Author : Sadeeya Ka-Oje Category : African Stories & Novels
katarda ita, "Madam
gashi yamimama bag🛍 mai k'yau, ta amsa tana tafad'in namiye Baba?. "Wannan yaron ne ya sake da
wowa, aiko da sauri Sultana ta nufi wajen tuni ya Ron ya ɓace, kai tsaye ta wuce ɗaki 🎁bud'ewa sukayi,
flower🌹ce tanata k'amshi, sai zobe Azurfa mai masifar kyau da tsada
Sultana tasauke ajiyar zuciya tareda tunanin sak'o makamancin wannan da aka taɓa bata wata ukku
dasuka wuce , da ƴar ƙaramar takarda,
*_kenafi ƙauna cikin matan duniya bani da buri sai muyo Auren dake!*
Wannan shine kawai arubuce, Sultana ta maimaita baitikan yafi sau goma, to wanenen wannan?,Kodai ya
NAS ne? Kai anya kuwa?.
Saikuma turare mai masifar k'amshi, Sultana ta shinshina turaren talumshr idonta.
Jitake tabbas tataɓajin wannan k'amshin, amma a ina?.
Shine abin tambayar.
Da sauri tatashi zuwa gurin ajiye muhimman abubuwanta ta aje su anan..
Koda Meena ta shigo ta bata labarin sosai Meena tayi mamaki,"Anty Sultana nifa ina zargin NAS ne ke
turo Miki saƙon nan gaskiya, "Nima Meena nafi zargin Shine!"
"Aiko Anty Sultana kiyi duk yadda Zakiyi ki gano ko waye. Suna cikin managar kiran Nas ya shigo,"
Yauwa Anty Sultana ki nuna mai sauƙonshi ya iso kin gode, Meena ta faɗa a hankali," mai Sultana ta gyaɗa
mata, "Assalamu alaikum ta faɗa cikin sanyi Murya, " daga can ɓangaren Nas ya sauke sassanyan Nunfashi
kana ya ce," Ina fatan saƙo Na ya samu ƙaɓuwa a wajenki?" da sauri Sultana ta waro manyan idanunta
kaman tana a gabansa tace ," daman kaine?" Nas ya saki Murmushi mai sauti, Meena ga baki daya
hankalin ta kan Sultana dake faman sakin Murmushi kaman gonar Auduga.
"Allah ka shammateni Nas!" Ta faɗa cike da shagoɓa, sun jima suna waya cike da zallar Soyayya....
★★★
"Anty Sultana Kinga Abinda nake faɗa Miki ko, "najina ina zargin shine"
Cike zumuɗi Sultana ta kira Jidda ta sanar da ita komi. Sosai Jidda ta taya murya, tun daga wannan lokaci
so da shaƙuwa mai ƙarfi ta ƙara shiga tsakanin Nas da Sultana....
(Hmmm 🥱🥱)
*Sultan*
Ba ƙaramin kyau yai ba cikin shirin sa na Shuit . Ɗauke da briefcase ɗin sa fito.daga ɗakin sa cikin takunsa
na girma da ƙasaita.
Ƙai tsaye wajen dining ya je
"Morning Ya Sultan" ya amsa tana ma sa murmushi
Shima Salim da ke gefe ya ce " Good morning Ya Sultan"
"Morning" ya faɗa a taƙaice.
Tea ɗin da ke gaban Salma ya ɗan ƙurɓa ya ce " sai na dawo ko" ina gai da Mommy da Daddy idon sun
fito..
Yana fita ya shiga matar sa kai tsaye ya wuce Office..
A hankali ta nufi kan step ɗin.
Dai-dai lokacin kuma Sultan ya fito daga wani ɗaki ya nufi ƙasa, a hankali yake take steps din yayinda
hankalinsa baki ɗaya yana kan file dayake kan hannunsa na dama yana duddubuwa da hannun hagunsa,
bisa dukkan alamu.
