Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

UNCLE NE Book 1,2,3 Complete Hausa Novel by Nimcey Sarauta

Author :  Nimcey Sarauta Category :  Romance

Chapter   19 / 41

54K to 57K   out of 120.1K words

suka nufi gida lokacin kusan 5:30.





A zaune ya samu Mama yana ganin ta yay saurin waro ido waje sbd gaba ɗaya ya manta da saton data bashi, haɗe rai yay tana ganinsa tace
"Allah yasa ba gwalmammiya mace ni ɗin, iyaye na basu haifi mayya ba,dake ni tambaɗaɗiyyace ni kawai babu sanu kawai sai na fara tambayarka abu, a'a wlh babu ruwana kaima kaji da kanka da hakkin da ka ɗauka,domin Allah na gama tamawa zanci tsire har albasa na yanka amma jibi hulaƙanci da yay min, a'a wlh babu komai"
da ido kawai ya kalleta tana gamawa ya shige part ɗinsa,
Mama ta bishi da kallo tace
"laaa wlh bai siyo ba,yau naji tsiya,wannan nanne irin abune ace dan bani da ko sisi ake wulaƙanta ni"
Nihila bata kula ta haura upstairs, Mama ta miƙe ta nufi part ɗin Abbou,a baƙin kofa taci karo da Mameey, Mameey tace "a'a Mama lafiya dai?" Mama tace
"to kini bau mijikin nazo gani idan da hali?" Mameey tace
"Mama yana shan tea ne" Mama ta riƙe haɓa tace a'a wlh babu ruwana meye kuma tea da wannan magaribar maza jeki min iso"
Mameey dawowa tayi tace
"yace ki shigo"
zama Mama tayi tace "sannu ku?"
Yace
"yawwa Mama ya ƙafar?" Tace
"yaushe mukai dakai bana da lafiya Kabeeru, a'a dan Allah kaima kada ka zama sallamamme mana"
kallonta yay yace
"i through jikin ne" Mama tace
"kai kasan wani turanci ni bani a wannan shashanci,daman cewa nayi wai anya kowa Jalalu jika nane ba'a sauya min wani ba?" Gaba ɗaya Abbou da Mummy suka kalleta fuskarsu ɗauke da zallar mamaki
"meye zaku wani tsareni da ido kamar wacce tai munafurci"
Abbou yace
"a'a Mama, meyasa kikace haka?"
Tace
"wlh Kabeeru dole na faɗa,yaro baya gani na daraja ga alƙawarin ƴan nefa,salin alin mukai magana dashi zai siyon abu amma ya shigo hannu na dukan cinya" ajjiyar zcya Abbou ya sauke yace
"a'a Mama kin san yanzu ya shiga busy sabida an kusa zaɓe,so duk yawanci abubuwa mantawa yake dasu,kinga nima yanzu ina son magana dashi amma dole nake ɗaga masa ƙafa"
Mama ta miƙe tsaye tace "au haba?"
Mameey tace
"eh Mama gaba ɗaya bai fi wata biyu bafa"
Mama tace
"kice gaf da azumi kenan ko?"
Mameey tace
"ehmn"
waje Mama tayi tace
"to Allah ya taimaka"..

