UNCLE NE BOOK 1,2,3 Hausa Novels By Sarauta.txt

Author :  Nimcey Sarauta Category :  Romance

Chapter   6 / 41

15K to 18K   out of 120.1K words

da tsane kansa da towel,yana gamawa ya fito ya ƙarasa wajan wardrope ya ɗauki wata ash ɗin jallabiya mara nauyi ya saka,bayan yyi komai ya fesa turare ya ɗauki paryer mat ya nufi waje parlour,da sauri tace "Uncle yaya zanyi?" ficewarsa yyi baiko tsaya ba bare ya tankata,a haka ya ƙarasa parlour ya shimfiɗa daddumar ya tada sallar lafila,sai da yyi raka'a huɗu ya lumshe idanunsa cike da tunani kala kala a ransa kafin ya fesar da wani numfashi mai zafi,ciki daddaɗar muryarsa mai amo da kuma sauti haɗi da sanyi,ya fara karanta suratul الكهف yadda yake karatun a nutse da kuma yadda yake fidda makarijin huruf da tajweed zaka fahimci ba ƙaramin ilimin addini garesa ba,sosai yake karantu yadda bazai damu wani ba, kuma yadda bazai takura kansa ba, ma'ana bai ɗaga murya ba haka kuma bai ƙasa da murya ba.

Lamo Jalilerh tayi tana sauraran muryasa dake fita a taushashe kuma cike da kuzari,haka nan taji ciwon nata ya lafa ga kuma daɗin karatun data samu kanta ciki,tun tana sauraran daddaɗar muryarsa har bacci ya ɗauke ta.

Jalal bai tashi a wajan ba,sai da aka kira sallar asuba yana zaune har akai assalatu, miƙewa yyi ya nufi cikin bedroom ƙwace ya ganta ta cure waje guda ga jinin gaba ɗaya ya ɓata jikinta da kuma bedsheet, taɓe baki yyi ya ƙara ɗaura sabuwar al'wala tare da ɗaukan hula tashi kafiya naci,irin hular nan da larabawa da suke sakawa,sosai ya fito tamkar balaraben gske,a haka ya fito zuwa part ɗin su Abbou, a babban parlour ya samu Abbou zaune da casbawa a hannu,can gefen kuma Irfan ne zaune shima cikin farar jallabiya,da alama Imran da Aryan suke jira,babu jimawa suka fito a tare,gaba ɗaya suka nufi masjid,suna shiga su kaga kowa a zaune ga lokacin sallah yayi, Abbou ne ya kalli maƙocinsa yace "Alhaji Naseer lafiya ina malam muktar ɗin?" "wlh baya da lfy shine aka rasa mai tada sallah" kafin Abbou yyi mgn yaji saukar Muryar Muhammad Jalal bobo a kunnansa na faɗi "sahuu iƙamun sallat" jin haka yasa kowa ya hau sahu,tare da dai-dai ta ƙafafuwa cikin sassanyar muryarsa ya fara tada kabbarar harama kafin a hankali kuma ya fara karanta fatiha kana sura ta biyo baya, sosai kowa ya nutsu har sukai raka'a biyu,bayan anyi sallama tare da addu'a masu tafiya suka fara tafiya wasu kuma suka watse, Jalal ko mutsawa bai yi sai Kur'ani daya jawo ya fara karantawa,kafin ya idar ya fara azkar.

ƙarfe 6 dai-dai ya dawo cikin gidan a main parlour ya samu Aryan na shirin fita motsa jiki,ganin Jalal yasa yayi saurin tsugunawa yace "Barka da asuba yaya" lumshe ido yyi cikin gajiyawa yace "yawwa barister" murmushi Aryan yyi yace "nina tafi motsa jiki sai na dawo" uhm kawai Jalal yace kai tsaye upstrais ya nufa inda Mummy ta koma,yana zuwa yyi knkg tana ciki tana tunanin waza ta gayawa ba taga Jalilerh gaba ɗaya hankalinta ya gama tashi tunda taje data Nihila tayi sallah taga bata cikin ɗakin ta kuma tabbatar wa kanta ba zata fita ba, gyara tsaiwa tayi tace "come in" jin haka yasa ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama ya shiga,ganinta tsaye ya sashi durkosawa yace "Mrng Mummy" kansa ta shafa tace "mrng too boo yaka tashi da kuma kwanan baƙunta" cije lips yace "Allahamdulillah" miƙewa yyi tare da juyawa sai kuma ya tsaya cikin tarin baccin dake a idanunsa yace "Mummy yarinyar can na side ɗina" da mamaki tace "a can ta ƙwana? shiyasa naga babu ita duk hankalina ya tashi" ɗauke kai yyi sam ya fara gajiya da yawan surutun nan haka nan,kamar zai kuka yace "wai mararta ke ciwo,i think period ne" murmushi tayi kafin tace "ok bari nazo jeka ƙwanta naga sai yanzu ka shigo" fita yyi ya nufi side ɗin nasa a parlour ya tsaya tare da zare jallabiyar jikinsa ya ajjiye gefen sofa sannan yay ƙwanciyarsa babu jimawa bacci ya ɗauke sa.



