Author : Nimcey Sarauta Category : Romance
Abbou ya ɗura kansa saman cinyarsa ya shiga sauke ajjiyar zuciya,shafa kansa Abbou yay kafin yace "yaya akai farin ciki Abbou'nsa?" Kwaɓe fuska yay kafin ya ɗago kansa ya kalli Abbou sai kuma ya saki Murmushi yace "alfarma nake nema wajanka Abbou'na"gyara zama Abbou yay yace "ta mecece? Allah ya ban ikon yi maka"Jalal ya sauke numfashi ya ce "zaka iya mana Abbou please"jinjina kai Abbou yay ya ce "ina jinka"shiru Jalal yay yama rasa ta ina zai fara,kansa a ƙasa yace "Abbou so nake a ɗan kwanakin auren nan koda sati guda ne please"da mmki Abbou ya ce "why?" JALAL ya marai-raice fuska ya ce "Abbou Jalilerh nake son kaiwa garinsu ta matsa sai kuka take,and kuma naiwa aljanunta al'ƙawari kamar yadda sukai min al'ƙawarin zasu rabo da ita idan har na kaita can garin"shiru Abbou yay yana nazarin maganar Jalal ɗin sai kuma yace "sune suka buƙaci hakan?" Ɗaga kai Jalal yay kamar ƙaramin yaro yana ƙara sauke kansa a saman cinyar Abbou, Murmushi Abbou yay yace "idan haka ne to ai harni za'a sbd na amsawa Aryan aurenta a wajan danginta ko?"shiru Jalal yay masa, miƙewa tsaye yay yace "gobe zamu koma can gidan gwamnati,kuma a goben zan fara shiga office,zan nema mana private jet jibi saimu huce ko?"Abbou yace "babu damuwa Allah ya kaimu,zanwa Mameey bayani da kuma Aryan,amma bana jin Mameey zata bimu zata zauna da baƙin ta da kuma su baby, ƙilan dai muje da Mama da kuma Irfan"jinjina kai kawai Jalal yay kana ya masa goodnight ya fice daga cikin part ɗin nasa. Washegari tun safe suka gama shiryawa kasan cewar babu abinda zasu ɗauka sai sutturar sawa yasa shirin bai masu wahala ba, Abbou a motarsa ya ɗauki Mameey da Asabe sai Mama a gaba,motar Irfan kuma Ikram ce gaba baya kuma Firdausi,motar Imran kuma su biyu ne daga shi sai Anty Sajida, Aryan kuma Jalilerh wacce tai tsaye ta rasa motar da zata shiga, Jalal dake tsaye yana jiran kowa ya gama shiga ya shiga tasa hannunsa riƙe da twins wanda suke masa surutu Shi dai yana jinsu amma baya fahimtar abinda suke faɗa, harya buɗe baki zaiwa Jalilerh magana ganin Aryan ya nufi inda take yasa yay shiru tare da ɗaukan tiwns duk su biyun ya nufi wata sabuwar bugatti daya sauya,yana zuwa security ya buɗe masa back seat ya shiga,yana shiga baby ma ta buɗe ƙofar ta shiga daman shi take jira sbd Abbou ne yace ta shiga motarsa, ya kasance su biyu ne a motar sai twins Husaynerh da Hassanerh wanda suka sukuwa a jikinsa wata taja gefenmu wata kuma ta cire farin glass ɗin idanunsa, Murmushi kawai yake masu domin har zuciyarsa yake son yaran he wish ace wata rana ya samu kamar su,motar securities guda biyu ta fara yin gaba sai kuma motar Abbou sai ta Irfan, Imran ma ya mara masu baya ganin haka yasa Aryan ya shige gaba kana driver Jalal yay mata key yabi bayansu,sai kuma wasu motocin y guda huɗu tabi bayan motar Jalal,a nutse motar suke tafiya suna cikin tafiya sukaci karo da motar ƴan jarida both tv da redio ga kuma jama'ar gari duk titin da sukabi ihu ake ana ɗagawa Jalal hannu wanda yasa drive ya sauke saman motar ta dawo half ana iya ganin komai na motar shima ɗaga masu hannu ya fara,ganin