Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dr Sultan Complete Hausa Novel by Sadeeya Ka-Oje

Author :  Sadeeya Ka-Oje Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 21

45K to 48K   out of 60.6K words

alawalan tare da
doguwar riga ta roba ta saka har zuwa lokacin jikinta na ƙamshin tularensa Sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da
Sallah...
Har aka kira sallah Sultan bai dawo ba, kiran Sultan ɗin Daddy ya yi, nan ya sanar dashi ya wuce Asbiti an
kawo wani Emacency,
Sultana yana isa gida kai tsaye ya wuce ɗakinsa kayan jikinsa ya cire kai tsaye toilet ɗin sa dake cikin
Bedroom ɗinsa ya nufa yana shiga ya sakarwa da kansa ruwan ɗumi batare daya cire boxer ba yana tsaye
ruwan ɗumin ya cigaba da zuba akansa
Sai da yay kusan mintuna ashirin a haka sannan ya kashe shower ɗin yana sauke numfashi a jajjere
babu abinda ke yawo a idanunsa kamar lokacin daya rungumi Sultana ga wani Daddaɗan ƙamshinta da
yake ji ajikinsa da ƙarfi ya Lumshe idanunsa.
Kai kawai yake girgiza wa cike da tashin hankali mara misaltuwa daya rufe idanunsa babu abinda yake
hange face yanayin da suka kasance,
bayan ya gama wanka al'wala ya ɗaura tare da fitowa, ya sanya lallausar jallabiya, a hankali ya tattaro duk
kan natsuwar kana ya kabbarta sallah. Har akayi Isha'i ya zauna a wajen,
Babu abinda kema Sultan yawo a zuciya da ruhi sai kalaman Sultana. Kalaman sunyi masifar tasiri a ransa
fiye da zaton mai karatu. Sai faman tisasu yake dalla-dalla kamar mai bitar karatu. Duk da A.c dake aiki a
dakin bai hana zufa tsatstsafo masa a goshi. Kana ya sauke wani irin nannauyan numfashi yana sake
tariyo kalaman Sultana ,"Allah ya isa ban yafe ba! Mugu Azzalumi!!,
ɗunbin takaici da dana sanin abinda ya aikata ma yarinyar yakeyi, wanda sam ba halinsa bane yin
hakan,bayan Maryama ba wata ɗiya macce da ya taɓa runguma, amma yasan ita da duk wanda zai iya ji ko
ganinsu a lokacin bazai taɓa yarda da shi ba. Ya ɗan ciza leɓensa na ƙasa da ƙarfin tsiya, ƙirjinsa na sake
masa zafi.
Mikewa tsaye ya yi tare da zaɓewa saman gadon tare da saurin dafe kansa dake barazanar rabewa biyu,
Tashi yay zaune zumbur yana huci, so yake abinda ya faru yabar ransa, amma tamkar ana ƙara kusanto
masa da hotonsa ne a zuciya. Da ya rufe ido babu abinda yake gani sai fuskar Sultana da ƙirjinta, sune kwai
Abinda yake gani...
Su Daddy sai bayan isha'i suka dawo gida.
Bayan ta fiyarsu Meena ta shigo ɗakin riƙe da 🎁 ta mikama Sultana, jiki a mace ta ƙarɓa ,.....
Washegari Duk yanda Sultana taso sakewa ta kasa hakan. Gani take kamar kowa yasan abinda ya faru
tsakaninta da Sultan,..ranar dai haka ta yini cikin sanyin jiki....A ɓangaren Sultan ma ranar gabaki ɗaya a
ɗaki ya yini sallah da cikin Abinci kwai ke fitar dashi..
Washe gari. Cikin sanyin jiki da damuwa Sultana ta shirya cikin Uniform ɗin ta da suka sha guka baki
daya ta kasa sakewa da zaran ta tuna, Sultan sai tashiga da muwa..cikin dauriya ta nufi Asbitin...tana kaffa
kaffa karsu haɗu da Sultan....
À ɓangaren Sultan ma tunda yashigo Asbiti ya wuce office ɗin su ya zauna cikin zullumi da damuwa.
idanunsa alumshe duk abin duniya ya Ishesa.
Haka dai Sultan ya yi Ni a Office har zuwa lokacin tashi ya wuce gida..
★★★★
Yana isa gida ya Parking ya fita Kai tsaye sashensa ya wuce cikin mutuwar jiki ya kwanta ruf da ciki tare
da lumshe idanunsa yayin da ƙwaƙwalwar sa ta shiga tariyo masa yanayin da suka kasance, sam Abin ya ƙi
barin ransa,
Miƙewa yayi cikin rashin sanin Abinda Zaiyi, ya zaiyi da wannan jarabar tun jiya yake fama da zaran ya
rufe Idanunsa yanayin da suka kasance da Sultana ne yake gani.
