Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dr Sultan Complete Hausa Novel by Sadeeya Ka-Oje

Author :  Sadeeya Ka-Oje Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 21

15K to 18K   out of 60.6K words

da kallonsa mutumen da sunanshi ya kewaye da duniya,tabbas shine" a hankali Alhaji
Nuraddeen ya ɗago ya kallonsa," Shi kowa sam Baisan Maganar ta fito ba,
ya miike tare da barin ɗakin kai tsaye suka wuce gida.....
Nuraddeen da Abdullahi tare sukayi jam'iya Nuraddeen Mahaifinshi Babban Attajiri ne kuma dan Kasuwa
ne a Kano Nuraddeen shi kadaine ɗanda suka haifa Nuraddeen yana Ss3 Allah ya yiwa Mahaifiyar shi
rayuwa, farkon shigarshi jami'a Allah ya haɗashi da Abdullahi kasan cewar Course ɗinsu ɗaya wasa wasa
shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su Nuraddeen yaro ne mai kirki da kyauta ga tausayi ga son taimako,
yadda yake rayuwar shi da mutane sam ba Zaka dauka ɗan masu kuɗi bane rayuwar shi yake kaman kowa,
shaƙuwar su tayi karfi sosai a makaranta ba wanda bai sannu ba baru wansu da ƴan mata karatun su suka
saka a gaba, bayan sun kammala jami'a sukaci ga da zumunci su, Abdullahi baida wani Aboki a duniya
kaman Nuraddeen haka shima Nuraddeen baida wani Aboki kaman Abdullahi duk abinda zasuyi sai sun
shawarci junan su, Mahaifin Nuraddeen haka ya dauki Abdullahi kaman ɗan cikin sa, Mahaifin Nuraddeen
mutum ne mai matsifar son yara, Haka Nuraddeen ma kusan halayen sa ɗaya da Mahaifinshi...
Nuraddeen can waje yawacen ya wace shi ƙauyuka wajen taimakawa ta takkawa Allah ya haɗashi da
Ummul khairi bafulatanar daji kyakkyawan da ita wasa wasa soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu ba bata
lokaci Akayi Auren bayan Auren su ya saka ta Kamaranta yaƙi da jahilci cikin ƙanƙanen lokacin ta fara
waye a bangaren ilimin Addini ma har gida malami ke zuwa koya mata karatu, bayan Aure su da shekara
Biyu Allah ya yiwa Mahaifin Nuraddeen rasuwa, Nuraddeen ya gaji duk a binda ya mallaka, tsawon
shekara goma sha biyar kenan da sukayi Aure, Allah bai taɓa basu haihuwa ba, likitoci sun tabbatar musu
da duk lafiyar su lau lokaci ne kwai bai yi ba, tun abin na damusu har suka barwa Allah, hakan yasa shida
Matar shi suke tsananin son yara, zuwa yanzu Nuraddeen baida kowa sai matarshi da Abdullahi da ya
kasance tamkar dan uwanshi haka ya dauƙi ƴa ƴan Abdullahi tamkar ƴa ƴan cikin sa wani lokaci a gidan shi
suke hudu ko weekend. Kubra har ta raru basa shiri da Ummul khairi, saboda ƙashi da hassada da tasawa
kanta ganin yadda Ummul khairi ta ke sharhiliya da dukiyar mijinta tare da ƙanwarta Ummul Kulsum,duk
da ta kasance ƴar Attajiri matar Attajiri, Abdullahi duk da ya kasance mai kudi Nuraddeen ya kereshi shi da
komai.....
Wannan kenan....👌🙌🤗
Gab da maggariba ya shigo gida Kai tsaye ya wuce masallaci dake cikin gidan Saida kayi Isha'i kana ya
wuce cikin gida cikin tsastsan farin ciki ta rungumeshi tare da manna shi hot kiss a kumatu, "Sannu da
zuwa Habibi ya mai jiki ina fatan yaji sauki?"