haka yasa twins ma suka fara ɗagawa guntayen hannayensu a haka suka isa har gidan gwamnati,duk inda ka duba securities ne birjik har can ciki suka shiga, faɗar haɗuwar gidan ɓata baki ne,kana shiga zaka samu babban parlour babu abinda babu a cikinsa,amma babu bedroom ko guda a cikinsa,wata hanya suka bi nan ma suka tarar da babban parlour wanda yafi na baya ƙyau,daga nan kuma wajan sides goma ne a wajan,banda upstairs,a nan Jalal ya nuna wani part yace shine na Abbou,kana ya nunawa Mameey nata, Mama haka,samarin gidan kuma yace kowa ya zama idan zasu zauna da matansu, Abbou ne ya kalli Jalal yace "to en matan gidan fa?" Sosa kai yay yace ai ga sauran parts ɗin nan ga kuma nasu Anty Sajida before they leave,yana faɗin haka ya haura saman upstairs hakan ya nuna shine nasa,shi kasan sai da tsarin part ɗinsa ya bashi tsoro,iya upstairs parts wajan huɗu ne,banda babban parlour'n da tsakanin parts ɗin,a hankali ya fara duba ko wanne harya samu wanda yafi ko wanne ƙyau,yana shiga shima yaga parlour ƙarami kuma mai dai-dai ci,amma tsaruwar parlour yasa dole ka kallesa ga wasu kujeru ƴan turkey masu a zabar ƙyau,wata ƙofa yabi ya bedroom ne tangameme ga wani ƙaton royal bed mai girman gaske ko mutum sai sun ƙwanta samansa,sai kuma wata wardrobe kana iya ganin duk kayan dake cikinta,sai dressing mirror,ga wata duguwar kujera dake gefen bed ɗin,wata ƙofa ya buɗe ya shiga nan kuma yaga wani ƙaramin office ne idan yana gida wanda zai dinga amfani dasu,bayan ya gama kalla ya ƙara buɗe wani ƙofar yaga Library ne shi kuma,bai tsaya kalla ba ya nufi wata ƙofar, lumshe idanunsa yay shi dai wajan kai tsaye ba za'a iya kiransa da lambu ba,amma yanayin flowers na wajan sai ka ɗauka lambu ne,ga wani abu a tsaye da ruwa yake zuba ta cikinsa wanda shi bawa flowers ɗin ruwa,grass ɗin wajan wacce tai kamar carpet tai green gwanin sha'awa wajan yay ƙyau sosai banda ƙamshin na'a² da sauran flowers ɗin wajan babu abinda yake, rufewa yay ya nufi wajan ta ƙofa nan yaga bathroom ne, komai na cikinsa light blue ne,ga jakuzzie ga shower ga sink ga towels kala² hakama bathrobe,wasu ma kayan baka iya faɗar sunan su,fitowa yay tare da zame kayan jikinsa ya anjiyesu cikin warshing machine kana ya sakarwa kansa shower sauke numfashi yay,kana ya kalli mararsa Murmushi kawai yay sbd ganin dick ɗinsa tai samɓal ga wani kauri da tai sai jijiyoyi da sukai birjik samanta, riƙeta yay yaji yadda take harbawa da sauri da sauri kuma ya saka yana astagafirullah sabida jin yanayinsa ya fara sauyawa, bayan ya kammala wankan yay brush ya ɗaura alwala sbd baya rabuwa da alwala,yana shiryawa ya ɗauki wani tattausan farin boyal mai taushi wanda yake da manyan flowers gashi shara² komai na jikinsa ana iya gani da farar singlet ɗin da kuma fatar jikinsa, agogon warist ya ɗaura a hannunsa kafin ya maƙala bluetooth sbd bai fiya yawo da waya,wasu Black ɗin takalmi ya sanya farar ƙafarsa,yana gama shiryawa ya fesa parfume kana ya fice daga bedroom ɗin,sai da ya isa parlour sannan ya kula da kitchen ɗin dake cikin parlour'n,fita yay daga part ɗinsa sai da yay tafiya mai ɗan tsayi ta huce sauran part ɗin da suke