Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dr Sultan Complete Hausa Novel by Sadeeya Ka-Oje

Author :  Sadeeya Ka-Oje Category :  African Stories & Novels

Chapter   19 / 21

54K to 57K   out of 60.6K words

Knocking d'in k'ofarsa da akeyi yasakashi jan tsaki, da k'yar yabud'e baki yace ashigo.
Ihsan ce d'aukeda tire Wanda aka shirya masa break d'insa. "Ina kwana Ya Sultan Cigaba yayi da saka
takalmansa batareda yad'ago ya kalletaba.
Taja table ta ajiye."Ina kwana"
Yanzunma bai d'agoba ya amsa da lafiya.
Duk atsorace take,
jin alamar tana tsaye akansa yasakashi d'ago jajayen idanunsa yazuba mata, cikin daburcewa tace dama
um..um.... Mommy ce tace akawo maka break fast naka, .
Baice komaiba yamaida kansa yana k'ara gyara igiyar takalminsa.
Da sauri Ihsan tabar d'akin,
Koda yagama bai kalli abincinba, yak'arasa gaban madubi yad'auki agogonsa yasaka, sannan yad'auki
jakkar lap-top nasa yanufi k'ofa. Sai kuma ya dawo, tareda jawo table d'in da Ihsan ta ajiye break fast d'in
gaban sofa.
Tea kawai yahad'a kad'an yasha, Dan bayajin cin komai ayanzun.
Yana gamawa yamik'e yafice.
Babu kowa afalon, yana ƙoƙarin haurawa Sama Mommy ta fito daga Kicin riƙe da Basket ɗinsu Salma
da Salim, dai dai lokacin suka suka fito daga ɗakin su, riƙe da School bag ɗin su, "Ya Sultan Good
Morning!"
"Morning kun tashi lafiya?"
"Lafiya lau Ya Sultan"
"Ya Sultan jiya na ganka a mafarki kaida Anty Sultana kuna riƙe da baby tana kuka, kace Anty Sultana ta
goya taƙi wai tagaji bayanta ciwo yake, shine kai kuma ka goya Baby! Ya Sultan ina son Baby tana da kyau
sosai!"
Tunda Salma ta fara magana Mommy ta kafeta da kallonta tana Murmushi, Sultan ya Lumshe idanunsa
kana ya buɗe a kan fuskar Salma dake Murmushi har yanzu....
"Mommy Ina kwana?"
"Lafiya lau Ya Babba!"
Ina fatan kayi breakfast ɗin ka?"
Kai ya gyaɗa mata. Kana yace "Ina Daddy?"
" Ya tafi wani jana'iza wani Makwoƙocin mune ya rayu a tsuhuwar Unguwarmu."Ayya Allah ya jikan
musulmi!"
",Amin"
"Zan wuce Mommy! "Allah ya kiyaye,"Amin yana fita bada jimawa Su Salma suka wuce School...
__________★★★★_________
Saida Kaka tayima Sultana jan ido sannan tad'an saki jikinta,
Duk Wanda yaga halin da Sultana take ciki tun ajiya zai tabbatar batason aurenne?.
Amma tasan yanda zata ɓulloma lamarin kodan ta kuɓtar da kanta....
Sultana wayarta ɗoka takoma can Ɗakin su ta rufe , Number Jidda takira, babu dad'ewa tad'aga.
Tana d'agawa tasaki kuka, cikin mamaki Jidda tace Daughter! Lfyarki kuwa? Ko wanine yarasu?.
'a, Sultana tafad'a cikin shashshekar kuka.
Tomiya faru?.
Sultana Na kuka ta zayyanema Jidda komai, a mamakin Sultana saitaji Jidda ta daddage ta rangad'a gud'a.
Da sauri Sultana ta janye wayar daga kunnenta, saida ta tabbatar Jidda tagama sannan tamaida wayar tana
kuma rushewa da kuka," Mommy na wallahi bana son sa!, daga can ɓangaren Jidda ta sauke Nannauyan
Ajiyar zuciya kana tace ,"Ha ba Daughter Miye aibun Dr Sultan! Ni fa wallahi na jima ina fatan Allah yasa
yazamo mijinki, baki yadda kuyi matuƙar dacewa ba!, " Mommy yanzu kema kina goyon bayan shi?,"
Sosai ma! Daughter"
"Shikenan daga haka ta katse wayar tana share hawaye..
_________★★★
Sultan zaune agaban Daddy da Mommy, kansa ak'asa yana sauraren iyayen nasa.