Batare daya shirya ba yaji hawaye Masu Zafi suna bin kuncinsa shi kansa baisan meyake so ba bai san
meke faruwa dashi ba yakasa sanin yana yin da yake ciki ji yayi kawai yana kuka hawaye na bin kuncinsa
yana sheshsheƙa. Nan take kuma zazzaɓi ya rufeshi lips ɗin sa suka shiga rawa.. A hankali Daddy ya tura
ƙofar ɗakin ya shiga, ganin Sultan kwance jikinsa na karkarwa ya nufi wajensa da sauri ya na kiran
sunansa,"Sultan!! Me ke damun ka? Baka da Lafiya ne?"
Sultan ko magana yake son yi Amman ya kasa, da kyar ya fisgo magana,," Daddy sanyi nake ji, Daddy ciki
na ciwo kaman zai ɓalle!"
da sauri Daddy ya lulluɓesa da blanket mai laushi..a hankali Daddy ya miƙe ya kashe A.c dakin kana ya
gyara mishi kwanciya, kasan cewar lokacin Sallah ya yi ya wuce masallaci, ana gama Sallah ya wuce
Asbitin Sultan dai dai lokacin Kuma Dr Aryan na ƙoƙarin barin Asbitin ganin motar Daddy yasa ya nufi
wajensa da saurin ya gaida shi cikin girmamawa, bayan sun gaida Daddy ya yi mai bayanin Sultan ba
lafiya,
Tare suka wuce can gida, koda suka iso Ana kiran Sallah, Saida sukayi sallah kana Daddy ya yi mishi
jakora zuwa ɗakin Sultan, yadda Daddy ya barsa kwance haka suka tarar dashi.
Dr Aryan ya fara dubasa. gyaran murya Dr Aryan yayi tare da cewa,"ciwon Mara ke damunsa,"Daddy Dr
Sultan na fama da matsananciyar Sha'awa!" Yanzu ma itace ta motsa" idan har aka bar shi da wannan
sha'awar zai iya zame masa matsala zata iya jefashi acikin damuwa.
Daddy ko sai kallon Dr Aryan yake.
A hankali Daddy ya sauke Nannauyan Numfashi kana sannan ya ce,"Miye mafita yanzu?"
"Mafita ɗaya ce yanzu Daddy kawai yayi ƙoƙari yayi aure”.
Nannauyan Ajiyar zuciya Daddy ya sauƙe tare da cewa.
"In sha Allahu zamu yi ƙoƙarin mu"
Magani Dr Aryan ya rubuta Mishi kana ya miƙama ,"ga wannan ya yi ƙoƙari yasha su kafin zuwa safe, a
samu ruwan ɗumi a masa laimun tsami da zuma a bashi ya sha.. godiya sosai Daddy ya yiwa Dr Aryan har
bakin mota ya rakashi..bayan ta fiyarshi Mommy ta kalli cike da damuwa tace ," mike damun sa?"
"Je ki daɗo min Lipton da Lemun tsami ki saka zuma kaɗan" da sauri Mommy ta wuce Kicin, jim kaɗan ta
dawo hannunta ɗauke da Mug sai tururi yake, Daddy ya ƙarɓa ya wuce ɗakin Sultan. da taimakon Daddy
Sultan ya sha ruwan Lipton ɗin nan take Zufa ta riƙa tsastafo mishi, Atake yafara jin abinda ke damunsa na
sauƙa kaɗan-kaɗan ahankali yaji lips ɗin sa ya daina rawan zamewa yayi ya kwanta akan gadon yana sakin
Ajiyar zuciya.. ya kallesa ya yi Murmushi kana ya fice daga ɗakin.
Sai wuraren ƙarfe ɗaya Sultan ya farki, da sauri ya nufi toilet ya watsa ruwa ya yi Alwala kana ya fito,
Sallah Maggariba da Isha'i ya yi da bai samu damar ya ba.
Washegari sosai ya ji sauƙi...wuraren ƙarfe Goma ya wuce Office, sai shidda ya dawo, haka suka ci gaba da
wasan buya shida Sultana...
Bayan Sati ɗaya,
Bayan Isha'i Suna zaune a Palo Sultan na zaune kusa Mommy, Daddy ya yi gyaran Murya tare da kallon
Sultan," My boy! Mun gama yanke shawara da nida Aminina, ya kuma mallakama Sultana halak malak don
haka ku dai daita tsakinin ku"
Tunda Daddy ya fara magana, gaban Sultan ke daɗuwa, Mommy ko sai murmushi take .
