Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dr Sultan Complete Hausa Novel by Sadeeya Ka-Oje

Author :  Sadeeya Ka-Oje Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 21

30K to 33K   out of 60.6K words

abinci ka kwanta ka huta. "Mommy bari nayi
sallalolin" ya faɗa fuska a tsuke, Mommy tai Murya kana ta fice daga ɗakin, Saida ya yi kana ya fice daga
ɗakin. Kai tsaye ya wuce palon duk suna zaune a palon, Daddy L "Ma sha Allah"
"Taso muje kaji Abinci, karkamin Kuka, cewar Mommy,gabaki. Suka wuce Darning a tsanake suka soma
cikin Abinci....
tun kafin ta iso mai gadi ya buɗe mata gate cike da kwarewa ta danna hanci motar cikin gida tana gama
Parking ta fito, mai gadi na rufe gate wani yaro ya yi knoking, "Gashi a ba Sultana, ba musu ya karɓa ya
nufi wajen Sultana dake ƙoƙarin shiga cikin gida, "Madam gashi akace a baki 🎁abinda ke hannunsa
yamiƙamata
Ido.Sultana tazaro waje, "Baba nifa?.
"Eh ked'in, cewar Baba.
Karɓa Sultana Tayi tabud'e, 💐filawa ce mai k'amshin tsiya aciki, saikuma turare mai masifar kyau da ƴar
ƙaramar takarda ta zaro anrubuta.
_for you! my Sweetheart_....✍️✍️
_More Comments and share_
*Sadeeya Ka'oje ce* ✍️
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍


PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗

*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 21-22*
_______tagaza gane wanene zai iya tura mata wannan sak'on?, tad'an shinshina fulawar, kamshi mai dad'i
yadaki hancinta, harsaida ta shak'a ta lumshe idanunta, kamar tataɓa jin k'amshinan, to amma a ina?,
wannan itace tambayar. Dai dai lokacin kuma Motar Haydar ta shigo gidan da wowarsu kenan daga school
tare da Meena, Cikin mamaki duk suke kallon Sultana, "Anty Sultana waye ya aiko miki?.
"Wlhy Haydar....ban saniba nima?.
Haydar.... Yamaida kallonsa ga Baba Mai Gadi, "waye yakawo?.
"Wata 'wani ɗan Saurayi ne.
"Saurayi" Sultana ta faɗa a hankali.
"Anty Sultana Kodai kinyi sabon Kamu ne?" cewar Meenah, "Bana son Iskanci fa kowaye ya yi a
banza,tana ƙoƙarin jefarda jakar Haydar ya yi saurin da katar da ita,"A'a Anty Sultana bai kamata ki jefar da
ita ba.taɓe baki tayi, Haydar da Meena sukayi Murmushi cikin gida suka nufa, "Maraba da mutanen Asbiti,
cewar Mami. fuska a yamutse Sultana ta nufi wajen su, "Mami Wlh na gaji"Sultana kuwa jingina bayanta
da jikin Kaka tayi tana sauke Ajiyar zuciya, "ina kika samo flowers kuma?"
"Say zaa nayi kaka ta bata Amsa a takaice, bari Naje nayi sallah a hankali ta mike Kai tsaye ta wuce ɗakin
ta jefar da jakar saman gado kana ta wuce toilet Wonka tayi da ruwan dumi tayi Alwalla ta fito a tsanake ta
yi Sallah, bayan ta gama ta wuce palon suka ci Abinci. hira suka dan taɓa kana kowa ya wuce
makwancinsa....
Washegari , Yau sama-sama Sultana ta wayi gari, dan ta tashi da ciwon Baya alamar zuwan period ɗinta. Ita
dama takan fara da ciwon Baya, randa yazo kuma zataita amai har saita jigata. Kafin daga bisani ta koma
normal sai shegen ƙwaɗayi kamar mai ciki.