Ya sauke Ajiyar zuciya kana yace jiki da sauki!"
"Masha Allah, Allah ya tashi kafaɗunshi Allah kuma ya baka ladan taimako, "Amin Habibity!!"
Tare suka ci Abinci kana suka wuce daki, sukayi Wonka a tare bayan suna gama shirin suka kwanta
rungume da juna nan take bacci ya yi awon ya gaba su......
*BAYAN KWANA HUƊU*
Zaune suka a Palo suna hira Kaka ta kalli Abdullahi cikin sanyi Murya tace "Abdullah ya kama mu koma
gida! Kodan makarantar Maryam kusan kwanan mu goma sha ukku kenan"
Abdullahi ya sake Nannauyan Ajiyar kana yace," Mama don Allah karon nan ki dawo nan da zama Ko dan
yaran nan! Kafin na samu mai kula dasu.don Allah Mama," nan take Idanunsa suka shiko da kwalla, Su
Haydar suka haɗa baki wajen faɗin "Kaka don Allah karki koma ƙauye! Murya a disashe Maryam tace "
Kaka Nima Bazan iya zama ƙauye ba tunda Ya Maleek baya nan! Nan take maryam ta fashe da kuka,"shike
nan ya isa ki Dena kuka nan zamu ci gaba da zama insha Allahu Kaka ta faɗa cikin sanyi Murya" tare da
sharewa Maryam hawaye, " Nagode sosai mama Allah ya ƙara Miki lafiya da nisan kwana!" cewar
Abdullahi,
"Amman ya kamata mu naje ƙaraye ko don nayiwa maƙotana sallama"
"shike nan mama ko yanzu zamu iya tafiya! " kaka Ni kam ba zanje ba cewar Maryam" Nan take Kaka ta
shirya suka wuce tare da Abdullahi"
*ƘARAYE*
Suna isowa kai tsaye suka wuce gidan cike da kewar Abdulmalik da ke mata gizo a tsakiyar gida, isowar
keda wuya Mutane Unguwar suka fara shigowa tare da yiwa Kaka Gaisuwar Abdulmalik da Kubra, nan
take Mutuwar ta dawo mata sabuwa, cikin dauri ta shiga amsa musu tare da faɗa musu zasu koma birni da
zama, kowa sai tambatayar Maryam yake, haka Kaka ta shiga rarraba kayan Abincinta ga duk wanda ya
shigo gidan, kana ya shiga haɗa musu kayan su da duk wani Abin mafani aka saka a motar Hilux dasuka zo
da ita, "Abdullahi sai batun gida ya za'ayi dashi kasan idon aka bashi ba kowa zai nakkashe miye shawarar
ka," Mama ina ga kwai ki kyautar dashi ga duk wanda kikega dama,
"Bana da sauran dengi a duniya kaman yadda kaima baka saura kowa a duniya. sai Ni, da iyayen
Hauwa'u suna rare sune suka fi cancanta dana mallakawa gidan!"
Abdullahi ya sauke Ajiyar zuciya kana yace Hakane Mama! Barinsa haka zai sa ya lalace ko bata garin su
samu wajen aikata barna"
"zan mallakawa Malam liman idon har ka amince, " Haba Mama miye saina wani Abince damu da gidan
duk a ƙarƙashin ikon ki muke duk wanda kika ba banda matsala!"
"Allah ya yi maka Albarka!"
"Amin Mama"
Bayan sun gama kwashe duk wani abinci mai mahimmanci suka wuce gidan Malam Liman, bayan ya fito
suka gaisa kana ya yi mata gaisuwa, a hankali Kaka ta miƙa mai makullin gida, batare da yasan na miye ba
karɓa,
"Malam Liman zanmu koma Kano da zama Insha Allahu, wannan makullin gidan muna na mallaka mashi
halak malak, cikin tsananin Mamaki Malam liman ya waro ido yana kallon Kaka,
Murya na rawa tace ," Mama kin mallakamin gida, saiga waye shar a fuskar malam liman har ƙasa ya
duƙa tare da yiwa Kaka godiya, Kaka tayi sauri dakar dashi," Haba Malam liman miye abin godiya anan,
da sauri ya nufi cikin gida jim kaɗan suka dawo tare damatar shi, fusaka a sake ta ciga yiwa Kaka godiya....
