Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dr Sultan Complete Hausa Novel by Sadeeya Ka-Oje

Author :  Sadeeya Ka-Oje Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 21

6K to 9K   out of 60.6K words

so, don bai taɓa
gaya mata dukiyar su a haɗe take ba, saboda Ibrahim ba dukiyar ce a gabanshi ba, Hauwa'u da Ibrahim
Rayuwar suke cikin tsananin farin ciki da kyaunar juna...
Kubra tun barin da tayi bata koma samun ciki ba, lokacin da ta fahinci Hauwa'u ciki gare sosai hankalin ya
tashi ƙiri ƙiri take nuna tsanar cikin, Abdullahi sam baya jin daɗin halaryar Kubra haka Ibrahim sukaci
gaba da renon cikin su cikin kwanciyar hankali, har Allah ya sauketa Lafiya ta haifo Kyakkyawar ƴarta,
murna wajen Abdullahi ba'a ko magana, narar suna yarinƴa ta ci sunan kaka Maryam, Kaka ta hana a saka
mata laƙani, wani lokaci su kira Maryam ko Mamana,
Maryam nada sheka ɗaya Allah ya yiwa Malam Gwani Rasuwa, ba ƙaramin tashin hankali suka shiga
ba, wannan lokaci Kaka tai kaman ta zare don ƙiɗima, Abdullahi shine ya zame musu Mahaifinsu bayan
rasuwar malam Gwani ya kama mahaifiyar su ɗa danwan shi, suka haɗa kansu ba mai jin su sai Allah suna
kyaunar junan su matuƙa da mutunta juna, komai zasuyi sai sun shawarci juna, bayan Kaka ta gama ta kaba
ba yadda basuyi ta dawo birnin ba taƙi haka suka haƙura suka barta, lokacin lokacin sukan kai mata ziyara,
itama takan kawo musu ziya, idon yazo har ta koma ba wani a bin ƙirƙi dake shiga tsakanin da Kubra,
rayuwar suke cikin kwanciyar hankali, Ranar da aka yaye Maryam suka shiya zuwa ƙauye kai maryam
wajen Yaye a hanƴar su ta dawowa sukayi hatsari nan take suka rasu,
A lokacin ba ƙaramin tashin hankali Kaka ta shiga ganin gawarwakin su a bangaren Abdullahi har akayi
jana'izar baya cikin Haiyacinsa, duk sanda Maryam take kukan yunwa haka zasu saka ta a gaba suna kuka,
tana kukan reshin Nono suko suna kukan tausayi ta, hakan ya sa suka ɗauƙi son duniya suka ɗorawa
Maryam, bayan wata biyu da rasuwar su Abdullahi yaso Mama ta dawo ɓangaren Ibrahim da zama taƙi
haka ya ƙukura ya barta a kyauye.
Maryam nada shekara Biyu da Rebi Kubra ta haihu murna wajen Kubra ba'a ko magana, Ranar suna Yaro
yaci sunan Malam Aliyu suna kiransa Haydar, Maryam tana son Haydar sam Kubra bata son Maryam ta
raɓeshi, duk yanda Abdullahi yake iya ƙoƙarin sa wajen nuna mata Maryam da Haydar duk ɗaya ne, sam
taƙi ɗaukar haka, daga ƙarshe ma ta ƙarar tsanar Maryam saboda irin son da Abdullahi da Kaka sukale~~~~
mata...
Bayan ƙura ta lafa aka raba gado Kaka da Abdullahi duk suka barwa Maryam, sai a lokacin Kubra tasan
dukiyar su a, haɗe take, Haka Abdullahi yaci gaba da juya Dukiyar maryam tare da tashi, Rayuwa naci
gaba da huɗewa, zuwa Kurba ƴaƴanta Ukku Haydar, Khalil, Hauwa'u, suna kiranta Nana, zuwa yanzu
Abdullahi Baida kowa sai Kaka da iyalinsa..... Haka Kaka taci gaba da kula da Maryam cikin kwanciyar
hankali, Abdullahi baya babbata Marayam da ƴaƴan sa, lokacin da ta cika shekara Ukku Abdullahi ya matsa
su dawo birnin saboda karatun Maryam ba yadda Kaka ta iya suka tattara suka dawo Birnin badon ta soba,
zuwanda ya zame mata damuwa, tunda Kaka da maryam suka dawo birnin da zama, Kurba na kullum
cikin Habaice Habaice take tana faɗin, tunda an raba gado an ba kowa nashi zaman me suke a gidan, ko so
suke suga bayan dukiyar Abdullahi, tun Kaka na haƙuru har takaiga yiwa Abdullahi magana ya jawa
Kubra kunne, hakan ya janyo tashin hankali tsakanin Kubra da Abdullahi har ya haifar da saki tsakanin su,
Ganin haka yasa Kaka ta yenke shawarar suka koma ƙauye tare da Maryam, ranar da zasu Tafi Abdullahi
da Hawayen shi, a ganin sa kaman bai riƙe Amana ba, nan Kaka tashiga lallashinshi kan yayi haƙuri
karatun birni da ƙauye duk inda mutum yayi bazai wuce Azzikinshi, tunda suma a ƙauye sukayi karatu har
suka kai matsayin da suke a yanzu, sosai maganar Kaka ta shigeshi bayan sun koma ƙauye ya gyara musu
gida da duk wani abun buƙata, saboda Kaka ba mai son kyale kyale ba ce, sam zaka ce tana ɗaya mai
kudin, duk da hakan gidan ta na ɗaya daga cikin gidajen masu kyau a ƙauyen kayan Abinci duk wata yake
turo mata.. haka suci gaba da rayuwa cikin kwanciyar da walwala... tuni an saka Maryam makaranta...