Ana kiran magrib ya fito sanye da milk ɗin jallabiya bai tsaya jiran kowa ba ya nufi masjid,a tare suka dawo da Abbou dasu Aryan,a hanya dai jan Jalal da magana Aryan yake amma yay masa banza,a parlour ya samu Mummy yace
"a kawomin abin buɗe baki"
da
"to"
Mummy ta amsa kana ta miƙe tsaye ta nufi ɗakin su Nihila, ƙwance ta samu Jalilerh idanunta a rufe kamar mai bacci kallon Nihila wacce ta gama sanya duguwar rigar baccinta tace
"sa hijab ki kawai bobo dinner"
kai ta gyaɗa kana Mummy tai waje,hijab ta ɗauka tayi waje tana fita Jalilerh ta miƙe tsaye tana mai dafe ƙirjinta dake buga mata,hannu tasa ta share hawayen fuskarta.
A ƙasan carpet ta sameta hannunsa riƙe da Cork yana sha, murmushi tayi tare da yin sallama,kansa a ƙasa ya amsa Batai magana ba ta juya zata fita yace
"ki ramin ita"
Nihila tace
"wa?"
Idanunsa ya ɗago ya sauke a fuskarta saurin janye nata tayi sbd yanayin data gansa,wani guntun murmushi yay yace "Jalilerh..
tana shiga ta samu Jalilerh tsaye ta rungome hannayen ta,huce ta tayi sai data gama shiryawa ta ƙwanta can ta kalli Jalilerh tace
"kije bobo na kira"
zaro ido waje tayi tare da fara rarraba idanunta kafin tai magana Imran ya leƙo cikin bedroom yace
"en matan Uncle, Uncle na jira"
idanunta na kawo ruwa tace
"ayya yaya kace bacci nake..





_UNCLE NE isn't free is for sale 300, account number 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616_




