Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Hadarin GABAS Book Complete Complete Hausa Novel by Nazeefa Sabo Nashe

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 32

66K to 69K   out of 93.3K words

 Ma sha Allah ka ga angon y ar riga. Allah ya tabbatar da alheri yasa a ce gwara da aka yi&  Cak ya tsaya da numfashinsa yana zubawa Jay ido cikin wani irin firgita ya ce  Y ar riga kuma?  Eeh, Y ar riga In sha Allahu yau za a d aura muku aure da ita, ita ta dace da kai. Na tabbata ba zata raina abinda Allah ya bamu ba&  Zuciyarsa ta dinga"

wani irin bugu& .

Yanzun ma bugun zuciyar tasa take yi. Musamman da Didi ta  d ora hannunta a saman kafa darsa hakan

yasa ya dawo daga tunanin da ya lula. Ya bu de idanunsa da suke fitar da maik on hawaye yana kallon Didin. Itama kallonsa take. Tana furta  Tunanin me kake Moddi? Ya ja ajiyar zuciya kafin ya girgiza Kai ya ce  Komai ma Didi. Didi ta jinjina Kai kawai kafin ta mayar da hoton y ar riga ta ajiye tana dubansa ta furta  Goben dai da wuri zaka kawo su Magajiya ko? Don Sam bana son zaman ka daita. Sannan ina son ka fita ka samo almajirai da zasu kwana suna saukar kur ani a gidan nan. Don na lura sosai Moddi lamarinka sai na dage da addu a. Ya jinjina Kai yana furta  Za a samo Didi. Cikin muryarsa take Jin wani irin weakness. Ya mik e ya fita daga d akin a hankali. Zuciyarsa kuwa tunanin y ar riga ne kawai a cikinta.

Yana fatan Allah yasa bata tafi da Jin haushinsa a ranta ba.

"Da Kansa ya saka a samo Malamai ya kuma bi shawarar Didi bai gayawa Safna zancen tashin ba, sai a"

"kashegarin ranar. A d akinta ya sameta fitowarta daga wanka kenan tana Shafa mai. Ya bita da kallo yana mamakin wata irin k iba da take sake yi Sam bata controlling jikinta. Ta  daga Kai tana kallonsa kafin ta ja mayafinta ta rufe jikinta don ita kanta ba zata so ya ganta ba kaya ba. Gaba d aya halittunta sun canja. Gefen gado ya samu ya zauna kafin ya sauke idonsa kan ta ya furta  Ki shirya za mu unguwa. Ta saki murmushi tana furta  Tom, ka jira ni a waje, yanzu zan fito. Bai sake kallonta ba ya fice daga bedroom D in. D akinsu Amani ya nufa. Sai da ya yi nocking k ofar sannan Amani da take tsaye hannunta rik e da comb tana taje kanta ta furta  Mama Talatu shigo mana. Idanunta ya sauka akan na Dada da yake tsaye yana kallonta da sauri ta janye nata idanun sanda yarda gabanta ya tsananta bugu. Shima janye nasa idon ya yi yana furta  Ku shirya zamu tafi. Ta d an waro ido tana furta  Yanzu kuma Dada? Ai basu gama kai mana kayan ba. Bai amsa mata ba ya fice daga d akin. Ta bi shi da kallo tana sake shak ar k amshin turarensa. Sai kuma ta saki murmushi ita ka dai tana tab e baki fa da take son yi da zuciyarta, amma ta kasa yarda laifin na zuciyarta ta ne. Sanda Iman ta fito ta gaya mata Dada ya ce su shirya wani irin farin ciki ne ya lullub eta ta tsani gidan da duka abinda yake cikinsa, ta tsani Safna, tana fatan komawarsu sabon gida yasa zasu koma da kowane bak in ciki ba, banda ma maganar aurensu Didi ta dakatar ita da zata fi so ta yi aurenta ta huta. Tsaf suka shirya cikin kyakykyawar shiga yau Amani ma hijab ta saka kamar Imaan. Suka fito parlorn. Safna na ganinsu ta ha de fuskarta sosai tana jin wani bak in ciki. Kafin ta kalli Moddi ta ce  Da su za a ne? Madadin amsa mata da baki, d aga mata kai kawai ya yi. Ta saki wani k aramin tsaki tana hararar Moddin k asa k asa. Ta lura kwana biyun nan wani Izza yake ji Amma zata yi maganinsa. Wata irin mota mai masifar kyau shiga. Tunda kuma ya fara driving bai ce komai ba. Baka jin komai sai surutun Amani da Ya cika motar. Zuciyar Safna a tunzire take da Amanin sosai. Ga Moddi bai gaya mata inda za su ba. Tafiyar sam bata mata ba, don haka kawai take jin gabanta na wani irin masifar fa duwa. Don haka cikin hassala ta ce  Wai ina za mu ne?  Unguwa Ya bata amsa ba tare da ya ko kalleta ba. Sai ta ja baki ta tsuke a ranta take lailayo ashar tana zuba masa. Amani tana baya farin ciki duk ya cikata jin Dada bai gayawa makirar matar inda za a ba. Da alama bata san ina za su ba, bata San ma za"

su koma sabon gida ba. Hakan yana nufin akwai Daru kenan&

Bai tsaya ko ina ba sai a harabar gidan. Safna ta dinga Ware ido tana kallon gidan da ya yi masifar tafiya