Abdul Maleek yaro ne na tsastse dawowar ƙaunyen bada jimawa Allah ya yiwa mahaifiyar shi rasu,
haka suka ci gaba da rayuwa tare da Mahaifinshi, a lokacin shekarar sa goma, zuwan da yake gidan Kaka
ɗibar ruwa nan Allah ya haɗa jinin shi da Maryam, wata irin shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, Ranar
da ba makaranta idon ya zo gidan su Maryam baya koma sai dare, Mahaifinshi ɗan kasuwa ne yana sayarda
dabbobi, duk lokacin da zaiyi tafiya a gidan kaka yake Barin Abdulmalik Kasan cewar Baida ɗan Uwan a
garin Kaka ce ta zame mishi dengi, haka suke rayuwa tare da Mahaifinshi cike da kyaunar juna, Mahaifin
Abdulmalik mutumen girki ne.
Abdulmalik na jss3 Allah yayi wa mahaifinsa rasuwa a can garin da yake zuwa kasuwanci, lokacin da
labarin mutuwar ta riski kaka da Abdulmalik sun shiga tsakanin tashin hankali, haka yaci gaba da rayuwar
shi cikin kulawar Kaka da ta ɗokeshi tamkar jikanta, ba yan rasuwar mahaifinsa ba yadda Kaka batayi ba a
kan ya dawo gidanta da zama ya ƙi a cewar shi baya son barin gidan saboda mallakin Mahaifinshi ne, da
taimakon Kaka Abdulmalik ya kammala Secondary, Abdulmalik yaro ne mai son neman na kasan ka,
bayan ya kammala Secondary yaci gaba da neman aiki duk da bai rasa komi ba duk abinda yake buƙa
Kaka nayi masa, hakan yasa ya nemi aiki a kasuwa nan Allah ya haɗa shi Oga Kabiru da yake fake masa
shago da ɗan aikace aikace duk sati yake biyan shi dubu biyar.. Kasan cewar Abdul Maleek yaro ne mai
natsuwa da Amana hakan yasa Oga Kabiru ke ƙaunarsa duk lokacin da yake zuwa birnin sayen kaya da
Abdulmalik yake zuwa Kasan cewar bai yai karatu ba duk cikin yaran shi ba kaman Abdulmalik...
Maryam ƴarinƴa ce kyakkyawa fara Masha Allah don tana kama da mahaifiyarta sosai maryam ƴarinƴa ce
mai shegen wayo ga reshin tsoro ga tsiwa ga miskilanci akwai shaƙuwa sosai tsakinin Abdulmalik da
Maryam...
wannan kenan....🤗
Bayan Isha'i suna zaune a tsakiyar gida, Abdul Maleek ya shigo gida da guda Maryam ta nufi wajensa ta
rungumesa, tana faɗin "Sannu da zuwa Ya Maleek!"
Sassanyan Nunfashi ya sauke cike da gajiya yace "yauwa Maryama ta!"
"Barka da dare Kaka,
"Abdulmalik An dawo lafiya?"
"Lafiya lau Kaka" yana gama cikin Abinci sukayi karatu, kana ya kalli Kaka cikin sanyi Muryar yace
"Kaka gobe idon Allah ya kaimu zamuje Birni sayen kaya tare da Oga, Nunfashi Kaka ta ja kana ta fesar,
murya a sanyaye tace "Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya!"
"Amin Kaka" cikin raunin Murya Maryam tace "Ya Maleek idon ka tafi yaushe zaku dawo!"