By
NIMCYLUV
6/20/21, 9:26 AM - Buhainat: Imran ya ce" meyasa? Bayan idonki biyu?" Shuru tayi domin ita kanta bata san dalili ba ya juya yace
"A'a babu ruwa na nikam, ƙilan ya ɗaga maki ƙafa,amma ni sai nai laifi"
Yana faɗin hakan ya fice,baby hijab ta ɗauka ta sanya a saman blue ɗin kayan baccin data saka kana ta sanya plat shoe ta nufi fita sauka, Nihila dake ƙwance ta gyara kwanciyar ta tace
"Kibi a hankali"
Tsayawa tayi tana tunanin maganar Nihila kafin taja jikinta zuwa downstairs,babu kowa a main parlour hakan yasa jiki a sanyaye ta nufi part ɗin samarin gidan,kusan duk sun rufe part ɗin su nasa ne kawai ya rage a buɗe.
Cikin siririyar murya tace
"Salumualak"
Shuru babu amsa hakan yasa ta fahimci babu kowa a parlour'n, lumshe idanunta tayi sbd sanyi da kuma ƙamshi parlour'n daya daki hancinta,jiki a saɓule ta nufi cikin bedroom ɗinsa,yana zaune tsakiyar bed ɗin dake ɗakin hannunsa riƙe da hisilin muslum,tace
"Salamualak" ba tare daya kalleta ba yace "wasalamu alaiki" tsayawa tayi daga bakin ƙofa kanta a ƙasa,ta gefen ido ya kalleta can ya miƙe tare ya ajjiye hislin musulm ɗin hannunsa, ƙara zama yay akan sofar dake kusan bed ɗin yace.
"Fita idan ba zaki shigo ba"
Jin haka yasa Jalilerh ta ƙarasa shiga tare da zama a gefen ƙafafunsa ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Shuru yay mata shima ba tare da yace komai ba,sama da 20minutes tana zaune shima haka yana latsa wayarsa, ɗan gyara zaman tayi tace.
"Uncle gani"
Shuru yay mata sai data ƙara cewa
"Uncle" sannan ya ajjiye wayar tare harɗe hannayen sa a ƙirji yace
"Kina da sha'awar karatu?"
Da sauri da ɗaga kai ta kallesa sai kuma tayi ƙasa da kanta tace
"Eh Uncle" kai ya ɗaga yace
"Ok which school the you like?"
Juya fararen idanunta tayi kafin tace
"University of California Merced (Stanford University, officially Leland Stanford Junior University,[12][13] is a private research university in Stanford, California. Stanford was founded in 1885 by Leland and Jane Stanford in memory of their only child, Leland Stanford Jr., who had died of typhoid fever at age 15 the previous year.[2] Stanford is ranked among the best universities in the world by academic publications.[14][15][16][17][18] It is also one of the top fundraising institutions in the country, becoming the first school to raise more than one billion dollars in a year.[19])"
Saurin zaro ido waje yay da ɗan mamaki a fuskarsa yace
"Lalle sai ita"
Da sauri tace
"Uncle nafi sonta itace ambition ɗina,ban jin idan ba ita ba zan so wata daban"
Miƙewa tsaye yayi tare da faɗin
"Ok hqr da karatun,nama fasa gaba ɗaya"
Idanunta na kawo ruwa tace
"Please Uncle"
Zama yay kan bed yace
"Daman ban niya ba,dole akai min" kuka ta sanya masa tare da kwanciya a saman carpet tana birgima,zaro ido waje yay yana mamakin yadda kuka bai mata wahala,gaba ɗaya ta sauya a ƴan kwanakin da yay bai ganta ba,ta ƙara girma sosai ga wani hankali daya zo mata,komai na girman ƴar mace ya gama bai yana a jikinta,amma kallo guda zakai mata ka fahimci zallar ƙuruciyar da take tare da ita,sam bata da wayo komai a shagwaɓe take yinsa,babban abinda yafi bashi mamaki yadda lokaci guda ta bar shisshige masa ta daina raɓar jikinsa.
Ajjiyar zcya ya sauke yana mai ƙara kallon yadda take kuka da birgima.
Idanunsa yaja ya rufe wani wahalallan bacci ke damunsa ga kuma yadda take kuka indai yaci gaba da sauraran kukan tabbas kansa sai ya amsa masa.
A hankali ya ƙarasa inda take ƙwance ya durƙosa tare da sanya hannunsa ya ɗago ta zaune, hannu yasa ya tallafo haɓarta murya can ƙasa yace.
"Mene?"
Jikinsa ta faɗa tare da sanya sabon kuka, shuru yay mata yana sauraren yadda take kukan da dukkan ƙarfin ta, miƙewa yay da ita har zuwa parlour'nsa
Yana zuwa ya ƙarasa saman sofa ya zauna, hannunsa yasa cikin sumar kanta yaji laushi gwanin sha'awa,can yace
"Shuru"
Fuska ta kwaɓe tace
"Uncle kace zaka kai Ni,ina so"
Yadda tai maganar kamar yarinyar goye yasa ya ɗan saki murmushi mai sauti yace
"da gske?"
Da sauri ta ɗaga masa kanta alamar
"Eh"
Lumshe idanunsa yay kafin ya buɗe yaja numfashi yace
"ok stop cry"
shuru tayi tana sauke ajjiyar zcy,shima shuru yay yana ɗan ƙara shigar da ita jikinsa
Kai ta ɗaga ta kallesa tace
"Uncle please"
Ta faɗa tana jan beard ɗinsa, kallon ta yay kafin ya ɗan janye jikinsa daga nata yace.
"Zaki,but not know"
Baki ta turo gaba tace "sai yaushe?"
Baya yay ya ƙwanta jikin sofar yana shafa sumar ƙasa yace
"Sai nai aure,sai na kaiki wajan Matana kinga basai kinyi nisa da dangi ba"
Shuru tai masa bata ƙara magana,har ya kula kamar bata mood ɗinta,hancinta yaja yace
"What!?"
Raurau tayi da ido tace
"To yaushe zakai?"
Cireta yay a jikinsa ba tare daya tanka ta ba yay shigewarsa cikin bedroom ɗinsa,yana shiga ya ƙwanta yaja duvet ya rufe jikinsa,kana ya kashe hasken ɗakin
Da ido kawai ta rakashi harya shige,kuka tasa ita kaɗai sai da tayi mai isar ta sannan ta miƙe ta nufi waje.
A hanya taga Aryan tsaye da ido kawai yake kallonta harta shige,a main parlour ta samu Abbou zaune yana shan tea,sunkuyar da kanta tayi tana wasa da hannunta
Murmushi yay yace
"Dear daga ina?"
Juya idanunta tayi tace
"Uncle ya kira ni"
Abbou yace
"ok goodnight"...



