Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIDA a RUWA 1 Complete Hausa Novel by Bilyn Abdull

Author :  Bilyn Abdull Category :  Drama

Chapter   14 / 35

39K to 42K   out of 104.8K words

hannu, baice mata komai ba ya ?auki fitila data ajiye zata fara alwala ya wuce bayi, sanda ya fito ta gama zata wuce. Dan haka cike da lallashi ya ce, ÒDan ALLAH ki zauna a gida to kada kije ko ina na dawo na baki tsarabarki da sa?on Inna, kada yazam akwai abin lalacewa a ciki kinga zai lalaceÓ.
Ê ÊÊ Kanta dake ?asa ta jinjina masa. Sannan sum-sum ta shige ciki. Shima yay alwala ya fita. Koda ya dawo da wannan bu?e tsaraba yaja ra'ayinta, har hantsi ya fito ya fita ya sayo mata shayi, sai kuma ga kayan kari Inna ta aiko. Da lalla?a, da lallashi da kwantar da kai ya samu wannan yini dai aka yi shi lafiya. Da dare kuma ya kafa ya tsare ya nuna mata shi tayi duk yanda take so. Ganin ya?i kulata da abinda take gudun a yinin ma ko kusa da ita bai zauna ba balle ya ta?a mata hannu sai ta ha?ura ta kwanta a gadonta, amma acewarta da ido ?aya zatai wannan barci. Da yake shi barcin ya fita wayon bata ma san ya kwasheta ba har wanda take tsoron ya zauna a bakin gadon kusa da ita yay mata addu'ar barci sannan ya koma nashi gadon. Wannan sabon yin biris daya ?auka ya kawo masalaha a tsakaninsu, itama ta sake jiki suka koma kamar da. Sai dai kwana kusan shida kuma yaji fa yana neman halaka, a daren ya kasa ha?uri ya sake maimaita na wancan daren, koma muce abinda yafi na wancan daren dan ya sameta fiye da waccan ranar, sai dai kuma ta fitgice masa dole ya barta batare da cimma buri ba. Daga nan ne fa ta sake birkice masa. A daren washe gari kuwa bata kwana a gidan ba, ta sake gudawa gidansu cikin su Nana ta kwana. Ita kanta Innar da su Nanar basu farga da ita ba sai da asuba da Inna ta tashesu suyi salla. Rasama abin fa?a tayi, yau ma sai tace su Alawiyya su rakata gida kawai.
Ê Ê Ê Kwanakin da suka biyo baya har hu?u A'isha bata daina yo tsere ba. Abdul-rasheed kuma ya zuba mata ido, hasalima ya koma maida hankalinsa batun bu?e wajen ?inkinsa ya ?yaleta. Hakama Baba yana sane A'isha a gidan take kwana, amma bai ce komai ba sai dai yayi murmushi kawai. Koda Inna tai masa magana a cikon kwana na hu?un sai cewa yay, ÒTo mizance, tunda shi bashi da ha?uri da kawaicin barin yarinya ta sarara ka?an ma kenan. Ke kuwa naga kema haka kika dinga yi min Karima, ?arshe sai da Baba ya rakoki da tsumagiya gidan nan saboda can kike zuwa.Ó
Ê Ê Ê Ê Ê ÒAi kai ka jika Malam, ana maganar arzi?i saika dinga sakko wadda ba'a tambayeka ba. Amma ka bani dabara nima da tsumagiyar zan korata yau. Ina laifin yaron nan ai yayi kawaici ma. Aure wata shida haba ai a yaba masa. Abdul-rasheed da ha?uri da zurfin ciki. Su sauran ?an uwansa wa yayi wannan ha?urin. Tijjani ma da yafi kowa rashin ta idonsa ko tsallake rana yayiÓ.Ê Haka ta fita tana sababi. Baba kuwa sai murmushi yake abinsa kawai...

