Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dr Sultan Complete Hausa Novel by Sadeeya Ka-Oje

Author :  Sadeeya Ka-Oje Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 21

27K to 30K   out of 60.6K words

ya yata haka riƙo. Rau rau ya
yi da ido kaman zai yi kuka!,
"Daddy ban san da wanne Abu zan saka ma A duniya ba! Daddy ko Mahaifiyana iya Abun..... Alhaji
Nuraddeen ya yi saurin da katar da shi ta hanyar rufe mishi baki, "kwanta ka huta good night my Boy ya
faɗa tare da shafa kanan Sultan, A hankali ya miƙe tare da barin ɗakin, yana fita Sultan ya sauke sassanyan
Nunfashi, tare da jan lallausar Katifa ya rufe jikin sa iya ƙirji kana ya haske ɗakin ya yi addu'a ba jima
bacci ya yi a waon gaba dashi......
Washe gari, A hankali ya fara buɗe idanunsa tare da yin Addu'ar tashi daga barci. Hannunsa ya saya ya
jawo wayar sa dake gefen Pillow ya sannan pawer karfe 5:8am, a hankali ya zuro siraran ƙafarun Farare
sol toilet ɗin sa ya nufa yana shiga ya yi brush ya yi Wonka da ruwan ɗimu ta re da Alwalla kana ya fito,
durowarsa ya buɗe wata lallausar jallabiya Milk color ya zura kana ya fesa turare ya fice daga ɗakin, tare
suka wuce masallaci da Daddy Saida gari ya fara haske suka dawo gida kai tsaye ya wuce ɗakin laptop ɗin
sa ya jawo ya fara sarrafata cike da ƙwarewa...
Wuraren kafe goma suka yi Breakfast a tare cikin kwanciyar hankali, Ranar haka suka yini cikin farin
ciki....
★★★★★★★
Bayan sati biyu tuni a kammala duk wani shirye shiryen fara aiki A Asbitin, yau ta kasance Monday tunda
safe ya shirya zuwa Office cike da ƙwarin Quiwa bayan sun kammala Breakfast ya fice daga palon, har
bakin mota Su mommy suka rashi tare da yi mai fatan nasara....
" Anty Sultana gaski kinyi kyau sosai ban taɓa ganin Unifrom ɗin nan sunyi Miki kyau kamar yau, Meena
na faɗa cike da zolaya, Harara Sultana ta dalla mata kana ta fice daga ɗakin Meena na biye da ita, "Abba
zan wuce wajen Aiki!"
"Ma sha Allah Mamana Allah yasa kin fara a Sa'a!"
Fusakar ta ɗauke da murmushi tace ," Amin Abba na gode sosai, "kaka Mami zan su ce, "Allah ya bada
Sa'a! "Amin" har bakin mota suka rakata cike da kwarewa ta ja motar ta ta fice daga gidan, kai tsaye ta
nufi Asbitin....
kusan lokaci ɗaya suka iso. A hankali ya fito daga cikin motar, ba tare da ya lura da ita ba, ya yi gaba abinsa
Cikin natsuwa ya fara taku yana ƙarasowa cikin farfajiyar Asbitin,
A hankali take ta kowa, suna fuskantar juna, sosai ya zuba mata ido, ita ko tafiya take kai a sunkuye Hakan
yasa bata san da mutum a gaban taba..
da sauri Sultan ya tsaya saboda warin matsiffen bugawa da Zuciyarsa take ganin ta yi dab da shi,
A hankali ta ɗaga da kanta ganinta tsaye kusa da Namiji, ya sa taja da baya da sauri tare da tsuke fuska, a
wani ɓangare kuma a ruɗe take saboda warin bugawa da Zuciyar take,
Bai kula taba sai kauda kanshi da ya yi fege kaman bai ganta ba.
Cike da tsiwa ta ce," miye na tsayawa a hanya"
Da mamaki ya ɗan kalleta ta gefen idonsa, kana ya tsuke fuska yaci gaba da tafiya, kai tsaye ya wuce
Office ɗinsa ya fara aikin da ya kawoshi...✍️✍️
_More Comments and share_.
_Domi neman ƙarin bayani ku tuntuɓi ta wannan Number👉 08149979652_
*Sadeeya Ka'oje ce*💋
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍


PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗


*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*

*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 19-20*
_____Da mamaki ya ɗan kalleta ta gefen idonsa, kana ya tsuke fuska yaci gaba da tafiya, kai tsaye ya
wuce Office ɗinsa ya fara aikin da ya kawoshi.