yana fita Mummy taje wardrope nata ta ɗauki pat da pan,bayan ta ɗauka taje ɗakin Nihila tana ƙwance sai bacci take tamkar kasa,duguwar riga ta atamfa mai ɗinkin stone,tana da faɗin wuya ga kuma shaf,ita Mummy ta ɗaukar mata,bayan ta ɗauka ta nufi side ɗin Jalal kai tsaye ta shiga bakinta ɗauke da sallama, tsayawa tayi sabida ganinsa da tayi ƙwance a saman sofa sai haɗa zufa yake,ga yadda jijiyoyin kansa da suka firfito,ko ba'a gaya mata tasan kan nasa ne ya mutsa,jitai babu daɗi a ranta domin har zuciyarta bata sha'awar taga wani abun yana damunsa, remote ta ɗauka ta ƙaro masa gudun a.c kafin tasa hannu ta miƙar masa ta ƙafarsa data langwashe,saman forehead ɗinsa ta taɓa taji wani zafi mai ratsa jikin mutum da sauri ta janye hannunta,tasan baccin kawai yana yin sane bawai dan daɗi ba,cikin zallar tausayinsa tace "sorry Bobona laifi nane" cikin bedroom ɗin ta huce a nan ta samu Jalilerh ra kuɓe sai shassheƙar kuka take cikin damuwa Mummy tace "sorry dear tashi muje bedroom" miƙewa tayi sai a lokacin Mummy taga irin jinin data zubar warm water ta haɗa mata a cikin jakuzzie tace ta shiga,batai gardama ba ta shiga ciki,runtsa idanunta tayi sabida zafin ruwan da taji,bayan ruwan ya gama ratsa ta, aka ƙara sauya mata wani kana Mummy ta wanke mata kan tas,har sai da rinin da tayiwa kanta ya fara fita,bayan ta gamayi mata komai tace "kinga yadda nai maki wanka jiya ko" kaita gyaɗa mata alamar "eh" murmushi Mummy tayi tace "good gril nasan you are a shy baki bari yanzu nai maki,maza kiyi ki wanke ko ina na jikinki lungu da saƙo i'm coming" tana faɗin hakan ta fice daga cikin bathroom ɗin, bedsheet ɗin ta cire ta naɗe waje guda,kana ta fita dashi zuwa washing machine,cikin bedroom ta ƙara komawa ta sauya wani bedsheet ɗin ta share ɗakin tayi mopping,ta fesa airfreshiner tare da kunna turaren huta,haka ma parlour ta gyara komai har t.v sai da ta goge bayan ta gama komai ta koma cikin bathroom ɗin tsaye ta sameta ɗaura da towel a jikinsa,ta juna handrayer tana busar da kanta, murmushi tayi tace "yawwa my dear kinsa pat ɗin yadda na nuna maki?"cikin jin kunya Jalilerh ta ɗaga kanta alamar "eh" handrayer ta amsa taci gaba da busar mata da kan tare da faɗin "ki daina kunya im ur mother ba kiga Jalal Mummy yake faɗi ba,so kema ni mummynki ne,duk abinda kikeso ki sanar dani kinji" murmushi tayi tare da sunkuyar da kai ƙasa cikin siririyar muryarta tace "Thank You Mummy" jinjina kai tayi tace "never mind you are my daughter" tana faɗin hakan ta jata zuwa bedroom ta bada underwear ta saka kana ta bata duguwar rigar tasa hannu ta haɗe waje guda alamar 👌🏻tace " wow! what a beautiful girl" sosai rigar ta amsheta ga yadda hips ɗinta ya zauna dass a jiki ka san cewar atamfar mai orange ce sai ta haska chocolate skin ɗinta,sam batai ƙoƙarin ɗaura mata vail a kanta ba sabida tasan ba hurumin ta bane,direct ficewa sukai daga bedroom ɗin tare da jawo masa ƙofar har yanzu yana ƙwance yana bacci, taso tashinsa ya koma cikin bedroom amma bata son katse masa baccinsa, hasken parlour'n ta rage masa nan ma ta jawo ƙofar suka fice daga ɓangaren samarin gidan.