"da imaninta. Sai dai gefe guda wani irin tsoro ne ya shigeta. Bata manta garga din Bokanta ba.  Kada ki sake ki tare a sabon gidan nan sai kin zo mun Miki aiki, idan ba haka ba komai ma zai iya faruwa. Aikinmu da duk abinda kike tak ama da shi zai warware& . Jikinta Har rawa yake da tuna hakan. Don haka da sauri ta kalli Moddi ta ce  Ina ne nan? Ba dai sabon gidan mu ba ne? Ba dai tarewa muka yi yau ba? Ya bita da kallo yana mamakin sauyawar yanayinta. Madadin amsa mata sai ya saka kawai zai shiga gidan. Da sauri ta ja hannunsa tana girgiza masa kai jikinta na rawa ta furta  Kada ka shiga Imaam, wallahi akwai matsala, ya zaka kawo ni gida ba tare da sani na ba. Me kake nufi ko zuwa muka yi mu gani mu koma. Ya  d an janye hannunsa yana furta  Mun dawo kenan, akwai matsala ne? Saura k iris fitsari ya zubo mata. Ta wani irin zaro ido tana girgiza kai ta furta  Me? Wallahi ba zan shiga ba, wannan ma ai rainin hankali ne, ta ya zaka ce min na dawo gida ba wani shiri& . Ya  d an k ura mata ido kafin ya saki wani murmushi"

"Ya furta  Shiri? Shirin me zaki yi? Duk wani shiri na gama shi a gidan nan, akwai duk abinda za ki buk ata a"

"ciki. Didi ma tun jiya ta tare&  wannan karan fitsarin sai da ya zubo. Ta runtse ido tana tuna sauran maganar da ta zauna mata daram a kwanya. Ta haddace ta kamar karatu.  Barin Uwarsa ta zauna inuwa d aya da shi, ina tabbatar miki kamar shigar ki matsaloli ne ba matsala ba. Dole ki raba Uwarsa da gidan sa&  Idan bata manta ba shine dalilin da yasa ta dinga zubawa Didi rashin kunya da rashin mutunci har ta gaji ta tattara ta bar gidan. Sannan yanzu ya gaya mata wai Didi na ciki. Kai ina ai ba ma zai yiwu ba. Gaba d aya duk ta rikice hakan yasa Moddi ya tsaya yi mata kallon mamaki su kansu su Amanin kallonta kawai suke. Har Moddi Ya k arasa gabanta yana murmushi ya ce  Akwai sauran shiri ko? Ya fa da k asa k asa sai kuma ya girgiza kai  Kin shigo kenan Safna. Idan kuma kika fita nan da kwanaki masu yawa ma ba tare da izinina ba, ina tabbatar miki a bakin aurenki. Ta ji wata irin hajijiya tana neman kada ita. Tana kallon su Amani suka bi bayansa Amanin na sakin dariya k asa-k asa. Sai da ta dafa bango tsabar yarda taji ana wujijjigata kada fa mafarkinta ya tabbata kada wannan gidan ya zame mata BAK IN GIDA& ganin Sun mata nisa yasa da sauri ta mik e ta bi bayansu. Tana aikin turawa Malaminta Message. Hannunta duk rawa yake& a haka ta isa babbar k ofar da taga sun shiga. Inda anan babban parlorn da ya raba sassan su da na Didi yake. Didin na zaune a saman kujera su Umma Tee zagaye da ita. Amani da sauri ta fa da jikin Umma Tee d in. Duk murna ta gama bayyana a saman fuskokinsu. Suka d ago suna kallon Safna da yake tsaye kamar ruwa ya ci ta. Sai fidgeting yatsunta take. Didi ta saki wani murmushi tana furta  Maraba lale, shigo mana Safna. Wani abu ya dunk ule mata a zuciya sai kawai ta juya da sauri ta nufi d aya k ofar da ta tabbatar nan ne part d inta. A zafafe ta mayar da k ofar ta kulle tana sakin huci da wani irin Zare ido. A tsorace take ta tsorata da komai ma, idan ba kallon tsoro ta yiwa Moddi ba, sai taga kamar kallon tsana yake mata. Da wani irin hanzari ta fara kiran wayar Malamin nata. Bugu guda ya d aga don shima yaga message d inta.  Safna kada ki shiga gidan nan, idan kika shiga komai ma zai iya faruwa, idan na ce komai ina nufin komai, kada ki shiga& . Safna ta runtse ido tana furta  Na shiga Malam, Na shiga ka gaya min ba abinda zai faru& . Daga d aya gefen Malam ya ce  Akwai Matsala, idan zai yiwu ki fito yanzu tun kafin abinda ake gudu ya faru& .  Malam ba zai yiwu na fito ba, ya ce idan na fito a bakin aure na& . Muryarta ta tsaya cak ganin Moddi a tsaye a gabanta yanayinsa ya nuna ya ji duk abinda ta ce. Don kallonta yake da birkitattun idanunsa da suka bayyana tsananin fitinarsa da rashin mutuncinsa, kamar"