Sultana da har yanzu ke ta faman jan tsakin takaici ta nufin cikin Asbitin, Nurse's sake tsake a wajen sai
faman kwallonta suke cike da mamaki,
Jidda tayi sauri riƙo hannuta, tana faɗin,"Daughter Lafiya?" da saurin Sultana ta juyo tana kallon Jidda
fuska a tsuke ta ce, "Ba komi Mommy na!" salin halin kawar ta ta, yasa ta yi shiru,
Jidda ƙawar Sultana ta re suka yi school of nursing. Kasan cewar tana da sunan haifiyar ya sa take Sultana
take kiranta da Mommy. Sosai suke mutunci,
"Daughter me a ka Miki Hlm?"
Kafin Sultana ta samu damar bata Amsa sai gashi ya fito daga Office ɗinsa Dr Aryan ta biye da shi a baya,
taku yake cike da natauwa irin ta zakaran Samari masuji da lokacin ƙuruciya da kwanciyar hankali har
yanzu fusakar a tsuke take, ƙoƙarin janye idanunta take daga kallon nasa Karab idanunta suka sauka kan
Sunan da ke rubuce a jikin rigarsa DR SULTAN da manyan Rubutu,
Cikin suɓutar Halshe ta ce, "don yana Asbitin sa yasa zaiyi wa Mutane tsaye a tsakiyar Hanya"
Karaf wannan Maganar ta sauka a hunnensa. ta gefensu ya raɓa ya barta da kamshin turaren sa mai
sanyi da daɗin shaƙa. Ko kallon ida take baiyi ba, zaka fahimci da wahala ma ace yaji Abin da ta faɗa.taɓe
baki ta yi tare da jan tsaki Jidda ko sai kallon ikon Allah ta ke, dai dai lokacin tawagar Nurse's suka i so
wajen Jidda ta ce ina zuwa haka," Dr ne ke son ganinmu ga baki ɗaya, Sultana Uffan bata ce ba. Dan ita
takaici yake bata...
(Hmm Sultana kenan bari dai nayi shuru 🤣🤣🤸)
Nan take kuwa, duk Nurse's suka fara haurawa sama suka shiga babban Hall ɗin nasu, maza gefe ɗaya
Mata gefe ɗaya. Sultana da Jidda zaune a waje ɗaya,
Cike da natsuwa da sanin darajar kansa ya gyara samansa saman Kujera Dr Aryan na zauna a gefensa, a
hankali ya gyara microphone tare da hura Iska a hankali kana ya yi gyara murya," “Bismillahir Rahmanir
Rahim!..
Sai kuma ya Lumshe idanunsa tare da sauke sassanyan Ajiyar zuciya cikin sanyi Muryar ya ci gaba da
cewa. "Ina mai farin cikin wannan rana mai dinbin Tarihi a Rayuwata! duk yabo da godiya sun tabbatar da
ga Allah ma ɗokakin sarki. Ina mai farin cikin zuwan ku Asbitin nan mai Albarka.daga nan yaci gaba da
bayanai masu ɗinbin mahimmanci da zasu taimake su gaba ki ɗaya.
Gaba ki ɗaya wajen ya yi shiru kowa ya maida hankalinsa ga Sultan dake magana, yan matan wajen ke jin
ina a ce su mullake sa a matsayin mijin.
Sultan ya sauke sanyayyar Ajiyar zuciy, Kana ya ce,"a kwai mai magana?"
Nan wasu suka soma tambayoyi, Shiko yana basu Amsa cikin natsuwa,
Kana ya mai da sauran kallonsa ga Dr Aryan dake gefensa cikin sanyi Muryar yace ,"A kwai mai
magana a cikin ku?"
Duk kan ninsu suka girkiza kai.
Dr Aryan ya nuna Jidda tare da fadin ki rufe muna taro da Addu'a,da saurin Jidda ta sunkuyar da kai kaman
bata ji me yace ba, tsawon mintu na Ukku, kana ya Kalli Sultana
Kai ta juya tare da taɓe baki, "Sultana!Dr Aryan ya kira sunanta,a hankali ta ɗago da kai tana kallonsa
dai dai lokacin na kansa, a tsanake ta mike tare da neman dukan natsuwarta ta amshi microphone ta fara
Addu'a cikin zazzaƙar Muryar mai cike da natsuwa..