Ê Ê ÊÊ Washe gari kuwa Inna ta shiryama A'isha tsaff, dan yanzu dai sune iyayen tunda babu wani nata a kusa. Kuma a wannan zamanin nasu na adalci ?a na kowa ne. Babu wani surukutar mugunta ga matar ?a da uwar miji, yanda suke ma ?a?ansu haka suke ma matan ?a?ansu saboda adalci da ?ya?y?yawar zuciya, haka suma surukan suna ?aukar iyayen miji iyayensu ba irin na yanzu ba da suke ganinsu kamar koshiyoyi. Kamar ko yanda ta saba ana cikin sallar isha'i sai gata ta shigo soron gidan da san?arta. Caraf Inna dake a soron ta dalleta da Torchlight, A'isha tai tsaye cak tsuru-tsuru da idanu, sai kuma ta du?a tana gaida Inna dake tsaye kawai tana kallonta. Batare da Inna ta amsa mata ba ta ce, ÒJuya mujeÓ.
Ê Ê Ê Kallonta A'isha tayi kamar zata fasa kuka, Inna ta ha?e fuska kuwa ci?in-ci?in. Sum-sum ta nufi ?ofa dan tasan dai yau ruwa ya ?arema ?an kada kam. Haka Inna ta sata a gaba har gida da ?ar tsumagiyarta a hannu, badan ta daketa ba sai dan ta tsoratata. Karo na farko da Inna tazo gidan kenan, suna isa ?ofar ?aki taci karo da buta, ?auketa tai ta maida gefe suka shiga ?akin. A mamakinta sai suka samu Abdul-rasheed a ciki kwance a tsakar ?aki kan tabarma. Ashe ma yana gidan ta fita, baida lafiya, amma saboda wauta saita wayance da ?aukar buta kamar zata fitsari daga nan ne ta sulale, butar ce Inna taci karo da ita yanzu da suna shigowa. Ganin Abdul-rasheed ?in a ?akin kuma yasata fahimtar ma'anar zaman butar a waje. Tashi yay da ?yar cikin dauriya yana ma Inna sannu da zuwa. Inna dake binsa da kallo ta ce, ÒLafiya kuwa ana salla kana gida Abdul-rasheed?Ó.
Ê Ê ÊÊ ÒBa komai Inna kawai banjin da?i ne, shiyyasa ma ban shigo gidan ba ?azun da yammaÓ.
Ê ÊÊ ÒSubahanallahi, amma shine ja'irar nan ta sulalo ta taho can. Nikam ya zanyi da A'isha jama'a. Mijinki na kwance a gida babu lafiya amma kina guduwa wani waje. A'isha wane haline wannan? Idan baki taimaki mijinki ba wa zaki taimaka. Kina son ki mutu a saki wuta ne? Ko kuwa na shirya naje Kano na gayawa Innarki halin nan da kike yi?Ó.
Ê Ê Ê ÊÊ Cikin sauri A'isha dake kuka ta shiga girgiza kai. ÒDan ALLAH Inna kiyi ha?uri bazan ?ara ba wlhy na tubaÓ.
Ê Ê ÊÊ ÒA'a nasan zaki ?ara A'isha. Wata nawa ana abu guda. Ai gara dai na tafi Kanon nan tunda mu baki ?aukemu iyaye ba. Shima Abdul-rasheed ?in ne ya ?yaleki, sai kace wadda tafi ?arfinka. Kafi son kaita fama da ciwo sai ka halaka kanka ne......Ó
Ê Ê Inna dai nata sababi ta inda take shiga bata nan take fita ba. Taima A'isha dake dur?ushe tana kuka, taima Abdul-rasheed dake zaune kansa a ?asa kunya da ciwo duk sun dabaibayesa. Sai da tai musu tas sannan ta wuce tana sake jaddama Ai'sha idan ta sake ganin ?afarta a waje koda da rana ne ma zuwa can gidan saita zane ta, kuma sai ta tafi Kano ta sanarma Innarta. A'isha tasan aka sanarma Inna ai taga boni, dan haka ta sake rikicewa, dan Innarsu akwai zafi sosai tana da fa?a, duk da tana jansu a jikinta idan sukai ba daidaiba bata raga musu, balle ma ita ?in nan da take kamar ?ar fari. Dan kafin ita Inna ta haifi yara kusan biyar suna rasuwa ne itace ta fara zama, a tsakanin ta da Bashir ma wani ya rasu shiyyasa ta bashi kusan shekara biyar........???