kallon farko da ya fara yi mata sanda suka fara ha duwa. Hantar cikinta ta ka da& .

JIKAR NASHEHADARIN GABAS& ..

26.

NAZEEFAH SABO NASHE&
'

8033748387.

BRIGHT PENS 2nd batch..

 Da wa kike waya? Ya yi amfani da bu daddiyar murya wajen tambayarta. Murya bata mata kama da ta

"Moddinta da ta sani ba, wani ne wannan daban, da ya jirkita zuwa wata halitta mai furgutarwa gareta. Bata tab a ganinsa a wannan yanayin ba don haka razanar da ta shiga ba ka dan ba ce. A fusacen Ya sake cewa  Ba kya ji ne? Ki yi magana mana& . Ko sai na bayyana Miki wanene ni? Ta ha diye wani yawu sannan cikin muryar da ta bayyana rashin gaskiyarta zalla ta furta  Da k awata nake fa, da wa zan yi waya.  K arya kike. Ya fa da direct yana kallon cikin idonta. Wata irin tsanarta yake ji a ransa. Ta sake tsorata da yanayinsa don gani take zai iya kai mata duka.  Ka yiwa girman Allah ka kyaleni Imam me na yi maka ne? Cije leb ensa ya yi sai kuma ya wancakalar da ita gefe yana jin idan har ya cigaba da tsayawa kusa da ita zai iya zama ajalinta, a yarda yake jin zuciyarsa na wani irin zafi& . Da wani irin sassarfa ya fita daga d akin. Sai sannan Safna ta ja ajiyar numfashi ta shak i iska. Kafin ta furzar da huci. Wani irin zafi take ji a ranta. Ita yau Imaam ya yiwa haka? Ta cije bakinta wasu hawaye da ta tabbatar na bak in ciki ne suka zubo mata. Ta zauna tallafa da kumatunta tana jin tunanin da yake cikin zuciyarta shine kawai abinda ya kamata ta yi. Ba dai burin y an uwan Moddibo su tozarta ta ba, burinsu ya yi aure ya haihu zata biyo musu ta yarda suke so. Wannan hawayen ta rantse ba zata zubar da su a banza ba. Da wani irin zafin nama ta shiga kiran Lady boss. Bata wani b oye mata komai ba, ta zayyano mata abinda ke faruwa. Cikin mamaki Lady Boss ta furta  Kan Uba! Shi Imaam D in ne ya aikata miki haka? To me ya shiga kansa?  Rashin mutunci, ko na ce Uwarsa da y an uwansa suma sun je sun yi nasu k ulunboton to wallahi wannan karan na shirya musu zan tabbatar musu ni gaba nake da su a iya shege, zan b ata musu sunan dangin da suke alfahari da shi, da ina jin ba zan iya aikata abinda Alwan ya saka ni ba, amma yanzu"

"zuciyata tana jin zan iya fin haka ma, zan iya sakawa Moddi ya yi zina da Uwarsa ma ba y arsa ba. So nake"

"na samu Makamin da zan hana shi aure. Na shirya wannan karan Lady Boss, kuma Didi ko da bala i sai na"

"rabata da D an nata, sai ta gwammace bata ma haifeshi a duniya ba& . Lady Boss da take jin komai ta saki dariya ta ce  Yanzu za ki iya kenan da kika ji Uwar bari, dama can ai ke kika saka tausayinsa a ranki da kishin ba kya son Ya kusanci wata matar. Idan banda haka Uwar me ye a cikin Uba ya yi zina da y ar sa, y ar ma da ba taki ba, y ar da ba kya so. Ai ko da Uwarsa aka ce ya yi Ban zata za ki yi wannan da dewar baki aikata ba. Riba biyu fa kenan ga ku di ga b ata masa suna. Safna ta ja ajiyar zuciya tana furta  Ki jira nan da kwanaki ka dan za ki ji dadda dan labari, zan saka zur ar Lamid o a cikin Bak ar rayuwa, da sai sun gwammace ba su takale ni da fa da&   Bana jin ki, na San za ki iya. Lady Boss ta fa da. Safna ta Zare wayar kafin ta sake mayar da kiran kan Malaminta. Ya tabbatar mata zai yi aikin da take so, zai kuma aiko mata da kayan aikin ta birne a cikin gidan inda kowa ba zai ganta ba. Amma ta tabbatar a sanda zata yi"

aikin kowa na barci cikin tsakiyar dare. Ba shakka ba komai ta ce ta amince& ..

