Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dr Sultan Complete Hausa Novel by Sadeeya Ka-Oje

Author :  Sadeeya Ka-Oje Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 21

18K to 21K   out of 60.6K words

fashe da kuka mai tsuma zuciya jikin kowa a wajen ya yi sanyi, sanin irin
shaƙuwar da ke tsakanin su,"Malam ya ɗora da cewa yanzu haka sun mallakamin gidan su,
Alhaji Nuraddeen ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, cikin tausasa halshe yace ," yanzu kenan sun koma
Kano da zama? Ko kana da Address ɗinsu ko number waya haka ,"wlh banda masaniya akan su, Number
Mama bata shiga shima ɗan nata kuma banda wata masaniya akan sa halima rabona dashi tunda mahaifinsu
ya rasu duk garin nan kuma ba wanda yake da masaniya a kansa, Saida yana kamfanin mai suna
Gwa....... Bai kai ga karasa ba Abdulmalik ya yenke jiki ya faɗi a sume, cikin tsananin tashin suka dukufa
akansa don ganin sun ceto rayuwar sa cikin aikon Allah ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya,
"Nagode sosai Alhaji Nuraddeen ya faɗa cikin girmamawa in sha Allahu kuma daga yau kula da
Abdulmalik ya rataya a kaina canzi gaba da kula dashi har ranar da Allah zai baiyanar da Kaka da Maryam
ɗin....
Godiya sosai malam Liman ya yi sama ko ba komai Alhaji Nuraddeen ya kwanta masa a rai duk da bai
naɗa musu koshi waye ba, a hankali Alhaji Nuraddeen ya kalli Abdulmalik kana yace ," Ko a wai abinda
zaka ɗauka?" a hankali ya gyaɗa mishi kai, lokacin da zasu tafi Alhaji Nuraddeen ya ba malam Liman
kusan 50k..... tare da Number wayarshi koda wani Abin ya taso..
Kai tsaye suka wuce dakin Abdulmalik cike da kewa ya riƙa bin dakin da kallo komai na yadda ya barshi,
yana kuka ya soma kwasar kayanshi da takardun sa na makaranta da duk wani abu mai mahimmanci kana
ya fito daga ɗakin jiki a mace ya nufi wajen mota ya shigar da kayan bayan Booth. a tsanake suka bar ƙofar
gidan... Kai tsaye suka kama hanyar Kano tafiya suke a hankali..
Abdulmalik ido kawai ya runtse cikin wani irin yanayi mai Tsananin kai kuma ya juyuwa ya runtse ido
tunowa da kalaman Maryam lokacin da zai tafi ," Ya Maleek Allah ya sada mu da Alheri!" Wannan kallama
ta tsaya mishi a rai haka ya riƙa tubka da warware har suka iso gida....
Tamkar wanda aka zarmewa lakkar jiki
Haka suka shigo cikin palon ," Habi......saikuma tayi shiru ganin Abdulmalik a tsaye ," Sannun ku da
zuwa!"
Jiki a Mace suka zauna Abdulmalik da dan kunshin kayan, " Lafiya dai?"
Lokaci ɗaya suka sauke Nannauyan Ajiyar," Alhaji Nuraddeen bai ɓoye mata komi ba ya sanar da ita
bayanin da Malam liman ya yi mi shi, "Allah yasa hakan shine Alheri!
"Amin"
Alhaji Nuraddeen ya yi gyaran Murya cikin tausasa halshe ya soma magana ," Abdulmalik!"
Cikin raunin Murya yace ," Na'am Baba!"
" Wannan itace Matata sunanta Ummul khairi tsowon Shekara Goma sha biyar kenan da Auren mu Allah
bai taɓa bamu Haihuwa!" daga yau ina son kadauƙi Ummul khairi a matsayin Mahaifiyarka, bana son ka a
jeta a wani matsayin da bana Mahaifiya ba!" Ummul khairi ta sauke sassanyan Ajiyar zuciya, kana ta kalli
Abdulmalik dake zaune jikinsa duk ya yi sanyi cikin sanyi Murya tace," Abdulmalik wannan shine mijina!
Alhaji Nuraddeen Mai Nerah! Ina son daga yau ga ɗaukeshi a matsayin Mahaifinka! Gidan nan gidan
Mahaifinka ne kayi duk abinda kake so,
Ina fatan zaka ɗauke mu tamkar yadda muka ɗauke ka!"
Cikin wani irin yanayi Abdulmalik ya gyaɗa kai dan damuwa ƙarara ta fusakar sa da cikin idanunsa cikin
ƙarfin hali ya sakar mata murmushi, " Yauwa Uncle ɗina .Allah ya yi maka Albarka! cewar Alhaji
Nuraddeen,"
Murya a disashe yace ," Amin!"