Ajiyar zuciya ya sauke kana yace," Ban sani ba" Maryama kaman Zatayi kuka," Ya Maleek zan bika, "A'a,
kana ya yi musu sallama ya wuce gida....
Washegari tunda safe bayan sun karya yayi Kaka Sallama kana ya wuce kasuwa... Yana barin gidan
Maryam ta fashe da Kuka tana kiran Ya Maleek...✍️✍️
*More comments and share*
*Sadeeya Ka'oje ce*
*DR SULTAN*
*( THE BEGINNING)*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*

💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍
Tallah ! Tallah !! Tallah!!!
Shahararriyar Marubuciyar nan Hafsat Muhammad Bature (Boss Bature) wacce ta nishadantar daku a
littafin ta mai suna *ABBAN SOJOJI*
yau ta sake dawowa muku da sabon labari mai ɗauke da sabon salo na musamman *KURKUKUN
ƘADDARA* labari ne mai kunshe da Butulci , tausayi , ban dariya , cin amana , soyayya mai shiga rai
karna cika Ku da surutu, *KURKUKUN ƘADDARA* littafine mai ɗauke da Rudani da ban Al'ajabi
kudai ku kasance da Alƙalamin *Boss Bature*💋💖 domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan Number
08103884440
*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*Page 7-8*
_______Yana barin gidan ta fashe da kuka tana kiran," Ya Maleek!" da kyar Kaka ta lallashe tayi shiru,
Abdulmalik bayan fitar dashi daga gidan Kai tsaye ya nufi Kasuwa ba wani jimawa motarsu ta ɗaga
cike da kewar Maryam....
Yinin Ranar gabaki ɗaya Haka maryam cikin fushi, da Daddare haka taƙi cin Abinci, Saida kaka tayi
mata zan ido kana ta ɗan ciki ƙaɗan, kwanan su Abdulmalik Ukku a birni suka dawo,
Wuraren ƙarfe Shidda ya shigo gida, " Maraba da mutanen Kano, Kaka ta faɗa cikin tsananin farin
ciki, dai dai lokacin Maryam ta shigo gida dawowar kenan daga Islamiya a guje ta nufi inda yake ta
rungumeshi, "Ya Maleek sannu da zuwa!!" A hankali ya juyo da ita suna fuskantar juna, "Kina Lafiya?" da
sauri ta ɗago ta kalleshi tare da sakin Murmushi Nan take ɗin dinta suka bayyana, A hankali ya motsa Lips
ɗinsa hakan ya sa ko Kaka dake kusa dasu bati me ya faɗaba, " Maryama ta!" ta kira sunanta cikin
kasalelliyar murya da ta sa Maryam sauri ɗagowa ta zuba mishi ido domin bata taɓa saninsa da irin
wannan Muryaba, a hankali ta sake yin ƙasa ta kanta cikin tsananin kunya, yatsun hannunta ya sha jan lalle
ya zubawa ido, ƙasa tayi da kanta tana ci gaba da wasa da yatsunta, a hankali Maryam ta Manyan idadunta
ta kallesa, ya ɗaga mata gira tare da jan Numfashi ya fesar,
Kaka dake gefe ta saki baki cike da Mamakin irin Kallon da suke wa juna, Abdulmalik har ga Allah ya
manta da Kaka na Wajen,
Ido a lumshe yaci gaba da kalli yatsun hannunta, Maryam tuni jikinta Yayi sanyi,
Kaka sam ta gaza ɗauke ido a kansu,
Murya can ƙasa ƙasa kaman mai raɗa yace "waya Miki lalle nan mai kyau!" Sassanyan Nunfashi ta fesar
cikin sanyi Murya tace "Kaka!" kaka kam sai Raba ido take ta kalli Abdulmalik ta kalli Maryam, a hankali
Maryam ta fara janye hannunta daga nashi, ciki wani irin yanayi da Baitaɓa rikar kanshi ya yi saurin janyo
Hannuta yana ci gaba da kallon su, a hankali ya lumshe idanunsa nan take hawaye Masu matsifar sanyi
suka zubo kan kyakkyawar fuskarsa, Maryam da Kaka cike da Mamaki suka zubawa fusakar ido ganin
Hawaye kwance a saman fusakar shi, haka Maryam ta tsinci kanta da share mishi Hawayen, a hankali ya
sauke sassanyan Ajiyar zuciya, " Ya Allah ka jiƙan Ummina!" Ya faɗa can ƙasan maƙoshi, Murya a dishace
Maryam tace ," Ya Maleek Kukan me Kake?" A karon farko ya saki Murmushi ƙarfin hali, cikin wani irin
yanayi da bai iya jurewa, sun ɗau tsawon lokaci a haka ba tare da sun sake Magana ba.
