Author : Nimcey Sarauta Category : Romance
ki gode Allah ki godewa Jalalu gashi ki rabauta da Muslunci,amma dai ki daina shige masa ni shawara nake baki ba cutarki zanyi ba ai kin sani ko? To Wlh Muhammad aure ya keso idan kuma kin jawa kanki ya turmushe ki shi kenan shima Arwan ɗin saiya fasa shikenan,amma dai ki daina shigewa jikinsa kuma...," Bata ƙarasa maganar ba taji yace "jikinki ta hau hala?" Haɗe rai tayi taci gaba da ninke kayanta wanda ta zazzago dasu daga cikin akwati wai tana neman goro, bata kulasa ba shima ya kalli Jalilerh wacce ta sauya kayan jikinta zuwa wasu riga da wando masu ƙyau ta ɗura after dress a kai, ya ce "ke dai tsohuwar nan kin fiya neman magana,sai kin gangara kin huce ma wuta" marai-raice fuska tayi ta ce "ai dai nai shiru ban kulaka ba ko?to dan Allah ka rufan asiri ka daina jamin masifa a wannan lokacin" bai ƙara magana ba harya fice daga ɗakin ba tare daya kula Jalilerh ba,room ɗin Abbou ya nufa yana zuwa ya gansa zaune saman bed yay shiru shi ɗaya sai irfy yana danna waya, ƙarasawa wajansa yay ya zauna tare da kallonsa yace "what happened Abbou?" Cikin Muryar rauni Abbou ya ce "Muhammad ina jin kamar nasan garin nan,sai nake ganin kamar nazo gida" Jalal da mmki ya gama kashe sa kawai ya zubawa Abbou ido sbd tunda suke dashi bai taɓa cewa yasan wani aduniya ko wani waje makamancin Birnin nufar ba,shiru Jalal yay domin bai son ya takura masa,ana haka wayarsa ya fara ƙara ɗauka yay yana picking yace "gani a reception" da "ok" kawai Jalal ya amsa masa kana ya miƙe yace "Abbou let's go" gaba ɗaya suka miƙe Jalal ne ya fara fita securities na biye dashi har zuwa reception ɗin,da Murmushi suka tari juna babu nuna baƙunta suka bawa juna side hug a haka suka nufi harabar hotel ɗin,kai tsaye motar Jabir ya shiga kuma yaywa securities alama da kada su biyosa lokacin dasu Abbou suka fito harsu Jalal sun nufi gate hakan yasa cikin sauri suka ƙarasa shiga mota Mama sai mita take,a haka har suka bi bayansu Jalal,a hankali Jabir ke driving jifa² yana sakin Murmushi yau dai yana ganin yankewar wahalarsa yazo ƙarshe musamman da yaga Zulfa ta samu ci gaba a daren jiya,daga jiya zuwa yau bata da abin faɗa sai Hubby Anty shine kawai abinda yake fita daga bakinta,matsalarsa ɗaya jinin da take zubarwa, lumshe ido Jalal yay yana ɗan sakin numfashi tym to tym yakan saci kallon Jabir haka nan yaji yana ƙaunar ganinsa gashi ya rasa dawa yake masa kama but he look familiar,da ƙyar dai ya samu bakinsa ya buɗe yace "lafiya dai nake ta ganin mutane a hanyar?" ɗan ɓata fuska Jabir yay kama bazai magana ba sai kuma yace "ranar haɗa samari da ƴan mata aure ce" Jalal ya waro idanunsa cikin ransa yace "ranar hauka dai" da sauri kuma ya zabura haka nan yaji gabansa ya faɗi sbd tunawa da Jalilerh da yay, Jabir ne ya kallesa dai² lokacin da yake karya ƙwana zuwa cikin babban estate ɗin yace "hala lafiya?" Jalal wanda fargaba ya gama cikasa ya ce "nothing" shiru sukai har suka shiga ciki cikin estate ɗin nan Jalal ya ƙara firgita ganin yadda maza kejan mata ta ƙarfi wasu kuma na tafiya da kansa an kafa bukka² wajan 30 a babban harabar estate ɗin,a haka har Jabir yay parking ya fito da sauri shima Jalal ya fito, Mama da Irfan da Jalilerh suma suka firfito Abbou kasa fitowa yay sbd yadda gabansa ke faɗuwa ga memory ɗinsa dake san dawowa hakan yasa gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa.