Abu mai mahimmanci ne yakeye karantawa.
A dai-dai lokacin kuma Sultana ta iso bakin steps ɗin, cikin sauri take tafiya, da alamun sauri
Da sauri take tattaka steps ɗin tanayi sama.
Steps biyu ta taka ana uku, taji juyo da kanta da sauri dan jiyo muryar Jidda
“Daugter sai yanzu?”.
Ba tare da ta tsaya ba, kana bata kuma juyo kanta ba taci gaba da tafiya a haka, hannunta na kan da ƙarfe
dake gefen steps ɗin."Dr Sultan na memanki,
Cikin sauri ta kuma juyo kanta da dama bata gama juyashi ba cike da tsiwa tace. "Mezan masa?"
“ oh ho miki Tun ɗazu.yake nemanki”
Cikin yanayin tsoro ta ɗan zaro manyan udanunta tare da cewa.
"Ba inda zanje
"Kaman ya ba inda zaki je?"
Haka taci gaba da haura saman steps ɗin ba tare da tana kallon gabanta ba.
Wanda kuma dai-dai lokacin Sultan ma ya taka step na ƙarshen bazato ba tsammani taji tayi karo da mutu.
Shi ma Sultan ba zato ba tsammani yaji kanta ya bugi ƙirjinsa yayinda hannunta ya bugi file ɗin dake
hannunsa ya subce ya tafi ƙasa ta kardun suka watse gabi ɗaya
Tagal-tagal Sultana tayi baya zata fadi yayin da shikuma Sultan da ƙyar ya tsaida kansa daga faduwar da
zai yi.
lokaci guda ta rumtse idanunta tare da sakin kara.
Sultan cikin hanzari yakai hannu ya riƙota sai alokacin idanunsa suka sauƙa akan fuskarta ita.
Sultana sassayan numfashi ta ssuƙe jin an riƙeta bata faɗiba yasa ta ɗago kan Idanunta ne suka sauƙa akan
fuskar Sultan, lokaci ɗaya zuciyoyin suka buga da masifar ƙarfi, cikin wani irin yanayi Sultana ta yi
ƙoƙarin janye hannuntata rumtse idonta wanda duhu mai tarin yawa ya mamaye mata , kana tayi baya baya
zata faɗi, ƙafarta ta sule yasa takuma sakin wani Nannauyan Ajiyar zuciyar
Gaba ɗaya ta sadakar,da faɗuwa,
Jidda da tuni ta fara yi musu video da Snapchat tana Murmushi.
Cikin zafin nama ya janyota da ƙarfi hakan yasa ta faɗa jikinsa.
jinta a jikin mutum ne yasa tayi masa wata irin rugguma mai cike da razani dan gani take kamar dai har
yanzu bata tsira ba.
Kanta ta cusa cikin ƙirjinsa tana mai shaƙan dadɗan ƙamshinsa turarensa mai sanyi da saka natsuwa..
Sultan cikin tsoro da wani irin yanayi abu da yaji ya soƙi tsakiyar kansa har zuwa zuciyarsa yana mai jin
baƙon al'amuri. a cikin jijiyoyin jikinsa da suka sa jikinsa sakin wani, ya ware hannunsa tare da rumtse
idanunsa da masifan ƙarfi....✍️
More comments and share
*Sadeeya Ka'oje ce* ✍️
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)
_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*
💖💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر
﷽
Bismillah........ ✍
PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗
*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 27-28*
_____Cikin sauri Sultan ya janye hannunta daga jikinsa tare da matsawa gefe da sauri.
Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da watsa mata kallon da yasa hantar cikinta kaɗawa. dai dai lokacin Dr
Aryan ya fito daga ɗakin da sauri ya durƙusa kasa ya tattara takardun ya maidasu cikin File kana yamiƙawa
Sultan, cikin wata irin murya mai cike da ɓacin rai ya ce,
“Biyoni!”.
