Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dr Sultan Complete Hausa Novel by Sadeeya Ka-Oje

Author :  Sadeeya Ka-Oje Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 21

51K to 54K   out of 60.6K words

duk da dama
ƙa'ida kullum sai an share an goge. Gudun a girshe su... A hankali ya zauna sannan ya kunna Computer ɗin
da ke a gaban sa . Yanda yayi matuƙar zuba idanunsa ga Computer ɗin zai tabbatar maka abunda yake yi a
ciki yana da matuƙar muhimmanci. A haka Dr Halima ta turo ƙofar bayan tayi knocking ta shigo, Batare
da ya ɗago ya kalleta ba yace, “Matsalar yarinyarnan babba ne, sai dai zan mata wani ƙaramin Aiki yanzun,
dan haka ku shiryata zuwa theatre room”. Ya miƙa mata file ɗin gabansa yana cigaba da faɗin, “Wannan
mahaifinta zai saka hannu anan, ko mahaifiyarta Kuma dole ɗaya da ga cikinsu ake buƙata kawai”.
gyaɗa masa kai da faɗin “Okay sir”. Daga haka ta fice...
Cikin girmamawa ta ƙarasa wajen su Abba Fuskarta ɗauke da murmushi tace, “Congratulations, mun samu
nasara babban likitan da ganinsa ke da matuƙar wahala ya amshi gayyatarmu”.
Cike da jin daɗi suka shiga faɗin "Alhamdulillah Allah mun gode maka!!"
Da ga haka ta buƙaci magana da Abba Babu musu ya bita office. Bayani tai musu akan ƙa'idar saka hannu
da Dr Sultan ya sanar mata, jikin Abba bar karkarwa yake ya ƙarɓi file ɗin ya saka hannu.....
Bayan Abba saka hannun da Dr Sultan da wasu likitocin biyu sai Dr Halima ta uku suka shiga theatre
room da Sultana da ko maƙiyinta ya ganta a wannan lokacin sai ya tausaya mata....
(Dr Sulta Allah yasa ayi aikin cikin nasara!!!💔🤲
Tsawon lokaci suka ɗauke a theater room ɗin Sai kusan ƙarfe takwas na dare dai-dai su Sultan suka fito,
duk su Abba suka miƙe tsaye don son jin yaya ake ciki? Su Doctor Halima ne kawai suka tsaya musu
bayani, dan Sultan yana ɗakin bai fito ba...
A tare suka shiga faɗin Alhamdulillah Koba komai sunɗan sami kwanciyar hankali duk da ba cewa akai
Sultana samu sauƙi ba,
Su Dr Halima da suma fuskokinsu ke nuna alamar nutsuwar jin daɗin yanda aikin ya kasance suka
sanar da su zasu iya tafiya gida. Dan Doctor yace babu wanda zai iya ganin Sultana a yanzu, hasalima ba'a
buƙatar kowa a gareta.
Duk da ba haka suka so ba sun gamsu da bayanin Doctor Sadiq... "Kulsum mu tafi gida ko zuwa
anjima sai Mudawo.... Jiki a mace suka wuce gida ...
______★★★★★★_______
Abba ya kalli Kaka Ɗan Murmushin ƙarfin hali tai masa ta duƙar da kanta. Shima sai ya ɗan murmusa
cike da jarumta ya kirayi sunanta a hankali. ɗagowa tai ta sake kallonsa. Muryarsa a sanyaye yace, " an
kammala Aiki cikin Nasara Mama, ki Kwantar da hankali ki!!" inason mu ɗauƙi komai matsayin
jarabawa,
Ƙwallar da suka cika mata idanu haɗiye da ƙyar, ta maida kanta ƙasa dan karya gani tana faɗin, “Allah ya
bata lafiya!!"
“Amen ya rabbi” ya amsa mata shima.
Shiru ɗakin yayi kowa na nazari a zuciyarsa,.
Washe gari tunda safe Sultan ya iso Asbitin ko da yaje ɗakin da Sultana take har yanzu kwance take tana
bacci cikin wani irin yanayi. tsowan mintuna goma Sultan na tsaye yana kallonta... A hankali ya sauke
Nannauyan Ajiyar zuciya kana ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce gida...
★★★★★★★
sai Kusan ƙarfe Ukku na rana Sultana ta farfaɗo. Dr Sadiq dake tare da ita dan duty ɗin rans ne da