a babban parlour suka samu Mama gabanta cike da kayan ciye-ciye plat ɗin farfesun kayan ciki daban,ga plat ɗin soyayyan dankalin turawa wanda yasha ƙwai daban,ga kuma wani cup ta cika tea dashi ga ƙaton biredi sai rarakar cikinsa take,dryar dake cin ran mummyce ta subace ai kafin tace wani abu tace "yau naji masifa,mutum yaƙi ci a tsiri kai sa asibiti,naci kuma abun ya zama abin magana,ita dai lfy abin tattalawace ina dalili ga kaya tili guda a gidan amma sai anyimin surutun jalala" shuru Mummy tayi kafin tace "ayya ba haka nake nufi ba,naga gaba ɗaya yanzu 8 tayi shiyasa,amma kiyi hqr ban ƙarawa" ƙarasa tura naman bakinta tayi har yawo na tsiyaya kafin ta haɗiye da kƴar tace "yanzu wannan ahlil kitab ɗin anan zata zauna salon da janye min hankalin jikata,ohhh ni yau naga ta kai na wannan zaƙo-zaƙon abin a hannu fa" ta ƙare maganar tana riƙe haɓa wacce take nuni da ba ƙaramin mamakin abin Mama ta keyi ba, ƙasa da murya Mummy tayi cikin damuwa da zan can da Mama tayi tace "haba Mama babu ƙyau fa,muda muke fatan ace sanadinmu ta samu rabauta da musulunci,amma mene yasa ke zaki faɗi hakan dan Allah" taɓe baki Mama tayi tace "yanzu kina saka ran wata rana wannan zata musulunta,ehh to kuma abun a hannu Allah yake" murmushi Mama tayi tana haurawa upstrais tace "ah to nufi ne na Ubangiji ai,my dear follow me" ta faɗi maganar tana shigewa ɗakin Nihila tana shiga Nihila na fitowa cikin sauri domin tayi late a school,tana ganin Mummy taje tai hugging ɗinta tace "good mrng Mummy" shafa kanta tayi tace "mrng baby how are you" cire jikinta tayi tace "Allahamdulillah bye sai na dawo" girgiza kai tayi domin tasan ba zata zauna yin brekfast ba,a haka Nihila ta fita zuwa compund tana fita drever ya jata zuwa N.S University of ibadan (kirkirarriyar makaranta ce) kwanciya Jalilerh tayi tana tunanin maganar Mama,abinda yake damunta shine mene banbancin nasu addini da kuma musulunci,taga kowa da kalan nasa addini kuma kowa aƙwai abinda yafi so game da addininsa,amma mene yasa Mummy keyi fatan ta musulunta? haka tai ta tunani a ranta ba tare data fahimci komai ba,sannan ta kasa gane banbancin nata addinin da kuma na Musulunci da suke faɗa.