Haka Kaka riƙa shiga gidan maƙota tana musu sallama, kana suka wuce cike da kewar ƴan uwa da abokan
arziki...Sai bayan Isha'i suka iso gida cike da gajiya nan masu aiki suka fara shigar da kayan cikin gida,
Kaka na shigowa Suka rungumeta gabaki ɗayan su suna mata Oyoyo kana suka wuce daƙi....
★★★
yana shigo wa dakin yana farka da sauri ya nufi wajen sa, a hankali ya fara idanunsa suka kaɗa sukayi jazir
cikin Wani irin mummunan yanayi ya soma magana murya a disashe yana faɗin ,"ruwa Maryama ta! Zan
sha ruwa Kaka ƙishi nake ji!Alhaji Nuraddeen dake tsaye a wajen cikin tausawa yace ",Ruwa kake so? A
hankali ya gyara kai, ruwa masu sanyi ya ɗauko cikin fridge a hankali ya fara murɗa wani ƙarfe dake jikin
gado,, gadon ya fara ɗagowa kana ya zauna kusa dashi ya buɗe marfin gorar ruwa ya ɗora mishi a baki
hannayenshi ya ɗoro saman gorar yana zukar ruwan da ƙarfi har kana iya jin sautin maƙoshinsa dake kwat
kwat cike da tausayawa Alhaji Nuraddeen ke kallo sai, da sauri ya janye bakinsa tare faɗin," Ruwa Kaka
ban kwoshi ba! a karo na biyu yasa ake dora mashi gorar ruwa ya shanye ta tsas kana ya sauke Nannauyan
Ajiyar nan take Zufa ta riƙa tsastafo mishi, dai dai lokacin Dr ya shigo fusakar ɗauke da murmushi, "
Masha Allah ya farka kenan?"
" Ranka ya dade yaushe kashigo?"
Alhaji Nuraddeen ya sauke Ajiyar zuciya mai ɗumu kana yace Ban jiba ina shigo yana farkawa ka"
Nan Dr ya shiga dubashi ," Masha Allah komai ya yi dai dai Insha Allahu, zuwa gobe za'a iya sallamar
shi!"
A hankali ya ware mayan idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir ya sauke su akan Alhaji Nuraddeen dake
zaune," murya a disashe yace ," Ina Kaka Ina Maryama ta!"
Alhaji Nuraddeen ya yi Murmushi kana ya kwantar da hankalinka kaji Wanne gari kake,"Karaye!" Nan
Alhaji Nuraddeen ya bashi labarin inda ya gansa a hankali abinda ya faru ya fara dawo mishi a kwakwalwa
nan take ya fashe da Kuka mai tsuma zuciya, da kyar Alhaji Nuraddeen ya shawo kanshi ya Dena kuka ,"
Kana da Numbar iyayenka na sanar dasu nasan yanzu yana suna cikin tsashin hankali," Murya na rawa
yace ," Iyayena sun rasu! bana da kowa sai Kaka da Maryam!"
Cikin tsananin tausai Alhaji Nuraddeen ya kalleshi kana da Numbar Kaka kota Maryam!?"kabani na
kirasu na sanar dasu Halinda kake ciki? A hankali ya gyara kai nan ya shiga faɗa mishin number kaka Kiran
farko aka sanar dashi number aka take a karo na Barka tai yariƙa kiran Number a kashe daga karshe ya
haƙura...
"Number a kashe take, ko Kanada wata number," A'a!"