shi yay saurin kiran Dr Sultan ya sanar dashi,
Cikin ƙanƙanen lokaci ya shigo asibitin. Tsabar yanda ransa ke a jagule sai ya toshe idanu da baƙin Glasses
da yay masifar sake fiddo masa ƙyawun fuskarsa da kwarjinin saTunda ya shigo asibitin baiyi magana da
kowa ba. Ko gaidashi da Nurses suke da sauran ma'aikatan hannu kawai ya dinga ɗaga musu kansa a ƙasa
ya rufe rabin fuskar da p-cap bayan glasess ɗin....
Ɗakin da Sultana ke a kwance ya tura a hankali ya shiga da sallama ƙasa-ƙasa. Dr Sadiq da Nurses guda
biyu dake a tare da shi suka amsa suna ɗagowa. Da girmamawa Nurses ɗin suka risina suna gaishesa.
Batare da ya amsa musu ba suma ɗin ya ɗaga musu hannu kawai. Kafin ya miƙama Dr Sadiq hannun suka
gaisa..
A hankali ya juya kansa zuwa ga sashen da kanta
Sultana ya ke. Ya ɗan ranƙwafa kanta ƙaɗan ya janye wani igiyan na'uran dake a gefen kanta gab da kunne.
Yanda ƙamshin turarensa ya buga mata hancine ya saka ƙirjinta harbawa. Buɗe idanun nata tayi da ƙyar
saboda bala'in nauyin ciwo da sukai mata. Dai-dai Sultan ya dubeta shima yana ƙoƙarin zare glasess ɗin
idonsa. Kallon ido cikin ido sukaima juna, duk da ita ɗin dishi-dishi take ganinsa hakan baisa ta gagara
ganesa ba.
Wani irin juyawa kanta ke mata, daga ciki tanaji kamar ana karta mata ƙarfe, zabura tayi, ta yunƙura
zata tashi Sai kuma tai saurin dafe kan nata tace, "Wayyooh kaina!’.
Sultan da shima zuciyar tasa ke wani irin harbawa, da sauri ya wani ɗauke idanunsa daga kanta cike
da basarwa, tamkar bai fahimci halin da take a ciki ba.
Yanda jikinta ke wani irin ɗan karkarwa ga kanta data riƙe da duka hannayenta tana jujjuyawa ya saka
Nurses ɗin nufarta da sauri tare da Dr Sadiq Sultan dai na tsaye baiko motsaba. Sai dai yana kallonsu ne ta
ƙasan ido. Yanda duk suka so Sultana ta nutsu hakan ya gagara, dan ganin Sultan ɗin ya sake dawo mata da
komai,
“Live her.” ya faɗa a hankali tamkar ba shine yayi maganar ba. Baya Nurses ɗin suka ja domin cika
umarninsa, amma tausayin Sultana fal ransu. Dr Sadiq ya yi ƙoƙarin riƙo hannun Sultana data riƙe kanta da
shi gam ya keyi. A bazata yaji an riƙe masa hannun lokacin da yake gab da ɗorasa saman nata.
Sosai mamaki ya kama Nurse's Sultan ya fiske abinsa tare da sake tsuke fuska tamkar ba shine ya aikata ba.
Sai tura tattausan nasa hannun yayi ƙarƙashin kan Sultana da dogon gashinta ke a tsefe duk ya baje a saman
filon.
Da sauri ta sake buɗe idanunta, dan kusancin da suka samu gaba ɗayansu neman haifar da barazana yake
a bugun Zucikatan su, cikin rawar ji kinta daya ƙaru ta sake buɗe baki zatai magana, sai dai kuma hakan
kamar da wuya a gareta. Dan saɓanin yin maganar sai hawaye sharrrr!! Suka fara bin kumatunta. Yanda
damshin ruwan hawayen nata suka sauka bisa fatar hannunsa ne ya sakashi lumshe idanu yana wani jan
numfashi da sassarfa. Sai kuma a hankali ya janye hannun nasa daga cikin kanta dama jikinta gaba ɗaya ya
ɗan matsa baya yana Lumshe ido..
idanu da ya zubama Sultana da jikinta ke Karkarwa a hankali, har zuwa yanzun kuma riƙe take da kan nata
da duka hannayenta tana ɗan mirginashi bisa filon. Kusan mintuna biyu yana kallon nata, kamar yanda su
Doctor Sadiq ke kallonsa a tsorace, kafin ya ɗauka file ɗin Sultana yaja da baya daga gaban gadon Ya
shiga buɗe takardun dake a ciki file ɗin yana bin rubutun ciki daki-daki da nazari a nutse.