Tunda Kaka ta shiga tadasu sallar asuba ta lura batajin daɗi, dan maimakon kwance saita isketa zaune
ƙasa a bakin gado kan kafet ta kife kanta a kan gadon. Meena nata da Nana barcinsu a kan gadon . Ita ta
fara tadawa kafin su Nana, har zata juya ta fita sai kuma ta dakata ta kalli Sultana data maida kanta ta kife
tsakanin ƙafafunta.......
“Ke kuma lafiya?”. Da ƙyar Sultana ta ɗaga kai ta kalli Kaka, sai dai gudun kar ace ta shirya aje asibiti
a mata allura sai ta daure tace, “Kaka lafiya lau, kawai gajiyace.
Ɗan ƙura mata idanu Kaka tayi na wasu mintuna, kafin ta janye tai ficewarta batare data sake cewa
komaiba. Meena ce ta ƙaraso wajen Sultana ɗin ta durƙusa. “Anty Sultana ƙarya kikaima Kaka wlhy, daga
gani baki da lafiya”.
Yamutsa fuska Sultana tayi kaɗan tana maida ƙwallar data cika mata ido. “Baya na ke ciwo Meena nasan
kuma period ɗinane zaizo zuwa gobe idan Allah ya kaimu ko anjima”.
Nana dake fitowa daga bayi tace, “To miyasa kikaƙi faɗar gaskiya?”. Meena dake tsokanar Sultana tai
saurin cewa, “Allura”. A tare suka kwashe da dariya ita da Nana Sultana kuma tai tsaki idonta cike da
ƙwalla ta miƙe. Da ɗingishi ta shiga bayi batare data kula dariyar dasu Meena ke mataba har yanzun.
Bayan sun idar da salla Meena da Nana suka soma shiri zuwa School, Sultana kam saita koma saman
gado ta kwanta. Babu jimawa barci ya yi gaba da ita.
kaka da duk ta gama fahimtarta bata nemeta ba, dan tasan zata gama zagayenta ne tazo ta nemeta. Bayan
sun kammala breakfast, Su Meena suka wuce makaranta ga baki dayan su, "Wai Nikam ina Sultana Mami
ta tambaya,"tana ɗaki ba Lafiya, cike da damuwa Mami ta ce," Subuhalillah Meya sameta ta faɗa tare da
ƙoƙarin barin wajen, kai tsaye ta wuce ɗakin su Sultana, koda ta shigo Sultana sai faman juyi take tana
damƙe da mara, "Sultana tashi maza ki shirya muje Asbiti, murya a disashe tace,"Anty naji sauƙi, dai dai
lokacin kuma wayarta ta soma Ringing, "Kinga ana kiranki Jidda ce,Mami ta faɗa tare da ɗaga wayar, daga
can ɓangaren Jidda ta ce,"Daughter Lafiya har yanzu Ban ganki ba?" cikin raunin Murya Sultana tace
Mommy banda Lafiya!"
"Mike damunki? Kinsha magani?"
Kai Sultana ta girgiza mata kaman tana gabanta, "turomin Address ɗin gidan ku ganinan zuwa, suna gama
wayar Mami ta tura mata Address ɗin, "tashi ki watsa ruwa kafin ta iso Mami ta taimaka mata zuwa toilet,
tana fotowa da Wonka dai dai lokacin Mami ta shigo ɗakin riƙe da Cup din tea Mai kwauri, cikin ɗauriya ta
kammala shirin, "karɓi Kisha, fuska a yamutse ta ce ,"Na ƙoshi Mami"
"Ƙarbi maza Kisha"
Ba yadda ta iya dole ta karba ta sha, kana suka fice ɗaga ɗakin, "Ya jiki Abba ta tambaye cikin kulawa,
"Naji sauƙi Abba, dai dai lokacin Jidda ta shigo cikin palon cike girmamawa ta gaishesu, "Asbitin zaku je?"
Mami ta tambaya,"Allah ya kiyaye,"Amin kana suka fice daga palon har bakin mota Mami da Kaka suka
rakaru,tunda suka shiga cikin motar Sultana ta Kwantar da kai tare Lumshe idanunta,har suka iso Asbitin.
