Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

UNCLE NE Book 1,2,3 Complete Hausa Novel by Nimcey Sarauta

Author :  Nimcey Sarauta Category :  Romance

Chapter   33 / 41

96K to 99K   out of 120.1K words

Mameey tace "yaje airport jirginsu Anuty ya sauka,yanzu haka ma suna hanya"miƙewa baby tayi tace "wow can wait to see matar yaya Irfan Anuty Ikram" Mameey tace "ai kam suna hanya, Jalal ya fito kowa? We getting late" girgiza kai tayi tace "bana jin ya fito,coz yanzu naga Jalilerh ta fito daga part ɗin sa"waro idanu Mameey tayi tace "sai yanzu ta fito?"sai kuma ta saki Murmushi tace "ok jeki ce masa duk an tafi wajan dinner shi ake jira"kamar jira take tace "ok Mameey" tana faɗin hakan ta nufi part ɗinsa, Jalilerh tana sane taƙi fitowa daga kitchen ɗin gani take kowa zai iya gane abinda Uncle ɗinta yay mata yau,tana zaune saman kujera taja idanunta ta lumshe,sai a lokacin taji tsigar jikinta na tashi musamman idan ta tuna lokacin daya sanya bakinsa cikin nata,takurewa tai a saman kujerar ta shiga sauke ajjiyar zuciya,a ƙwance Nihila ta samesa yay rufda ciki yana fitar da numfashi a hankali, wato bacci yake nan?ta tambaya a ranta,shine ya sanya tana ta Knocking bai magana ba, ƙarasa shiga cikin bedroom ɗin tayi tare da bubbuga gefen kanta,shiru yay mata duk da cewa yana jinta amma yay pretending kamar bacci yake, leƙa fuskarsa tayi aikam kamar ance ya buɗe idanunsa nan suka haɗa ido, kallonta kawai yay na ɗan wani lokaci kana ya janye idanunsa daga gare ta,magana ta fara while idanunta na kansa tace "we getting late bobo, Mameey tace ka tashi ka shirya"banza yay mata sai data ƙara magana yace "to bazani ba"zaro ido tayi waje kafin tace "kamar ya?,bobo dinner ɗinka ce fa"haɗe rai sosai kana yace "kee get out,idan zaki adawo lfy nace bazani"fita tai da sauri idanunta cike da hawaye, Mameey na ganinta tace "Mameey wai ba zashi ba"Mameey tace "kamar ya kenan?"baby tace "haka dai yace min,kuma hadda kuruni ai da Jalilerh ce bazai kurota ba"miƙewa Mameey tai tace "ya isa,ban son magana irin wanann, just wait for me"tana faɗin hakan tai part ɗinsa tsayawa tai sbd ganin ƙofar a rufe, Knocking ta shigayi amma akai mata banza,dole yasa ta hqr ta juya abinta, parlour ta dawo a nan ta samu Nihila tsaye idanunta cike da hawaye,tana ganinta tace "wayata na sama,kiramin Irfan" babu musu tai dailing number da aka sawa sweet bro,yana picking ta bawa Mameey,daga chan Irfan yace "en mata kun ƙarasu ne?" Mameey tace "a'a wanann uwar mata ce, Jalal bazai zo ba,but kada ka gayawa kowa har Jafar ɗin sbd kada yaji babu daɗi,idan aka shiru a tashi daga nan Jafar nasan zai zo nida kai na zan masa bayani"Irfan kamar zai kuka yace "but Mameey...," Da sauri Mameey tace "don't question me Irfan" da sauri yace "ok I'm sorry" kashe wayar tayi sannan ta kalli Laure dake shiga kitchen tace "ki cewa ta kitchen ɗin nan kada nazo na sameta ciki"da