Kaman wata soloɓiyo ta bi bayan sa har zuwa Office ɗin sa,.Ya na so ya ma ta faɗa, ya na so ya nuna ma ta
ko shi waye, amma ba zai iya ba saboda ransa da ke a ɓace.
Tsawon lokacin Sultana na tsaye a Office, ƙanta ta ɗago ta kalli Sultan dake zauna a saman lallausar
kujerarsa yana danna laptop, "Nifa na gaji da tsayin nan"
Ƙoƙarin fice wa ta yi daga Office ɗin,"Come Back"
da sauri ta juyo ta kallesa kaman bashi ya yi maganar ba, a hankali ya mike ya nufi ƙofar fita, sai muka ya
juyo ya kalleta," ki biyo da file ɗin can, ya faɗa a hankali,
"A kwai aikin da Zanyi" Sultana ta ka tseshi daga kallon walaƙanci da yake jifanta dashi..
Shut up" Sultan ya katse Sultana da tsawa.
Hannu Sultan ya kai zai ma ta mari sai kuma ya tsaya yana huci hannun na reto a sama " I'm warning you,
ki kama matsayin ki ko kuma na nuna mi ki"
Haɗiye miyaun da ya tokare ma ta maƙoshi ta yi lokacin da Sultan shi ma ya juya ya bar wajen. Ta gama
sadakarwa Sultan marin ta zai yi. Har ta hango yadda fiskarta zai koma idan da marin ya sauka a fiskarta.
"Aikin banza" ta faɗa sannan ta bar wajen. Da sauri Jidda ta bi bayanta tana kiran sunan ta.
Ta shiga wani ɗaki amma kafin ƙofar ta rufe Jidda yai saurin sa hannu ya tare sannan ya shiga,"Daughter
Lafiya?"
"Nida ɗan renin hankalin can ma ya Kaini Office ɗin sa ya tsayar dani kaman wata kunki." Oh ni jidda
Daughter wai mike tsakin ki da Dr Sultan?"
"Mtsss Sultana taja tsaki
"Daughter pls ki daina fushin nan mana, Allah ɗazu ba ƙaramin dacewa da juna kikayi ba. ta ƙara sa
maganar tare da nunama Sultana video da tayi musu ɗazu,
da sauri Sultana ta fisge wayar da niyar goge video Jidda yayi sauri saka wayar a key, "Allah Bazaki goge
ba Daughter, wlh baki ga yadda mukayi matuƙar dacewa ba ina a ce ki Auresa!"
Juyowa da saurin Sultana ta yi tana kallon Jidda ,"Allah ya kiyaye, Ni matar Nas ce da yarda Allah!
"Nawa ba irin na kowa ba ne
Batun nayi bayani ko jawabi akan sanda zuciyata take masa hakan ba Abu ne mai sauƙi ba na sai san ina
son sa domin ya kasance na mummunan a rayuwata hakan yasa na kulle ƙofa daga kansa ba wani a
gabansa kuma ba wani a bayansa!
Jidda da ta tsura mata ido tana kallon ta kaman ta samu tv.
Sultan Idanu ya zuba musu na wasu sakanni fuska a matuƙar ɗaure. Sai kuma ya ɗauke kansa ya cigaba da
abinda ya keyi.
"Lallai Daughter kin kamu da Soyayyar Nas, to wai Daughter kintaɓa haɗuwa dashi, kai Sultana ta gyaɗa
mata alamar A'a, Jidda ta sauƙe Nannauyan Ajiyar zuciya kana yace ,"Daughter Anya bakiyi kuskure ba?
Yanzu duniya ta sauya Daughter Mutane ba Amana!"
"Nas baya ɗaya daga cikin Mutanen da kike tunani"
"Daughter ya kamata ki....."