"Zan yi Sallah! A karon farko Alhaji Nuraddeen ya saki Murmushi, " Kasan kwananka nawa a Asbitin nan
kai ya gyaɗa a lamar a'a, yau kwanan ka Hudu" a Asibitin nan,,
"Murya a disashe yace yau nawa ga wata?" Alhaji Nuraddeen ya faɗa mishin," Nan ya fahimci iya a
daɗin kwanakin da ya rasa sallah Alhaji Nuraddeen ya taimaka masa zuwa toilet wanka yayi da duwa ɗumi
kana ya yi Alwala ya fito sosai yaji daɗin jikin sa....kasan cewar baida karfi jiki da zaune ya yi Sallah
tsawon lokaci ya dauka yana rama sallalolin da ake biyar shi, duk wani motsin sa akan idon Alhaji
Nuraddeen sosai yaron ya burkeshi,
Bayan ya gama sallah ya zuba mai Abici palpesu kayan ciki kana ya haɗa mishi tea mai ƙauri kana ya
miƙa miƙa mishi," Kaci kasha magani ko Yarona!" da sauri ya ɗago ya kalleshi ya sakar mai murmushi, a
tsanake ya soma cikin Abinci, sosai palpesu ya yi mishi daɗi, bayan ya gama cikin Abinci yasha magani
nan take bacci ya yi awaon gaba dashi.....
Saida Baccinsa ya yi nisa sosai kana ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce gida a gajiye,
Washe gari tunda sassafe ya wuce Asbiti koda ya shigo dakin yana zaune a Dr na dubashi ," Ranka ya
dade sannu da zuwa" yauwa ya mai jiki?" Alhamdulillah zaku iya tafiya gida yanzu," rubuce rubuce ya yi a
takar da kana ya miƙa mishi,
Murya a disashe yace "Ina kwana Baba!" A hankali ya sauke sassanyan Ajiyar zuciya,
"Lafiya lau Yarona ya jiki?" A karon farko ya saki Murmushi kana yace ," Lafiya lau Baba!"
Yauwa sha tea sai mu tafi gida ko, cikin tsananin farin ciki ya daga mishi kai, tea ya haɗa mishi mai kaura
kana ya bashi a hankali ya riƙa sha yana Lumshe ido, bayan ya gama suka fice daga ɗakin tare da yiwa Dr
godiya kai tsaye suka wuce Nasarawa, lokacin da suka iso gidan haka ya saki baki yana kallon gidan a
rayuwarshi ta duniya bai taɓa ganin gida mai kyau irin wannan duk abinda yake a kan idon Alhaji
Nuraddeen, koda suka shigo palon zaune take tana kallon,"Habi..... sai kuma yayi shiru ganin yaron dake
tsaye, fuska a sake ya gaisheta, "gabaki ɗaya ta kasa ɗauke idonta akan shi, "Ummul khairi lafiya?" Tadanyi
Murmushi kana tace ba komai shine marar lafiyan?"