"Ya Naji baka ce komi ba ?"
"Duk yadda kace haka za'ayi Daddy"
"Good haka neke son ji, mun riga da mun gama magana da Mahaifinta, ko wanne lokaci zaka iya zuwa,
Allah ya tabbatar da Alheri," Amin Mommy ta faɗa cikin tsananin farin ciki...
A ɓangaren Abba tuni ya sanar da su Mami da Kaka halin da ake ciki, sosai kuma sukayi farin ciki,
musamman Kaka, saboda Sultan ya kwanta mata a rai sosai duk da bata taɓa ganin sa ba, Abba ya so A
sanar da Sultana komi Amman kaka ta hana shi, a cewar a yiwa Sultana ba zata...
Yau ta kasance Friend
Tunda safe, Massege ɗin Nas ya tashi Sultana daga barci.
*Aminci Allah ya tabbata a gare ki yake ma'abociyar kyau, da kuma kyawun sura burin zuciya ta kasance
dake, duk wanda ya samu mace tamkar ya dace, kece mai ɗebin min kewa kece mai Shogoɓa Ni,kece farin
ciki na, kin kasance komai a rayuwanah Sonki ya mamaye Zuciyarta cikikar burkina shine ki zamo uwar ya
yana Sonki ya mamaye Zuciyarta ba zan iya rayuwa idon har ba keba ki riƙe min Alƙawari ki zamo jigo a
rayuwata Good Morning my Hubby, I love you so much *
Wani irn murmushi ta saki.tare da sumbatar wayar.
*Kayar dani my Hubby Babu wani da zai kwace Zuciyata, domin Zuciyata ta kece har Abada Idanuwana
kai kaidai suke kallo a matsayin Abokin rayuwata in son ka! Ina kyaunar ka da fatan ka tashi Lafiya
Hubbyna i love you so much 💋*
(Hmmm🤣🤣🤐)
★★★
tsananin mamaki ta kalli Mami da tuni ta bar wajen, Baƙo ta faɗa a hankali.. tsawon lokaci Sultana na
zaune tana maimai ta kalmar baƙo a ranta,tana zaune a wajen har Abba ya fito," Wai zaman me kike
anan,"firgit ta mike tsaye tare da barin Palon kai tsaye ta wuce palon Abba...✍️
( Oh ni Halimatu ko ya za'a tarbi baƙo oh ho 🥲🤣🤣)
_More Comments and share pls_
*Sadeeya Ka'oje ce*✍️
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*
💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬

Bismillah........ ✍
PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗

*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*

*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 31-32*
_______Murya a sanyaye tai sallama a ƙofar falon har kusan sau uku. jin shiru ba'a amsaba ya sakata tura
kanta ciki da haushi. rashin amsa mata sallamar da ba'ayiba ne ya sakata ƙin kallon baƙon ma balle tasan
wanene.
murya a cinkushe batare data kallesa ba tace, "ina wuni".
Sultan dake zaune yana dannar waya .ya ɗan ɗago kansa dan sam baiji sallamarta ba balle shigowartaba
ma shi, sai gilmawarta kawai ya gani yanzu da take ƙoƙarin fita. Cikin tsautsayi ta bigi Center table da
ƙafa. baya tai taga-taga zata faɗi cikin sa'a yayi saurin saka mata ƙafa dan son kareta bisa tsautsayi ta faɗa
saman cinyarsa.. Daddan turarensa ta Shaƙa tayi tai azamar ɗagowa cikin tashin hankali da tsantsar takaici.
Idanunsu ne ya shige cikin na juna, cike da firgici Sultana ta sake waro masa idanunta da kware baki
zatai ihu saboda harga Allah ta tsorata da ganinsa. Saurin saka tattausan hannunsa yayi ya rufe mata
bakin , tare da sake manneta a jikinsa sosai shima a cikin ɗan firgice.
Wani irin mugun bugawa ƙirjinta ya sakeyi, jikinta ya hau ɓari tamkar mazari mutsu-mutsun ƙwace kanta
tana kai masa duka a ƙirji..
"Oh my God!. Please calm dawn”. Ya faɗa yana janye hannayensa duka daga jikinta.
Cikin rawar jiki hawaye na zirara ta miƙe, sake bigewa tai da kujera ƙafarta ta tuzguɗe ta sake yin gaba
kuma zata kifa yayi saurin riƙo mata hannu ta sake dawowa jikin nasa.