_Littafi na kuɗi ne kada ki karanta baki biya ba please 300 babu yawa 08119237616 chat me up_
Jalilerh dake rakaɓe a bayan Mama zai zaro ido take Musamman da idanunta ya sauka akan Joshua wanda yake tsaye sai raba idanu yake tamkar mai neman wani abu,kamar daga sama sukaji Muryar Papa na faɗin "Barka da dawowa jikanyata,hhhhhhh abin da kike gudu still shi Kika zo kika tarar wonderful" ba ita da aka kira sunanta ba,hatta Jalal sai da hanjin cikinsa ya kaɗa,da sauri kuma ya juya ya nufi inda Jalilerh take tsaye, Jabir kowa mutuwar tsaye yay sbd arba da yay da Jalilerh kasa kuma ɗauke idanunsa yay a kanta, jikinsa banda rawa babu abinda yake,daman tare da suke da ita? Mene yasa basu gaya mai suna tare da wata budurwa ba?shin Jalilerh daya sani ce ko kowa wata ce da ban? Kenan duk tsayin shekarun nan tana tare da wannan bawan Allah? Wannan tambayoyin ya kewa kansa amma ya gagara samun amsa, Jalal na zuwa yau saurin kama hannun Jalilerh ya nufi motar da Abbou ke ciki kafin ya ƙarasa wajan motar yaji an riƙe hannunsa,da sauri ya juya idanu biyu sukai da Joshua,kallan kallo aka shiga aikawa juna,ganin bashi da wani lokaci yasa ya saki hannun Jalal ya nufi inda Jalilerh take tsaye,da sauri tayi bayan bobo ta ƙanƙamesa jikinta duka rawa yake ta shiga faɗin "Uncle shine wanda nake faɗa maka, please Uncle help me dan Allah kada ka bari ya ɗauke ni zuwa zai ya ƙwanta dani"wata shegiyar dry Joshua yay idanunsa ya kaɗa yay jajirrr kamar gauta,bai tsaya jiran wani abu ba ya ƙara nufar inda Jalilerh take,cikin zafin nama Jalal ya dawo da ita gabansa ya sanyata jikinsa ya rungome, idanunsa a kan Joshua cikin harshen turanci yace "never, ƙarya kake kace zaka mallaki jikinta ta huce wannan level,har abada babu kai babu ita,bare har kayi banza tunani a kan mu'amala da ita, jikinta a tsarkake yake ba irin naka da datti yay masa yawa ba" ya faɗi maganar yana sauke numfashi sbd ya daɗe bai magana mai tsayin wannan ba,da idanu Joshua yaywa wasu matasa magana da sauri suka zo wajan suna zuwa suka kwaɗawa Jalal abu a kansa nan take jini ya ɓalle masa,duk da tsananin zafi da azabar daya keji hakan bai sanya ya saki Jalilerh ba saima ƙara matseta da yay a jikinsa,cikin tashin hankali Irfan ya shiga neman number securities ɗin Jalal amma bai samu ba,yama rasa mai zaiyi kawai sai ya fashe da kuka ganin yadda jini ya rufewa Jalal fuska, Jabir kam da gudu yay wajan Papa ya zube gabansa yana rusar kuka dare dayi masa magiya,dukkan abinda ke faruwa uwa sundu na gani,sai ɓaɓɓaka dry take tare da farin ciki sbd gani take yau itama burinta na ɗauka fansa ya cika,ganin Jalal yaƙi sakin Jalilerh yasa wani ya ƙara ɗaukan wata sanda ya ƙara saukewa Jalal a kansa, ƴar ƙara ya saki sbd ba ƙaramin shigarsa dukan yay ba,da gudu Irfan ya nufi wajansa kafin ya ƙarasa wani ya riƙesa da ƙarfin gaske,kuka Jalilerh ta fashe dashi cikin kuka ta fara ƙoƙarin zame tana faɗin "No Uncle ka sakeni,dasu kasheka gwamma na bisa yay duk abinda ya keso zan jure hakan,amma bazan jure ganinka haka ba,bazan iya rayuwa babu kai ba dan Allah Uncle ka sake ni" kai kawai yake girgiza masa yayinda idanunsa suka fara rufewa sbd jirin daya fara kwasar sa,a hankali kuma jikinsa ya fara saki ganinsa ya fara ɗaukewa,duk Wannan abun Abbou na cikin mota bai san abin da ake sbd shima ta kansa yake infact ma bai san wacce duniya yake ba, Mama kan tun kan faruwar haka taga giftawar wata kamar Zulfa da sauri tai wajan hakan yasa bata san abinda yake faruwa ba, Jabir kam yana can durƙoshe gaban Papa,ganin yaƙi sakinta yasa Joshua da kansa yasa wata sandar ya daki ƙafar Jalal,da wani irin sauri Jalal ya saki Jalilerh idanunsa na zubar da hawaye sai kuma yay baya ya faɗi ƙasa babu numfashi, Joshua cak ya ɗauke Jalilerh wacce ta kusa zau cewa sbd halin da taga Uncle ɗinta a ciki,kai tsaye wata bukka ya nufa da ita, Abbou wanda abinda ya faruwa na ƙarshe a kan idanunsa yay saurin ƙarasawa wajan Jalal wanda yake ƙwance,da wani irin ihu Abbou yace "wake up Muhammad wannan ba lokacin suma bane, Lokaci ne da zaka amshi matarka daga hannun wannan azzaluman,tashi maza kace ka amshi budurcin MATARKA..