A hankali suke takowa suna fuskantar juna.
Sosai ya zuba mata ido sabida ya lura gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi alamun tsananin ciwo takeji gashi
a hankali take taku.
Ita kuwa Sultana, tafiya takeyi da kyer sabida azaban ciwo da bayan ta da mararta keyi.
Kanta a sunkuye take tafiya, Jidda na biye da ita a baya.
Ganin yayi ta wani irin sunkuyawa tasa hannunta duka biyu ta damƙe mararta dake matsifar ciwo.
"Yauwa ga Dr Sultan na ma yanzu ya iso, muje ya duba ki ko?" hannu tasa ta matse mararta tare da
cewa."Allah ya tsareni ya Dubani duk Doctors dake Asbitin nan A rasa wanda zai Dubani sai shi.ta ƙarasa
maganar cikin yanayin muryar mara lafiya.
"Sir ga marar lafiya nan"Jidda ta faɗa,
Dai-dai lokacin kuma suka kutsa kansu cikin asibitin.
Kai kawai ya gyaɗa musu yaci gaba da tafiya, har ya shiga cikin wani ɗan corridor ya shiga wanda zai
sadashi da Office dinshi ba tare daya ratsa ta cikin Reception ɗin su ba.. A Gurguje Jidda ta buɗe mata File
ta wuce dashi Office ɗin Sultan. Jim kaɗan ta dawo. ta kama hannu Sultana,Da ƙarfi ta damƙi hannun Jidda
Cikin tausayawa Jidda tace.
"Sannu, in sha Allah bazamu jimaba za'a kiraki, dan na nemi al'farman sauran sun yadda.Kai kawai ta iya
gyaɗa mata, sai taune lips ɗinta da takeyi. Suna isa office ɗin sa dai dai lokacin ya kira sunanta, batare da ta
san waye ba ta nufi Office ɗin.Nurse namiji na ga banta.A haka suka shiga,
Ajiyan zuciya taja a hankali sabida tsaruwa da kyau da tsabta da ɗan karen ƙamshin da ya ziyarci hancinta,
su sukasa ta son bin Office ɗin da kallo amman ina ciwo bazai bartaba... A hankali ta iso gaban table ɗin
baƙin Glass dake gabanshi.
Ɗaya daga cikin kujerun biyu dake gaban table ɗin ta zauna.
Ƙasa tayi da kanta cikin tarin ciwo da fargaba.Shiru tayi zaune bisa kujerar tayi ƙasa da kanta.Sultan ko
kanshi bai ɗago ya kalli inda takeba.shiru Office ɗin sai sautin A.C da yake busawa,
Kusan tsawon 2 minute suna a haka, cikin dakiya da rauni ta ɗan ɗago kanta ta kalleshi,
Ga mamakinta sai taga asalima hankalinshi baya kanta, baki ta ɗan taɓe, a hankali tace,"Wai daman nan
Jidda ta kawo Ni?" Sultan duk abinda takeyi yana ganinta ta ƙasan ido.cikin sanyi Murya ta ce, Nifa Lafiya
ta lau. Shiru bai kulataba har sawon wasu mintuna 3 har ta fara zaton ko bai jita bane.
Da sauri ta ɗago kanta jin yayi mata magana, cikin wata zazzaƙar murya a takaice yace.
"Suna?".
Cikin fargaba ta tace."Sultana Abdullahi. Shine sunan da jidda ta buɗe mata file dashi. A hankali ya ɗan
ɗago ƙwayan idanunshi ya kalleta.
Kanta a sunkuye hannunta biyu duka na kan mararta cikin wani, irin yanayi take wanda yake nuni da tana
cikin wahala... Sultana ya maimaita sunan a Zuciyarsa.