Washegari da yamma
Governor Mubarak Yahya cibo ne zau ne shida Lamir suna shan kayan fruit, Lamir yay murmushi yace
"yanzu lokacin hutunsa ne,ranar da yake muradi ranar da yake jira tazo masa,muma ita muke jira a ranar zamu tar watsa farin cikinsa,a ranar zamu tarwatsa haɗin kan da suke dashi a gidan,a ranar zamu wargatsa komai nasa,tabbas zamu shayar dashi mamaki,mamakin irin wanda ba'a taɓa bashi ba,zamu bashi ƙyauta,gift ɗin da bazai taɓa mantawa da shi ba a rayuwarsa"
Lamir ya ƙare maganar yana saki wata dryar, Mubarak Yahya cibo yace
"A barshi ya huta,yaji daɗin rayuwarsa yay komai cikin farin ciki"
Lamir ya ce
"wannan ranar zanfi kowa farin ciki,a kuma wannan ranar zan ƙara sa cika muradina ta hanyar da babu wanda yay tunaninsa"
Hon Faisal Lawan yace
"Kai Lamir babu ɗan iska irinka,wlh muguntar na sani nishaɗi kai tantiri ne na ajin farko,baka da tausayi ko imani"
Lamir ya ajjiye bottle water ɗin hannunsa yace
"Ai munsan takan siya,nifa ƙadangaren kan tulo ne dole a barni a yadda aka ganni"
Mubarak Yahya cibo yace
"Wannan gsky ne,amma yaya kukai dashi Aryan ɗin?"
Lamir yace
"wannan na sai tashi a hanya,daga ko yaushe zaka iya jin kiransa a waya,shi kuma dashi za muyi amfani wajan ruguza rayuwar Wannan shegiyar yarinyar"...

A can Birnin nufar Papa durƙoshe gaban Uwa sundu yace
"Jinjina ga uwa sundu ban gama gasgata zancen ki ba sai jiya,nayi mafarki wanda nake da tabbacin zai zama gsky,sbd yadda abubuwa suka dinga zuwarmi ɗaya bayan ɗaya,abu mai cike da almara,tabbas jikanyata zata dawo gareni,kuma zan haɗata da mutumin da zai ma garkuwata,wanda zai zama jigon wannan birnin"
Uwa sundu ta kyakkyata dry kafin tasa hannu ta daki wani dotse nan take dotse ya fitar da wani baƙin hayaƙi,hayaƙin yay sama ya ɓace ɓat
Kana tasa hannu ta buga wani ƙaho shiga jini yana zuba tace.
"Mun daɗe da fara farautar rayuwarsa tun yana jariri,za muci gaba da hakan har lokacin da burinmu zai cika,wannan hayaƙin da jinin sune makaman mu a garesa,tabbas zai halaƙa tunda ya nemi shiga gonar da bana sa ba"
Papa ya miƙe tsaye yace
"Dukkan abinda uwa sundu tayi dai-dai ne,ina goyan baya"
Yana faɗin hakan ya doƙa mata ya fita.
A harabar gidan yaci karo da Jafar shida zulfa,da sauri tayi bayan Jafar tana ɓoyewa, Jafar ya kalli mahaifin nasa yace
"Gaisuwa ga shugaban nufar"
Wani kallo yaywa Jafar yace
"Ina kaje shekaran jiya" ba tare da komai ba Jafar yace
"naje karɓar magani ne" kallonsa kawai yaya kana juyawa yay shigewarsa cikin tirakarsa,yana zuwa ya samu Shila zaune tana ganinsa tace
"Barka da shigowa shugaban nufar"
zama yay yana hura hanci yace
"Yawwa an gaida matar shugaban nufar.