“Wayyo Kaka ɗan isk.........” ta wage baki da iya ƙarfinta zata faɗa yay azamar saka hannu ya sake
toshe bakinta da manneta sosai a jikinsa yanda bazata iya ko motsawa ba.
da ƙarfi Sultana ta janye jikinta
Sultana dake ja da baya tana ja da baya da kallonsa tace, “Ɗan iska kawai, Allah ya isa ban yafeba.
Wallahi daga yau ka sake ƙoƙarin taɓamin koda hannu sai na illataka.
A hankali ya nufi wajen Sultana dake durƙushe har yanzu tana kukan tashin hankalin,
Handkherchief ya ciro a aljihunsa tare da tsugunawa gabanta, murya ƙasa-ƙasa yace, “ Stop crying!”.
A razane Sultana da batasan da isowar tasaba ta ɗago danjin maganarsa gab da ita. Kamo hannunta
yayi, da sauri ta dawo da dubanta garesa tare da fisgewa da ƙarfi. Sai dai ko gezau baiyiba balle tai tunanin
ƙwacewar. “Kai wane irin......”
Yatsansa ɗaya ya ɗaura akan baki. “Shii!" ya faɗa cikin katseta da zazzaro mata idanunsa sosai.
Tai saurin rufe bakin kuwa. Dan wani irin shakkarsa da tsoronsa da bata taɓa fuskantaba daga
gareshine ya shigeta yau ɗin. Ga wani irin kwarjini mai bala'in cika idanu da yayi mata. Batare da yayi
magana ba ya saka mata handkherchief ɗin cikin tafin hannunta tare da matso da fuskarsa gab da tata cikin
wata irin raunanniyar murya yace, " It okey"
daga haka ya fice daga palon Ya tabbata idan ya cigaba da zama a falon to lallai zai iya aikata abinda shi
kansa bazai yafema kansaba.
da kyar Sultana ta tattaro da duk natsuwar Kana ta wuce gida tana sauke Ajiyar zuciya, Palo ta tarar da
Abba da Mami da Kaka. Sai faman kallonta suke, Kaka ta ce ,"Ina mijin namu yake?" Shine ya wuce ko
gaksuwa babu?"
Ciki reshin fahinta Sultana tace ,"Miji Kuma?"
"Mamana! Sultan shine mijin da zaki Aure"
Sultana dake jin jiri na neman zubar da ita ƙasa ta faɗa tana mai dafe kanta,Da ƙyar ta iya kai hannu domin
lalubar bango. Sai dai kuma ina bai kai ga bangonba wani duhu ya mamaye idanunta. a take ta zube ƙasa
jikinta na karkarwa saboda wani bala'in sara mata da kanta yayi lokaci ɗaya, cikin tsananin tashin hankali
suka nufi wajenta da sauri Abba ya zabura dan jin jikinta yayi sanyi ƙalau ya saki. Yayi saurin maida
yatsunsa biyu wajen hancinta. tabbas bata numfashi’l ya ambata a zuciyarsa yana ɗagota gaba ɗayanta.
Mami da Kaka duk sun ruɗe
Cikin tashin hankali Kaka tace, "Abdullahi mike damunta "Ban saniba nima Mama, kinga miƙo ruwa
dan bata numfashi"
. da sauri Mami ta ɗakko masa ruwan , ya miƙa hannu ta tsiyaya masa. shafama Sultana yayi a fuska. sai
dai ko motsi batayiba balle ai tunanun zata farko. Hankalin Abba ya sake tashi matuƙa. Ya ɗago idanunsa
da sukai jajur ya kalli Mami
dai dai lokacin Haydar da Khalil suka shigo palon, hankali a tashe suka nufi wajen Sultana dake kwance
kaman babu a rai a cikinta, cikin raunin Murya Abba yace Haydar fito da mota, aiko da sauri ya ɗauke key
mota ya wuce wajen jikinsa na karkarwa, Abba ya ɗauki Sultana suka wuce waje, Kaka ta bi bayansa da
Mami kai tsaye suka wuce private hospital dake cikin Unguwar su,
Tun isowarsu asibitin aka fara bama Sultana dake a sume taimakon gaggawa. tsawon lokaci bata farfaɗo ba
Hakan sai ya sake ɗaga hankalinsu. musamman ma Kaka dake ta faman sharɓar hawaye. Cike da kulawa
Abba ya zauna kusa da ita duk da kunyar ɗan fari dake tsakaninsu. Murya a tausashe da nuna ɗunbin
kulawa da ladabi ya fara lallashinta da faɗa mata kalamai masu taushi da nutsuwa irin na masu ilimi. Ya
nuna mata koda rasa Sultana sukayi su zama masu haƙuri da godema Allah . Dan lokacin da ya basu ita
baiyi shawara da suba. A yansu kuwa idan ya karɓeta ya fisu bukatarta ne. Haka ya cigaba da mata nasiha
harta samu nutsuwa tai shiru. Ya saka handkherchief ya share mata hawayen.