sauri Laure tace "to Hajiya" ana kiran sallar issha'i Aryan yay sallama shida su Ikram da Anty Sajida da kuma Firdausi sai wasu twisn guda biyu duk mata shekarunsu bazai huce 3 ba,sosai sukai murna da ganin ƴar uwar tasu,Anuty Sajida yayace a wajan Mameey, Firdausi kuma ƙanwa, Ikram kuma ƴar gidan Anty Sajida ce wacce Irfan ya keso, twins ɗin kuma yaran Firdausi ne,da gudu baby ta fito tama manta abinda bobo yay mata,tana zuwa ta faɗa jikin Anty Sajida rabonta da ita tun sau ɗaya da da Mameey taje da ita tana ƙarama, buɗe ido Anty Sajida tayi tace "Hajiya Salmerh don't tell me baby ce wannan,wow ma sha Allah"dry Mameey tayi tace "wlh fa gata nan tana shirin Aure"Anty Sajida tace "kai kice munzo a dai²?" Firdausi ce tai Murmushi tace "Allah dai ya jiƙan Mummy" gaba ɗaya suka amsa da ameen, ƙamshi da kuma alamun tafiyar da sukaji yasa gaba ɗaya sukai kai dubansu zuwa upstairs,a hankali Jalilerh ke sakkowa kanta ƙasa,ta sanya zumbulelen hijab har ƙasa wanda ya kance blue sai fararen idanunta da take juya,ga jajeyen lips ɗinta da suke ta ƙyalli, Firdausi ce tace "tubarkallah bisimillah,ma sha Allah, Anty wannan kyakkyawar fa?kai gsky na daɗe banga beauty irinta ba"Anty Sajida ce tace "Jalilerh right?"Mameey tace "eh kam kin ganeta kenan?" Anuty Sajida tace"gsky ta huce tunani na,hatta ɓakar fata wlh banga mai ƙyan nata ba,ko fari bazai nuna mata ƙyau ba,gashi Hajia Salmerh tana shirin kamaki a halitta" dry sukai Mameey tace "ai tubarkallah ni kina mmkin girman daughter nake,nan fa baby ta girmeta amma Yanzu bata goye baby a baya ba" Firdausi tace "itace wacce Aryan zai aura ko? gsky na tayashi murna ya samu baƙar balarabiya" ita dai tana jinsu bata iya cewa komai ba,sai da taji sun ambaci Aryan sannan ta ɗaga kai aikam ido biyu sukai tashi yana zaune saman kujera ya harɗe hannayensa yana aika mata da wani irin kallo, zamewa tayi a ƙasa cikin ƙaramar muryarta tace "Fatan kun sauka lfy?"gaba ɗaya suka amsa da lfy lou,baki baby ta taɓe kama da haura upstairs, Mameey kuma taja su Anty Sajida zuwa inda zasu sauka, parlour ya rage daga Jalilerh sai Aryan, miƙewa yay tare ƙarasawa inda take zaunan yana zuwa ya ɗuka wajanta yace "meyake faruwa dake ne?"shiru tai masa ba tace komai ba,cije lips ɗinsa yayi yace "ok tashi kije"kamar jira take ta miƙe da sauri tare dayin upstairs ne,iska ya fesar daga cikin bakinsa kafin ya juya ya nufi part ɗinsa zuciyarsa duk babu daɗi, Mama daman tunda taja Asabe ɗakinta tace "yi zamanki a nan,bayan ɗan naki gantalalle ne,yooo banda sallamamme ne tayaya zai zuba ido matarsa tana hulaƙantaki?Keba uwarsa bace?bazan manta ba a haihuwarsa har kusa makancewa kikai sbd wahala,wata rana da kwana tara yana cikin amma dake bashi da liffasi yake bari ana maki haka, a'a dama can dai ba'a san zuciyarsa ba"Asabe tace "kuma kuɗi garesa"a fusace Mama tace "uban me kuɗin nasa ya amfana maki Asabe?kina dai kallo jibi