*NIMCYLUV*
7/25/21, 5:44 PM - Buhainat: UCL NE
_104-105_
Kamar a cikin mafarki Jalal yaji saukar Muryar Abbou'nsa,wace matar tasa?ko dai bai ji dai-dai ba ne? ƙara runtsa idanunsa yay yana jin wata azaba da raɗaɗi a tsakiyar kansa ga wani jani dake fita harda guda,jan ƙafarsa yay wacce yake tunanin idan har ba karyewa bace to tabbas targaɗe yayi,duk yadda Jalal yay ƙoƙarin tashi kasawa yay cikin tashi hankali Abbou ya ƙara girgiza Jalal yana faɗin "Are u mad Muhammada? Kana ƙwance wani banza zai disvirgin na matarka,what the fuck ahaaa? Abeg my friend get up tashi kaje ga matarka lokacin ka ne,kada ka bari wani banza yaje gonar da ba tasa ba,i knew you love ur wife so get up and go to her" wani ƙarfi da guzari ne ya saukarwa bobo duk da cewa ƙasan zuciyarsa tarin mmki ne da kuma tambayoyi amma a yanzu basu yake buƙatar ji ba,burinsa bai huce ya ganta kusa dashi ba yasan cewa ko da wasa Joshua ya riƙe ko ya taɓa wani sashe na jikinta bazai taɓa barinsa ba, miƙewa tsaye yay yana dafe kansa da sauri Irfan ya ƙara so wajan ya sa hannu ta ƙarfi ya yaƙi Ƙasan rigar sa ya ɗaurewar bobo kansa da ita,kai tsaye ƴar bukkar da aka shiga da ita ya nufa ganin haka yasa zaratan samarin wajan suka nufesa da gudu kafin su ƙarasa ya rigasu,da sauri wani ya cimma sa yana zuwa ya rigesa,sam koda wasa Jalal bai san yaya ake faɗa ba bare ya kwatanta yin faɗa dasu,kamar daga sama sai ganin securities ɗinsa sukai suna ta parking da motocin su,wani Murmushin jin daɗi Abbou yay dan haka yaja baya sai a lokacin ya fara ƙare wa cikin birnin nasu idanu,komai na garin ya sauya sanin da yay masa ada da kuma yanzu akwai banbanci mai yawan gaske a tsakani,jin hayaniya tai yawa a bakin bukkar yasa Joshua sakin Jalilerh wacce tunda ya shigo suke faɗa ko rigar jikinta ya gagara cirewa, ƙofar ya buɗe tare da leƙo kansa,yana leƙowa wani security yasa ƙasan gun ya dakar masa kanshi da ita,wani gigitaccen ihu Joshua ya saka tare dayin baya zai koma cikin bukkar cikin zafin nama bobo yasa hannu ya fisgoshi waje nan faɗa ya kacame tsakanin matasan garin da kuma Joshua ganin abin na shirin zama hauka yasa suka fara sakin ruwan harsashi ba kajin komai sai ƙarar guns, da sauri Jalilerh wacce take tsaye sai rusar kuka take jikinta sai vibration yake idanunta sunyi jajirr sbd kukan da take banda kiran sunan Uncle ba abinda take,jin an taɓa ƙofar kaɗan yasa tayi saurin ɗago kanta ta kalli wajan,tsaye ta kansa ya lumshe idanunsa yana da sauke ajjiyar zuciya ya harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa,bata tsaya jiran komai ba tai wajansa da gudu tana zuwa ta faɗa jikinsa tare da ƙanƙamesa ta saki wani sabon kuka kamar ranta zai fita sai fisgar numfashi take, cikin kukan ta fara magana tana faɗin "Uncle dan Allah kada kabarsa yaci mutunci na, you're my friend,my Daddy,my Mummy,my Besty you're my uncle