Mutsu mutsu ta fara tare da ƙoƙarin janye hannunta dake sarƙe da nashi, kansa ya ɗago ya kalleta da
rikitattun idanunsa,
Nan taga yadda idanunsa suka kaɗa sukayi jazir sun sake cika da tace da hawaye,
Ƙoƙarin janye hannunta taci gaba da yi jiki a ya ɗago da kansa ya kalleta sai kuma ya Lumshe idon
Hawayen da suka cika a idonsa suka zubo, a hankali yaja dogon Numfashi mai bala'in ɗumi da kyar ya
tattaro da ƙarfisa, murya a dishace yace," ga wannan, ba tare da yadda sun haɗa ido ba, murya a dishace
Maryam tace ," Ya Maleek baka son lalle na Dena!" ba tare da ya kalleta cikin sanyi Murya yace Ina s....
Karab Idanunsa suka sauka kan Kaka dake tsaye ta zuba musu ido, da sauri ya janye Idanunsa daga kallon
Kaka, a hankali ya sunkuyar kai tare da shafa kanshi cikin sanɗa sanɗa ya yi ƙoƙarin ficewa daga gidan,"
Abdulmalik cak ya tsaya jin Muryar Kaka ," Ina zaka je? Cikin sanyi Muryar ya soma Magana," Gida
zanje Kaka!"
"Dawo Kaci abinci" a hankali ya sauke Ajiyar zuciya, kai a sunkuye ya dawo ya zauna a tsakiyar
gida Kana kaka ta aje mishi abincin sa yaci, Kaka na janshi hira har ya kammala, dai dai lokacin Maryam ta
iso riƙe da perpar," Ya Maleek duba ga ki waye wannan?" A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe
akan takardar, da sauri ya runtse idanunsa, wani irin Amitattacen Nunfashi mai cike da yanayi na
Musamman ya fesar da idanunsa suka kan Hoton da jikin takardar, "Ya Rabbi!!" Shine a binda ya iya furta,
a hankali yaci gaba da kallon kyakkyawan Saurayin da ke cikin takardar, Kaka ma zajen take kallo,
"Maryam waye kuma kika zana?"
Wani irin sassanyan Nunfashi ta fesar," cikin sanyi Muryar tace,"Kaka Ya Maleek!! Ne"
Wani irin lumshe idanunsa ya yi, wani irin kallo mai tafiya da dukan natsuwa yake binta dashi tun daga
farko hoton har zuwa sama ina Aka rubuta YAYA ABDULMALIK da manƴan haruffa, hoton shine sak
Maryam ta zana, zane na ɗaya daga cikin bawarda Allah ya yi Maryam, "Maryama ta!" Nina kika zata
haka, ai zanen ya fini kyau, Harara ta zabga mishi, murmushi yayi tare da ƙarɓan zane yana Kallo,
"Maryam ta! Allah zanen nan ya fini kyau!" da sauri Abdulmalik ya juya yana kallon Kaka," Kaka da zanen
nan dani wa yafi kyau!"?yadda yayi maganar da kuma yadda ya marairaice abin yaba Kaka Dariya,"
fusakar Kaka ɗauke da murmushi tace ," Abdulmalik ai kafi zanen nan kyau kaifa kyakkyawa ne! Ma sha
Allah!"
Rau rau Maryam tayi da ido sai kun ta ta tsuke fuska kana tace ,"Ya Maleek kaifa kyakkyawa ne!"
Abdulmalik a hankali ya tauna lips kana yace," Ki bani hoton nan na tafi dashi ɗakina"
Harara ta dalla mishi ,"Allah Bazan Bazan ba daba, Saida na zana ma wani ta karasa maganar cike da
tsiwa da murguɗa baki, Abdulmalik ya yi Murmushi, haka suka kasance cikin farin ciki zuwa bayan Isha'i
bayan sunyi gama karatu suka ɗanyi hira kana ya wuce gida cike da gajiya...
Yana isowa ya ɗan yi yi gyare-gyare a ɗakin.Abdulmalik Gwani ne a fanni tsabta kana ya yi Wonka ya
kwanta nan take bacci gajiya ya yi awon gaba shi....