zamu koma gidan gwamnati, sabon gida da motoci da masu tsaro haka aka bawa Muhammad,haba² ai Allah ya ƙara Annabi daraja,shifa jikane a wajena amma ba kiga yadda ya kemin ba,nidai abinda na keso dake kiyi zamanki nan sai ya nemeki,kee ko nan yazo zance masa kawai kin mutu ko?"zaro ido Asabe tayi tace "mutuwa kuma?a'a adai sauya haka nan kuma nazo na mutum?"dry Mama tace "taje ji ido?kai Asabe har yau kina nan da tsoran mutuwa"daga nan kuma suka ɗura da hira suna zaune Mama tasa Laure ta cika mata ƙatuwar warmer da soyayyan naman rago,ga dafaffiyar ganda,ga farfesun kifi,haka suka cika ɗakin da nama sai ci suke,a nan sukai sallar magrib da issha'i a nan kuma bacci ya ɗauke su. Washegari da yamma Jalal da Abbou suna zaune suna maganar yadda za'a koma gidan gwamnati gaba ɗayansu, shi kuma Abbou yace a'a ya koma shi ɗaya sai baby idan an ɗaura masu aure,tunda gaba ɗaya auren saura kwana biyu,kamar daga sama suka fara jiyo ihun Jalilerh, miƙewa sukai a tare,chan kuma sukaji ta ƙara fasa wani ihun ai Jalal bai tsaya Abbou ya bashi umarni ba ya ruga da gudu zuwa upstairs,a hanya sukaci karo da ita daga ita sai wata ƙaramar riga idanunta a rufe bakinta sai kumfa yake fitarwa,tana ganinsa tayi kansa da gudu.


*Nimcyluv*
08119237616
7/22/21, 8:02 AM - Buhainat: UCL NE
_100-101_
Kafin ta ƙarasa inda Jalal yake tsaye ta yanke jiki ta faɗi kanta ya bugo da jikin bango,dake bata hayyacinta yasa ta ƙara zabura ta miƙe tsaye suna nan still a gabanta sun kasa koda ƙwaƙƙwaran mutsi,ganin da gaske downstairs take niyyar yi yasa Abbou faɗin "Muhammad do something,kamar bata hayyacinta"bayanta Jalal yabi lokacin harta kai ga sauka dwonstrais tana ƙoƙarin fiyewa daga cikin gidan,da sauri cikin gudu² ya mara mata baya,tana ƙoƙarin ficewa yay saurin saka ƙafa ya taɗeta tayi baya zata faɗi yaya saurin tareta ta faɗa jikinsa, Murmushi kawai yay lokacin da yaga ta zabura zata ƙwace daga jikinsa, kokawa suka shigayi da ita ganin da gaske tana ƙoƙarin fin karfinsa yasa saka hannu ya ɗagata cak, dai-dai lokacin Abbou ya sakko, Aryan da Irfan suka fito daga part ɗinsu,da sauri su Mameey suka fito,gaba ɗaya suka tsaya a parlour'n suna kallon ikon Allah, Abbou ne yace "Muhammad take her into your room"babu musu yay part ɗinsa da ita zuciyarsa babu daɗi,da ido kawai Aryan yabi Jalal dashi yana haɗiye wani abu mai zafi a maƙoshinsa, Mameey ce tace "Abbou Jalal wai abunne ya dawo ko me?"girgiza kai kawai yay kafin yace "haka muka ganta muma"ya faɗi hakan yana miƙawa twins hannu da gudu suka tawo wajansa sbd daman shi suke kallo, ɗaukan Husainerh yay kana ya riƙe hannun Hassanerh, Mameey tace "Allah ya ƙyauta,amma dai aƙwai matsala yarinya ƙarama su sata gaba"bai ce komai ya nufi upstairs ɗauke dasu Husainerh, Aryan ficewa yay daga gidan,shi kuma Irfan ya nufi upstairs, Mameey ce tace "ina zaka?"yace "Mameey ba wani abu zan ba,baby zan duba"haɗe fuskarta