Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dr Sultan Complete Hausa Novel by Sadeeya Ka-Oje

Author :  Sadeeya Ka-Oje Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 21

3K to 6K   out of 60.6K words

matan ta soma kiran sunanshi ciki wata irin zazzaƙar Muryar mai cike da
natsuwa," Abdul M.....!" dai dai lokacin ya farka daga baccin da yake cikin wani irin ya nayi, wata irin Zufa
ce me bala'in ɗumi ke sauƙo daga saman kanshi, cike da Razata da kaɗuwa, dafe kai ya yi dake junjuyawa,
ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar mai ɗumi ya juya gefen hagu ya kwanta ta re da yin Addu'a ya sake
juya hannu izuwa dama ya yi Addu'a...
Sam bacci ya ƙi zuwa sai faman juyi yake cikin wani irin mummunan ya nayin da ke faruwa dashi duk
lokacin da ya yi irin wannan markin da yake duk bayan shekara, karatun Alkur'ani ya riƙa cikin sassanyan
murya mai cike da kasala.. cikin ikon Allah ya samu bacci ya yi awon gaba da shi......✍️✍️✍️
_More comments and share_
*Sadeeya Ka'oje ce*✍️
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬


.Bismillah........ ✍
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*

*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*

*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
*Page 3-4*

_______ Washe gari , gaba ki ɗaya yinin wannan Rana haka ya yini a kasalance, komai a hankali yake
yinsa, zaune suke a tsakiyar gida, suna hira, Kaka ta kalleshi cikin sanyi Murya ta soma magana,
"Abdul Maleek mike da munka"? cewar Kaka, " sassanyan Nunfashi ya sauke, " Ba komi Kaka, gaji ya
kawai ke da muna, " Ka tattabar ba komi"? A karon farko ya saki Murmushi,"ALLAH Ba komai Kaka!,
"Shikenan, "taso muyi karatu, ya faɗa yana kallon Maryam dake kwance, a hankali ta mike ta nufi daƙi ta
dawo dauke da jakar Makarantar, nan suka soma yin karatu cikin natsuwa da kwanciyar hankali, kana ya yi
musu sallama, bayan ta fiyar shi Kaka ta rufe gida kana suka wuce ɗaki suka kwanta,
Washe gari ma haka ya tashi ba wani kuzahari, jikin sa ya musu sosai da mafarki, duk da ba wannan ne
karo na farko da ya fa irin wannan mafarkin, tawon sati guda kenan yana fama da kasala, Kaka tayi
tambatayar duniya ya ki ya faɗa mata,
Bayan Isha'i kamar ko yau she tana tsaye a ƙafar gida, tana jiran da wowar shi, ta ɗau tsawon lokaci
tsaye a ƙofar gida tana jiran da wowar shi, " Maryam wai miki ke a waje"? " Kaka Ya Maleek nake jira!"
Ajiyar zuciya Kaka ta sauke, tare da faɗin Allah ya sa yaron nan lafiya yake? bai taɓa kai irin wannan
lokaci ba, "Allah ka tsare shi a duk inda yake"
Cikin tsananin da muwa Maryam ta shigo gida, " Kaka ya Maleek bai dawo ba har yanzu ta faɗa kaman
Za tayi kuka, Murya na rawa tace" Kaka muje mu nemo shi Kaka!" Bata jira me Kaka zata ce ba ta wuce
ɗakin ta ɗauko jiha bi da fitala, kana suka fice daga gidan hankali a tashe, saboda bai taɓa kar War haka ba,
"Kaka ko zamuje Kasuwa ƙila yana can, Maryam ta faɗa a hankali, "Bana tunanin yana kasuwa wani
lokacin idon Oga ya riƙe shi a kasuwa, yakan kirani da wayar Oganshiya ya sanar dani, " Kaka ƙila ya ƙira
ba Network, "da wuya idon yana Kasuwa, ganin Maryam ta matsa sai sunje kasuwa,hakan ya sa suka wuce
kasuwa, Nan mai shagon ya sanarda su tun bayan Isha'i ya wuce gida, cikin tsananin tashin hankali da dake
tattare dasu, suka baro kasuwar,Nan suka ruƙa neman shi cikin Unguwa,duk sun san baya zuwa gidan
koma ha salima ko aboki Baida idon ka ganshi tare da wani to Maryam ce, " Kaka ko zamuje ɗakin sa"?
cewar Maryam, "Anya wuya yana ɗakinsa, "Kaka muje mu duba, Haka suka ɗunguwa zuwa ɗakinsa, iso
warsu ya yi dai dai sakin wata irin ƙara mai razanarwa, nan take jikin Maryam ya soma
ƙarƙarwa,"“Innalillahi wa innailaihi raji'un!! Abdul Maleek ta kira sunansa a rauna ce, da sauri ta nufi cikin
ɗaƙin, tana kiran Sunanshi" Abdul Maleek! Abdul Maleek!! tsawa tayi cak, tuni Abdul Maleek ya suma
babu a lamar Nunfashi atare dashi, Rungumeshi Kaka tayi tana kiran Sunanshi, cikin tsananin tashin
hankali Kaka ta fashe da Kuka tana kiran Sunanshi....
A Ɓangaren Maryam tuni ta fita haiyacinta,
jikin Kaka sai karkarwa da kyar ta tattaro ƙarfi ta, kana ta janye shi daga jikinta, ta zuba Nishi ruwa, ya
sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, a hankali ya shiga karanto Addu'oi cikin ikon Allah hankalinsa ya fara
dawowa jikinsa, a hankali ya ɗago da idanunsa da suka kaɗan sukayi jazir ya kalli Kaka ya yi ƙasa da
kanshi, Murya a dishace ya ce "Kaka! zasu tafi dani sai kuma ya fashe da Kuka, A razaje Kaka ta ɗago ta
kallesa Zuciyarta na bugawa da ƙarfi idanunta a kansa, "Suwa ye zasu tafi da kai Abdul Maleek!" su tafi da
kai su kaika Ina?"
Kai ya gyaɗa mata cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare dashi ya fashe da kuka mai tsuma
zuciya, Murya a dishace yace,"Kaka wlh tafiya zasuyi dani Kaka bana son rabuwa daku! "Kaka Ina
Maryama ta!"
Wani sabon Kuka Kaka ta fashe dashi tana girkiza kai" Abdul Maleek ba inda zasu kai ka, Abdul Maleek
sam baya cikin Haiyacinsa sai sabbatu yake,
Maryam dake baƙin ƙofa tana sauraren sabbatu da Abdul Maleek yake, ta durƙu she a wajen ta saki wanin
irin marayan kuka,
Kwallnshi kaka keyi cike da tausayawa ganin yadda ya takure a waje ɗaya yana sabbatu, cikin
raunan'nanyar Murya Abdul Maleek yaci gaba da fadin "Kaka gasu nan zasu tafi dani, Wayyo Allah na!!
nan Kaka ta shiga tafa Nishi Addu'oi, a hankali ya fara sauke Ajiyar zuciya, Nan take jikinsa ya sake, sai
lokacin Maryam ta samu damar shigowa ɗakin, cikin tsananin tashin hankali ta kalli Kaka Murya a dishace
ta ce,"Kaka don Allah karsu rabani da Ya Maleek! zujjuya kai ta farayi kaman zautacciya hawaye na bin
fusakar ta cikin muryar Kuka ta soma kiran Sunansa, "Ya Maleek karka tafi ka barni don Allah Ya Maleek
idon ka tafi ka barni mutu.... ta kasa ƙarasa maganar tayi sai kwai ta fashe da Kuka..... Kaka kam tunu
jikinta Ya yi sanyi, Ajiyar nan ta sauke tare da fesar da Numfashi, cikin raunin Murya ta ce "Maryam ki
dena kuka karki ta dashi daga bacci Kinga da kyar na samu ya koma Bacci, da sauri tasa hannayenta tana
share hawayen, "Kaka na dena Kuka" murmushi ƙarfin hali Kaka tayi kana tace Yauwa " Yar Albarka!"
haka suka kasance a dakin na ɗan wani lokaci, lokaci lokaci kaka na tofa mishi Addu'oi, shiko sai sauke
Ajiyar zuciya yake, fusakar shi tayi fayau duk da bacci yake Amman tashin hankali da fargaba ke kwance a
saman fusakar sa,,
Wuraren 11:30 ya fara buɗe idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir bishi bishi yake gani cikin wani irin ya nayi
ya danƙi hannu kaka cikin nasa bugun zuciyarshi na tsananta,a hankali ya fara buɗe idanunsa da sukayi
masifar nauhi ya sauke su a kan Kaka dake riƙe da Hannu sa, Maryam ta ɗora nata a sama, cikin wata irin
murya mai ciki da rauni yace "Kaka zansha ruwa!" da sauri Maryam ta janye hannunta ta ɗebo ruwa cikin
robar fenta dake cikin ɗakin, "Gashi Kaka a hankali ya ɗari da kanshi Maryam ta saka Nishi ƙofin A baki
haka ya riƙa zukar ruwan maƙoshin na bata wani irin sauti kwat kwat tas ya shanye ruwan, wata irin Zufa
ce ta riƙa tsastafo mishi daga saman kai, ya sauƙe sassanyan Numfashi, Murya a dishace yace, " Nagane
Maryama ta!."Abdul Maleek me kame ji Yanzu? Kaka ta tambataye shi cike da kulawa" Murmushi ƙarfin
hali ya yi cike da ɗauriya, " Bana jin komi kak, " Ka tabbatar"? Kai ya gyada mata a lamar ehh, tashi muje
gida ka kwana a can kaga dare yayi ba'a san me zai faru ba, "A'a Kaka ki bari kwai zan kwana a nan,
Maryam kowa idanuta ne suka shiko da kwalla, cikin sanyi Abdul Maleek ya dafa kafaɗar Maryam, cikin
sanyi Muryar mai cike da natsuwa," Maryama ta kiyi haƙuri ki Dena kuka Kinji kina son Nima nayi
kuka!"? da sauri ta girkiza kai, "Yauwa" Kaka kam sai kallon su take, Ajiyar zuciya ta sauke tare da fesar
da Numfashi ta kalli Abdul Maleek ɗin, " kasan baka da Lafiya me saya Baka je gida ba? A hankali Abdul
Maleek ya tauna lip dinsa, cikin sanyi Muryar yace," Kaka wlh lafiya kau na baro kasuwa, ina shigowa
Unguwar nan kaina ya yi mugun sarawa nan take zazzaɓi mai ƙarfi ya rufeni da kyar na iso ɗaki na tare da
taimakon Kabiru" Kaka ko ido ta tsurawa Abdul Maleek kaman mai son gano wani Abu, A karon farko ya
saki Murmushi...✍️✍️
*DR SULTAN*
*( THE BEGINNING)*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬




Bismillah........ ✍


https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*

*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
*Page 5-6*
_________ A karon farko ya saki Murmushi wanda ya fito daga ai nihin zuciyarshi, Nunfashi Kaka ta fesar
tare da sauke Ajiyar zuciya, Kana tace "Maryam tashi mu tafi gida dare nayi, a hankali ta ɗago idanunta
suka sarƙe da na Abdul Maleek daya wani irin zuba mata matattun idanunsa da suka sake can launi izuwa
ja ko ƙittawa baiyi, cikin wani irin yanayi na tsananin kunyarsa da take a kwana nan, tayi sauri janye Idonta
daga nasa, cikin sanyi Muryar mai dauke da kunya tace ," Ya Maleek Saida safe" jin Muryar Kaka ta faɗin,"
Abdul Maleek zamu tafi Allah ya ƙara sauƙi!, " Mu tafi Kaka"
Jin Muryar Maryam ta ratsa dodon kunnesa ya yi sauri Lumshe idanunsa, tare da sauke sassanyan
Numfashi, " Kaka bari nazo na raka ku, "A'a Abdul Maleek yi zaman ka kaida baka da Lafiya,"Kaka bana
jin komi yanzu, "a'a Abdul Maleek" tana kai ƙarshe Maganar ta ja hannu Maryam suka fice daga dakin kai
suka wuce gida....
A hankali ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, tare da fesar da Numfashi mai Zafi, nan abinda ya faru da
shi ya riƙa dawo mishi a kwakwalwa, "Ya rabb" ka kareni daga wannan mummunan Al'amari, narar yabaki
ɗaya bai runtsaba, haka ya kwana yana nafilfili tare da kai kukan sa ga Allah sai gab da Assuba mai mai
daɗi yayi awon gaba da shi......
A ɓangaren Kaka ma ranar bata runtsa, Washegari tunda sassafe ta wuce gidan Liman, dai dai lokacin
zai shiga gida dawowar shi kenan daga masallaci, "Mama ina kwana, ya faɗa cike da girmamawa, "Lafiya
lau malam liman ya iyali," Alhamdulillahi Mama"
"Mushiga daga ciki" yayi maganar tare da nuna mata ɗan ƙaramin ɗakin dake suka dasu,
Bayan sun shiga sun zauna, Mama ta Kalli Malam liman, ta sauke sassanyan Nunfashi cikin sanyi
Murya ta soma magana," Malam Liman batun Abdul Maleek ne, lamarin nashi sai ƙara tsauri yake, nan ta
shiga bashi labarin abinda ya faru jiya, Ajiyar zuciya Malam Liman ya sauke tare da kallon Kaka da jikinta
duk Ya yi sanyi, "Mama tabbas akwai wani babban Al'amari dake tattare da wannan yaro! Daga ɗayan
Ɓangare kuma kwai masu son cutar dashi, jin haka yasa a tsorace ta zaro ido jin Abinda Malam liman ya
faɗa" Malam liman wannan wane irin Al'amari ne?"
" malam Liman Meye ma fita yanzu?" Kaka ta faɗa a rauna ce, "Mama mafita ɗaya ce ya dage da Addu'a
saboda rayuwar shi tana cikin hatsari mudɗin miyagun mutanen nan sukayi nasara a kanshi, "Innalillahi!
Allah ka tsare shi daga Sherri su..."
"Amin ya Rabbi Mama ina Abdul Maleek ɗin yake? Nunfashi Kaka taja kana ta fesar, cikin tsananin
damuwa da tashin hankali da take ciki Murya a dishace ta ce,"yana ɗakin sa, komi Malam Liman bai sake