Abba yayi garan murya irintasu ta manya, idonsa akan Sultan d'in, cikin murmushi yace Sultan anzama
Ango.
Alhamdulillahi munje anyi maganar aurenka da mahaifinta
Sun yanke mana ranar d'aurin aure nanda wata biyu , Sun yanke sadaki naira dubu 50k kacal, dan
albarka ake nema acikin auren.
Sultan yakuma yin k'asa da kansa, dama can shi mutumne mai kunya, Mommy tayi murmushi kana ce
Allah ya nuna muna," Amin" cewar Daddy.
★★★★★ __________★★★★
Sultana na zaune ta saka waya a gaba tana magana tana kuka," Nas ya sanyi!! Nas yanzu haka an saka
ranar Aure na!!..daga can ɓangaren Nas yake ya sauke Nannauyan Numfashi kana yace ,"Bazan iya jure
reshin ki ba hawaye na baza iya wonke damuwar da Zuciya zata shiga ba hawayena sunyi ƙanƙanta
matuƙa su hana rayuwata gangar jikina ban taɓa sonki ƙasa da yadda zan iya rayuwa batare da ke ba ina
sonki Sultana!!!.. Soyayyarki a cikin jinina take, ban taɓa tunanin zan tsinci kaina a cikin wannan yanayi
ba, zan kasance cikin sonki har Abada,kin koyamin soyayya,kin koyamin farin ciki,kin koyamin dariya,
Amman kin manta baki koyamin yadda zan manta dake bayan kin rabu dani💔, ki talla fawa rayuwata data
tsunduma akan tsakanin kyaunar ki, ki tausayawa Zuciyata da ta shagala akan tsakanin Soyayyarki, ki
taimaki idanuna da sauraren zazzaƙar Muryar fusakar ki, ina sonki Sosai Sultana!!!!!." Wani irin
matsanancin kuka Sultana ta fashe dashi Zuciyarta na mata zafi kaman zata fashe. Cikin shekarar kuka tace
," Nas Bazan iya butulcema iyayena ba, Nas mesa tun lokacin baka bayyanar da kan ka a wajen iyaye ba?
Nas bana son fushin iyayena Nas Nima Kai banza iya zuje reshin kaba, Amman dole zanyi haƙuri!!! ta ƙara
sa maganar cikin raunin Murya,
_________★★★★_____
"Ya Sultan Daddy yace ka kaini wajen Anty Sultana, "my little sis, ki bari sai gobe na kaiku ku yini a can,
nan take Salma ta ɓata fuska kaman Zatayi Kuku," Ya Sultan Nidai yanzu nake so!"
"Ya Babba tun ɗazu ta isheni sai an kaita wajen Anty Sultana ta ga Baby, Sultan ya sunkuyar da kai ƙasa
cike da Kunyar Mahaifiyar sa, " Jeki shirya da sauri Salma ta wuce ɗakin jim kaɗan ta dawo.." Ina
Salim? "Ya yi bacci,haka suka wuce, tunda suka fita Salma ke mai mai yawa Sultan mafarki har suka iso
gida, a farfajiyar gidan ya yi Parking kana ya kira Haydar bai ɗaga ba har kiran ya tsinke,Khalil ya kira
bugu biyu ya ɗaya, nan take sai ga Khalil ya fito fuskarsa ɗauke da Murmushi,"Ya Sultana kazo a Sa'a ko
ga Anty Sultana can ta birkice muna" gaban Sultan yay matsifar tsinkewa, Amman ko kaɗan bazakace ga
yanayin da yake cikiba, tare suka wuce cikin gida.
__________Sultana zaune a ɗakin tun bayar gama wayarta da Nas. ta ɗora hanunta saman kai ta riƙe.
Cusashi tai a tsakanin cinyoyinta jikinta na wani irin tsuma. Ga kanta ya fara sara mata sama-sama. Duk
yanda taso ta daure ta kasa. Dan haka cikin ƙarfin hali ta shiga laluben wanda ke a kusa da ita. dai dai
lokacin kuma Meena ta shigo ɗakin Cikin sa'a ta damƙo hanun Hankali tashe Meena ta dubeta, sai kuma
yanda taga jikinta na karkarwane ya sakata ambaton ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ da ƙarfi.da sauri
Abba da Mami suka shigo ɗakin.. Sultana ta damƙi hannun Abba tana cigaba da jujjuya kanta da fisgar
numfashi a wahalce. A hankali take magana wadda idan ba'a kusa da ita kakeba ma bazakajita da ƙyau ba.