"Mommy ya isa pls! Bana son mu samu matsala"
"Shiken Daughter Allah ya tabbatar muku da Alheri"
Fuska a sake tace "Amin Mommy na koke fa"
Jidda ta sauke Ajiyar zuciya. haka suka ci gaba da aiki a ranar har zuwa lokacin tashi kowa ya nufi gida....
Washe gari ta kasance Weekend ne Sultana basu tashiba sai around 9, wanka sukayi sannan mami takawo
musu breakfast sukayi,
Mami takallesu cikin soda k'aunar y'ay'an nata, tace, "kutashi Ku shirya kuje shoprite,
To suka fad'a suna mik'ewa, Sultana tasaka wando da Riga sannan ta ɗaura After dress sunmata k'yau
sosai,
Meena na rik'eda ATM d'in Abba tare da Nana suka fice daga gidan.
Tunda suka Isa shoprite d'in k'irjin Sultana ke bugu da sauri-sauri, addu'a tafara karantowa ahankali,
basuwani ɓata lokaciba suka fara duba abinda suke buk'ata, Sultana ce rik'eda keken🛒tana zaɓa tana
sakawa,
Bugun zuciyarta ne yatsananta, waige-waige tafara, Dan lamarin yafara tsoratata, babu wani alamar abinda
yashafi rayuwarta awajen, Dan haka ta dake tacigaba da duba abinda take buk'ata.
Sanye yake cikin ƙananan kaya sun masa kyau sosai. Taku yakeyi cikin nuna shinfa jarumine mai
wadataccen jini, kasaitarsa da kwarjini sun taka rawar gani wajen bayyana kwarjininsa, dasuka k'ara haska
farar batar sa mai matuk'ar taushi da d'aukar idanu, k'asumba tad'an taru masa afuska, hakama kansa akwai
Y'ar kwantacciyar suma, hakan yanada nasaba darashin lokacin kai, Dan aiki ya cakud'e masa sosai a ɗan
kwanannan.
Yana tafiyane kunnensa manne da waya, magana yakeyi ahankali kuma cikin nutsuwa, Wanda baisaniba
saiya d'auka da matarsa ko budurwarsa yakeyin wayar, fuskarsa babu walwala, yanayi yana duba abinda
yad'auka, saiya d'an karanta kafin yajuyo yasaka a keke.
Wannan salo nasa yayi masifar tafiya da y'an Matan wajen,
Dukda zuciyarta Na masifar harbawa hakan baisa tadamu da kallon waɗanda ke bayanta da gabantaba,
anutse takai hannu zata d'auki wani turare , shima yakai hannu. Akan nata hannun yaɗora nashi, da sauri
kowa yajanye danjin wani masifaffen shock daya jasu atare, lokaci ɗaya suka zubama juna idanu,
burkitattun idanunsa masu girma da haske suka shige cikin Na Sultana manya masu yalwataccen gazar-
gazard'in gashi.
Da sauri Sultana ta janye idonta cikin nasa.
Ahankali ya sauke ajiyar zuciya tareda jan tsaki afili, yacigaba da ɗaukar abinda yakeso.
"Ya Sultana Meena ta kira sunansa cikin tsananin farin ciki, tare suka iso wajensa da Nana, ba kunya ta
faɗa jikinsa ta rungumesa hannu bibbiyu ya sa shima ya rungumeta tare da Nana, yan matan dake tsaye a
wajen ko waccenta ta tsuke fuska 🤣,
A hankali ta janye jikinta, "Ya Sultan ina Mommy da su Salma," Murmushi ɗauke a fusakar yace ,"lafiya
lau suke , " ya Sultan ina nan tafe Weekend ka gaya Mommy idon ka koma gida. Kai ya gyada mata, haka
suci gaba da seyayyar su,
Awajen biyan kud'i suka iske Sultana, Sultan ya miƙama Meena ATM ɗinsa, aiko da sauri ta miƙa ma su
Aiki..
tare suka fito daga shoprite ɗin. Kowa ya nufi motarsa Meena da Nana na yiwa Sultan Bye bye...