_Zaku sameshi a wa?an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER????- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ?asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya??_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: ??_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number ??_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number??_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*

*_Typing??_*








*_??KI?A A RUWA.....!!??_*




*_Bilyn Abdull ce ????_*


*_?????? ??????? ???????????? ?????????_*
_Da s?nan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._



_Chapter 17_

__________________

_A KANO KI KEÉ? Kina neman inda zaki siyi abinci mai da?i? Kina ?iyar yin girki gashi zaki yi ba?i?, kina neman inda zaki yi order abinci mai da?i wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai da?i akwai a lalla?a. Kina son ki siyi abincin da zaki ?auka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda da?i da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ?angare, tazo muku da nauÕin abinci kala-kala na gargajiya da na ?asar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZO?O mai za?i, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ?ara lafiya, akwai wanda bashi da za?i domin masu ciwon sugar da masu gudun ?iba._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ?asan rubutun nan._

INSTAGRAM
????????????
https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr
CALL/WHATSAPP
????????
wa.me/2349030398006

TIKTOK
????
https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1




Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da ku?i gida.????????

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Bayan ficewar Inna ?akin yay shiru, sai shashshekar kukan A'isha daya cikashi, shi dai Abdul-rasheed yana zaune har yanzu kansa a ?asa yana saurarenta. Sai da yaga ba dainawa zatai ba sannan ya ?ago cike da ?arfin hali dan da gaske baida lafiya ya zuba mata idanunsa dake jajur irin na mai ciwo. Muryarsa da sanyi sosai ya ce, ÒKibar kukan nan ya isa haka, ko kina son kanki yay ciwo ne?Ó.
Ê Ê Kanta ta girgiza masa alamar A'a. Ya ce, ÒTo share hawayen ya isa. Kin daiji abinda Inna tace. Ke ko tsoro ma ba?yaji kiyita kai kawo a tsakanin dare. A'isha auren soyayya mukayi bana ?iyayya ba. Mu da kanmu muka za?i juna muka kuma so mu zama ma'aurata ba ha?amu akai ba balle muce an mana auren dole ne. Kina da muhimmancin da bazan iya bari wani ya cutar dake ba balle ma ni kaina. Abinda kike gani yana faruwa tsakanina dake shi ne aure. Ina ga dole zamu fara karatu daga gobe, ba karatun Alkur'ani kawai kike bu?ata ba a rayuwa da ibada, duk da Alkur'ani yazo mana da komai, amma dole sai mun ha?a da hadisi sannan zamu san su wanene mu da abinda ya kamata muyi. In sha ALLAHU hakan zai sa ki fahimci minene auren ma kansaÓ.
Ê Ê Ê ÊKanta ta jinjina masa, sai kuma cikin rawar murya ta ce, ÒKayi ha?uri bazan sake ba. Kuma dan ALLAH ka bama Inna ha?uri, sannan kace dan girman ALLAH kada taje Kano ta fa?ama Innata, ALLAH idan ta gaya mata zata iya zane ni, kuma tayi fushi da niÓ.
Ê Ê Ê ?aramin murmushi yayi, a ransa yana ayyana ga tsoro ga rashin ji. A fili kam sai yace, ÒShike nan zan bata ha?uri. Nikam baki min laifin komai ba. Tashi ma kije ki wanke idonki. Kinyi sallar isha'i kuwa?Ó.
Ê Ê Ê Ê ÒA'aÓ.
Ê Ê ÒTo maza yo alwala kizo kiyi. Sai ki matsa min lemon tsamin can a ruwan zafi ai da saura a cikin flaks ?in ko?Ó.
Ê Ê ÒEh, tun wanda kasha shayi ?azun ba'a ?ara ?iba ba aiÓ.
Ê Ê Yauwa to yi sallar sai ki ha?a min wani shayin nasha kinji. ALLAH yay miki albarka ya shirya min ke ki daina haura katanga, dan nasan yanzu dai Shatuna ta girma, ta girmi haura katanga ta barma ?an baya ko?Ó.
Ê ÊÊ Kanta ta jinjina masa, sai kuma ta ce, ÒNifa bana haura katanga ALLAH. Kullum ta ?ofa nake fitaÓ.
Ê Ê Ê Dariya yayi yanzu kam. Ya ce, ÒOh oh matar Abdul-rasheed tafi Abdul-rasheed wayoÓ.
Ê ÊÊ Dariya tayi itama tana rufe fuska da tafukan hannunta. A haka ta fita a ?akin, shiko yana binta da kallo da murmushi...