“Abba kaina, kaina zai fashe Abbah. Kamin addu'a kaina zai fashe, Innalillahi... Abbana zan mutu..".
Bazaki mutuba Mamana kinji, daina magana kiyita addu'a a ranki insha Allah bari na kira Doctor kinji”. Ya
ƙare maganar da saka ɗan yatsa ya ɗauke hawayen da suka tsatstsafo masa saman fatar ido. Meena da
Mami ma hawaye sukeyi.
Dai lokacin Khalil ya shigo ɗakin,"Abba ga Ya Sultan nan yazo tare da Salma, Abba ya sauke sassanyan
Nunfashi tare faɗin ,"Alhamdulillahi!!... "Don Allah ayi a hankali kar a tashi da kaka daga Bacci. "In sha
Allah Abba, tare suka fito da Sultana zuwa Palo.
Tunda yay sallama Abba da Mami suka zuba masa idanu cike da jin daɗin isowarsa a kan lokacin da ya
dace. Cikin girmamawa ya gaida su . Suma sun amsa masa da kulawa Meena harda ƴar tsokana. Kaɗan
gefen bakinsa ya motsa alamar murmushi yana Lumshe ido. Abba ya nuna masa alamar ya zauna anan. Bai
musaba ya zauna idanunsa akan Sultana da har yanzu take riƙe da kanta. Sai da yay mata kusan kallon
minti ɗaya da wasu sakanni sannan ya ɗago. Ɗan kallonsu yayi sai kuma ya sake maida idanun nasa kan
Sultana.
Hannunsa da Sultana ta riƙo ne ya sakashi saurin juyawa gareta. Cikin yanayin ciwo ta sake matse lallausan
tafin hanun nasa cikin nata tare da ɗorasa bisa kanta, “Abba ka riƙemin zai fashe”.
A hankali Sultan ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. Baiyi magana ba, bai kuma janye
hannunsa data ɗora akanta ba ta danne da hannunta kuma. Salma gabaki ɗaya jijinta yay sanyi ganin
Halinda Sultana take ciki.
"Tunda ga Shi yazo mu barshi ya yi aikin sa ko, cewar Abba Janye idanunsa yay daga kallon da yakema
Sultana, sai dai kafin ma ya ɗago su duk sun fice. Meena da Haydar kawai aka bari. Baice komaiba sai
hannunsa da yay ƙoƙarin janyewa daga kanta. Amma sai ta sake riƙesa da ƙyau tana faɗin, “Abba don Allah
karka tafi ka barni, kaimin addu'a kaji Abba”.
Sosai tausayinta ya sake lulluɓe su Meena . Sultan ya ɗan matsar da kansa kusa da nata kaɗan, a hankali
yace, “Ki daina magana zan baki magani yanzu zai Dena ciwo Kinji,
Sultana duk da bata cikin haiyacinta ta gane ba Muryar Abba ne,
Hayda buɗe mota na ka ɗauke box a ciki, da sauri Haydar ya fice daga palon jim kaɗan ya dawo hannunsa
rike da ɗan ƙaramin Akwati mai kyau , Kallon Haydar Sultan yayi, Please ko zaka iya haɗamin allurar
nan?” kasan cewar shima a school of nursing yake karatu . “to ya Sultan" ya jawo box ɗin.
Wata irin zabura Sultana da zancen ya shigarma kunne tayi, batare da sun fargaba suka ganta tsaye bisa
ƙafafunta jikinta na rawa. “Bana son allura, Abba! Abba! banason allura...” ta faɗa a wahale tana riƙe kanta
da hannu biyu duka tai baya luuuu zata zube. Cikin zafin nama Sultan ya miƙe tsayen shima, hakan yasa
Sultana faɗawa jikinsa nata jikin na wani irin karkarwa. Saurin riƙota yayi shima yana faɗin, “ Please calm
dawn!”

Ina batama san yana faɗa ba, kanta kawai take jujjuyawa a ƙirjinsa da faɗin, “Banason allura, Abba
banaso”.