A fili kuma kauda idonshi yayi daga kanta ya maida idanunshi kan files dake gabanshi, wanda sunanta ke
rubuce akan na samanshi yaja da yatsu biyu.Tsiraran idanunshi ya lumshe sabida wani irin bugu da yakeji
zuciyarshi nayi tun lokacin ya kasance kusa da ita har zuwa yanzun nan da take gabanshi a zaune.
Rubuce-rubuce yayi a ciki file.
Kanshi ya kuma ɗagowa ya kalleta a fizge da gefen idonshi,
sunkuyar da kanshi yayi tare da cewa.
"Meke damunki?".
Murya a disashe da son danne kukan da ke son kabce mata tace."Baya da Marata. Kai ya ɗan jujjuya tare
da kallon shekarunta dake rubuce a cikin File din,
Yar shekara ashirin kuma da ƙorafin ciwon baya, cikin sanyi Murya yace.
"Yaushe ya fara miki ciwo?".
Hannu tasa ta share hwayenta a hankali tace.
"Shekara Huɗu da suka wuce".
"Meyasa bakije asibitiba tun lokacin?". Ya tambayeta.
"Ina zuwa asibiti duk sanda ya tashi".
"Kamar yaushe da yaushe yake tashi?". Ya jefo mata tambayar kamar yadda zuciyarshi ke harbawa da
ƙarfin tsiya da kuma sauri-sauri, cikin ɗauriya tace," duk ƙarshen wata. Kawar da kanshi ya yi gefe kaman
bai jita ba yaci gaba da Rubuce rubucensa. Saida ya gama ya tura mata file ɗin a gabanta, Jikinta na rawa
tasa hannu ta ɗauki file ɗin, ta yunƙura zata tashine, ya basu damar samun kusanci da juna,
da sauri ya rumtse idanunshi sabida wani irin matsiffen bugawa da zuciyarshi keyi.
cikin zuciyarshi yake maimaita.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun."
A hankali ya buɗe kyawar kyawan idanunshi jin bugun zuciyarshin ya fara yin ƙasa-ƙasa, ido ya zubawa
mata ganin ta juya tana tafiya,
wani abin al'ajabin a gareshi shine duk taku ɗaya da zatayi tana nesanta dashi sai yaji zuciyarshi na
tsinkewa yana bada wani mugun bugun , yayinda bugun tsinkewanta kuwa yaketa dai-dai-ta,
Cikin mamaki ya sunkiyar da kanshi yana kallon yadda takeyin taku, tana riƙe da mararta, taje gab bakin
fofar fitane,
Taji wani irin murɗa da kartan da mararta ya farane yasa ta sakin wani sauti mai cike da wuya.
"Wayyo! Allah na, Wayyo Mami cikina Wayyoo Ka...."
Da sauri Jidda ɗin nan yayi kanta tare da cewa."Sannu Sultana"a hankali jidda ta zaunar da ita kujerun
ƙarfe dake gab da bakin ƙofar.
Bata da zaɓin daya wuce ta zauna ɗin, domin gaba ɗaya ƙafafuwan ta rawa sukeyi alamun bazasu iya
ɗaukar nauyinta ba ga duhun daya rufe mata ido.
Sunkuyowa Jidda ɗin yayi ya amshi file kana tace.
"Zauna bari inje Pharmacy in amso miki magungunan da alluran sai ayi miki".
Kai kawai ta iya gyaɗa mata... da sauri Jidda ta bar wajen.bayan mintuna goma ta dawo tuni Sultana ta fara
fita haiyacinta," kije ki mata Allurar, Jidda ta ware manyan idanuny," Sir Wallahi Bazan iya ba tsoron
Allurar tsiyane da ita , Ta gefen idonshi ya ɗan kalli Sultana da keta durƙushe a wajen ɗaya. cikin bada
murni ya ce ."Tazo".
Da sauri Jidda ɗin ya juyo ya nufoshi,
hannu yasa ya amshi allurar,
kana ya ɗan kalleta a fakaice yace.
"Zo nan".