Su Dr Halima duk sun rikice, sai dai sun kasa fahimtar wane taimako ya dace su bata ne. Dawowar da
yayi gaban gadon riƙe da file ɗinne ya sakasu zuba masa idanu su duka. Ya ajiye file ɗin a saman drawer'n
gefen gadon da take sannan yayi magana a ɗan kausashe yana kallon Sultana " ki nutsu"
wani irin masifar zabura zata miƙe. Cikin sassarfa Dr Halima ta ƙaraso ta tareta. Da ƙyar ta iya dannata
saman gadon ta kwantar, duk da hakan kuma fisge-fisge takeyi har yanzun. Batare da Sultan , razananniyar
ƙara da ta amsa duka Word ɗin, Shiko yana tsaye ko gezau, duk da kuwa ƙarar tata jiyay tamkar zata
tarwatse kansa. Lumshe idanu yayi ya buɗe a hankali, a hankali ya nufi wajen Sultana
ya maida saman gadon, a kallo ɗaya zaka fahimci batama yin numfashi. Sai da yaja bargo ya lulluɓa
mata sannan ya maida mata duka na'urorin da ke manne da kanta ɗazun. Juyawa yay yayima su Dr Sadiq
alamar su fita. Suna gaba yana biye dasu riƙe da file ɗin Sultana...
a ƙofar ɗakin ya tarar da Abba da Mami tsaye sunyi zugum, sosai Abba da Mami sukayi mamakin ganin sa,
basuyi tunin shine Dr da aka gaiyata ba, "Abba mu tafi Office" kai tsaye suka wuce Officer...."
"Sultan pls ina bukatar ganinta Sultana!!" Sultan da yake wani irin jin kunyarsu da nauyinsu ne yay musu
rakkiya har ɗakin da Sultana ke kwance. Ba ƙaramin tashi hankalinsu yayiba ganin yanda aka jajjone kan
Sultana da na'urori, Mami harda hawayenta. Basu wani jimaba suka fito. Office ɗin Sultan suka sake
komawa. Inda ya sake musu bayanin komai dalla-dalla a nutse. “Abba Alhamdulillah ta farfaɗo, sai dai
kuma.......” Sai yay shiru kuma. Cike da dauriya yace, “Sultan ! Sai dai me? Karkaji komai kai min bayani
akan duk halin da Sultana take.. Abba tanama da ranta, sai dai dama bawai mun mata aikin ainahin
matsalarta bane kamar yanda Dr tai maka bayani ɗazun kafin mu taɓata. Aikin da mukai mata zai bata
taimakone kawai wajen hana ƙwaƙwalwarta goge komai da take barazanar yi, sannan zai sassauta mata
raɗaɗin da takeji a duk lokacin da matsalar ta motsa, insha Allahu zai hana ta iya rasa hankalinta. Nayi
tunanin aikin zai bata kariyar da zamu iya ɗaukar kamar watanni ai mata aikin gaba ɗaya, dan dole sai an
fita da ita waje, a ƙasarnan bamu da isassun kayan aikin, hankalinsu nakan abinda ya dace suyi bane. To a
yanzu dai matsalar dana fahimta dolene ai gaggawar yimata aikin koda nan da wata ɗaya ne insha Allahu,
inba hakaba zata iya rasa hankalinta a koda yaushe”.
Ɗan rumtse idanu Abba yayi ,cikin jarumta yace, “Shikenan Sultan , duk yanda kake ganin ya kamata
akai kayi tunda aikinka ne,
. Sosai suka gamsu da bayaninsa, wanda a take duk murmushi ya baibaiye fuskokinsu, suka shiga saka
masa albarka da jera masa addu'oin fatan alkairi. Har wajen mota ya rakosu, sai da yaga tafiyarsu sannan ya
koma ciki, dan yau a asibitin zai sake kwana saboda Sultana zata iya farkowa a kowane irin lokaci
wani Abokinsa dake India ya kira Yana buƙatar a aiko masa da wasu allurai ne masu matuƙar tsada da
zaima Sultana amfani da su. Kuma yana buƙatar sune da gaggawa daga nan zuwa gobe idan Allah ya
kaimu. Bayan sun gama maganar Sultan ya yi mashi transfer na maƙuddan kuɗi........✍️
_More Comments and share pls_
*Sadeeya Ka'oje ce ✍️*
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍


PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗


*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*

*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*

*Alkalaminmu abin alfaharn mu*

https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 35-36*
________ Washe gari, Wuraren ƙarfe Huɗu sakon Sultan ya iso, kai tsaye ya wuce Airport ya karɓi saƙon
Ya nufi ɗakin da Sultana take ya nufa. Dr Sadiq na biye da shi ɗauke da wata madaidaiciyar bag. A ciki ya
samu Nurse ɗin data gama gogema Sultana jiki.
Da girmamawa ta gaida shi, Dr Sadiq kuma ya ajiye bag ɗin ya fice. Matsawa yay gaban gadon
lumsassun idanunsa akan Sultana da fuskarta tai wani irin fayau. ta ƙara haske sosai Ya kafe Laɓɓanta da
sukayi wani irin jajur gwanin sha'awa, gashi taɗan tsuke bakin ya sake komawa ɗan mitsitsi,
Ajiyar Zuciya sauƙe kana ya janye idanunsa daga kallonta, ’ ya gyara kujerar gefen gadon ya zauna tare da
ɗaukar bag ɗin da Dr Sadiq ya ajiye ya buɗeta. Madaidaicin abu ya fiddo cikin kwali mai kama da kula, ya
buɗesa sai ga ƙanƙara a sama tanata huci. a ƙasan ƙanƙarar ya zaro kwalaben alluran kusan guda guda
bakwai ƴan ƙananu, zaune da ƙafafunsu. Sai da ya gama duba takardar dake a cikinsu kafin ya maidasu
ciki ya fiddo ɗaya kawai.
Miƙama Nurse ɗin dake a ɗakin yayi, murya a daƙile yace “Kiyi mata allurar nan yanzun nan”. Amsa
tayi da girmamawa. A gabansa ta buɗe syringe ta kwashe ɗan ruwan allurar da ko ganinsa bama ayi sosai
cikin syringe ɗin. Shine ya nuna mata a inda zatayi.
Nan take wani irin mahaukacin zufa ya fara tsatstsafowa a kowacce ƙofar gashi ta jikin Sultana
Kafeta da kallo Sultan dake zaune ƙafa kan ɗaya ya harɗe hannayensa a ƙirji yayi. Yanda take wani irin
mutsu-mutsu ya sakin wani tattausan murmushi daya ƙawata cikar haibarsa da kwarjinin Ya ɗan lumshe
idanunsa ya sake buɗewa a kanta yana jan ajiyar zuciya.
Bayan Isha'i Su Abba suka zo gabaki ɗayan su, kamar ko yaushe basu duka aka bari suka shigaba. Abba ne
kawai . Sai Kaka da Mami. Basu jima a asibitinba suka dawo gidan, cike da tausayin Sultana. Bayan ta
tafiyar su bada jimawa Jidda ta iso, da kyar ta shawo kan Dr Sadiq ya barta ta ga Sultana, sosai Hankalin
Jidda ya tashi ganin halin da Sultana take ciki...
Bayan kwana Biyar, tsawon kwanakin nan Daddy bai san mike faruwa, Abba bai sanar dashi ba, Sultan ɗin
ma bai gaya Mishi ba, Abba ya yi hakan ne saboda ya san halin Daddy yanzu sai yace sai an fitar da
Sultana waje don nema mata lafiya.....
Alhamdulillahi cikin hukuncin Allah Sultana ta farfaɗo. cikin hankalinta, sai dai ramar da tayi dolene ta
baka tausayi, hancin nan ya sake tsaho. Haka ma ta ƙara haske idanun sun fita da ƙyau masha Allah .
Ramarma sai ta sake fiddo mata da ƙyawun nata.
Ba ƙaramin farin ciki ahalinta suka tsinci kansu ba. Dan tunda farar safiya aka fara tururuwar zuwa
ganinta. Washe gari Sultan ya basu Umurnin sallamarta..dan insha Allahu ya tabbatar ta dawo cikin
hayyacinta. Zata kuma lallaɓa jikin har lokacin da za'a fita da ita ai mata aiki a ƙwaƙwalwarta ɗin...
Suna isowa gida Kaka ta sakata ta shiga wanka da ruwan data haɗa mata mai ɗumi. Yanda take jin jikinta
wani irine yasata nutsuwa sosai tai wanka mai ƙyau, dan ta kwashe tsahon lokaci a ciki kafin ta fito, Abinci
na musamman Kaka ta haɗa mata bayan ta gama ci ta bata maganinta kana ta kwanta nan take bacci ya yi a
won gaba da ita....
Sai bayan la'asar Sultana ta tashi. Wanka ta sakeyi da ruwa mai zafi tai sallah. Su Mami sai nan nan suke da
ita duk abinda take so shi aka mata,