Ana haka Doctor ya fito daga ɗakin da aka sanya Sultana. Ya buƙaci ganin ɗaya daga cikinsu cikin Abba da
Kaka suka bisa Zuwa Office,
A office ɗin likita kuwa ya nutsu ne wajen rubuce-rubuce a wata takarda kafin ya maida hankalinsa
gasu Abba," Alhamdulillahi ta farfaɗo,.Sai dai kuma kamar yanda kuka sani raunin dake a cikin
ƙwaƙwalwarta shine ya motsa mata. Kuma gaskiya a bincikenmu yarinyarnan tana matuƙar buƙatar son
ganin babban likita. Idan ba hakaba a koda yaushe zata iya fuskantar gogewar komai na ƙwaƙwalwar ta. . A
duk kuma lokacin data shiga ƙunci ciwon na mata kuɗa a cikin kanta, ba dan ma tana samun kulawa da
kuma addu'oi ba da gaskiya bana zaton yarinyarnan zata kai wannan lokaci batare data tsinci kanta a ciwon
hauka ba. Duk da komai na Allah ne, babu wani bawa daya isa canja ƙaddarar wani bawa daga yanda tazo
a littafinsa. Amma a wannan karon ayi himmar sadata da likitan daya dace da matsalarta, munan taimako
kawai muke bata na dakatar da raɗaɗin a gareta a lokacin daya taso. Amma matsalarta sake hauhawa takeyi
gaskiya,
Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare da Kaka ta kalli Abba cikin raunan'nanyar murya ta ce ,"
Abdullahi mike damun Sultana!!!? Naji likita na faɗin kwakwalwarta ta samu matsala yaushe hakan ya
faru ban sani ba? Abdullahi mi kake ɓoyemin akan Maryama!!? A iya sanina Maryam lafiya kau aka haifeta
bata da wata matsala!!"
Abdullahi da gabaki ɗaya jikinsa ya yi sanyi, irin wannan rana yake gudu da tun lokacin da abin ya faru ya
yiwa Kaka bayani da han bata baruba.. Abdullahi ya sauke Nannauyan Numfashi kana ya kalli Kaka cikin
sanyi Murya mai cike da lallashi ya ce ," Mama ki gafarceni akan reshin faɗa Miki gaskiya da banyi ba,
Mama shekara Takwas da suka wuce Sultana tana fama da wannan matsalar Sanaɗiyar Wannan yaron da ta
rasa Abdulmalik dake ƙayare, saboda so da shaƙuwar dake tsakaninsu jin labarin mutuwarsa a bazata shine
ya haifarda wannan matsalar!"
Kaka ba baki ɗaya jikinta Ya yi sanyi, duk abinda aka ce mata ya faru da Sultana sanaɗiyar rashin
Abdulmalik ba zayi musu ba, saboda tafi kusanshi dasu tafi kowa sanin irin shaƙuwar dake tsakinsu, cikin
raunin Murya tace ,"Allah ya jikanka da Rahama Abdulmalik!! Allah yasa ka huta"
"Amin Abba da Dr suka amsa mata.
Abba da duk jikinsa yay sanyi godiya sosai sukaima Doctor Tare da tabbatar masa insha Allahu a wannan
karon zasuyi abinda ya dace.
Yaji daɗin hakan sosai. Ya sake ɗan musu wasu bayanan da suka dace akan yanayin kula da Sultana.
Godiya sukai masa sosai, sannan suka fito. Ɗakin da aka Kwantar da Sultana suka shiga Sultana dake
barci suka bar Kaka, sanin halinta koda Ance taje gida bazata yadda ba, hakan yasa suka wuce gida, koda
suka iso gida Haydar Meena Khalil Nana duk suna zaune a Palon kallo ɗaya zaka musu ka fahimci suna
cikin damuwa, lokacin da Abba ya shigo ya tabbatar musu Sultana tana cikin kwacin lafiya, hakan yasa
suka wuce ɗaki..
___________★★★
Sultan dake kwance idanu a lumshe, hannunsa har yanzu dafe yake da kansa. Yama rasa wane kalar tunani
ya dace yayi akan matsalarnan . Abinda ya aikatama Sultana.
awannan dare haka ya kwana cikin mawuyacin hali saboda wani azabebben yanayi dake damunsa sai.
Wajajen ƙarfe Huɗu wani irin bacci mai shegen daɗi ya ɗauke sa.
Washe gari tunda safe

16 / 21