Ranar juma'a juma'a da safe duk jama'ar gidan suna zaune a main parlour ana hira, Jalal na can gefe yana sauraren wa'azi a cikin wayarsa ya sanya airpies sbd hayaniyar jama'a, Mama ta kalli kowa ta taɓe baki kafin tace.
"Wai Kabeeru baka da iko da gidan ka ne ban sani ba?"
Gaba ɗaya parlour'n sukai shuru suna kallon Mama, Abbou yace
"A'a,me kika gani Mama?" Mama ta tura ɗan kallabin dake ganta,furfurar dake ganta ya bai yana tace
"Duba zabga zabgan masari a gabanka,ga wasu ƴan matan biyu gabanka,shin kai baka tausayin kanka kenan,kai ta ciyar da ƙartin banza, a'a wlh wannan sangarta tace Kabeeru"
Cike da rashin fahimta Abbou yace
"Ban gane ba Mama,wani abun sukai bana da labari kuma?"
Dakakken goran data daka ɗazo takai bakinta tare da faɗin
"Me kuwa za suyi min Kabeeru? Ni ina da hankali ko sumin ba kulasu zan ba,ina magana akan yadda ka zuba masu ido shin kai baka sha'awar ace yau an haifa maka jika?"
Ajjiyar zcy Abbou ya sauke kafin yace
"Ai Mama ina jin sai munje ƙauye kin zaɓa masu"
Mama ta washe baki tace
"Wlh daka faranta min,ga ƴar ƴan Zuwaira nan duk sun girma, musamman babbar Zaituna zata fi dacewa da Jalalu"
Dan jim Abbou yay kafin yace
"Mama kibar maganar Muhammad"
turo ɗan kwali tayi gaba tace
"dalili bani hujja yanzu,bashi da lafiya ne ko mene?"
Abbou yace
"eh sabida alrdy yana da matar aure...




_is not free is for sale 08119237616_





By
NIMCYLUV
6/20/21, 9:26 AM - Buhainat: 56-57
6/22/21, 9:26 PM - Buhainat: *UCL NE*
*BOOK 2*

58-59


*Littafin UNCLE NE littafin kuɗi ne akan farashi mai sauƙi, zaka karanta book 1,2,3 akan naira 300 mai sun vip inda zai samu sauran littafai na 600 dan,zaka iya turo da kuɗin ka ta wannan asusun 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616*