"Wai da gaske sunan Uncle ɗin mu gareshi," Alhaji Nuraddeen ya gyaɗa mata kai," Yayan Mama ne
Kuma yana bala'in so na!" Lokaci kafin ya rasu kullum a gidansa nake kwana"
"Allah ya gafarta mishi tare suka Amsa da "Amin"
"Wannan ai babban suna ne gaskiya Bazan iya kiran sunan Uncle kai tsaye ba"
Shidai Abdulmalik sai kallon su yake,
Cike da zumuɗi Alhaji Nuraddeen yace ," wanne suna zaki riƙa kiran sa?"
Kai ta ɗan daga kaman mai tunani ," Uhmm Aryan! cike da zolaya Alhaji Nuraddeen yake ,"A'a bakin
ta.dan turo cike da Shogoɓa da sauri Abdulmalik ya sunkuyar da kai, a karo na biyu ta sake cewa,"Affan!
"a'a Abba! Ya girkiza mata Kai," Ayman! "A'a Aslam! A karo na Barka tai tariƙa faɗin sunaye," yana faɗin
A'a," fuska a tsuke taci gaba da faɗin sunayen ," Allah na gaji!" kana taci gaba,"Muslim! Arif! Sultan!!" da
sauri Alhaji Nuraddeen yace ," Yes wannan ya yi! SULTAN!! Allah sunan ya yi daɗi sosai kuma ya dace
dashi," Abdulmalik ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe akan fusakarsu,
"A hankali ta sauke sassanyan Nunfashi kana tace ," da gaske sunan ya yi!?"
"Sosai ma"
"Sultan! Sultan!! Sultan!!!" Abdulmalik da sauri ya juya yana Kallonta" a karon farko Alhaji Nuraddeen ya
saki Murmushi, kana yace Mahaifiyar ka ta maidaka Sultan saboda sunan Uncle ɗin a gareka!"
Ɗan Murmushi ya sanka masa da sadda kai a kamar jin kunya, shima ya yi Murmushi, shekarar ka Nawa?
Kai a sunkuye yace ," Ashirin da Biyu!"
"Masha na kai ga saurayi!" Tashi muje muje a binci ko? tare suka nufi darning sukaci Abinci cike da
natsuwa,
Bayan suna gama ya wuce ɗaki ya yi wanka kana ya kwanta cike da damuwar sabuwar rayuwa da ya tsinci
kansa a ciki da wannan tunani bacci ya yi a won gaba dashi......
"Habibi gaskiya ya ron nan ya kwanta mi har ga Allah hakan nake jisan kaman ɗan da na haifa!" idanunsa
ya lumshe tare da kwantar da ita a jikn nasa da kyau ya zame hular kanta yana shafa kanta dake cike da
gashi dogo mai tsantsi, sunja tsawo lokaci a haka a hankali yaja musu lallausar Blanket ya rufe su dashi....
Washe garin wuraren karfe 10 security gidan suka shiko palon a kwataiya kusan set ɗaya kowanne cike
maƙil da kaya... Anan tsakiyar Palon suka ajiye su... Cikin tsantsan farin Ummul khairi ta soma buɗe kayan
tana kallon kaya ne kala kaya na maza shadda, ƙananan kaya jallabiyoyi kayan bacci, turarukka da muyun
kan shafawa masu kyau da tsada ta takalma Kala kala e.t.c Abdulmalik kam haka ya saki baki yana kallon
ikon Allah wai yau shike da kayan nan masu matsifar kyau da tsada... dai dai lokacin Alhaji Nuraddeen ya
shigo Palon fusakar ɗauke da murmushi kamr ko yaushe, cikin raunin Murya Yace ," Sannu da zuwa
Baba ," Yauwa my Son! Zo kaga kayan ka idon akwai a binda baiyi ba sai a canza,"Baba Allah ya saka da
Alh..... Alhaji Nuraddeen ya yi saurin da katar dashi," bana son gidoya ƙarɓi nan ya yi maganar tare da
miƙa Mishi waya kwalin wuyar Samsung Galaxy S23 Ultra mai matsifar kyau da tsada sai ga hawaye shar
a fuskar Abdulmalik," Lokacin ɗaya suka sauke Nannauyan Ajiyar ," Sultan!! suka.kira sunan sa tare! A
hankali ya ɗago da idanunsa da sukayi kaɗa sukayi jazir cikin wani irin yanayi ," Yace Na'am Baba miye na
muka ya yi maganar tare da share mishi hawayen, Sultan ya sauke sassanyan Nunfashi," ashe bayan kaka
zan sake haɗuwa da mutane masu kirki ya faɗa a zuciyar sa," Karna sake ganin hawayen nan kaji," kai ya
gyaɗa mashi" je kaka wayar ka charge "Ta Baba har ya juya zai tafi Alhaji Nuraddeen ya dakatar shi," Bana
son Baba nan da kake kirana ya faɗa cike da zolaya," A karon farko ya saki Murmushi har haƙora sa suka
bayyana"
Nima dai bana son Maman nan kaman wata tsohuwa lokaci ɗaya suka saki Murmushi," a nan cikin palon
ya saka wayar charge, " Larai ina Abu kuzo ku shigar da kayan nan ɗaki ku jera moki yadda ya dace"
"TOH Ranki ya daɗe"
Ranar haka suka kwance cikin tsantsan farin ciki.....