you're my hero you're my everything dan Allah do something kada kabar Joshua ya rabani da kimata wlh zan iya mutuwa,da wani ya samu damar cin mutuncina gwamma na mutu" ta faɗi hakan ta ƙara rirriƙesa tana begging nasa akan kada yabar Joshua yay mata wani abu,duk abinda take yana jinta ko buɗe idanunsa ya gagara yi,yadda yaji zuciyarsa na bugawa da ƙarfi yasa tai saurin sanya hannunta a satin zuciyarsa ihu ta saki kar muryarta sbd sabar firgici da kuma tsoron tashin hankalinta bai huce ace wani abu ya samu Uncle ɗinta ba,da sauri ya buɗe gajiyayyun idanunsa wanda suka sauya launi,ganin yadda ta gigice yasa ya sauri saka hannu ya riƙe mata hannun tare da ɗan dukan kumatunta idanunta ta buɗe idanu suka haɗa tai saurin sakin ajjiyar zuciya still kuma wani kukan na ƙara cikin ƙarfinta, hannunta yaja suka fito wajan ƙofar da sauri wani security yazo ya tsaya,da hannu Jalal yay masa maganar a bashi mota,babu daɗewa akai parking motar a gabansa driver ya shiga Jalal yay masa nuni ɗaya fito waje,zagayawa yay ya buɗe murfin motar ya sanyata ciki shi kuma ya nufi ɗaya side ya zauna mazaunin driver key yaywa motar tare dayin reverse ya jata da wani irin speed yabar wajan,a hanya ya hangi Jabir da wata farar matashiyar mata ƙyakkyawar gaske,binta yay da kallo har suka ƙarasu wajan,tsayawa Jalal yay sbd hannun da matar take ɗaga masa,zuge glass ɗin yay a hankali ya zuba mata gigitattun idanunsa, Jabir ne ya leƙo wajan yace "ayyya jeka kawai kada ka biye mata" kasa ɗauke idanunsa yay daga kanta itama kallonsa take kafin a hankali ta miƙa hannunta kamar mai tsoran wani abu ta ɗura hannunta saman sumar kansa ajjiyar zuciya mai ƙarfin gaske ya sauke,mmki sosai a kan fuskar Jabir tunda yake banda shi da Katarina babu wanda take iya tsayawa wajansa amma gashi ta tsaida mutum harda taɓasa, Jalilerh tayi saurin cewa "Ammina" kallon Jalilerh tai sai kuma ta kalli Jalal ta sakar masa Murmushi tare da ɗaga hannunta tai alamar👌🏼 perfect Jabir na kallon Jalal yace "ya kamata kaje kafin Papa ya fito daga wajan uwa sundu" har zuwa lokacin Jalal ya kasa ɗauke idanunsa daga kan Zulfa wacce itama tai masa ƙuri da idanunta tana kallonsa, kasa daurewa yay sai da ya buɗe motar ya fito,kamar jira take yana fitowa ta faɗa jikinsa yana jin lokacin data sauke ajjiyar zuciya kanta ta ɗaga tare da jawo kansa ƙasa ta sakar masa peak a fuska, Jabir ne ya ƙarasu wajanta tare da kamota ya ce "ki barsa haka bana,ko kin sanshi ne" Murmushi tayi da maƙale kafaɗa tace "Ya Allah" sosai yay mmkin kafin su ƙara magana Papa ya nufu inda suke da sauri Jabir yace "ya subuhana kaga abinda nake magana ko?maza jeka kada ka tsaya" da sauri Jalal ya shiga motar ya jata da gudu yabar wajan, Zulfa tana ganin tafiyarsa ta faɗa jikin Jabir ta saki kuka kanata ya shafa yace "sorry" babu zato babu tsammani yaji tace "kaga ya tafi?"