Washe gari ranar baije kasuwa ba wonki yayi musu kayanshi dana Kaka da Maryam, Maryam na tayashi
gwanin burgewa, "Kinga ki Dena wankin Nan kar lallenki ya goge, "Ya Maleek idon ya goge Kaka zata
min wani, haka suka ci gaba da wonki har suka kammala, ranar gabaki ɗaya a gidan kaka ya yini sai dare
ya wuce gida tare da kayan shi da wonke Kaka sai saka mishi Albarka take.....
A hankali Rayuwa taci gaba da tafi cikin kwanciyar hankali tuni su Maryam sun koma Makaranta, sosai ta
maida hankali wajen karatun, duk abin ya shige mata duhu takan tuntuɓi Abdulmalik, hakan yasa komi ke
zuwa mata da sauƙi, a ɓangaren islamiya ma ba'a barta a baya ba, Rayuwar suke cikin kwanciyar hankali
da ƙaunar juna, zuwa yanzu Maryam Na gaba da cika shekara goma sha ukku a duniya,
A Ɓangaren Abdullahi ma duk bayan wata ɗaya yakan aiko musu da kayan Abinci kaman yadda ya saba da
duk wani abun buƙata, kusan kullum sai ya kira su, Abdulmalik da Abdullahi basu taɓa haduwa kasan
cewar yana jimawa bai zo ƙauye ba saboda yanayin aikin sa, duk lokaci zaizo ko tunda safe yake zuwa
haka zai zauna suyi hira da Kaka harzu zuwa lakacin da Maryam zata dawo daga Kamaranta, kana ya wuce
Kano...
“Kaka Abba ya Kira, kiran na gab da tsinkewa ta ɗaga, cikin sanyi Murya ta soma magana "Abba ina
wuni ya gida Abba ina su Haydar"? daga can ɓangaren Abba ya sauke Ajiyar zuciya Kana," Mamana Lafiya
lau suke, Ina Mama"? "Gata Abba" tayi Maganar ta re ɗorawa Kaka wayar a kunnen,
"Abdullahi Ya gida"? ta faɗa cike da kewar ɗanta, " Lafiya lau Mama" cikin raɗa Maryam tace "Kaka
ga ki gaya mishi na kusan sauka, ranar walima yazo dasu Haydar" Kaka ta talla mata Harara,nan take
Maryam ta tsuke fuska tana turo baki, haka suka ci gaba da hira gwanin burgewa, Kana kaka ta mikawa
Maryam waya nan ta sanar da shi abinda ta gayawa Kaka," Insha Allahu zamu zo tare, Kafin nan ma zamu
shigo Ranar Assabar tare dasu, wani Irin daɗi Maryam taji, sun jima suna hira tana bashi labari Abdulmalik
da yajima da sanin sunan sa a baki, Kafin nan sukayi Sallama,
cikin wani irin ya nayi mai ɗauke da tsantsan farin ciki.tace , " Kaka Abba ya ce zasu zo ranar Assabar
tare da su Haydar! Allah ya nuna Muna," Amin Kaka..."
Washegari tunda da sassafe Abdulmalik na shigo ta bashi Labarin su Haydar zasu zo, "Ya Maleek karka je
Kasu kaji," "saboda me?"
"ka zauna gida muyi hira tare dasu Haydar"
"Maryama ta! Idon na zauna a gida wazai min aiki na?"
"Ya Maleek don Allah fa nace"
" Shike nan zan zauna Amman idon suka jima basu zoba zan wuce kasuwa kin yadda"
"Ehh Na yadda na san Abba da wuri zai yake zuwa duk lokacin da zai zo"
"Nadai faɗa Miki"
"Naji" ta faɗa cike da tsiwa tare da murguɗa baki"
"Wannan bakin wata rana saina canye shi idon baki dena murguɗa shi ba"
Kallonta Abdulmalik ya yi kana ya yi Murmushi a hankali ya ce ,"Maryama Sarkin tsiwa"
A gurguje suka karaya ganin lokaci na tafiya, lokaci ɗaya suka kammala kana sukayi Kaka sallama kai
tsaye suka wuce makaranta daga can ya wuce Kasuwa.... sai dare ya dawo,
Yau take Assabar tunda sassafe Kaka ke aikin Abinci nan take gidan ya gauraye da ƙamshi mai daɗin
gaske koda 8:30 tayi Kaka ta kammala komi tare da taimakon Maryam suka gyara gida tare da kunna turare
mai matsifsr ƙamshi da saka natsuwa.....
Wuraren 8:46 Abdulmalik ya shigo gidan, "Kaka ina kwana,
" Lafiya lau Abdulmalik"
" Kaka baƙin basu iso ba?"
"Nunfashi Kaka taja kana ta fesar,"muma zaman jiran su muke Abdulmalik"
"Gashi har

3 / 21