Ahaka suka k'arasa gida, suna shiga harabar gidan taci karo da motar Daddy, da sauri suka wuce cikin gida
nan Palo suka tarar da su gabaki dayan suna hira," Daddy sannu da zuwa, suka faɗa a tare ,"yauwa my
Daughter's, daman wajen ku nazo, Mommyn ku tace nazo na ɗaukeku kuyi Weekend a gida, wani irin farin
ciki ne ya lulluɓe Meena da Nana," don haka kuje ku haɗo kayan ku," Daddy Nidai Bazan je ba! Sultana ta
faɗa cike da Shogoɓa," wani irin kallo Abba ya watsa mata, nan take ta kama kanta, ,"Abba ga Atm ɗinka
cewar Meena," Banji debit Alert ba har yanzu. "Abba ya Sultan ne ya biya muna"
"Toh ma sha Allah, maza kuje ku haɗo kayan ku, da sauri suka wuce ɗakin , Sultana na kumbure
kumbure, jim kaɗan suka fito, Kaka ta kalli Sultana cikin tsokana tace idon kunje ina gaida Sultan, wani
irin kallo Sultana ya yi kaka tare da murguɗa mata baƙi... Har bakin Mota Mami ta raka ƴa ƴan nata, dai dai
lokacin kuma Motar Haydar ta jigo. Yana gama Parking suka fito gabaki ɗayan su, "Daddy Abba Ina wunin
ku, "lafiya lau Haydar,"Khalil ya kalli Sultana," Anty Sultana ina zuwa haka ?"
Ya Khalil gidan Mommy zamu tafi Nana ta bashi amsa.
"Allah ya tsare sai mun shigo"
"Amin"
"Ina Arif halam ko bada shi za'a je ba?"
"Ya Haydar bacci yake kansa ke ciwo,
Saida suka wuce sanna su Haydar suka wuce cikin gida.
Tafiyar Mintuna Kaɗan sukayi suka isa gidan Daddy Hon yayi mai gadin ya taho da sauri ya buɗe musu
tamfatsetsen gate din.
Aɓangaren Sultan bayan ya dawo daga shoprite
Side ɗinsa ya wuce,
Ruwa ya watsa tare da sauya kayan jikinsa, wani tattausan riga da wondo blue mai taushi ya zira, tare da
fesa turarensa mai masifar ƙamshi,
System ɗinsa da wayarsa ya ɗauka kana ya fito, a hankali ya lumshe idanunsa jin yadda sassanyar kamshi
turarensa ya mamaye ko'ina
A hankali yake taku wani irin masifeffen kyau yayi collor kayan jikinsa yayi matuƙar amsarsa farar
fatarsa.kai tsaye ya nufi babban palon ya zauna,
Cikin wani irin farin ciki Sultana ke bin ilahirin gidan da kallo ganin yanda flowes da shuke shuken
kayan marmari suka zagaye gidan, Da sauri ta juyo da kallonta kan Meena tare da cewa. "masha Allah wai
daman haka gidan yake da kyau? gaskiya yayi kyau sosai"
ta ƙare mgnar tana lumshe idanunta tare da shaƙar sassayan iskar dake haɗe da ƙamshi flawers,y
"Anty Sultana yanzu kam kin Dena fushi ko? Kinga gida mai kyau?"
"Wallahi Meena gidan nan ya yi kyau sosai komai kuma ya burgeni gawani irin ƙamshi da suke, ji yanda
ilahirin gidan ke fitar da wani Daddaɗan ƙamshi,har Naji ina son yaruwa a gidan nan!"
Meena Kam dariyar dake cinta take ƙunshewa,
Tunda sukayi sallama su Salma da Salim dake falon suka taso da gudu suka rungume Sultana
Meena gefe takoma tana kallonsu cikeda birgewa, saida suka gama murnarsu sannan suka lura da Meena da
Nana , suma suka rungumesu tare da Nana.