upstairs ɗin,sanann ya nufi downstairs,stepfoots ɗin da sukaji yasa suka ɗaga idanunsa, Murmushi Abbou yay ganin yadda ɗan nasa yay wani bala'in ƙyau da kwarjini ga kuma haiba,daman shi suke jira suyi lunch a danning Area,gaba ɗaya suka miƙe suka nufi danning Area twins na ganinsa sukai wajansa da gudu duƙawa yay ya ɗauki Husaynerh aikam kamar take Hassanerh ta sanya ihu hadda birgima,yana dry wacce ya daɗe bai irinta ba ya ɗauke ta itama,gaba ɗaya dai kallonsa suke sun rasa mene ya sashi farin ciki haka,bayansu yabi yaja kujerar dake farcing ta Abbou ya zauna,kafin su fara cin abinci Abbou yace "munyi magana amma Aryan ba zai samu damar zuwa ba sbd yana da shari'ar da zai gabatar,su iya ni dakai da Jalilerh zamu sai Mama da Irfan" Jalal ya lumshe idanunsa yana sauke ajjiyar zuciya yace "Allah ya nuna mana goben" suka amsa da Ameen, Mameey ce tace "Amma ba daɗewa za kuyi ba ko?sbd a satin nan za'a fara azumi,ga kuma bikin nidai dan Abbou ya matsa ne da sai ya bari a sauke azumi sai a bikin zaifi" Abbou yana ɗaukan spoon yace "banji za muyi ƙwana uku,zan dai yi tunani akai,ina daughter ɗinma?" Mameey tace "ai kwana biyu miskilanci take ji da shi,ga yawan kuka kamar matar mamaci,nadai gaya mata so tasan da tafiyar alrdy an shirya mata kayan ta,yanzu ma nace ta fito taci abincin tace ta ƙoshi"shi dai Jalal bai ce komai ba sai abincinsa daya keci a hankali,yana zaune telephone ɗin parlour'n ta fara ƙara, Irfan ne yaje ya ɗauka daga can wani security yace "aƙwai baƙo a waje zai sunansa Jafar kusan da zuwansa?" Irfan yace "let him come" Yana faɗin hakan ya ajjiye kiran,babu jimawa Jafar ya shigo tun daga nesa ya sakarwa Jalal Murmushi shima ya mayar masa ya sunkuyar da kansa ƙasa, ƙarasawa yay ya fara gaida Abbou sannan sauran Irfan da Aryan da Imran suka gaida shi, Ikram da baby suka gaishesa, idanunsa akan baby ganinta ƙara ƙyau sbd gyaran jikin da Anty Sajida ta farayi masu su duk ukun tun ranar da tazo,gaba ɗaya sun sauya kadama Jalilerh taji labari,zama yay yace "afuwa rabuna daku tun a wajan dinner wallahi naje Niger ne"Mameey tace "Allah sarki,aina ɗauka fushi kayi damu,to ya Maman taka?"yace "Allahamdulillah tana gaidaku"bayan sun gama suka dawo parlour Jalal kuma ya nufi wajan hutawa shida Jafar,sun taɓa hira kaɗan,kafin Jafar yay masu sallama ya fita,shima Jalal part ɗinsa ya koma ya fara duba files wanda aka bashi yau wanda mataimakin gwamna ya saka hannu a cikinsa,bayan yay bincike sosai ya duba muhimmanci gyaran titin sai ya buga stam, washegari da safe sun gama shiryawa sbd alrdy jet ya sauka su ake jira, Abbou ya shirya cikin manyan kaya hakama Jalal kusan kaya iri ɗaya suka sanya har da Irfan, Mama kuma atamface jikinta sai babban mayafi, Jalilerh kuma wata haɗaɗɗiyar abaya ta sanya sky blue sosai tai mata, kasan cewar helicopter ne yasa a cikin gidan gwamnatin ya sauka,har waje sukai masa rakiya Aryan kam tun safe ya shiga part ɗin yaywa sahibar tasa sallama,suna tsaye har suka shiga ciki, Jalal da Jalilerh suna baya, Abbou da Irfan suna tsakiya sai kuma Mama da wasu securities a side ɗin gaba,a haka jirginsu ya ɗaga zuwa Birnin nufar...