cewa ba, rubuta ya somayi a allo cike da natsuwa bayan ya kammala ya wonko da ruwan zam zam kana ya
zuba su cikin gorar ruwa, " Yauwa Mama ga wannan ya riƙa sha yana shafe jikinsa, hannu biyu Kaka ta
karɓi gorar ruwa cikin tsananin farin ciki ta shiga yi mai godiya, da sauri ya da katar da ita cikin
girmamawa ya soma magana"Haba Mama miye abin godiya ai yiwa kaine, mahaifin ya Ron nan kafin
Allah yayi mashi rasuwa munyi zaman mutunci dashi Allah dai ya tsare shi daga sharrin miya gun nan,
"Amin ya rabbi Malam Liman"
"Ke ma Allah ya biya ki Mama yadda ki kayi tsayin daka akan Abdul Maleek Allah ya ƙara Miki lafiya
da nisan kwana!"
"Amin Allah ya yi Albarka!" har ƙofar gida ya rakata kana ta wuce gida cike da ƙwarin Quiwa, tana
gab da shiga gida Abdul Maleek ya iso fuskar shi ɗauke da murmushi kallo ɗaya zaka mishi ka fahimci
akwai reshin isasshen bacci a tattare dashi, cikin sun kuyar da Kai da Muryar shi dake dishace har yanzu
yace " Kaka ina kwana,"Abdul Maleek an tashi lafiya?"
"Lafiya kau Kaka, " ya jiki?" haka ta riƙa jerin mai tambayoyi yana bata Amsa, kana suka wuce cikin
gida,
da guda Maryam ta ƙaraso wajen shi ta rugumeshi ya ɗanyi baya kaman zai faɗi, "Ke kiyi a hankali fa karki
kada shi, cewar Kaka,
Kai ta cuta cikin ƙirjinsa tana shaƙar dadɗan khamshi mai daɗi, cikin wani irin ya nayi mai cike da
kasala ya fara janyeta daga jikinsa, " Ya Maleek! "
Hakan yasa ya buɗe idanunsa cikin sauri ya janyeta daga jikinsa tare da matsawa gefe kallo ɗaya yayi
mata ya kawar da kai gefe, maryam ta Lumshe ido ta buɗe akan fusakar sa, " Ya Maleek jiya bakayi bacci
ba?"
Juyawa ya yi ta re da kallon Kaka, cike da tsuke fuska yace, "Nayi!"
Kallon Mamaki kaka ke masa,
Wani irin kallo ya watsa mata cikin ɗaya girarsa ta sama," Kiyi sauri mu wuce makaranta, a Gurguje suka
karya, kana Kaka ta bashi ruwan maganin ya sha ba tare da yasan na miye ba, saboda ya san kaka bazata
cutar da shiba bayan ya sha ya shafe jikin sa, kana suka fice daga gidan, yana kaita makaranta, kana ya
wuce kasuwa......
A hankali kwanaki sukaci gaba da shuɗewa, ya yin da Kaka taci gaba da ba Abdul Maleek rubutu da
Malam Liman ke aiko mata duk safe, a ɓangaren Abdul Maleek da Maryam shaƙuwar su sai ƙara ƙarfi
take.....
tunu Su Maryam sun kammala jarabawar su, Ranar da ta karɓo sakamakon ta, Ranar kowa ya shaida
saboda tsananin farin ciki da take ciki, Ƙasan cewar ta ƴarinƴa mai kwazo tun shigarta makarantar ita ke
dauƙar na ɗaya a class ɗin su, duk da sunyi Hutu kullum dare sai sunyi karatu kaman yadda suka saba, a
ɓangaren islamiya tana daya daga cikin yara masu kwazo da hazaƙa, tana daga da cikin wa ƴanda zasu
sauke a shekarar nan....
*WAIWAYE ADON TAFIYA*
Malam Aliyu Gwani shine cikakken sunan mijin Kaka, Babban Malami ne mai tarin ilimin Addini, daya