tayi tace "to ba zaka ba"kafin yay magana Anty Sajida tace "huce kaje a binka"juyawa yay cikin sauri ya nufi upstairs, Mameey tace "haba Anty yafa huce shiga part ɗin en matan nan,yanzu ai baki san yaya suke ba,idan suna naked fa?"Murmushi Firdausi tayi tace "Allah ya kiyaye"yana shiga part ɗin ya samu Ikram ita ɗaya zaune saman bed, ganinsa yasa tayi saurin ɗaukan hijab ta saka, Murmushi yay mata kafin yace "meye kike ɓoyewa kuma?"ɓata fuska tai tace "why ka shigo without our permission?" Yace "sbd nasan aƙwai ajjiyeta a nan ɗin,ko ba haka bane?"shiru tai masa ƙara sawa yay wajanta yace "mene ya samu wayarki?na kira but u did pick my call" juyawa idanunta tai tace "ohh ya rabb,wlh tana vibration ne" yace "ok zan kira anjima" tace "to"juyawa yay sai kuma ya kalleta yaga shi take kallo yace "i luv u" kanta a ƙasa tace "luv u too" yace "sure?" Tace "yeah" fita yay tabisa da kallo,yana fita baby ta fito daga bathroom tana sauke numfashi,dry Ikram tai tace "kedai badai tsoro ba"dry itama tayi tace "haba sister aljanu fa?" JALAL na shiga part ɗinsa kai tsaye ya nufi bedroom ɗinsa yana shiga ya sauketa akan bed kana shima ya zauna,bayan ya gama kallonta ya sauke numfashi yace "Jalileeee..rhhh"shiru tai masa tai lamo jikinsa tana zazzare ido, ɗan yatsarsa yasa ya taɓa tsakiyar goshinta, ƙara ta saki tare da fashewa da kuka,cikin wata murya tace "wayyo idona"cije lips yay kafin ya fesar da iska daga bakinsa yace "ido a goshi? weldone mene ya dawo ko?" Ɓata fuska tayi tace "ina ruwanka?" Girgiza kai Jalal yay kafin yace "babu fa,matsala ta ɗaya daku da kuka rasa jikinwa zaku shiga sai nata"dry tai sosai kafin suce "meye haɗin ka da ita?" Shima yay Murmushi yace "niwai?" Sukace "eh fa"zama ya gyara yace "ita ɗin rayuwar Muhammad Jalal Kabeer bobo ce" shiru sukai kafin suce "sonta kake kenan?" Ɓata fuska yay kana yace "yeah? what's your problem?" Girgiza kai Jalilerh tai tamkar ita take magana tace "a'a!baka sonta tunda har zaka iya zuba ido wani ya AURETA bakai ba,bayan kuma kana da iko da ita,ita ɗin mallakinka ce"shiru yay masu bai ce komai,chan kuma yaga ta zabura tace "gida zani ka rabu dani,ka sakeni wajan Ammina zani bana son zama daku na gaji,gida zani" with soo much surprised Jalal yace "alright,zaki gida soon kuma at this week,amma ku fara sakinta" sukace "to kayi mana al'ƙawarin zaka kawota cikin satin nan?" Yace "Nima kuyi min alkawarin kun bar jikinta har abada?" Shiru sukai chan kuma sukace "a ranar daka mai data a ranar zamu rabu da ita" yace "sure?" Suka ce yace "yeah" idanunsa a lumshe yaji tai hamma tare dayin miƙa sai kuma jikinta ya saiki tai luff jikinsa tana sauke numfashi a hankali, gajiyayyun idanunsa ya sauke a kanta lokaci ɗaya yaji wani mugun tausayinta ya kamashi,kasa tashi yay kamar yadda ya kasa janyeta daga jikinsa,yana nan zaune harta farka daga baccin wahalar daya ɗauke ta,hamma tayi tare da buɗe