Ê ÊÊ Bayan A'isha tayi salla ta ha?a masa shayin lemon tsami ya sha. Ita kuma ta ha?a mai madara dan tace bazataci tuwo ba. Shi kuma bazai iya fita sayo mata nama ko kifin daya saba kullum ba. Dan bayi ma da ?yar ya iya fita yaje. Hira ya dinga janta da shi yanda suka saba. A hankali ta saki jiki tanata masa dariya, dan labarin ?annenta su Bashir yake ta bata da yaran gidan su Nasiru. Sai da yaga ta fara hamma sannan yace taje ta kwanta.
Ê Ê Ê Maimakon ita shi zaman lalubo litattafan da zai fara mata amfani da su ya shiga yi. Dan dama yana da burin hakan a kanta tuni. Sai da ya ajiye komai sannan yay tashi kwanciyar a ?asa ma yau, dan bai hau gadon ba. Washe gari kamar yanda yay al?awari hakan akai. Da hantsi bayan ta kammala aikin gida ya fita ya dawo sukai zaman karatu. A ?angaren Alkur'ani kam A'isha Alhamdullah, sai gyara na abinda baza'a rasa ba dai. Dan haka ya fara mata da sauran littatafai. Abin nasu kamar wasa sai ya fahimci tana ?okin karatun, cikin kwanaki ka?an kuma ta maida hankali. Har takai yanzu karatun ma yafi cinye lokacinta fiye da biyema yara masu shigo mata da rana. Sun ja kwanaki suna karatun yana bu?e mata komai yanda zata fahimta da ?yau, abinda yake na kunya taita sinne kai sai yayi kamar bai ganta ba ma, a dalilin wannan karatun ya fahimci A'isha ko jini bata fara ba ashe. Eh lallai aiki babba a gabansa, dole kam ta dinga masa gudun fanfala?e ashe. Ganin tana fahimta ya ha?a mata da karatun boko, sosai al'amarin ya fara bashi mamaki, dan gaskiya Alhamdullah tana da brain na fahimtar abu da wuri, gata kuma da nacin son karatun.
Ê Ê Ê Satin su uku da fara wannan karatu al'amarin UBANGIJI A'isha ta samu ba?uncin prioud ?inta a bazata, babu ciwon mara babu komai. Da yake ya karantar da ita hakan sai bata ru?e ba, sai ma matsananciyar kunya data sata ?oye masa, ta shiga kici-kicin gyara kanta ita ka?ai. Sai dai ba'ai nisa ba tun a yinin ya ganota. Haka ya zaunar da ita ya sake mata dalla-dalla akan abinda ya shafi jinin haila, ya kuma sake koya mata yanda zata dinga tsaftace kanta da ?yau. Wato ilimin addini duniya ne, dan kuwa babu mace ?ar gata kuma sarauniya irin mai ilimin addini, mata mu farka dan ALLAH musan kammu, ba'ace karki boko ba, amma ki tuna shifa bokon nan amfaninsa nada iyaka, shiko wannan da muke ?auka ?auyanci da shine za'a mori rayuwa mafi tsada dake can gaba garemu. Ba zaki gane wannan zancen ba sai randa mala'ikan mutuwa ya ?wan?wasa miki ?ofar amsa kiran ALLAH wlhy??.
Ê Ê Ê ÊÊ Kwanaki uku A'ishatul-humairah tayi, a kwana na hu?u tai wanka abinta ta koma salla, sai da ta koma sallar ne ma Abdul-rasheed ya fahimci ba?o dai ya tafi, ya zaunar da ita ya mata tambayoyi akan yanda ta tsaftace kanta. Tana ?oye-?oyen fuska ta sanar masa da komai. Shi dai nashi dariya ne. Fara ?inkinsa da samuwar aikin koyarwa ta rage masa zaman gida, sai dai kuma a ?an tsakanin ya gama shiryama tsuntsuwarsa. Dan kuwa a wani dare na juma'a ya maida Shatunsa cikakkiyar mace. Ya dai sha rigima mai saka ciwon kai da rakinta. Haka yayta lallashi da riritawa, dan sai da ya koma komai shike mata a wannan yinin. Ya kuma sanarma Inna cewar A'isha ta kawo mutuncinta, bawai da baki ko gatsal ba, a'a ya sayi abubuwa ne ya kai ma Innar, kansa a ?asa ya furta, ÒSa?o ne da za'a kai can gidansu A'isha, ai musu godiya da karamciÓ.