taka muhimmiyar rawa a duniyar Musulunci, Kasan cewar ya yi gwagwarmaya Rayuwarsa ta neman
ilimin lokacin ƙuruciyar shi a garin ƘARAYE ta jahar Kano , hakan yasa ake kiran sa Malam Gwani
Ƙaraye,
matar sa ɗaya A duniya Maryam (Kaka) wanda ta Kasance ƴar Gwoggon sa, Ƴaƴansu biyu Abdullahi
shine Babba sai Ibrahim Mahaifin Maryam dun daga Ibrahim Kaka bata sake haihuba, haka suka ci gaba
da renon yayan su cikin kwanciyar hankali Abdullah da Ibrahim sun taso cikin haɗin kai da tausayin juna
da kyaunar junan su hakan yasa iyayayen ke tsakanin son su komai a tare suke, Haka kwanaki suka ci gaba
da shuɗewa zuwa yanzu Abdullahi da Ibrahim sun zama samari, tuni sun kammala secondary school, har
Abdullah ya tafi jami'a, Ibrahim kuma ya ci gaba da neman ilimin addini a wajen Mahaifinsu, ya Rayuwa ta
yi ta tafiya cikin kwanciyar hankali, Abdullahi bayan ya kammala jami'a Malam Aliyu Gwani ya basu jari
suyi kasuwanci cikin hukunci Allah kasuwancin su ya fara ha ɓaka ciki suka biyawa iyayen na su aikin
hajji,
Koda suka dawo sun gida musu guda dai dai da na masu kuɗin ƙauye, suna da kamfani da ke sarrafa
shimkafa kan farashi mai sauƙi kamfanin su sanannen kamfanin ne saboda sauƙin kayans su, wanda suka
saka wa *GWANI RICE LMD* Zuwan da Abdullahi yake a birni nan Allah ya haɗashi da Kubra
Galadima mafinta babban Attajiri ne kuma sananne, itace ƴa ɗaya tilo a wajen sa, Kubra yarinƴa ce da tashi
cikin gata, tun tana kara Mahaifiyarta Allah ya yi mata rasuwa wajen haihuwa, cikin ƙanƙanen lokaci
Soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, ba wani bata lokaci kayi buki taro ya tashi lafiya, Ranar su Kaka
suka kai masu ziya a birnin sam basu samu tarɓar kwarai ba daga wajen Kubra daga karshe dai suka tattara
kayan su suka dawo ƙauye, bayan Auren su da wata biyu Allah ya yiwa mahaifin Kabra Rasuwa, sun shiga
tsakanin tashin hankali hakan ya haifar da zubewar ɗan ƙaramin cikin da take ɗauke da shi, saida ta yi
jinya a Asbiti tsawon sati biyu, haka suka ci gaba da rayuwa, cikin kwanciyar hankali Azziki tana haɓaka,
tsawon shekaru biyu kenan da Auren, zuwa yanzu Ibrahim ya zama cikekken Malamin Addini kaman
Mahaifinsu, a dayan ɓangaren kuma babban Attajiri a ƙauye su, lokacin Hauwa'u ta kawo masu jiya ɗayar
ƙanwar Kaka, Yarinya ce kyakkyawa ga natsuwa da kunya, soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninta da
Ibrahim hakan ya yi wa Kaka daɗi Kasan cewar ƴar uwarci ce ta ko'ina, bada ɓata lokaci ba akayi bukin su,
suka tattara kuka wuce Birni Kasan cewar gidan su a haɗe yake, a lokacin Kubra ta shiga da muwa da jin
gida ɗaya zasu zauna da Ibrahim, tunda Hauwa'u ta tare a birni bata jituwa da Kubra kullum cikin hantarar
Hauwa'u da zaginta taken da ita har Ibrahim ɗin ita a tunaninta dukiyar Abdullahi suke

2 / 21