Mama ta kalli Abbou tace "eyee haka akai bani da labari Kabeeru?, yaushe kai ma ka zama sallamamme wanda bai son laifin yaransa? Fisabilillahi ace samari manya kuma ƙarti a gidanka amma kaƙi aurar dasu, a'a wlh wannan sangarta ce ban taɓa ganin inda akai wannan abun kunyar ba,da ƙauye ne duk suna da yara ƴan dugui dugui gwanin sha'awa"
Kafin Abbou yace komai Mameey tace
"Eyee! mata aka samawa yaron namu babu labari Abbou Jalal?"
Da ido Abbou ya kalleta ba tare kuma daya bata amsar maganarta ba ya kalli Mama yace
"Kiyi haƙuri in sha Allah da zarar komai ya lafa duk zasu lalubu matan auren"
Taɓe baki Mama tayi tace
"Dadai yafi,amma shi wancan basa mudan ai sai dai a sama masa,dan naga alama kamar ma tsoran matan yake,bazai iya tsayawa da mace har yace yana sonta ba,oh ohhh ohhhh banda ma zamani ina zaka kalli indon mutum kace kana sonsa kuma ya tsaya ai sai gudu,amma yanzu abin naga kamar wani gasa ne,haka jiya a talabijin naji ana ta faɗar wani abu kai abindai sai dai su, hadda runguma fa"
Ta faɗa tana ɗan saka hannunta a haɓarta alamar mamaki
Murmushi Mummy tayi a zcyarta tace
"Tsofa labari"
A fili kuma tace
"Mama wannan ai ɗari'arsu ce haka,kinga Film ɗin hausawanmu babu haka,so ko wanne yare aƙwai al'adar su da kuma ɗabi'ar su,da ga Kennywood ɗin zuwa India duk daban daban ne"
Mama ta ya tsuna fuska tace
"Tirr da wannan ɗabi'ar mutane kamar tsirara" kafin ta kuma kallon Abbou tace
"Yawwa! Nace wacce mata ka zaɓawa Jalalun?"
Miƙewa Abbou yay ganin lokacin masallaci ya kusa yace
"Wata ce,soon za kiji komai ai"
Mama ta kwaɓe fuska tace
"Meya suun kuma?"
Aryan yay dry mai yawwa kafin yace
"Wai da wuri,ai Abbou daka faɗa mana domin mu fara shirin ganin Antyn tamu wacce tayi dacen samun zan kaɗeɗen saurayi irin yaya"
Abbou bai ƙara magana ba sai kallon Jalal da yay wanda ko inda suke bai kala ba bare su saka ran zai tanka maganarsu yace
"Muhammad lokacin masallaci yayi fa"
Idanunsa ya buɗe tare da saukesu akan Abbou bai ce komai ya miƙe tare da nufar part ɗinsa, Mama tace
"Allah ɗaya gari babban"
Sarai yaji maganarta amma yay gaba abunsa, Aryan ma miƙewa yay tare da shigewa nasa part ɗin ya rage daga Mama sai Mummy da Mameey, Mameey tace "Mummyn Jalal me za'ai a gidanne yau?"
Mummy tace
"Haba Mameey duk abinda kikai dai-dai ne,tunda yau friday duk samarin gidan suna nan"
Kai Mameey ta ɗaga tace
"Bari naje wajan Laure idan yaso taje anjima ta shigo,kin san indai tasa hannu to Jalal da Abbou Jalal baza su ci ba"
Tana faɗin hakan ta nufi hanyar kitchen Mummy kuma tayi upstairs part ɗin su Jalilerh.
Jalal na shiga part ɗinsa ya nufa cikin bedroom kai tsaye ya shige cikin bathroom yana zare ƴar ƙaramar singlet ɗin jikinsa da kuma wando three gaiter daya saka, shower ya sakarwa kansa yana mai lumshe idanunsa,maganar Abbou ce ta faɗo masa,mai yasa har yanzu babu wanda yake ƙoƙarin fahimtar abinda yake damunsa ne? Mene yasa har yanzu babu wanda zai iya tararsa ya tambaye sa dalilin yasa bai son yin aure? Ko kuma hakan da akai masa yana nuni da suna son suga hankalinsa ne? Wa zai aura? Zata iya fahimtar sa kamar yadda ya fahimci kansa? Zata iya zama dashi a haka? Ko kuma ba zata iya ba? Wanne kallo zatai masa idan ta san bazai iya biya mata buƙata ba?zata raina sa ko kuma zata tausaya masa ne?mene dalilin daya sanya za'a takura rayuwarsa akan yay wani aure ne?
Yana da tabbacin sun san shi ba yaro bane indai yana buƙatar aure zaiyi ba tare da an takurasa ba
Babu wanda ya isa ya sanya shi yin aure ba tare da yay niyya ba,
Koda an tilasta shi yay auren, tabbas matar zata zama kayan wanki ne wanda basu da ranar wanke wa,
Iska ya fesar mai zafi ta cikin bakin lokacin guda yanayinsa ya sauya, shower ya kashe,tare da yin brush ya ɗaura alwala,yana fitowa ya nufi dressing mirror lotion ya shafa mai ɗan sauƙin zafi, tare da fesa body spray a saman fresh skin ɗinsa,wajan wardrobe ya nufa wata shadda majic ya ɗauka mai kalar sky blue tare hula mai kalar light blue,cikin sauri yake komai sbd ganin lokacin na neman yanke masa,black half shoe ya sanya,tare da ɗaukan paryaer mat ya fita a ɗakin
Yana fita parlour yaga babu kowa kai tsaye ya shige part ɗin Mama zaune ya sameta tana faman daka goro, a kanta ya tsaya tare dayin shuru yana tunanin ta inda zai fara,dan idan yace cikin ɓacin

19 / 41