“Okay shike nan, kinga baza'ai mikiba, ya isa ki daina magana, tana sa miki ciwo kai”. Yay maganar da
ɗaukarta gaba ɗayanta ya maida a kujerar zai kwantar. Sake ruƙunƙumesa tai, sautin muryarta na ƙara fita
da ƙarfi wajen faɗin, “Abbah karka bari sumin allura dan Allah ” ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
Meena da Haydar suka fice daga palon.... Sultana ta kanannaɗema jiki Sultan..........✍️
*Muna gab da kammala book 1 in sha Allahu*
PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗
_More comments and share pls_
*Sadeeya Ka'oje ce 💋*
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*
💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍
PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗
*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 37-38*
___________Ajiyar zuciya ya sauke a hankali jin yanda Sultana take sake tura kanta cikin ƙirjinsa. Ya ɗan
lumshe idanu ya buɗe akan dogon gashinta dake ta uban ƙamshi “Sultana ” ya faɗa a hankali yana kai
bakinsa dai-dai kunnenta. Batare da ya jira amsarta ba ya sake miƙewa da ita ɗauke a hannunsa. Zama ya
farayi saman kujerar sannan ita kuma ta koma saman cinyarsa da ƙyau batare da tasan mi takeyi ba. Syringe
ɗin da Haydar ya ajiye ya ɗauka, ɗan guntun ruwan allurar dake ciki ya kalla, ya ɗan fesar da huxi kaɗan da
zare hular kansa ya ajiye gefe. Ya sake kallon Sultana ya girgiza kansa, cikin ƙwarewa da sanin makamar
aiki ya kuma turata jikinsa da ƙyau tare da ranƙwafowa ya ɗaura bakinsa akan kunnenta. Wata irin
sassanyar iska ya shiga hura mata cikin kunne a hankali, yayinda can kuma hannunsa ke saita inda zai mata
allurar batare da ta saniba.
A hankali ta saki wani irin nannauyan ajiyar zuciya da sake shigewa jikinsa, saboda ƙamshinsa na sake
jan hankalinta. Hakane ya bashi dama tsira mata allurar dai-dai inda ya dace. Da masifar ƙarfi ta zabura tare
da fasa ƙara ta sake damƙesa da ƙyau jikinta na wani irin karkarwa.
Zare allurar yay yana sakin wani lallausan murmushi daya sake fidda annurin fuskarsa. “I am sorry”. ya
faɗa a hankali cikin kunnen nata.
idanunsa ƙyam akan Sultana dake ta juyi a jikinsa, sai zufa dake ta faman tsatstsafo mata a goshi.
Handkerchief ɗinsa fari ƙal ya fiddo cikin aljihun gaban rigarsa ya shiga share mata zufar, tsahon mintuna
biyar suna a haka kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere, a hankali kuma sai jikinta ya fara saki alamar
barci. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi. Kwanciyar ya gyara mata a cinyarsa yanda zataji daɗi
sosai, sai kuma ya kai hannu saman gashinta daya barbaje ya tattaresa cikin hannunsa. Ribbon ɗin ya ɗauka
ya ɗaure mata shi a tsakkiya ya nannaɗesa da ƙyau yanda bazai takura mata ba. Baya yayi ya kwanta jikin
kujerar shima, ya lumshe idanunsa da sakin sassanyar ajiyar zuciya.
Tsawon mintuna biyar suna a haka,
A hankali ya shimfiɗe Sultana a kujerar da ƙyau ya gyara mata kwanciya, kana ya fito daga palon
Duk kallon Sultan sukai cike da farin ciki, suka shiga jera masa sannu da godiya. Shi dai kansa a ƙasa yake
faɗin, “Abba karku damu aikina ne ai. Insha Allahu zata tashi kamarma komai bai faruba dan amfanin
allurar kenan. Sai dai a dinga kula dan abu kaɗan ita yanzu zai iya birkita,
“Insha Allahu za'a kiyaye. Allah ya saka maka da alkairi, ita kuma Allah ya bata lafiya yasa kaffara
ne”.
A tare suka amsa da amin, "Ni zan tafi, "A sauka Lafiya ina gaida Daddy ku, 20k Abba yaba Salma
gashi kuma sai Ice cream, Abinka da yaro nan take ta karɓe kuɗin tana murna, suna tsaye a wajen har su
motar Sultan ta fice daga gidan,....
Bayan wucewar Sultan duk suka shiga har falon yadda suka ganta. Hakan ya ƙara musu nutsuwa sosai,
Kwanaki Ukku Sultana tayi tana jinyar kanta, amma Alhamdulillah da sauki, dantana samun kulawa daga
Kaka da Mami,
___________★★★★____________
Yau tunda safe Sultana ta shirya zuwa wajen aiki kwanta huɗu kenan bata je ba.ta fito fes Abinta sai zuba
kamshi take, Kai tsaye ta wuce Asbiti kusan lokaci ɗaya ta iso tare da Jidda,
Gaban Sultana yafad'i lokacin da idonta ya sauka akan ya Sultan dake jingine jikin mota, sanye yake da
Shuit Ash color, yayi masifar k'yau, tunda take yaune karon farko data ƙare mata kallo,Jidda tace woow
wlhy Dr Sultan yahad'u Daughter kin more miji gaskiya! Allah nuna min ranar Auren ku!!"