_ki biya ki karanta dan Allah,08119237616 🌚_
*Nimcyluv*
7/22/21, 8:02 AM - Buhainat: UCL NE
_102-103_
Tafiyar 1hour and 20minutes ne ya kai su Birnin nufar,a filin tashi da saukar jirgi na birnin private jet ɗinsu ya sauka,suna zuwa motocin wajan goma sukai parking suna jiran zuwansa sbd alrdy an san da tafiyar tasa duk da cewa ta sirri ce,a hankali suka fara fitowa ya rage daga Jalal sai Jalilerh yana tunanin yadda zai mata gashi bacci ya ɗauke ta,jin shiru yay yawa yasa Abbou leƙawa jikin jirgin a zaune ya gansu da mmki yace "what are u waiting for?"fesar da iskar bakinsa yay kana ya kalli Abbou yace "tai bacci fa" Abbou yace "And then..?" JALAL yace "ban san yaya zai manta ba" taɓe baki Abbou kafin yace "abeg my friend carry her" yana faɗin hakan ya fice daga cikin jirgin,cikin nutsuwa ya zare belet ɗin jikin jirgin wanda ta maƙala a jikinsa,kana ya zare mata ta jikinta miƙewa yay ya zubuwa fuskarta idanu sosai take bacci cike da nutsuwa,fesar da iska yay daga cikin bakinsa kafin ya durƙosa dai-dai saitin da slowly ya ɗauke ta izuwa jikinsa a hankali kuma ya fara tafiya da ita harya fice daga cikin jirgin,yana fita yaga duk sun shiga mota sai securities ɗinsa dake bakin jirgin suna jiran fitowar sa, da sauri wasu sukai gaba wasu kuma suka tsaya a bayansa, a haka ya ƙarasa gaban wata ƙaramar mota mai ƙyau fara tass da ita,back seat baka buɗe masa ya zauna still tana jikinsa,rufe ƙofar akai driver ya koma wajasa,haka securities ɗin ma duk suka shiga taso motar, lumshe idanunsa yay yana ƙara gyara mata zama a jikinsa a haka suka ɗauki hanyar hotel ɗin da zasu sauka, Abbou tunda suka sauka daga jikin jirgin ya keji kansa na sara masa ƙirjinsa na bugawa,ɗaya runtsa idanunsa sai yaga garin yana masa gizo gani yake tamkar ya taɓa sanin garin,haka yayta salati cikin ransa amma kamar ana ƙara masa abinda ya keji daga bisani ma idanunsa ne suka rufewa ya fara gani dishi²,cikin kunnansa kuma sautin ihu ya keji da kuka sama² yana cikin wannan halin suka ƙara sa cikin Hotel ɗin,suna parking Jalilerh na buɗe ido ganin ta a cikin garinsu yasa tai saurin buɗe ido tare da ƙara ware idanunta domin tabbatar da abinda take gani,da sauri kuma ta juya ta kalli Jalal ashe shima kallonta yake, driver ne ya gama parking security yazo da gudu ya buɗewa Jalal ƙofa,shine ya fara fitowa kafin ya tsaya a bakin motar yana jiran ta fito, Jalilerh kan tsoro da farga ba ne ya gama kamata, jikinta ya ɗauki rawa idanunta yay raurau harga Allah tsoron haɗuwa take da Papa da Joshua uwa uba uwa sundu, haɗe rai Jalal yay tare da miƙa mata hannunsa da sauri itama ta kama sbd duk a tsorace take,haka Abbou da Mama da Irfan duk suka fito daga cikin motocin su,kai tsaye reception dubu hotel ɗin suka nufa kafin su ƙarasa an kammala masu komai kai tsaye rooms ɗin su suka nufa,duk rooms ɗin a jere suke Mama da Jalilerh akace su shiga room guda ɗaya kwaɓe fuska tayi tana kallon bobo sbd tsoran masifar Mama take ga kuma yanayin firgici data shiga,da idanu yay mata alama data shiga haka tabi bayan Mama idanunta na fidda ƙwalla, Jalal kam tuni ya gama lura da yanayin da mahaifin nasa ke ciki hakan yasa yaja ya tsaya a bakin room ɗinsa yana jiran yaga shigarsa cikin ɗakinsa,duk dauriyar Abbou kasa juyewa yay yana zuwa bakin room ɗin yay baya zai faɗin Jalal da Irfan sukai saurin taresa a haka ya faɗa jikinsu babu numfashi, ɗauka sa sukai zuwa cikin room ɗin tare da ƙwantar dashi akan bed,babbar rigar jikinsa Jalal ya cire ya kalli Irfan yace "ƙaro gudun ac nan" da sauri ya ɗauki remote yay exactly abinda bobo yace,fara dubasa yay ya tabbatar da shocked ya shiga yasa ya gyara masa kwanciya ya shiga murza tafin hannunsa Irfan kuma ya fara murza tafin ƙafarsa,suna zaune a haka harya fara sauke ajjiyar zuciya tare da jan numfashi,a hankali