Kana aka tashi kowa ya wuce wajen aikin sa,
Sultan kai tsaye office ɗin sa daya amsa sunan Office ya nufa, baka jin komi sai Dadɗan khamshi turaren
dana Ac mai sanyi dake tashi, ya zauna saman lallausar kujerar yana sauke sassanyan Nunfashi, dai dai
lokacin Dr Aryan ya shigo Office ɗin fuskarsa dauke da murmushi cikin sanyin murya ya ce,"Sir kwai
wanda zaka duba yanzu ya yi maganar tare da aje mishi files a gaban sa, kana ya fice daga Office ɗin, files
ɗin ya duba kana ya fice daga Office ɗin...
★★★
Bayan Awa Ukku, Fitowarsa kenan ɗakin theater a gajiye.yanda yake tafiya kwai zai tabbatar ma yanayin
da yake ciki.tare da Doctors Biyu da suka tayasa Aiki, da Nurse Biyu rike da kayan Aiki.a dai dai lokacin
suka ƙaraso Office ɗinsa hand gloves ɗin hannunsa ya cire kana ya jefa a tasar dake hannu Nurse. Hannu ya
ɗaga musu alamar su daga ta daga anan a hankali ya tura ƙofar ya shige.
Bayan mintuna goma Dr Aryan ya shigo Office ɗin, "Sannu da hutawa Sir ya faɗa cike da kulawa,
"Sir ga wasu files"
Kansa ya ɗaga masa fuska a ya mutse na Almar gajiya,kana ya ƙara sa kusa da Sultan ya aje mishi wasu
files ya fara singing, a hankali Dr Aryan ya mike murmushi na ƙara faɗaɗa akan fuskarsa kana ya ce,"
Kwai mutun biyu da zaka Duba yanzu kafin kaje Hutun awa biyu,Da sauri Sultan ya ɗago yana kallon Dr
Aryan fuska a marairaice kaman Zaiyi Kuka. Dr Aryan ya yi saurin sunkuyar da kai ƙasa yana haɗiye
dauriyar dake neman kubce masa dan yasan shima da gaske Sultan ɗin ya kai iyakar gajiya, amma sai ya
fiske yace,"Da gaske nake Sir, gama files nasu na kammala dubawa"
"Aryan Please, wallahi na gaji, sai dai kai ka dubasu” ya faɗa yana sauke numfashi da miƙewa ya nufi
wata ƙofa.
Murmushi Aryan yayi yana binsa da kallo harya shige. Ya ɗan girgiza kansa da kwasar files ɗin ya fice
daga office ɗin zuwa nashi shima.
Ɗan madaidaicin ɗakin dake cikin Office ɗinsa ya nufa dake ɗauke da kayan daɗi compiled, shima sai
kamshi yake mai daɗi.kamar ba'a cikin asibiti ba. Kai tsaye toilet ya nufa yana faman lullumshe idanu dan
barci yake matuƙar ji.
Bayan wasu mintuna ya fito daga toilet ɗin sanye da rigar wanka Fara, sai hular wanka data kare gashinsa
daga jiƙewa, da alama dai baya buƙatar jiƙawar. A bakin gadon ya zauna yana mai furzar da iskar daya cika
bakinsa da ita, yajawo wayarsa dake a drowar gefen gadon a jiye ya cireta a silent. Dan ya sakata a silent
ɗinne tun lokacin dazai shiga theatre room. Aziz ya kira, sai akai rashin sa'a ya samu wayarsa a busy.
Kume fuska ya sakeyi alamar baiso hakanba, ya ajiye wayar. ɗayar ya ɗauka itama ya cireta a plane
mode daya sakata. Kamar jira ake ya cire ɗin sai ga kira ya shigo, kafin ya amsa kuma akai knocking ƙofar.
Rasa wanne zai farayi yayi. Ɗaga wayar? Kokuwa buɗe ƙofar?.
“Sir" ya tsinkayi muryar Dr Aryan na kiransa. Duk da yayi tunanin akan maganar patients ɗin da Dr ɗin ya
yi maganar zai dubane hakan bai hanashi tashi ya buɗe masa ƙofaba, sai dai ya sake haɗe fuska alamar da
gaske ya gaji baison takura.
Yana buɗe ƙofar yace, “Aryan plea.....”