"Maraba da baƙi" cewar Mommy.
Lokaci ɗaya suka juya suna kallonta karab Idanunta ya sauka kan Sultan
zaune akan sofa, dagashi sai wando 3quter idonsa a wayarsa yana danne-danne.
Rumtse ido Sultana tayi gabanta Na fad'uwa, bak'aramar firgita tayiba daganinsa haka, Dan damtsen
hannunsa yamugun tsoratata, tai saurin kauda kanta daga kallonsa.
Har yanzu idonsa nakan waya, tare suka wuce tsakiyar palon suka zauna.
Kafeta tayayi da idon nasa, wannan yasakata gaza koda kallonsa,
"Mommy Ina ihsan?"
"Tana ɗaki bansa uban me take kitsawa a ɗakin, kullum tana ɗaki kaman wata Amarya.
"Sultana kun gaisa da Sultan, cewar Mommy. Kai ta gyaɗa a lamar a a'a, bazaki gaida Ogan na Kiba?"
"Mommy nan ai ba Asbiti ba ne" ta yi maganar tana kallon Sultan,
Mommy tayi ya yi Murmushi kana tace," Oga oga ne a duk inda yake Sultana,
Batasan sanda bakinta yasuɓuce tace kamarya? Banda waje na ?, tak'arashe maganar da murgud'a baki.
Aransa yace akwaifa rashin kunya sosai awajen yarinyarnan..
Afili kuma saiya gallah mata harara.
, harta samu kwarin guywar kallon cikin idonsa, amma kwarjinin dake taredashi yasakata saurin janye
idon nata,
Kuttt! Yafad'a yana binta da kallo, yana rasa mizaice, saikawai yaja ajiyar zuciya, dolenema yayi
bincike akan yarinyarnan, danyasan wacece ita?, shifa mamaki take basa, saikace aljana, tunda yake babu
macen data taɓa kallon tsakkiyar idonsa sai yarinyarnan, duk girman mace kwarjini yake mata takasa masa
kallon minti2 ma, bare cikin idonsa, duk jidakan yarinya da isarta, inhar zatazo wajensa tace tana sonsa,
kotazo suyi wata magana, wlhy inhar yadasa mata idonsannan na yan sakannnu kawai saikaga jikinta
narawa, tashiga hankalinta daganin bakin Rijiya bawajen wasan makaho baneba.
Amma yau ga yarinya k'arama, ta kalli tsakkiyar idonsa.
Ya furzar da huci daga bakinsa, Wanda yasaka su Daddy kallonsa.
"Sultana kuje sama kukai kayan a ɗakina.
"Mommy yau a ɗakinki zamu kwana wajen Anty Sultana, Salma da Salim suka faɗa, "Salma a zaku takure
a ɗakin ku barsu Kinji, ,"nan ta ke ta marairaice fuska kakam Zatayi Kuku, Mommy ki barsu zamu kwana a
tare, "A'a sai dai Salma ta kwana tare da kuku, Nana taje ɗakin Ihsan su kwana tare,
"Mommy Nifa".
"Kaje ɗakin Ya Sultan ka kwana, dai dai lokacin kuma su Haydar suka iso da Khalil da Arif, "Yauwa ga Ya
Arif nan ma yazo zamu kwana a tare..
Nan take palon ya ƙara hargitse wa da hayaniyar su, kafinan suka ci Abinci na musamman da Mommy ta
girka musu. Sai bayan Isha'i Ihsan ta fito daga ɗakin fuska a tsuke, sama sama suka gaisa dasu Sultana,
Ƙarfe 8:50 su Haydar suka wuce gida haka a bar Arif.. bayan ta fiyarsu Sultana ta wuce ɗakin Mommy tare
da Meena, "Anty Sultana karku rufe ɗaki ina nan tafe, ,"sai kinzo...
Suna shiga ɗakin Meena ta wuce toilet Wonka tayi ta fito ta saka kayan bacci ta