misalin 11 na safe kowa ya haɗu a wajan danning, Mummy, Mameey, Mama, Abbou, Imran,Irfan tun 7 yabar gida sabida aikin bank yake, Aryan shima yana da Shari'a yau,tun 7 yabar gida, JALAL kuma har yanzu bai fito ba,bayan sun kammala breakfast ɗin ne, Abbou ya miƙe yace "nizan tafi ina da meeting by 10:30 i will be back soon" gaba ɗaya sukai masa sai ya dawo,kasan cewar a ɗakin Mameey yake har jikin mota ta rakashi, Mama kam main parlour ta koma ta kunna t.v ta fara kallon cartton,turo ƙofar ɗakin Mummy tayi a hankali Jalilerh ta ɗago kanta tare dayin murmushi fararan haƙoranta sukai bai yana,cikin nutsuwa ta miƙe daga zaunan har Mummy ta ƙarasu inda take tsaye tace "my dear ke ɗaya a ɗaki ko" murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba,kama hannunta Mummy tayi tace "ban son shurun nan naki yana takurani Jalilerh" kallon Mummyn tayi tace "babu yare sosai a baki" dry ce ta ƙwacewa Mummy sai da tayi mai isarta tace "ehee haka kikaji hausa ashe" kafin ta ɗura da faɗin "haka za kice babu hausa a bakina sosai" turo baki tayi tare da shagwaɓe fuska kamar zatai kuka tace "that's what i mean" "okey dear muje ki kiramin bobo" tana faɗin haka suka nufi downstrias a parlour suka samu Mameey da Mama na zaune, Mameey na kitsewa Mama kanta,tanayi amma Mama na bata basifar babu abinda ta iya,dry kawai Mummy tayi tare neman wajan zama ta zauna,ganin har yanzu Jalilerh na tsaye bata je inda ta aiketa ba,ya sata faɗin "maza jeki kiransa mana" da "okey" kawai ta amsa ta nufi part ɗin nasu kai tsaye side ɗinsa ta nufa,a hankali ta ɗura hannunta a saman handle ɗin tare da tura kanta cikin kyakkyawan parlour'n nasa,ganin babu kowa sai ƙarar a.c da kuma ƙamshin airfreshner, rarraba idanunta ta fara yi kamar mara gsky,sam bata son shiga cikin bedroom ɗin,amma idan ta koma mene zata cema Mummy? sanin bata da abin faɗa yasa ta ƙarasa baƙin ƙofar shiga bedroom ɗin cikin tsoro daya kamata ta tura kanta ciki,wata nauyayyiyar ajjiyar zuciya ta sauke ganin babu shi a bedroom ɗin, ƙarar watsa ruwa da taji ya tabbatar mata yana cikin bathroom,a hankali ta ƙarasa wajan dressing mirrow tare da saka hannu ta ɗauki parfume ɗinsa wanda yafi so,ta shiga fesawa a jikinta,nan da nan ƙamshin ya shiga cikin bedroom ɗin,ya haɗu da ƙamshin airfreshner da kuma sanyin a.c ya bada wani kalan ƙamshin mai daɗin gaske, ƙarar buɗe ƙofa da taji yasa tayi saurin juyawa a tsaye ta gansa ya juya mata baya hannunsa riƙe da ƙaramin pech ɗin towel yana goge ruwan dake sauka daga sumar kansa zuwa fresh skin ɗinsa,tana tsaye harya ƙarasu wajan dressing mirrow'n ya fara ƙoƙarin juna handrayer,duk abinda take yana kallonta sai dai sam ba ita ya bawa attention nasa ba,juyawa tayi zata bar ɗakin yyi saurin saka hannu ya jawota zuwa gabansa, kallonta yyi sama da ƙasa kafin ya lumshe idanunsa tare da sanya tafin hannunsa a saman wuyanta, ƙara matsuwa yyi sosai kusa da ita har numfashinsu na haɗuwa waje ɗaya cikin wata kasalalliyar murya wace take ɗauke da manufofi kala-kala yace.



_Uncle ne na kuɗi ne ka biya ka karanta cikin kwanciyar hankali, akan farashi mai sauƙi 300 for vip grp 600 asusun turo da kuɗi 0116886243 sulaiman naima s unioun, proof of payment 08119237616_
6/10/21, 1:04 PM - Buhainat: _17-18_

"kin iya gulma ko?" ya faɗi hakan yana zare hannunsa daga wuyanta daman yyi hakanne domin yaji zafin jikin nata kuma thanks God she is fine ba kamar jiya ba,baya yaja kaɗan tare da jan stool ya zauna ya fara busar da sumar kansa wacce take a jiƙe,bayan ya gama ya ɗauki wani lotion mai daɗin ƙamshin da kuma sauƙin zafi a jiki,har zai zare towel ɗin jikinsa sai kuma ya fasa,ba tare daya kalli inda take ba bare yasan ina take kallo yace .
"get out"
lumshe ido tayi sabida yadda muryarsa ta daki kunnanta,yatsun hannunta ta fara wasa dashi,a haka ta samu damar ware ƙaramin bakinta wanda yake ɗauke da jajayen laɓɓa tace.
"Mummy ne yace kazo"
shuru yyi mata kamar yadda bai motsa ba,haka itama bata fita ba kamar yadda yace,a ransa yake mmkin rashin kunyarta, anata ɓangaren kuma jira take taji amsarsa shiyasa bata fita ba,abinda bata sani ba indai Jalal ne ƙala bazai ƙara cewa da ita ba.
bayan ya gama shafa lotion ɗin a ƙirjinsa zuwa cikinsa ya fara zare towel ɗin dake ɗaure a waist ɗin sa,da sauri ta juya masa baya and she closed her eyes,hannu tasa ta dafe ƙirjinta dake bugawa sabida bata taɓa ganin kyakkyawar sura mai ɗaukan hankali kamar tasa ba,a hakanma Allah ya taimake ta ba taga tsarai cinsa ba,sai kwantacciyar sumar data gani ƙwance on his lap abin ya bata mmki,domin bata taɓa ganin suma a cinya ba sai a kansa.
Jalal duk miskilancinsa sai da ya kusa yin dry sabida yadda yaga ta tsorata abin ba ƙaramin dry ya basa ba,amma taurin zuciya da mislikanci irin nasa ko murmushi bai yi ba,sai ci gaba da shafa lotion ɗin yake a saman farar fatarsa,tsaki yaja kaɗan a zuciyarsa yace.
"tayaya zan bar wata taga jikina,wannan al'ƙawari ne daga zuciyata zuwa zuciyar dana aminta taga tsarai cina,amma ba wata middle class like Jalilerh ba"