baki ta shiga karanto addu'ar tashi daga bacci,jin laushi ga kuma wani sihirtaccen ƙamshi da yake ratsa cikin hancinta yasa ta ƙara tura fuskarta cikin ƙirjinsa ha tare da tasan ko mene ba, still idanunsa a kanta while hannunsa na cikin sumar kanta Murya can ƙasa yace "Takwaraaaa" ware idanunta tayi tare da juyasu kafin ta ɗaga ƙwayar idanunta a hankali ta sauke ganinta a kan bobo,da sauri ta miƙe daga jikinsa sai kallonsa take,a zuciyarta tana mmkin yadda akai tazo ɗakinsa, bakinta na rawa jikinta ma vibration tace "Uncle"gira ya ɗaga mata kafin yace "meye kikazo yi ɗaki na da har kike min bacci?"kwaɓe fuska tai kamar zatai kuka tace "ayya!wlh nifa ban san yaya akai ba" bai kulata ba ya miƙe tsaye kana ya mai alama data miƙe tsaye,tashi tayi yazo dai-dai kusa da ita, fuskarsa a haɗe ya jawota jikinsa tare da rungome ta, ajjiyar zuciya duka suka saki,kafin ya ɗura bakinsa saman kunanta ya shiga karanta Ayatullah KURSIYO,luff tayi jikinsa tana sauke numfashi tana jin yadda karatun nasa ke ratsa ta,a hankali kuma ya zura hannunsa ta bayanta, ƙara shigewa jikinsa tayi sbd saukar hannunsa da taji a saman fresh skin ɗinta,a hankali kuma yay sama da hannunsa harya sauke a jikin brezia ta data buɗe,kama duka side ɗin yay ya shiga haɗe maɓalllan,jin booms ɗinta sun matse yasa ta fahimci ta brezia a buɗe take,sai lokacin ta tuna tana fitowa daga bathroom bayan ta shirya sai ta manta bata rufe brezia bar,wajan Ikram ta nufi ganin baby ba wani amsa mata take yanzu ba,taje daniyyar a gyara mata daga nan bata ƙara fahimtar komai ba,sai yanzu data farka da ganta da a ɗakinsa, hannunsa ya zame bayan ya gyara mata kana ya cire a jikinsa ya fara kallonta, idanunsa ya ɗauke daga gare ta kafin ya ce "wait a moment" yana faɗin hakan ya fita, a main parlour ya samu Mama da Asabe sai kuma Firdausi da twins,ya na zuwa baby na sakkowa daga upstairs,zama yay idanunsa a kan Mama wacce take ta raba idanu tana jiran taga daga ina Jalilerh zata fito,bayan ya zauna ya ce "ina yininku" Murmushi Firdausi tayi tace "yamai jiki?" Idanunsa akan baby yace "she's fine" kana ya cewa baby "jeki kawo min hijab ɗin ta" tsaye tayi kamar ba taji mene yace ba sai kuma ta juya ta nufi upstairs, Mama tai salati tare da tafa hannu ta ce "kai dai Jalalu ka banu,yanzo kana ganin ƙawar tawa kaƙi gaisheta sbd mugun abu ko me? a'a mugun abu mana,banda haka gaisuwa ta fatar baki ta gagara?nidai wannan muƙamin mugun abu kawai ya ƙara maka da kuma nuƙufarci,wlh nidai babu ruwana dole na faɗa maka gsky"yana jinta baiko kulata ba, idanunsa a rufe har baby ta dawo karɓar hijab ɗin yay tare da miƙewa,gaba yay baby ta bisa a baya,kai tsaye bedroom ɗinsa ya shiga yana tsaye inda ya barta yana zuwa ya zura mata hijab ɗin, kallon yadda take lumshe idanunta da kuma yadda numfashinta yake fita da zafi yasa ya dafa saman kanta da sauri ya cire sbd a zababban zafin da yaji, hannunta ya