Hakan yasa jikinta keta ƙara warwarewa. Bata fita ko ina, ko yaushe tana ɗakin Kaka . Sai dai taci ta ƙoshi
tasha magani tayi barci. Wani lokacin Meena da Nana kan shiga su tayata hira.
Bayan sati ɗaya, Still Abba ya sake tunkar Kaka da maganar Auren Sultana... Sultana na toilet Nana ya
shigo ɗakin Su,"Anty Sultana Abba na kiran ki. Da Sauri Sultana ta fito da wanka ta zura dogon hijjab
akan zanin wanka ta fita kiran da Nana sake zuwa tai mata. Ta iske kowa ya hallara ita kawai ake jira,
zuciyarta cike da mamakin taron ta ƙarasa garesu. Kusa da ƙafafun Kaka ta zauna tana gaishe da iyayen
nata. Duk suka amsa mata da kulawa suna sake tambayarta ƙarfin jikinta.
"Alhamdulillahi Naji sauƙi sosai!"
A kusan tare suma sukace Alhamdulillah "Allah ƙara sauƙi, "Amin Abba"
Abba ne ya buɗe taron da addu'a kamar yanda shari'a ta koyar da mu. Bayan sun kammala Kaka ta fara
magana akan abinda ya tarasu.
"Sultana! Har yanzu dai muna kan maganar Aurenki da Sultan, Wani irin faɗuwa gaban Sultana yayi, ta
dubi Abba. Nan Kaka ta soma yi mata Natsiha cikin ruwan sanyi, ta yadda Abun zai zo musu da sauƙi..
Zuciyarta na wani irin harbawa ta sake duban su Abba Yanda duk suka zuba mata idanu cike da tashin
hankali sai itama suka sake ɗaga nata hankali ƙololuwa. Saurin maida kanta ƙasa tai tanajin anya kuwa zata
iya?. A take rauninta ya sake bayyana bisa fuska tamkar yanda suma duk suke a raunane zukatansu na rawa
da barazanar son faso ƙirazansu su fito.........
"Mamana ke muke saurare daure ki faɗa mana abinda ke a ranki kinji,
Kuka Sultana ta fashe da shi, bakinta na sake rawa tace, “Abba Abbah ni Nas nake so!!!.. "Sultana Abba
ya kira sunanta da ƙarfi.
Bayan ta ɗan zabura kaɗan ta ƙara mannewa da jikin Kaka . Sai ɗan girgiza kanta take hawaye na zubo
mata da sauri-sauri...
Cikin sanyi Murya Mami tace ," Abban Haydar Abita a hankali kasan matsalar dake tare da ita"
"Sultana ki kwantar da hankalinki kinji, cewar Mami,
Kanta ta jinjina tana share hawayenta. Ta ɗago a hankali ta zubama su Abba dake kallonta idanun.
Kowannensu a kallo ɗaya zaka fahimci roƙonta sukeyi da idanu ta zaɓesa. Hakanne ya sake saka zuciyarta
sake raunana. Cikin rauni Murya tace Abba na Amince zan Au..... Sai kuma ta fashe da kuka mai tsuma
zuciya.
Fusakar su ɗauke da murmushi, suka shiga sanya mata Albarka...
"tashi kije mun gama da ke. Ki kuma share waɗan nan hawayen ki kwantar da hankalinki, dan munsan
abinda mukeyi”. Kai kawai ta jinjina mata tana miƙewa. Batare da ta sake duban inda su Abba suke zaune
ba ta fice a falon jikinta duk a sanyaye. Zuciyarta kuwa wani irin zafi take..
Sultana na zaune a ɗakin kaka tana sharɓar kuka, ahaka Kaka tashigo ta isketa. Da sauri tak'arasa gareta
tajawota jikinta ta rungume, tana mai lallashinta.
Kiyi hak'uri Sultana, nima bazan yarda a cutarmin dakeba, Sosai Kaka ta lallesheta tare da Kwantar mata
da hankali...
_______★★★★★_______
Sultan Komai yinsa yakeyi cikin wani yanayi, kokad'an babu alamar d'igon walwala tattare dashi, ga
d'unbin kasala daya tashi da ita ayau, hakan tafarune saboda k'arancin barci dabai samuba a kwanan nan ,
saboda Feshin lafiyar Sultana, siririn tsaki tareda yaye towel d'in dake kugunsa bayan yasaka boxer, yad'an
Mirza mai kad'an ajikinsa tareda feshe ko ina Na jikinsa da body spry d'insa mai dad'in k'amshi, yasaka
farar vest sannan yasaka Shuit , yayi k'yau sosai,
Wani turaren yakuma d'an fesawa kad'an, sannan yajawo takalmansa da safa yazauna kan sofa yana
k'ok'arin sakawa.

18 / 21