"Ba Amin ba!"
Dariya Jidda tayi tana fad'in ," Ai tun tuni Allah ya ƙarɓi Addu'ar mu"
Lumshe Idanunsa yayi tare da saurin dafe ƙirjinsa kana ya buɗe Idanunsa tare da Kallonsu ɗaya bayan
ɗaya, har suka shige cikin Asbitin, daga can ɓangaren Aziz yace ," Bros baka jina? A hankali ya sauke
Ajiyar zuciya kana ya fesar da Numfashi,"Ina jikin ka Bros!"
Aziz yaci gaba da faɗin ," jikin Abie ya tsananta sosai Wallahi! Harta kai ga sai amma sa aiki a zuciya,
Sultan ya sake Nannauyan Ajiyar zuciya tare da farin ,"Allah ya bashi lafiya!"
"Amin Bros! Ya shirye shiryen Aure wai Ni kam har yanzu baka haɗani da matar tamu ba, Murmushi mai
sauti Sultan ya yi tare da faɗin ,"zaka ganta idon lokacin ya yi, " Bros nifa Very Soon Zanyi Auren nan, cike
da farin ciki Sultan yace ,"Allah ya nuna muna!"
"Amin Bros Ina gaida Amarya kuma In sha Allahu Aure saura sati ɗaya zanzo, da ga haka sukaci gaba da
yin waya, zuwa na ɗan wani lokaci kana ya wuce Office...... sai ƙarfe Shidda suka tashi, Sultana na ƙoƙarin
shiga Motarta Jidda ta Kalleta cike da tsoka tace ," Daughter duk yadda namiji yake sonki karki taɓayin
wasa da damarki har kici masa mutunci da rashin kunya, a duk lokacin da nakilli Dr Sultan nakan ga
tsantsan Soyayyarki a cikin idanunsa wanda ke kika kasa ganewa, Sultana ta taɓe baki tare da faɗin,"Aure
mafi daɗi da.kwanciyar hankali, babu kamar Auren wanda kake so yake sonka!!"
Sultan dake bayan su yana sauraren duk a binda suke faɗi, kai kawai ya sunkuyar yaci gaba da tafiya har
zuwa wajen motarsa ya shiga ya yi tafiyarsa...
Jidda tuni ta yi mutuwar tsaye, Sultana ko a jikinta, haka ko wannen su ya shiga motarsa ya wuce gida...
Sultana ya isa gida ta watsa ruwa tayi sallah, woyarta ta fara suwa tun kafin ta d'aga tasan waye ne dan
sautin kiran kawai ke shaida mata Nas ne ke kiran ta haka yasa cikin shauk'i da k'aunar juna suka fara
magana a waya cikin sanyin muryar da ko kana gefen ta a kan gadon bazaka ji abin da take fad'i ba,
Ido ta lumshe cikin sauk'e ajiyar zuciya tace.
"Hubbyna!"
"Na'am."
Yace mata tare da cewa.
"Sultana kina sani d'imuwa soyayyarki tana cazamin kai da jinin jikina k'ok'olwata na cushe in banji
muryar ki na awa 3 ba Sultana ki daure ki soni ko rabin yadda nake sonki."
Ido ta kuma lumshe wa cikin hura mishi iska a kunne murya can k'asa maƙoshi tace
" Hubbyna ka kontar da hankalin ka Sultana taka ce jiki da jini da duk wani motsina kana cikin raina ko
bacci nake muyarka nake jiki a kunnuwata.
A can Ɓangaren Nas kam k'ara sakewa yayi kan kujerar da yake konce gaba d'aya tsikar jikin shi yana
mik'ewa lokaci d'aya kalaman ta suka sakar mai wani kasala da shauk'i k'aunar ta yakeji na ratsashi har
cikin k'ahon zuciyarshi,
yayin da ita kuwa Sultana take jin duk duniya ba yanayin da take so da jin dad'in shi kamar kasan cewa a
haka suna musayan zantukan so masu sanyi,
ji take matuk'ar babu Nas a rayuwarta toh gani take kamar ba nunfashi tare da ita.
Haka sukaci gaba da soyewa kamar su shiga jikin juna, bayan ta gama wayar tayi salla Isha'i kana ta wuce
Palo Abinci suka ci gabaki ɗayan su kana kowa ya wuce makwancinsa......
_*five

19 / 21