"Ehh shine an sallame shi"
" Masha Allah ,Allah ya ƙara sauki"
"Amin"
Kaisa ɗakin ɓaki ya huta koda yake bari yayi breakfast" tare suka wuce darning shiko sai ɗari ɗari yake
sam ya kasa sakin jikin sa abinci ma kaɗan ya ci, kana ta kaishi ɗadakin baƙi, mashi Allah dakin ne na
Alfarma komi na ɗakin farii ne, " Kayi Wonka sannan ka kwanta ko zakaji daɗin jikin ka" cikin sanyi
Murya yace ," Toh Mama! Nagode"
tana fitan ya kalli dakin da kyau kana ya sauke sassanyan Nunfashi, ƙofor dake like a dakin ya kallon hakan
ya tabbatar mai da toilet ne a hankali ya buɗe kofar ya yi Addu'a kana ya shiga Wonka ya yi da ruwan dumi
ya fito nan ya tarar da kaya saman gado ciki da mamaki ya riƙa bin kayan da kallon,ƙananun kaya ne masu
matsifar kyau da tsada bayan ya saka kayan ya kalli kanshi a madubi ganin yadda ya yi matsifar kyau," Ina
kike Maryama ki ga wannan kyau! Yana jima yana kallon kanshi a madubi, can muka ya ɗan ya mutsa
fuska ganin yadda ya rame, sanyi ɗakin ya sakar mai da matsananciyar kasala hana yasa ya kwanta saman
katafaren kadon ya lunlube da laulausar blanket nan take bacci ya yi awon gaba da shi.....✍️✍️
_More comments and share_
*Sadeeya Ka'oje ce*💋💋
*DR SULTAN*


_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬




Bismillah........ ✍
*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

*The beginning*
*Page 13-14*
___Bacci sosai ya yi sai gab da maggariba ya farka a gurguje ya yi Wonka ya rama sallalolin da bai samu
damar yi ba, yana zauna saman sallah, aka buɗe ƙofar ɗakin a hankali ya ɗaga kansa tare da kallon ƙofar
tsaye take fusakar ɗauke da murmushi," Ka farka kenan?"
tun dazu nake kai da komowa," kai a sunkuye yace,"Mama! Barka da warhaka," Barka kadai Yarona! Ya
ƙarfin jiki?" "Alhamdulillahi!"
" taso muje Kaci abinci ko kafin aka kira sallah"
"Cikin sanyi Murya yace ," Mama saina yi Sallah.maggariba"
"Aa Yarona Ci yana gaba da Sallah don. Haka taso muje Kaci abinci," Kaman wani ƙaramin yaro taja
hanunsa suka wuce Darning da kanta tayi sarcevig ɗinsa Kana ta tura mishi Plate ɗin a gaban sa, a tsanake
ya soma cikin Abinci yana Lumshe ido,"
"Yauwa ko kaifa ba gashi kana gamawa ba ana kiran sallah" dai dai lokacin Alhaji Nuraddeen ya shigo
Palon fusakar ɗauke da murmushi ya kalli matar tashi ," Ya tashi ke nan?"
Murmushi na kara faɗaɗa a fuskarshi tace ya tashi da kyar ya yadda zai ci Abin wai nabari sai anyi
sallah," Raron nan naki inga shine limamin unguwar su ya faɗa cike da zolaya, lokacin ɗaya suka saki
Murmushi,"
"Tashi muje masallaci ko? Kaman jira yake da sauri ya mike tare suka fice daga palon a hankali ta sauke
sassanyan Ajiyar zuciya," Barka da warka Ranki ya daɗe"
"Yauwa Ladidi ya aiki ," Alhamdulillahi"
" ina fatan An kammala Abinci?"
"Ehh Ranki ya daɗe"
"Yauwa a jera komi saman Darning"tana kai ƙarshe Maganar ta wuce ɗakin,
Sai bayan Isha'i suka shigo palon dai dai lokacin ta iso palon ," Sannun ku dazuwa"
"Yauwa"
"Mama ina wuni"
"Lafiya lau Yarona"
"An kammala abinci,"
"Nidai a kwoshe nake bana jin yunwa, aiko zanma ɗure a gidan ta faɗa cikin zolaya" ga baki danyan
su suka wuce Darning Abinci su sukaci cikin. Kwanciyar hankali da natauwa,
Bayan sun gama cikn Abinci Alhaji Nuraddeen ya kalleshi cikin sanyi Murya ya soma Magana,"gashi har
yau bamu san sunanka ba!"
a karon farko ya saki Murmushi tare da fesar da Numfash Kana yace ," Sunana Abdulmalik!" a hankali ta
sauke Nannauyan Ajiyar kana ta fesar da iska," Kallonta Alhaji Nuraddeen ya yi kana yace ,"Lafiya?"
"Ba komai fa!"
"Are you sure!?