A hankali ta taso cikin sanyi takeyin taku tana matsoshi.
A take kuma bugun zuciyarshin ya fara tsananta Taku biyu tayi ana uku yaji ƙirjinshi ya bar tsinkewar da
yaketa yi ɗin, sai kuma bugun da yakeyi da sauri-saurin ne yaketa tsananta.da sauri ya dafe ƙirjinshi lokacin
da ta iso gab dashi, cikin ranshi ya kuma cewa.
"Ya Rabb"
A zahiri kuwa, da kai ya nuna mata ta kuma matsowa, ba musu ta matso,
yatsarshi ya jujjuya mata alamun ta juya mishi baya,
still babu musu ta juya, a hankali ya murza kujerar da yake kanta, ya juyo ya fuskanci bayanta, dai-dai
saman mazaunanta ta sama ta ɗan gefe kaɗan, ya saita, tsinin bakin allurar, cikin iyawa da gwarewa rumtse
idanunta tayi da azaban ƙarfi sabida, wani zafi da taji yana ratsata, hannunshi yanada masifar zafine,
Da ƙarfi tace.
"Wach Allah na zafi-zaffi."
Wani irin azaba taji lokacin daya fara sakar mata ruwan allurar a jikinta, babu zato babu sammani yaji tasa
hannu damanta ta damƙe hannunshi dake mata alluran hannunta na hagu kuwa yarfashi take tare dasa kuka
da sauti tace. "Wayyoo Allah na Zafi nake ji, bugun zuciyarsa ko tsananta yake, ya kusan hallakashi lokacin
data riko hannunshi, da sauri ya tura mata ruwan kana ya zare Allurar da ƙarfi. Sannan ya miƙe tsaye,
sabida muddin yana kusa da ita babu makawa wata ƙil zuciyarshi zata faso ƙirjinshi ta fito woje.
Wani dogon tsaki yaja tare da juyawa ya bi gefen Jidda ɗin ya fice daga Office ɗin...
da sauri Jidda ta riƙo hannuta suka fice ɗaga Office ɗin. Ta kaita ɗakin ta kwantar da ita nan take bacci ya
yi awon gaba da ita...
Sultan da sauri yake tafiya sabid iya yedda yake nesanta da ita iya yadda kirjinshi ke dai-dai ta bugawa, sai
kuma tsinƙewa da zuciyarshi keyi...
Bacci Sai Sultana ta yi sai ƙarfe Shidda ta farka, ba ɓata lokaci suka wuce gida, har gida Jidda ta kaita, sai
lokaci ta tuna da wayar ashe cikin mota tabarta, Miss Call ɗin Mami da Kaka. Da Abba ba iyaka... lokacin
da suka iso ƙofar gida Sultana ta kalli Jidda ta ce," me yasa zaki kai wajen Ɗan is..... "ya isa Sultana Jidda
ta yi sauri dakatar da ita," to in ba iskanci ba zai sani a gaba yana mun tambayoyi, wannan sam bai dace da
zama likita ba ɗan jarida yafi dace wa dashi... "Kai Nikam me Dr Sultan ya yi Miki kika tsaneshi haka,
karfa ƙiyayyar da kike mai ta kowa so! Wata rana, " Allah Ubangijin ya tsare ni ko shine Autan maza a
duniya Bazan zaɓa Auren sa ba!"
(Ni dai nace Humm😅).
Jidda ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar,kana tace,"Allah ya kyauta"
Ƙala Sultana bata ce mata ba ta fice daga motar ta nufi cikin gida...
Kai tsaye bathroom ta wuce, tabbas kuwa baƙon ya iso, Wonka tayi kana tayi al'wala dan ko bata salla bata
zama babu al'wala.
Tana fitowa ta kimtsa jikinta kana ta zura tattausan doguwar riga.
Tana kokarin fitowa falo Meena na ƙoƙarin shigowa da sauri Meena ta zaro ido tare da cewa.
"Yaushe kika dawo?".