A ɓangaren su Maryam a hankali ta fara sakin jiki zuwa yanzu harta fara maida jikinta tuni an saka ta
makarkatar su Haydar a jss3 saboda ƙoƙarinta haka kaka ta rungumu jikokinta tana kulada dasu tare da
masu Aiki... A ɓangaren islamiya sosai ta maida hankali da karatun hadisai da harda,
Abdullahi ma ya fara maida jikinsa kullum Kaka a gaba take sashi harsai yaci Abincin... a hankali shaƙuwa
mai ƙarfi ta shiga tsakin kaka da jikokinta Rayuwar suke gwanin burgewa,
Washe gari tunda sassafe Alhaji Nuraddeen suka wuce Asbiti wajen likita tare da saka Dr ya bincika mai
lafiyar Sultan ko yana ɗauke da wata cuta, Alhamdulillah duk wasu kwaje kwaje da ya kamata ayi Mishi an
kammala tsab bai dauke da kowacce cuta.... Nan ya ƙara jin son yaron A ranshi.. godiya sosai Alhaji
Nuraddeen ya yi kana suka wuce gida....
Bayan sun iso gida ya kira Abdullahi ya sanardashi abinda ya faru tare da ɓoyemai wasu bayanai kan
Abdulmalik ɗin kan Ainiyin sunanshi da garin da yake da kaka da Maryam da ya rasa, haka wai yaji yana
kyaunar yaron shima,nan ya shiga taya shi murna sun jima suna waya kana sukayi Sallama....
Sannu a hankali shaƙuwa mai ƙarfi ta fara shiga tsakanin su zuwa yanzu Abdulmalik ya fara sauyawa sosai
ya yi warin fari mai matsifar kyau da ɗaukar ido fatarshi har wani glowing take sumar kanshi ta kara
cikowa da tsowo ga wani sheƙi da take... Wasa wasa Abdulmalik ya fara saba wanda sabon sunanshi
Sultan da kowa ke kiransa a gidan hasalima ba wanda ya san Ainiyin sunansa na gaskiya, a Wani ɓangaren
kuma duk lokacin da ya tuna da Maryama da Kaka har kuwa yake. Sosai facebook ke ɗebi Mishi kewa.
haka suka ci gaba da rayuwar su cikin kwanciyar hankalinki,
Yau ta kasan ce Assabar Tun safe Ummul khairi keta aiki abinci tare da masu aiki tuni gidan ya gauraye da
kamshi, a hankali yake yaku har izuwa Darning erea a hankali ya ɗan juyo jin an jamai kujera tsaye yake
fuskar sa ɗauke da murmushi ," Daddy Ina Kwana? A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe a kan
kyakkyawar Fuskarsa,"lafiya lau"
"Wai me Mommy ka ke girkawa haka niji gidan sai khamshi yake?"
"Aiko haƙura Zakuyi da khamshin nan don ban dafa daku ba ta karasa maganar cike zoyala lokacin ɗaya
suka saki Murmushi,
" Laifin me muka aikata haka?"
Dai dai lokacin kwata Kyakkyawar mata shigo," Fuskar cike da damuwa," sauri Mommy ta nufi wajen ta
tana faɗin Kulsum lafiya sai kuma ta fashe da kuka lokaci ɗaya Alhaji Nuraddeen da Sultan suka miƙe tare
da barin Darning suka nufi wajen su, cike da damuwa ," Mommy ta soma tambatayar ,"Kulsum lafiya mike
faruwa? a hankali ta share hawayen murya a disashe tace ,"Anty wlh na gaji da walaƙanci da Dengin
Marigayi suke min yau suksan sati guda kenan da suka sani a gaba wai saina bar musu gida tunda an raba
gado na tashi na bar musu gida," Shine na ce banza tashi ba zan Ƴa ƴa na ke," Yauwa da safe koda na kaisu
Meena islamiya na dawo sun rufe gida wai na tafi na bar musu gida, ba yadda banyi dasu akan subarni
suka ƙi, ta ƙara sa maganar tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya," da kyar suka shawo kanta ta Dena
kukan," Yanzu ina su Meena ɗin?"