Gira ɗaya ta daga mai tare da sakin Murmushi"
"Ma sha Allah suna nan Uncle ɗina!
In sha Allahu idon ka ƙara jin sauƙi sai ka koma gida ko, kar Kaka da Maryam su shiga damuwa," dai sauri
ya gyada mai kai tare da faɗin Ni Ko yanzu ma zanje wajen su!
"Mai sunan Uncle yanzu kam dare ya yi " ka bari ka huta nida kaina in sha Allah zan maida ka gida!"cikin
tsastsan farin ciki ya yi mai godiya,
"Kaje ka kwanta ko" a hankali ya mike Kai tsaye ya wuce ɗaki ya watsa ruwa Kana ya kwanta cike da
kewar Maryam da Kaka da haka har Bacci ya yi a won gaba shi......
★★★★★..........★★
Jikin Abdulmalik ya yi sauki sosai Alhamdulillah kwana huɗu kenan da samun sauƙin sa, tunda sassafe
suka wuce Ƙaraye cike da zumuɗin ganin Maryam da Kaka, lokacin da suka iso da taimakon Abdulmalik
Alhaji Nuraddeen ya iso gidan su Kaka, . lokacin da suka iso yara cike a ƙofar gida wasu na shiga sawu na
fitowa masu shiga kowannen rike da kaya, cikin tsananin damuwa da tashin Abdulmalik ya fito daga Mota
lokacin da yaron Unguwa sukayi ido huɗu dashi suka kwasa a guje tare da faɗin fetalwa ta shiga gari, nan
take mutane suka fara guduwa, da farkon abin yaba wa Alhaji Nuraddeen dariya, nan take gari ya dauƙa da
labarin bayyana Abdulmalik,
haka mutane suka tsaya cirko cirko a ƙofar gidan Kaka, cikin tsananin tashin hankali da ruɗu Abdulmalik
yariƙa binsu da kallo ɗaya ba dayan ɗaya,
Alhaji Nuraddeen ya yi gyaran Murya cikin sanyi Murya ya soma magana ," wai mike faruwa?"
Nan hankali kowa ya dawo kan Alhaji Nuraddeen," lokaci ɗaya mutanen dake wajen suka sauke
Nannauyan Ajiyar zuciya," Abdulmalik daman kana yare?"
Sai lokaci Alhaji Nuraddeen ya fahimci mike faruwa,
Ayuba yaci gaba faɗin ai tsawon sati Ukku kenan da labarin mutuwarsu, Alhaji Nuraddeen ya sauke
sassanyan Nunfashi kana yace," Abdulmalik bai mutu ba nan ya shiga basu labarin da Abdulmalik ɗin ya
bashi har izuwa haɗu warsu, sosai Al'ajabi ya kama su da jin Labarin da Alhaji Nuraddeen ya basu,
Sai lokacin Abdulmalik ya samu damar ya yi magana cikin raunin Murya ya soma magana," Ina Kaka da
Maryama ta!?" dai lokacin Malam liman ya iso ƙafar gida da farko ya tsorata da ganin Abdulmalik tsaye,
cikin ɗauriya ya ƙaraso wajen tare da ba Alhaji Nuraddeen hannu suka gaisa kana ya maida kallon da
Abdulmalik. Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare dashi ya gaida malam Liman,
Kana Alhaji Nuraddeen ya shiga yiwa Malam liman Abinda ke tafe da su da labarin abin ya faru, Cikin
tsananin mamaki Malam Liman ya Kalli Abdulmalik cikin sanyi Murya ya soma tambayarshi ya jiki,"
Murya a dishace ya soma magana ," naji sauƙi!"
"Allah ya ƙara sauƙin!"
"Malam Liman ina Maryama da Kaka!"
Nan Malam Liman ya shiga bashin labarin koma warsu Kaka birni, cikin tsananin tashin hankali jikinsa ya
soma karkawa," sai kuma ya

6 / 21