Hararanta ta ɗanyi tare da cewa.
"Ban sani ba"
Cikin tausayawa Meena tace. "Sorry Anty Sultana
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana tace. "Ya jikin naki Anty Sultana!"
"Naji sauƙin"
"Na dawo a guje fa, wannan Sultan ɗin hannunsa zafi.
Zaro ido na mamaki Meena tayi tare da cewa.
"Anty Sultana Shida kanshi ya miki?".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Eh".
Cikin taɓe baki tace.
"Lallai yau kin tashi da ƙafar dama, gashi kuwa naga har kin worke".
Wucewa sukayi zuwa tsakiyar falon, cikin sauƙe numfashin Sultana tace.
"Ba doleba Ko don mugutar da ya yi min dole na warke,
Dariya Meena tayi tare da cewa.
"Kinji allurar manyan likitocin da duniya keji dasu dai".
Uhum kawai tace sannan suka fara cin abinci, sunaci suna hira. "Wai ina Mami da Kaka, "Barci suke, sai
gab magriba kaka ta farka daga Barci ruwa ta watsa don taji daɗin jikinta...
"Sultana ya jiki"
"Lafiya lau Mami, tun ɗazu na dawo ai. su Khalil basu dawo ba har yanzu, "Mami Kinsan yau hadda
suke sai 8 zasu dawo..."
"Na manta Sam"
A hankali Meena ta wuce ɗaki don yin Sallah, Sultan ta nufin ɗakin Kaka , koda ta shigo tana Sallah zama
tayi tana karanta Askar a wayarta bayan ta kammala ta kunna Data tana chatting da Jidda dake tsokanarta..
Kaka ko bayan ta sallame sallah taci gaba da Addu'oi...har zuwa bayan Isha'i, ƙarfe 8:15 su Khalil suka
dawo a gajiye,bayan sunyi Wonka suka ciki Abinci,kana kowa ya wuce ɗakin sa.....,
Sultan bai samu dawowa gida ba sai bayan magrib...haka kuwa ya shigo gidan rai a hade saboda tsabar
gajia da yayi...driver na shigowa ya samu wuri yayi parking sanan ya bude motan ya fito saidai tun kafin ya
zagaya ya bude mishi kofa mai Security yazo ya bude yana mishi sannu da zuwa, Sultan bai iya ce mishi
komai ba sai hannu daya daga mishi kafin ya nufi cikin gida a yayi da fusakarsa zai baka daria sosai...ya
lumshe idanunsa tareda dora kanshi shoulder din Mommy murya can kasa cikin yace"Mummy na gaji ta
shafa kanshi fuskanta daukeda murmushi itama tace,"welcome back son..akwai gajiyan aiki koh"...ya ɗan
tauna lips dinshi kana ya ce "Akwai gajia sosai Mommy.. "ina Salma da Salim?"
"Sunyi Bacci tun ɗazu" je ka watsa ruwa kazo muci Abinci, jiki a mace ya wuce ɗakinsa ya watsa ruwa
ya fito ya shirya cikin lallausar jallabiya yana zuba kamshi, ya fito palon ruwan tea kawai ya sha ya wuce
ɗaki......
Haka Sultana ta kwana ranar cikin takaicin Sultan da jidda da duk ta tattara laifin a kan Jidda da ta kaita
wajen Sultan ɗin, Bata da riko sam idan akai mata abu. amma sai gashi Jiya da yau Abun ya tsaya mata a
rai da tarkacensa sun kasa barin ranta harma washe gari da shima dai haka ta yini babu walwala saboda
jininin tana, Jidda tuni ta kama kanta don ko a Asibiti bata sakar mata fuska ba....
Washegari ya gama shirya kanshi cikin suit kaman ko yaushe ya nufi parlon Mummy don yin breakfast, A
Gurguje ya yi Breakfast ya wuce Office. Cikin ƙanƙanen lokaci ya iso, bayan mintuna 5 Sultana ta iso
kallon

11 / 21