"Da tafiyar sassarfa Ya koma sashen Didin, inda ya bar y an uwansa. Yau kam zuciyarsa fresh yake jinta,"

"cikin tarin soyayya da k aunar y an uwansa. Kamar wani labulai ne aka yaye a cikin zuciyarsa ya bu de idonsa daga duhun da ya mamaye ganinsa. Ya dinga Jin abubuwan da Ya aikata bai kyauta ba. Jikinsa a sanyaye ya zauna daf da Didi da Kan Amani yake samanta. Tana sosa mata gashin. Idanun Amanin a lumshe tana shak ar k amshin Dahdan.  Zan yi magana da ku, yaran nan su bani waje. Moddi ya fa da cikin wata irin Husky Voice da take d auke da karyewar harshe mai da din sauraro. Duk yaran wajen suka mik e, banda Amani da ta yi kamar barci take. Ta gefen ido ya kalleta kafin ya furta  Ke ba zaki tashi ba ne? Don ya san sarai ba barci take ba. Idonta ta sake lumshewa sai kuma ta mik e daga jikin Didin ta tafi cikin d akunan da suka kasance nasu. Moddi sai da ya ji rufe k ofarta sannan ya mayar da kallonsa kan y an uwansa.  Da ku zan fara, Don Allah idan da Wanda yake rik e da ni a ransa ya yi min uziri Ya yafe min.. Ba Wanda bai zuba masa ido a wajen ba cikin wani irin tsananin farin cikin dawowar d an uwansu cikin hayyacinsa. Didi kuwa murmushi take saki hannunta cikin na Moddi da ya damk e sosai. Tana jin yarda jikin nasa yake rawa.  Mun yafe maka. Shine abinda suka dinga fa da. Sai kuma ya zube a gaban Didi. Ya kama hannayenta kasa furta komai ya yi sai hawaye da ya fara zuba sharrr daga idonsa. Didi ta kama shi tana girgiza maka kai.  Ban tab a rik e ka da komai ba Moddi, na yafe maka abinda na San ka aikata da Wanda ban sani ba&   Na amince Didi zan yi aure, zan auri duk matar da kike son na aura na amince ko gobe ki d aura min aure&  zallar farin cikin da zuciyar Didi take ciki ta kasa b uya a saman fuskarta kawai sai ta rungume Moddin a jikinta tana furta  Barakallahu fika Moddibo, Allahu Akbar Allah ka nuna min girmanka, ka nuna min komai yana faruwa ne cikin buwaya da izzarka tabbas kai Alhakimu ne mai yawan hikima& ka cancanci a kiraka Alwahhabu mai kyauta da k ari. Almujibu mai amsar addu ar bayansa. La Sharika laka, Allah ka cigaba da kare min zuri ata. Ba ni da boka bani da Malam.  Ameen "

suka amsa gaba d aya Umma dee ce kawai bata wajen.

Moddibo ya d an saki murmushi kawai kafin ya mik e ya bar parlorn. Shikkenan hirar ta koma kan kalar

matar da ya kamata su samowa Moddibo kowa ya dinga fa dar albarkacin bakinsa. Na irin matar da ta dace da Moddin.

&&&&

"Driving d in take idanunta sanye da black shade da ya yi masifar yi mata kyau, ya kuma sake bayyana"

"gayunta. Chewingum take ci. Fuskarta cike take da damuwa. Ta samu gefen Titi ta yi parking hannunta ta saka ta Zare shades D in da ya saka ba a ganin jan idanunta suka yi. Muryarta a dashe ta ce  Alwan ka kasa cika min buri na, me yasa? Da Kai na yarda duk wani hope d ina yana wajenka. Ka San dai rashin cikar burina yana nufin komai ko? Alwan ya saki ajiyar zuciya ransa a b ace ya fara furzar da huci shi kansa zuciyarsa bata masa da di Akan hakan, amma ya zai yi? Duk ta inda ya b illowa Imaam sai ya waske& .  Ko wata dabarar zamu canja? Ta fa da idanunta suna lumshewa. Sai kuma

23 / 32