Saurin katsesa Aryan yayi da faɗin, “Yi haƙuri ba wancan maganar bane, akwai damuwa Sir ɗaya
daga cikin Nurse ɗin nan ta yiwa Yaro Allura ta kare a jikinsa.
“What?!” ya faɗa hankali tashe. Shima Aryan da hankalin nasa ke a tashe ya shiga jinjina masa kai.
Juyawa cikin ɗakin ya yida sauri, yama manta da wata gajiyarsa. A Gurguje ya shiya ya fice daga ɗakin Dr
Aryan zauna a Office ɗinsa tare suka fice daga Office ɗin, tun kafin su ƙaraso suke juyo Murya yaro na
kuka, sauri sauri gugu gudu suka ƙasaso wajen, Sultana nabaki ɗaya a ruɗe take jikinta har karkarwa ya ke,
Cikin tsananin tashin hankali da tsagwaron damuwa yace, " ta yaya hakan ta faru? Ince duk yanda ya
kamata a ba mara lafiya kulawa na sanar muku. Miyasa kuke da sakaci akan rayukan mutane!!?” ya ƙare
maganar da ɗan raunin murya.
Sultana da maganar Dr Sultan tai mata zafi ya buɗe baki zaiyi magana cikin ƙoƙarin danne fushinsa,
amma sai Sultan ɗin ya kuma dakatar da ita ta hanyar faɗin, “Bana buƙatar jin komai please" yaron ko sai
kuka yake kaman Ranshi zai fita, cikin dubara Sultan ya cire Allurar wajen harya kumbura, kana ya shika
lallaɓa yaro har Saida yayi Barci ya bar wajen Sultana ta rakashi da Harara. Dai dai lokacin Jidda ta ƙara so
wajen tana faɗin ,"Daughter Lafiya Sultana ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar kana,"tace ni da ɗan renin
hankali,bai ko tsaya jin bahasi ba zai rufeni da faɗa ta ƙara sa maganar cike da tsiwa, "kimin baya Meya
faru Daughter, "wai yaron nan ne fa ya ƙi tsayi nayi mishi Allura garin mutsu mutsun sa Allura ta kare a
jikinsa, da sauri Jidda ta ware mayan idanunsa kana yace," nashiga ukku Ni Kuluwa!"
"Haka kwai zai hauni da faɗa kaman wani ubana"
"Daughter gaskiya ne Dr ya faɗa ki riƙa kula Allah ya tsare gaba"
Ƙala Sultana bata ce mata ba. Kana sukaci gaba da aikin su.
A bangaren Sultan yana komawa office yayi wonke hanneyensa sannan ya fada kan sofa ya zauna yana
jin haushin abunda ya faru...gaba daya bacin ranshi sai ya karu fiyeda wanda yake ciki already...tunda yake
bai taɓa ganin sangartacciyar yarinya kaman wannan yarinyar ba...maida kanshi ya lafe jikin kujera tareda
lumshe ido.. a hankali ya mike yaci gaba da aikin da ke gabansa,
Wuraren ƙarfe 5:40 ya kira Direba, bayan mintuna 20 ya iso, bayan ya kammala a binda yake ya fice daga
Office ɗin kai tsaye ya wuce Parking space, dai dai lokacin Sultana ta iso wajen tattausan sumar ƙeyansa
dake kwance lib-lib ta zubawa harara.
Numfashi mai sanyi taja tare da shaƙa daddaɗan ƙamshin turarensa mai sanyi.
Sai kuma tayi ƙasa da kwayar idanunta,baki ta ɗan tura sama ta da liƙa ƙeyarshi wani sabon harara tare da
zan tsaki
hankali ya ɗan juyo gefen damansa, jin inda sautin tsaki yake ɗan tashi ya kauda kai gefe kaman bai jita ba
ya shige mota, motar na ɗagawa Jidda ta iso wajen tana faɗin ," Daughter tsaya ki rage min hanya, ba musu
ta tsaya jidda ta shiga kana suka fice daga Asibiti, cikin mota kuwa Jidda sai labarin Sultan take,har suka
iso gidan su, kana Sultana ta kalleta,"Allah kika ƙara min maganar Shi a mota zai dai na sauke ki a hanya,
"haba Daughter Meya yayi zafi haka gama Insha Allahu da mota na zanjo daman ɗazu koda na fito aba'a
wanke taba, "Nadai gaya Miki" yana kai ƙarshen Maganar ta wuce, a hankali Jidda ta sauke sassanyan
Nunfashi kana ta nufi cikin gida...