,"Suna islamiya Anty," shikenan ki Dena kuka," je ɗaki ki watsa ruwa ki fito muyi Breakfast, " Anty Don
Allah a karbo min ƴa ƴa na bana son su zauna tare su, zasu.. ya isa za'a karɓo su cewar Alhaji Nuraddeen,"
jiki a mace ta wuce ɗakin ta watsa ruwa koda ta fito Mommy ya aje mata kaya a saman gado bayan ta
shirya ta fito Palo suka karya....
"Wacce islamiya suke" Madarasatu Norul Islam ta faɗa cikin sanyi Murya, shike nan zan tura Dogo ya
dauko su, batun gida kuma ki bar musu gidan Yara muka canzi gaba da kula dasu,"mommy ta sauke
sassanyan Nunfashi tare da kallon Mijin nata ,"Alhaji Allah ya.... "Ya isa"
"Ya Nuraddeen nagode sosai itama ya yi sauri da Katar da ita, sanin halinsa na reshin son godiya idon ya
aikata alheri..
dai dai lokacin Dogo Deribe ya shigo Palon, "Yau dogo su Meenah zaka ɗauƙo a islamiya Yaya bari na
bishi mu tafi tare okay ba damuwa, tare suka fice daga palon....
"Daddy mun gama shirin Maryam tace bazata jeba karatun Hadda Zatayi, Abdullahi ya Kalli Maryam dake
zauna,"Mamana tashi ki shirya mu tafi Kinji! Ke kadai za'a bari gida sai ran sunday zasu dawo,
"Abba Malam yace idon ban iya sai ya zaneni!"ta ƙarasa maganar kaman Zatayi kuka," Shike nan"
Abdullahi ya kalli Kaka," Kaka yace Mama zamu tafi," toh Abdullahi Allah ya Tsare," Amin Amma!"
Har bakin kaka ta sakaru tare da Maryam, bayan tafiyar suka wuce cikin gida....✍️✍️✍️
_More comments and share_
*Sadeeya Ka'oje ce* ✍️
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*
💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍
PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗
*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 15-16*
_______Lokaci ɗaya su ka iso ta re da Dogo Deribe, ya na ga ma Parking su ka buɗe motar cikin tsananin
farin ciki har wa ni tsalle su ke saboda mur na, dai lokacin Ummu Kulsum ta fi to cikin mota ta re da wa su
kyawawan Yara gu da Ukku kusan kama su ɗaya Ummul Kulsum ga baki ɗayan su suka nufi palon,
Sunyi nisa sosai da kallon tv Alhaji Nuraddeen ji kwai ya yi a rungumeshi a hankali ya juyo da fusakar
karab Idanunsa suka sauka kan Abdullahi dake tsaye murmushi na ƙara faɗaɗa akan fuskarsa, Alhaji
Nuraddeen ya sauke sassanyan murya tare rungume Abdullahi yana faɗin ,"Sannu da zuwa Aminina irin
wannan bazata haka?"
Bayan sun zauna Mommy ta kalli Abdullahi cike da girmamawa ta ce ,"Abban Haydar sannu da zuwa yasu
Mama?"
"Duk lafiya lau su ke tace a gaishe ki,"
,"Amin ina mai sunan Mama!"
"Tana gida ba yadda banyi da ita ta zo muje ta ce a'a saboda karatun Hadda da take!"
"ma sha Allah!, Allah ya ƙara basira mai Albarka"
"Ga ba ki ɗaya su ka Am sa da "Amin"
"Ina yaron Nawa?" Abdullahi ya tambaya murmushi na ƙara faɗaɗa akan kyakkyawar fuskarsa,"
Cikin girmamawa Sultan ya ce ,"Abba Barka da zuwa"
"Yauwa My boy ya gida"
"Alhamdulillah Abba!"
"Daddy waye wannan Haydar ya faɗa tare da nuna Sultan,"Alhaji Nuraddeen ya yi Murmushi tare faɗin ,"
Yayan kune Sultan! " Daddy ban taɓa ganin saba"
"Ehh a school yake last Month ya dawo daga yanzu ku riƙa kiransa Ya Sultan! kaji"
"Toh Daddy"
"Yauwa my Boy!"