Ê Ê ÊÊ Wannan batu nashi kai tsaye ya fahimtar da Inna ina ya dosa, dan wannan al'adace mai girma da a wannan lokacin baka da dalilin ?oyewa kodan mutunta matarka da kimanta iyayenta a idon naka iyayen.
Ê ÊÊ Sosai Inna ta nuna farin ciki tare da sanyawa A'isha albarka matu?a itama. Shi dai Abdul-rasheed kansa a ?asa yana amsawa a la??a. ?anwar mahaifinsu da suke kira Gwaggo Gaji aka aika aka kira, itace taje can wajen A'isha domin bata kulawa. Anan kuma Inna ta shiga ha?a garar arzi?i itama bayan ta sanar da Baba wannan dadda?an labari. Ba A'isha kawai aka shiryama garar arzi?i ba, harda mutanen Kanon dabo. Dan abubuwa sosai aka ha?a aka tada ?an aike tun daga Bauchi har Kano gidansu A'isha shaidar ta kawo mutuncinta gidan aurenta, hakan kuma shine zai ?arama iyayenta nutsuwa da farin ciki. Dan kuwa abin zai baka mamaki, sanda ?an sa?o yaje da wannan albishir gu?e-gu?e aka dinga yi a gidan Inna. Daga ?arshe aka raba kayan arzi?in da aka aiko aka dinga kaisu gidajen ma?wafta da abokan arzi?i. Suko sai gasu suna shigowa taya Inna murna da barka da arzi?i. Dan kuwa ashe anata ?an ?ananun magana tun bayan auren A'isha cewar ba'aji komai daga dangin miji A'isha takai budurci ba, ashe-ashe angon mai kunya ne da kamun kai. Sai ko aka shiga yabonsa dan ya nuna dattako mai girma. Ita kanta Inna ranta fes, dan harda hawayenta tayi sosai a wannan ga?ar. A'isha ta gama biyanta, ita ka?ai ?walli ?aya mace dama gareta.
Ê Ê ÊÊ
Ê Ê ÊÊ ________?
Ê Ê ÊÊ
Ê Ê Anan Bauchi ma dai A'isha taga gata tako ina daga gidan su Abdul-rasheed dama dangin mahaifiyarsa. Dan labari har Maiduguri, haka suma kuwa suka ha?o garar arzi?i aka kawo mata har Bauchi. Bawai ana zancen bane haya-haya, a'a cikin hikima ne irin ta manya kawai. Kamar dai yanda Abdul-rasheed ya nuna alama ga Inna ta hanyar sayen abubuwa masu daraja yakai yace a aika su Kano gidan su Ai'sha ai musu godiya irin ta mutuntawa. Bayan ?an kwanaki ta mi?e, sai dai ?ar kunya tsakaninta da Abdul-rasheed, shi dai nashi lallashi da lalla?a. Gashi yanzu an bata girki, zata fara girki da kanta a gidanta an daina kawo mata daga gidan surukanta kuma.
Ê Ê Ê Ê Wannan shine tushe kuma mafari, na fara gina sabuwar ?ya?y?yawar rayuwa tsakanin A'isha da Abdul-rasheed data ninka ta farkon aure matu?a. Ku?i suka fara shigo masa ta ?angaren albashinsa na aiki da harkar ?inkinsa. Lokacin da suke cika shekara ?aya da rabi da aure ya gyara gidan Baba sannan ya ?ara gyara nashi, ba wani gini ne sabo kona zamani ba, a'a buhunan siminti ya saya aka shafe ko'ina ginin laka ya ?oye. Bai tsaya anan ba suma ?an uwansa ya fara bin nasu gidajen yana gyarawa. Ya kuma dinga ?ara musu jari a harkar sana'o'in su. Bai tsaya anan ba ta kai har haihuwa idan anyi musu shine mai ?awainiyar komai, yaransu kuwa ya ?iba yakai makaranta. Baba kuwa ya hanashi yin komai hatta zuwa gidan

14 / 35