta kafewa tayi ganin yayi wurgi da kayan jikinshi tareda barin guntun wando kawai yana nufota yakeyin komai cikin zafi zafi,



"Ki daina min taibayoyi kawai kimatso kiji dani Aike kikaja koma Meye don haka wallahi kisan nayi,...... 🖊





Na boni wannan shawar Ummu jidda ce don na lura itama uwar dakin MA ce don haka nayi nan,



*Matar Soja*

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*BARIKI*
_Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻



Written by FENERH




*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby



*Addu a agareku tareda dumbin godiya zuwa ga fan's din BARIKI Auren Soja ina matukar jinjinawq kokarin ku na bani goyon baya ta hanyar zafafan Addu oin ku ina matukar godiya Allah ya karo kauna mai yawa masoya*



45&46


Ja da baya tayi tareda fitoda kyawawan idanun ta "please mana MUHM'D Meye haka don girman Allah a gidan mu kake shirin jamun wani Abin kunyar bayan Wanda Kayi a baya? Fisgota yayi cikin karfi "come on my friend karki bata min lokaci harsu baba su dawo, wurgata kawai yayi kan katifar batareda ya bata damar kuma furta komai ba ya hade bakin su tuni na gudu nabar dakin ganin da gaske yi zaiyi a cikin gidan surukai,





Saida ya murjeta na minti talatin kafin ya barta ya koma gefe yana maida numfashi tareda riko hannun ta cike da gamsuwa ya bata kiss itadai kallon shi tayi tareda cewa "tunda Kayi son ranka ka tashi kamayar da kayan ka kafita don Allah kafin mama ko su baba sudawo, "munyi son ranmu dai baby kema fa kinaso banason gulma kitashi muje muyi wanka kafin intafi, zabura tayi tana mai wani irin kallo "in wasa kakeyi kadaina please katashi don Allah, "kinsan dai banason zama da najasa ko kaje gida Kayi wanka nidai katashi ta mike tareda janyo zanin gadon ta domin rufe jikinta ya fisge tareda zubawa kirjinta ido "kinsan banason kina min boyon kayana ko Meye na rufe min jikin ki bayan har ciki na shiga nayi iyo,



Itadai kokarin take taga yatashi kafin yakaita ga kunya kayan shi ta mikamai ya tashi zaune tareda zuba ma jikinshi da ya baci da sparm ido, ya yatsine fuska, "kizo ki goge min wannan Abin baby, yafada yana mata wani irin salon kallo, batada da zabi don haka towel dinta ta janyo tareda gogemai yana runtse idanun shi "Allah ban koshiba baby zan dawo da dare in kara kafin in tafi gobe, Kinga zanyi kewarki fa sosai zanyi sati kafin inshigo ko sati biyu, idan nadawo zaki tare gidana so you have to be ready baby kinsan waye mijinki me yasa zaki daga hankalin ki akan wata y'ar iska no matter what kece matata kece na Aura su bakya ganin bakin ciki suke miki, and so what idan Kinga wata da ciki tace nawa ne baki yarda da mijinkiba baby that's why,

"any way nasan dama kallon d'an iska mai kwaso mata kike min ko yes inada Y'an mata Kala Kala Wasu ni keneman su Wasu suke nema na and don't blame me for that kaddara tace hakan but believe in me duk Abinda nayi baya I want repeat it again insha Allah, Amma inaso kizama strong woman be like a soldier wife ki zama jaruma yanda nasanki now you are weak because of my love, yafada yana janyota dakyau zuwa jikinshi,
Zaki fara koyan mota fa na sa ayi miki booking a driving school don haka zan Ajiye miki driver da zai rika kaiki banason matana a motar haya, "wait a minutes a me kika dawo gida jiya? Yafada tareda zuba mata ido cike da tuhuma, "mashin ta fada kai tsaye, ya bata rai tareda mata mugun kallon da bai taba yimata shiba, "matana a bayan wani kato how dare you yanzu haka kika hau bayan wani kazaki kirjinki na gogar. bayan shi kina matsayin matata, impact let me make it clear to you daga yau idan zaki fita idan baki iya mota ba ki jira duk inda driver yake yazo in ba hakaba Allah bazan yafe miki ba, ya fada cike da kishi tareda rufewar idanu ya zura kayanshi ya fita,