"Meenah Zo non Mommy ta faɗa a hankali yariyan ta ƙara so wajen ta zauna ƴar kimanin shekara goma
sha sha biyu, "Meya sameki?"
cikin raunan'nanyar murya ta ce ,"Mommy kaina ke ciwo!," Cike da damuwa Mommy tace ,"Ayya
sorry Mamana!" Shiko Sultan sai kallon yarinƴar yake, Yana mai jin. tsakanin son a Ranshi, ga baki ɗaya
hankalin sa nan kansu, ,"kinci abinci?" A hankali ta gyaɗa kai, "Yauwa to je ɗaki ki watsa ruwa kizo na
baki magani,"toh Mommy kana ta wuce ɗaki,
Ummul Kulsum ta sake Nannauyan Ajiyar zuciya,"Anty dole Kanta Ya yi ciwo jiya a zauna kuma kwana
reshin barci ne ya sakan mata ciwon kai nan, jiya tunda ƙannen magariyi suka zo gidan a suna faɗamin na
tattara kayana na bar musu gida, tun a lokacin ta ke ta na kuka! haka muka kwana zaune"
"Mommy ta fesar da Numfashi mai zafi, cikin tausasa halshe ta ce ,"Allah ya jiƙan Aminu sam basu
hali!"
"Ya isa hakan nan cewar Alhaji Nuraddeen,.. In sha Allahu daga yau wannan matsalar tazo ƙarshe!"
"toh Allah ya sa hakan shine Alheri Mommy ta faɗa cikin wani irin yanayi," ga baki ɗayan su suka Amsa da
Amin,..
Sai lokacin Sultan ya samu damar gaida Ummul Kulsum,"Ina kwana Mommy!" Lokaci ɗaya su ka juyo da
Ummul khairi, ko waccen su furkarta ɗauke da murmushi," shima murmushin ya sakar musu," Ummul
Kulsum haka kawai ta tsinci kanta da kallon Sultan..
"Wai bakiji yana gaishe ki ba da sauri Ummul Kulsum ta janye hannunta,"Kana ta ce ,"Lafiya lau!"
su Haydar kam sai guje guje suka a Palon suna wasa,
"Mommy nayi Wonka"
"Yuwa Mamana muje na bakin maganin tare suke wuce ɗaki bayan ta bata bamagani ta Kwantar da ita
tare da lulluɓeta da laulausar blanket nan take Barci ya yi won gaba da ita.
Ranar dai haka suka yi cikin tsastsan farin karfe Abdullahi sai bayan isha'i ya wuce gida..
Sultan ma tunu ya wuce ɗakin sa tare da Haydar da Khalifa...
"Anty wai Nikam ina kuka samo yaro nan?" cewar Ummul Kulsum,"Mommy bata ɓoye mata komi,"Kai
gaskiya Anty ya Nuraddeen nada kirki Allah ya saka Mishi da Alheri, shiko Sultan Allah yasa ya zame
muki ɗan Halak duk da dai naga bashi da matsala"
"Amin ya rabbi!"
Kinga Saida safe wlh Barci nake ji sosai jiya ga baki ɗaya ban runtsa ɓa"
"Allah ya tashe mu tafiya lokaci ɗaya suka miƙe ko waccen su ta nufi ɗakinta, Ummul Kulsum koda ta shi
Meenah na zaune a tsakiyar gado ta dafe kai, da sauri Ummul Kulsum ta nufi wajen ta zauna tare da
Rungume ta kana ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar cikin raunin Murya tace," Mamana lafiya mike da
munki?"
Murya a disashe Meenah ta ce wannan mafarkin na sake yi! da sauri ta Ummul Kulsum ta waro manyan
idanunta cikin raunin Murya ta ce ," Yau kuma?" Mamana! Kai ta gyaɗa mata, a hankali ta rumtse idanunta
ta na mai jin wani irin Radaɗi a Zuciyarta, "Mami Yauwa cewa sukayi Zasu ta fi da.....Ya isa Mamana tayi
saurin da katar da ita," idanunta duk a rufe take Maganar," Mamana Kodai baki Addu'a ba?"
Mame Wlh nayi harda Alwalla nayi kafin na kwanta"
a hankali ta riƙa shafa kanshi ita ko sai ƙara shigewa jikinta take, a hankali ta Kwantar da ita ta re da
tofa mata Addu'oi, tana sauke Ajiyar zuciya, haka dai har Barci ya yi awaon gaba da ita....
a hankali ta gyara masu kwanciya kana ta kwanta cike da ruɗu da tashin hankali ta ɗau tsawon lokaci a
haka sai faman juyi take, har wuraren karfe 2:20 kana wani Nannauyan Barci

7 / 21