Da sauri ya ɗaga ta daga jikinsa yana kallonta yayinda ita kuma take kallon direction ɗin da motar ta bi,cikin farin ciki ya ce "what are you saying,ohyyyaa say it again yi magana" kasa magana tayi sai kwaɓe fuska ta dake kamar zata saki kuka kamata yay suka nufi cikin wajan,tun daga nesa Jabir yake bin Abbou da kallo Abbou kuma yana tsaye jikin mota yana kallon Mama wacce take masa bayanin taga mai kama da Zulfa amma ta nemeta ta rasa, da fashin da akai yasa yay sauri juyawa da sauri ya ware idanunsa ganin ƙanin nasa tsaye a gabansa,cikin rawar muryars Abbou yace "Lily.." kasa magana Jabir yay sai jikin yayan nasa daya faɗa a tare kuma suka saki kukan farin ciki, cikin kuka Abbou yace "Lily..ashe aƙwai ranar da zata zo na ganka? Ashe zan ƙara ganin wani nawa a duniya?tunda muka zo nan nake ganin kamar nasan Birnin cikin ikon Allah kuma na tuna komai nawa har na fahimci asalina nazo,naƙi ƙarasawa ne sbd tsoro da kuma fargaba"Jabir ma yace "am happy to see you Loly na, kullum cikin kewarka nake ina kuma roƙan Allah ya nuna min kai sai gashi dalilin cutar Zulfa Allah ya kawoka kuma dalilin ƴarka" zare jikinsa Abbou yay Lokaci guda kuma yaji kansa ya sara da sauri kuma yace "wacece Zulfa? Wace kuma ƴarta?" Murmushi Jabir yay yace "Loly Jalilerh is my daughter" da sauri kuma Abbou ya ce "Da gaske kake Lily..?"jinjina kai Jabir yay yace "I'll tell you everything Loly,bari nakai wannan ƴar rigimar ciki"Irfan dai na tsaye tun zuwan Jabir idanunsa ya sauka akan Zulfa kasa ɗauke idanunsa yay sbd sallar kamarta da bobo daya gani,komai nasu ɗaya ne, bambanci tsakanin shine ita mace shi namiji,tun kafin su ƙara su wajan da Mama tai cikin motar tana faɗin "wannan wanne kalar lukutar masifa ce? Gari duk tarin arna huuuuuu² yau naga abinda yafi ƙarfina" tana mita ta shige motar, Abbou ya ce "wace haka kake magana?" Jabir yay Murmushi tare da juyawa bayansa yaga ta juyawa bayanta idanunta na kan hanyar da Jalal yabi duk tunaninta ko zai dawo,a hankali Abbou ya ɗura idanunsa a bayanta ya fara kallonta from head to toe gabansa yaji ya buga da ƙarfin gaske da sauri kuma ya nufi inda take yana zuwa ya kalleta da sauri juyawa jin motsin mutum idanu huɗu sukai da Abbou tana ganinsa tai saurin jaa baya sbd tsoran da taji,da wani mugun sauri Abbou ya fisgota ta faɗa jikinsa ƙanƙameta yay sosai a jikinsa ko tunanin Irfan da Mama da suke wajan bai yi ba, duk halinda Zulfa take ciki bai hana ta saki ajjiyar zuciya mai ƙarfi ba,wani sanyi taji yana ratsata bata san lokacin data rungome Abbou ba,cikin tsantsar farin ciki Abbou yace "Hubby da gaske kece,ma sha Allah, Allhamdulillah birahamatikaaaa tsarki ya tabbata ga Allah subhanahu wata'ala"sai kuma hawaye shaaaa ya fara bin fuskarsa,lufff Zulfa tayi jikin mijin nata duk da bata gama gane wane ba,amma yaji zuciyarta ta samu nutsuwa dashi,sakinta yay yana kallon Jabir yace "Lily..ina kasameta?da mmki Jabir yace "shekaru masu yawa ina tare da ita,kusan a ranar data haihu ne ma,amma who is she?"ajjiyar zuciya Abbou ya sauke ya ce "she is my wife" jinjina kai Jabir yay yace "ikon Allah,muje ciki to" gaba ɗaya sukabi bayan Jabir ganin hakan yasa Zulfa tayi sauri ta zame hannunta daga na Abbou tai wajan Jabir ta sakar masa dry,da idanu kawai Abbou ya bita ganin babu abin da ya sauya daga gare ta tai wani mugun ƙyau babu wanda zai ce ita haifi Jalal ta zama kamar wata budurwa duk da tarin shekarunta,amma yanayin hutu kuma daɗin da ɗawa ba haihu take ba bare ta tsofa,har side ɗin Papa Jabir ya shigar dasu da sauri Abbou ya sunkuyar da kansa sbd kallon da yaga Papa na aika masa dashi, gaba ɗaya suka zube gabansa banda Mama da tai