Bayan shi tabi da kallo tareda yin dariya ya mugun bata dariya waishi kishi, saurin zura katon hijabi tayi tareda fita ta hada ruwan wanka cikin sauri ta tsalkake jikinta ta fito tana mai fitarda wani irin Annuri a fuskar ta "I love that shameless man, ta yi sa a har ya fita mama bata tashiba cikin sauri ta fara kokarin shirya musu lunch,



Shi kuwa yana fita ya haduda Ahmad ya dawo yace yaje ya kaishi gida yayi wanka kafin su koma office, kallon mamaki Ahmad yabishi dashi kallo ba halin tanbaya lallai in har Abinda yake tunani yafaru to Oga karshe ne a duniyanci, tare ya tafi da d'an shi Shima domin gwara Shima ya dana rashin kunyar don yana bukatar d'an shi a kusa dashi, saidai mama ta shafa taji shiru,




Maryam tayi mamakin ganin shi da Auwal din tace dakko shi Kayi? "Gashi kingani zahiri gaskiya baka kyauta ba sun gama shakuwa dashi zaka rabosu da shi, "ah ai gwara ni da Oga, "me yayi ogan? Kema kinsan halin shi yanzufa wanka yace min zaiyi bayan bai dade dayiba muka fita, yagama bata labarin komai tayi dariya "shine dai dai da yasmin din, yaron ta mikawa hannu tuni yasa mata kuka shi a mayarda shi mama,
"To nima inada yarinya ta ka mayar musu da d'an su baya bukatar mu,



*************
Mama na tashi ta fara tanbayar Auwal "Yasmin ina yarona? ", ai sunfita da babanshi kila ya dauke kayanshi, "hmm Allah ya kyauta zamani muna fama da surukai, dariya yasmin tayi ta reda cewa a zuciyar ta rashin kunya ya wuce namu ai Ahmad yasan kunya,
Bacci ta kwanta bayan ta kammala komai sai karfe biyu ta tashi a makare ta yi wanka tayi sallah tafito jin hayaniyar mutane a gidan nasu,



Su mama hindatu ne da Wasu Y'an uwansu na zango sukazo domin karbar kayan Auren nata da batasan da zancen ba tana isowa ta dukar da kanta cikeda jin kunya ta gaidasu mama hindatu tafara yimata tsiya ", kaga Amaryar zamani lefe bayan ta kai kanta to bari mujira muga Amaryar da za ayi biki da ciki, "kai hinde wani irin ciki kuma? Daya daga cikin su ta fada, "to zakuce na fada muku muje zuwa irin wannan kyalli da takeyi ai daga gani na kusa samun wani jika, "saikace wasan yara yaushe akayi Abin bare har ciki ya samu, ? "Nabar zancen yaya Saude, shiru kawai tayi musu tana jin suna zancen su itada ta kusa ganin ma Al adarrta suke zancen ciki yaushe nema suka fara saduwar da Har za a hango mata ciki,


MA bai samu kanshi ba a yau saboda shirin tafiyar su tunda ya koma office suke kaida kawowa naganin sojojin shi sun shirya sosai domin tunkarar mugayen barayin, Y'an Uwan shi ma koda suka kirashi zasu kai kayan motoci kawai ya bada yace aje a kaisu gidan,
Kamar shine ke shigowa Unguwar motocine guda goma a jere guda biyu sababbi wa inda aka zubo kayan Aciki sauran kuwa Y'an Uwan shi ne tareda escorts din shi dake take mai baya,




Kasan cewar falon baba yafi girma nan suka bude musu aka gyara Aunty maryam ma tazo suma sun hadu harda Zainab din ismail tazo domin tarbar kayan yasmin Y'an Uwa sun shirya musu tarba irin ta Al Ada, mama hindatu uwar gayya tuni ta mike tareda musu tarbar girma su Aunty Halima dukan su sukazo kawo lefen na kanin nasu guda daya tal, sunyi matukar yabawa da tarbar girman da suka gani daga gidan na su yasmin,


Umarni Babba

22 / 37