duk wannan maganar a zuciya yake yinta, Jalilerh data tabbatar bazai magana ta sauke ajjiyar zuciya tare dajan ƙafafunta tayi waje ta barsa da mislikanci sa,tana fita yana gama shafa lotion ɗin body spray ya fesa a saman fatarsa,kana ya shafa wani mai a saman sumar sa,tare dasa cump ya ƙara ƙwantar da sumar ta sauka har wuyansa,wajan wardrope ya ƙarasa ya ɗauki farar singlet da kuma farin boxer ya saka a jikinsa,bayan ya gama ya ɗauki wata ɗan yar shadda getzner lemon colour,ya saka a jikinsa, a gogan adidas ya maƙala a hannunsa tare da saƙala farin bluetooth a kunansa, ohud mood ya fesa a jikinsa kana ya ɗauki farin glass ɗinsa ya manna a idanunsa, yana gama shiryawa ya kwashi wayoyinsa yyi waje.

A zaune Jalilerh ta samu Mummy ita da Mameey suna shira sai Abbou da dawowarsa kenan, ya zauna tare da fara kallon labarai b.b.c news, cikin sanyin jiki da kuma na muryar tace.
"Hello"
gaba ɗaya suka kalleta a tare kafin Mameey tace "ya naga ke ɗaya where is he?" ta tambaya tana leƙa bayan Jalilerh,ganin babu kowa kuma Jalilerh batai magana ba yasa Mummy faɗin.
"how is he? hope ba jikin nasa bane,dan ɗazo na samesa baya jin daɗi"

"bobo ne babu lfy? kuma shine baki gayan ba,bayan kinfi kowa sanin halin da yake shiga idan jikin nasa ya mutsa wannan ai sakaci ne dear,yanzu yana ina?"
kafin su ƙara magana yyi sallama cikin daddaɗar muryarsa mai cike da kamala, miƙewa Abbou yyi ya ƙarasu inda yake tsaye yace.
"bobona yaya jikin when ka kasance babu lfy?"
ya jera masa tambayoyi lokaci ɗaya, lumshe ido yyi tare da ware su a saman fuskar Abbou kamar yaro haka ya kwaɓe fuska sai kuma yyi hugging Abbou yace.
"i'm fine Abbou na,bana jin ciwo"
sumar kansa ya shafa tare da ɗan bubbuga bayansa cikin nuna jin daɗi yace "ma sha Allah, Allah ya ƙara sauƙi bobona" da "Ameen" ya amsa kafin ya ƙarasa kusan Mummy ya zauna yace "Barka da hutawa Mummyna"
hanci ta lakuce masa tace "naƙi na amsa,tun safe nake jimaminka sbd na sameka kana fama da ciwon kai yanzu kuma kace a'a"
murmushi yyi kaɗan wanda iya kacinsa saman labɓansa yace.
"eh Allahamdulillah sai yunwa"
cikin nasa ta shafa tace "ai dole kaji yunwa,rabonka da aminci tunda jiya da daddare shima kuma coffee da indomie,bobo tayaya rayuwa zata yiwo kanama kanka huran yunwa?"
langwaɓar da kai yyi gefe ba tare da yace komai ba,sabida yasan dukkan abinda zai faɗa baza ta taɓa ganewa ba,a duk sanda yaci abinci mai nauyi ranar baya ƙwana da lfy,shi kaɗai yasan abinda ke damunsa,babu wanda zai iya gayawa sirrinsa,babu wanda zai yadda ya bashi damar da zai fahimci rauninsa,yasan komai mai hucewa ne,daman haka rayuwar take,zai ci gama da zama da lalurar dake damunsa,idan yana da rabon samun lfy babu shakka shima zai zama mutum mai kuzari da kuma cikakkiyar lfy,zai zama na miji mai taƙama da kansa,amma yanzu bashi da wannan ikon shi ɗin kamar fankon asha na ne wanda bashi da wani amfani,idan lalurarsa bata warkewa bace zaici gama da zama a haka daga nan har lokacin da zai koma ga ubangijinka, ajjiyar zuciya ya sauke Lokaci da Mummy tace.

"mene kake tunani tun ɗazo ina magana shuru ko aƙwai matsala ne?"
Kafin yyi magana Mama tayi saurin cafe zan

6 / 41