kuma bakinsa ya fara mutsi he's trying to say something, ganin haka yasa Jalal matsawa garesa ya ɗura kunnansa wajan bakinsa,sai a lokacin kuma maganganun sa suke bakin Abbou suka fara fitar da kansu ba tare daya sani ba,shiru Jalal yay sbd abin da yaji Abbou na faɗa kamar haka "No!Papa please kada kace haka, I'm your son dan Allah Wlh bazan ƙara ba"sosai mmki ya bai yana a fuskar Jalal yana mmkin daya sanya Abbou faɗin Wannan maganganu,waye Papa?me ya aikatawa Papan har haka? Janye jikinsa yay tare da miƙewa tsaye ya kalli Irfan yace "lemme freshen up" jinjina kai Irfan yay yace "to Yaya" yana fita yana faɗin "ka kula before I'm coming back" Irfan yace "I'll" bai ƙara magana ba ya fice daga cikin room ɗin, kai tsaye nasa room ɗin ya koma yana zuwa ya cire kayan jikinsa kai tsaye bathroom ya shiga ya sakarwa kansa shower yay wanka sosai kana ya fito sanye da bathrobe yana fitowa ya tsaya gaban dressing mirror yana kallon kansa haka nan ya samu kansa da sakin wani tattausan murmushi mai tarwatsa zuciyar en mata,jin garin sanyi sosai ga hadari yana haɗuwa duk da cewa ko Asr bai ba,hakan yasa ya shafa wani body lotion mai daɗin ƙamshi mararsa yabi da kallo yaga fess take babu gashi domin da safe ya saka mai yay sheving nasa daga na hammta harna gaba,bayan ya gama shafa lotion ɗin ya ɗauki body spray ya feshe jikinsa dashi,cump ya ɗauka ya tashe sumar kansa tai ƙwance lufff sai sheƙi take,bayan ya gama komai ya miƙe ya nufi inda trolly ɗin sa take ga buɗe ya ɗauki wani tissue ɗin yadi black an masa ɗinki da red ɗin zare sosai ya amshi farar fatarsa, ɗinkin irin half ɗin nanne babu babbar riga,takalmi ya ɗauka red mai ƙyau haka ma hular kansa,yay wani irin sahihihin ƙyau mai ɗaukar hankali bayan ya ɗauki Uhud mood ya fesa ya nemi waje ya zauna yana maida numfashi,sai Lokacin maganganun Abbou suka fara dawowa cikin brain ɗinsa, lumshe idanunsa yay yana fesar da numfashi,a hankali kuma ya ware fararen idanun nasa jin ana kiran private sim ɗinsa,bai ɗauka ba sbd ganin baƙuwar number har akai kira wajan 4 ana biyar ɗin yay answering tare da manna wayar a kunnansa yana sauraren mai magana,a hankali yaji ance "Assalamu alaika" gabansa ne ya faɗi ji yay kamar ya taɓa sanin Muryar,sai da aka maimaita sallamar sannan ya ce "Wasalamu alaika" daga can ɓangaren Jabir yace "fatan kana lfy? Naji abin farin ciki ina tayaka murna sosai wlh, Ubangiji ya tayaka riƙo" a kasalance Jalal ya amsa da "Amin ya hayyu ya ƙayyumu" Jabir yay Murmushi ka ɗan yace "nasan ba lalle ka gane mai magana ba,amma dai da izininka aka ban wannan layin,sunana Jabir munyi magana akan zaka duba ƴar uwa ta after election,to gashi wajan wata gudu da satintika akai shiyasa na yanke hukuncin tunasar dakai idan babu damuwa sai na kawota" cije lips Jalal yay sai lokacin ya tuna Jabir cikin sanyin Murya yace "ohh! Allah sarki gashi nai tafiya zuwa Birnin nufar yanzu" da sauri Jabir yace "what!? Nufar fa? To ai a nan nake da zama nanne gari na"Murmushi Jalal yay yace "babu damuwa saika turomin address ina ganin zanzo da kai na nima na zaga gari" cike da farin ciki Jabir yace "No! Please gayamin inda kake zanzo da kai na yanzu na ɗauke ka" jinjina kai Jalal yay kana ya basa address ɗin Hotel kafin suyi sallama, miƙewa tsaye yay ya nufi fita daga room ɗin kai tsaye room ɗin su Jalilerh ya shiga yana shiga ya tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannayensa a saman faffaɗan ƙirjinsa, Mama taci gaba da faɗin "a'a kedai kin fiye kini bibi wlh, yanzu da baice ki biyoni ba shiza kibi ko?dake a garin mahaukata aike sai kawai a barki da ƙaton namiji a ɗaki ko?kai yau naga masifa ido biyu,ko da yake ai garin naku duk Alhalil kitab ne daga mai kuntun abu a gefen ɗuwaiwai sai wanda zaka ganshi tsirara,nidai yau nai mugun gamo kedai