kama har zuwa parlour a zaune suka samu Nihila itama idanunta a kansu musamman ganin yadda bobo ya riƙe mata hannu, ɗauke idanunta tayi,da sauri Jalilerh ta ƙwace hannunta tana kwallon bobo kamar zatai kuka, gyara tsaiwarsa yay yace "jira nai maki allura" da sauri hadda gudu tai waje jikinta yana tsuma,waje ya nema ya zauna tare da ɗaukan remote ya kunna cenema, ganin baiko kalli inda take ba bare ta saka ran zai kulata yasa ta fashe da kuka tana jin wani irin a ranta,jiyowa yay ya zuba mata idanu shi har ransa mmkin yadda kuka baiwa mata wahala yake,yanzu suke lfy yanzu zaka gansu suna kuka, ɗauke idanunsa yana ci gaba da kallon series ɗin Begusarai wanda zee world suke haskawa lokacin,sai da tayi mai isar ta sannan ta shiru miƙewa tai zata fita muryarsa yana faɗin "Zo nan" tsayawa tai sai kuma ta ƙarasa inda yake zauy,zama tayi a saman kujerar da yake, idanunsa akan kallon yace "mene?" Turo baki tai kafin tace "bakai ka daina kulani ba" taɓe baki yay kafin yace "haba?"sosai mgnarsa ta bata haushi amma ta daure tace "ehmn,gashi yanzu ma ko inda nake baka kalla,ka nunawa Jalilerh ta fini a wajanku, bayan kuma kasan ni zaka au...,"kasa ƙarasawa tai sbd kallon da yake mata, Murmushi yay yace "nasan ni zan aureki right?"kasa bashi amsa tayi,shi kuma ya juyawa gaba ɗaya yana kallonta kafin ya sanya hannunsa ya ɗago haɓarta yace "look at me"kallonsa tai kamar yadda yace shi kuma ya ɗura da faɗin "da ke da ita kuna da bambanci,tunda nake da ita bata taɓa shigowa part ɗina ba tare dana bata izini ba,bata taɓa zama kujerar da nake zaune akai ba, anytime a ƙasan ƙafafuwana take zama,bata taɓa yimin complain a kanki ba,sai gashi ke kinyi yanzu abinda nakeso dake bana son irin wannan shirmen,idan ma kishi kike da ita is better for you ki daina,ita babu komai a ranta tana min kallon wani jigo nata ko damuwa ce da ita idan bani da faɗawa ba zata iya gaya wa kowa ba,dake da ita duk ɗaya kuke a wajena ke jini nace ita kuma rayuwata ce kinga babu bambanci ko?" Tunda ya fara magana dake kallonsa kamar wacce bata gane me yake faɗa ba,kasa cewa komai tayi sai saukar muryrsa da taji yana faɗin "tashi kije" miƙewa tai tare da fashewa da kuka yana jin zuciyarta kamar zata fito,ita dai bata san mene hakan ba,amma tun sanda akace zata auri Jalal shikenan taji Jalilerh ta fice mata a rai,ko hakan na nufin kishi take dashi ohuuuu?fice tai daga part ɗin a hanya ta tsayawa ta gama kukanta sannan wa goge fuskarta ta nufi part ɗinsu.at the same day da daddare Jalal yana sanye da black ɗin jallabiya da kuma wata red ɗin hula ta sanyi sbd busawar sanyin da akai a lokacin sakamakon ruwan sama da akai, knocking Ƙofar parlon yay daga chan Abbou yace "come in" tura ƙofar yay a hankali bakinsa ɗauke da sallama, Abbou ya na daga zaunan da yake ya amsa sallamar tare da ajjiye cup ɗin hannunsa, ƙarasawa Jalal yay tare da zamewa ya zauna kusa da ƙafafun

33 / 41