Tunda suka baro cikin Asbitin ɗin ya kwantar da kansa jikin kujera yayi shiru idanunsa dake da cikar baƙin
gashi da gira a sama suna a lumshe. Sai faman juya zoben hannunsa dake a hannunsa na dama.
Duk abinda ya keyi drivernsa na kula ta cikin mirror,
Haka dai suka cigaba da tafiya kowa da abinda yake saƙawa a cikin rai. Gashi mahaukacin gudu yakai
Tunda 6pm tayi kiran Mommy da Daddy ya fara shigowa a wayarsa, sai dai ko sau ɗaya bai amsa masu ba
ya share, sai ma kwanciya daya gyara cikin lallausar kujerar motar ya cigaba da latse-latsen laptop ɗinsa
har yanzu da takaicin Sultana a ransa.
Ƙarfe 7:20 suka iso gida Tunkan su gama dai-daita parking idanunsu suka sauka akan Mommy da Ihsan
dake ta faman kai kawo ta barandar saman bene. Sai dai ganin shigowar motocin tuni tabar wajen da alama
zata fitone.
Tare suka iso wajen harda su Salma da gudu suka rungumeta tare da faɗin,"Sannu dazuwa Ya Sultan"
Ihsan ko wani irin kallo take binsa dashi, a hankali ya janye su daga jikinsa ya nufi wajen
Mahaifinyarsa, "Sultan ya Aiki?"
"Alhamdulillahi Mommy Ina Daddy?"
"Yana masallaci"
"Ya Sultan sannu da zuwa Ihsan ta faɗa cikin sanyi Muryar, "Lafiya" yaba Amsa, kana ya wuce cikin gida,
yana zame baƙar jacket ɗin jinsa tunkan ya buɗe. Ya riƙeta a hannu ɗaya sannan ya ƙarasa ya murda
handle ɗin ƙofar ya tura ya shiga.
Fes ɗakin yake shima, yanata tashin ƙamshin fresheners data haɗe da turaren da yake amfani da shi.
Jefa jacket ɗin yayi saman gadon ya ƙarasa gaban mirror yana ajiye wayoyin saman mirrorn. Zama yay a
stool ɗin gaban madubin yanata faman yamutse fuska dan yunwa yakeji, sai da ya cire takalman ƙafarsa da
safar, farar ƙafarsa dake fes ta bayyana kafin ya miƙe kansa tsaye ya nufi toilet
Yana shiga aka fara knocking ƙofar falonsa, amma sai ya share ya cigaba da abinda yake a ciki. Anyi kusan
sau uku sannan aka bari. Ya ɗauki tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe Milk color.
Hannunsa riƙe da ƙaramin towel yana tsane sumar kansa da kallo ɗaya zakai mata ka fahimci tana masifar
lasar kuɗaɗe kodan ƙyawun da take dashi ga mai kallo a ido balle kuma wanda ya taɓa.
“Sultan! Buɗe min ƙofa”. Ya tsinkayo muryar Mommy tana faɗa cikin yaren fulatanci da tun zuwansa
gidan ta fahimci yanaji da ɗan buga ƙofar yanda tasan bazai takurasa ba. Gefe ya karyar da wuyansa yana
yamutsa fuska da yarfar da hannayensa duka alamar shifa an takura masa. Fuskarsa cike da takaici yaje ya
buɗe mata tare da juyowa a binsa batare da ya tsaya saurarenta ba.
Ƴar dariya tayi abinta, dan ko ɗan hakan bai dametaba, tasan ya gajine matuƙa, shikuma idan ya gaji to
lallai sannan baƙin ransa ke ƙara hauhawa, kowa kuma yimawa yakeyi har ita da Daddy. Ƙarasawa tai inda
yake tsaye a gaban mirror yana cigaba da tsane kansa. Kama hannunsa tai ta zaunar, ta amshi towel ɗin ta
cigaba da goge masa kan tana kallonsa ta cikin mirror fuskarta washe da murmushi.
Shiko ya ciskule tasa kamar zai fasa ihu. Sai da ta tsane masa kan tas kafin tajawo hand dryer ta jona a
jikin soket ta fara busar masa da shi. Ajiye dryer ɗin tayi da jan hancinsa tana faɗin, “Nasan wannan fushin
bana komai bane sai yunwa da gajiya Taso kaje kaci

10 / 21