karfe A Wuta book 1 Complete Hausa Novel By Ayshercool .pdf

Author :  Aysha Cool Category :  Romance

Chapter   8 / 19

21K to 24K   out of 54.3K words

za ka yi wa sharri, ki in ƙunar baƙin waken zan kai, zan tsaya saurarku ne, da
yanzu wani zancen ake ba wannan ba".

Ana ta ƙoƙarin sasanta magana, amma Nabila ta ƙi yin shiru.

Ta ciro wayarta, ta kira Nasir sai huci take yi.

Yana ɗagawa ta ce "Yaya, ya ake ciki ne? Akwai wani labari ne?"

Ya ce "No, wallahi arfa kin ganni, na zagaya station uku a yankin, duk ba a kai su ba, amma
wata majiya ta tabattar mini da sakinsu aka yi, just recently"

"Sakin su kuma? Saboda me?"

"Ban sani ba, a kan abun da nake ƙoƙarin yin bincike kenan"

"Ka hanzarta ka taho asibitin cikin gari, akwai waɗanda aka kwantar, police sun hana shiga sun
hana fita, an hana kowa shiga, ko da kuwa kusa da ɗakin. Har da ƴan jarida ma an hana su"

Cikin sauri ya ce "Ok shikenan, gani nan in sha Allah, hankalina bai kai kan in zo asibiti ba ma
na duba ko akwai abun da zai taimaka mini, amma gani nan stay safe"

Ta amsa da "Ok"

Ta ajiye Wayar a jakarta, ta cigaba da kaiwa tana komowa, ƴan sandan suka saka mata ido, dan
kar ta yi wani mummunan yinƙuri, dan ba su san manufarta na dagewa a kan son shiga wurin
ba.

Babu tsammanni aka fito da matasan, wasu ɗauke da raunuka, wanda ba za su iya tafiya ba, an
turo su a kan gado, an nufi hanyar barin emergency da su.

Nabila ta nufe su cikin sauri, amma ƴan sanda suka tare ta.

Ta kalli ɗaya ta ce "Yallaɓai ina za a kai su? Na ga wasu a mugun yanayi, ya za a bar asibiti da

su?"

Babu wanda ya kula Nabila, aka saka matasan a cikin ambulance, har da iyayen wasu daga
cikin matasan jami'an tsaron suka hana su bin su, suka rufe ambulance ɗin, su kuma su ka hau
ta su motar ta ƴan sanda, suka bar harabar asibitin.

Ƴan jaridar da suka yi ƙoƙarin bin su ma, aka dakatar da su, aka hana su ƙarasawa ma in da
motar take har suka tafi.

Tsayawa ta yi kamar wata shashasha, tana mamakin yadda abubuwa suke tafiya, kamar a film.

Motar DSP Nasir ce ta shigo cikin harabar asibitin, yayi parking ya fito, yana ƙoƙarin kiran
Nabila a waya,ya tambayi tana ina.

Da sauri ta ƙarasa in da yake, tana kallonsa, amma ta kasa magana.

Ya ce "Yaya dai? A wane ɓangaren suke, kin samu ganin na su kuwa?"

Nan ta kwashe duk abun da ya faru, ta gaya masa.

Cikin asibitin ya shiga, tana biye da shi, ya tambayi office ɗin incharge na A&E ɗin, ya gabatar
masa da kansa, tare da yi masa tambayoyi, a kan dalilin da ya sa, aka sallami mutane da
raunuka a jikinsu. Amma ya tabbattar masa da cewa, babu wanda yayi musu wani cikakken
bayani, kawai ƴan sanda sun kawo musu yaran jina-jina tun a daren jiya, sun ba su kulawar da
ta dace, daga bisani ƴan sandan suka ce asibiti za su canza musu, aka tafi da su.

Nabila ta yi shiru, sannan ta ce "Akwai wata a ƙasa yaya Nasir, ko waye wannan Aminun, ya na
da wanda su ke sponsiring ɗin sa. Shi an kasa kama shi, amma ya na saka yaran mutane
ta'addanci, you need to put more effort, and i will hundred percent support you, everyone is
equal before the law, dole a nemo shi a hukunta shi"
Ayshercool
08081012143
[7/20, 2:02 PM] null: *ƘARFE A WUTA*



AISHA ADAM (AYSHERCOOL)


https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g.

6


Nasir ya ce "Sannu da ƙoƙari arfanmu, amma ki daina saka kanki a risk kin ji ko? Zan cigaba da
ƙoƙarina in sha Allah sai na yi sanadin kawo ƙarshen ta'addanci da harkar daba a garin nan,
domin kuwa yana ci mini tuwo a ƙwarya nima, but for now mu je na kai ki wurin aikinki"

Nabila ta ce "DSP, dan Allah idan ka gano wani abu na rashin gaskiya, ko waye yake da hannu
a ciki, ka tona masa asiri. Dan ina ga sumy zan yi wa magana, su faɗi abun da ya faru a gidan
rediyo, an saki waɗanda aka kama, kuma wanda aka ji wa rauni ma, an hana kowa zuwa
wurinsu, daga bisani kuma jami'an tsaro sun kwashe su daga asibiti, babu wanda ya san in da
aka kai su, wannan wane irin abu ne?" tayi maganar cikin haƙiƙancewa.

Yayi murmushi ya ce "Kar ki soma, ki na wasa da hukuma arfa, yanzu sai ki kwana a ciki ke,
yanzu dai mu je mota" haka ya tasa ta a gaba zuwa mota, suna tafe tana mita.

"Wallahi yaya na fara sarewa da lamarin ƙasar nan, anya kuwa gyaran ake so ayi da gaske, ta
yaya za ace an gagara kama mutum ɗaya? Ana yekuwar ana nemansa, amma kuma ana kare
laifukan da yake aikatawa, ni na kasa gane kan wannan lamarin.
Ni fa muddin na gano wani abu na rashin gaskiya, sai na yi magana"

"No Arfa, ba huruminki bane ba, ba kuma aikinki ba ne ba, kar ki kuskura ki saka kanki a
hatsari, ƴa mace ce ke lamarin ƙasar nan ya wuce tunaninki, ba abu ne mai sauƙi kamar yadda
ki ke hangensa ba"

Ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ce "Yaya garin nan yana kan gaba a garuruwan da ake ta'amalli
da miyagun ƙwayoyi, duk al'ummar da matasanta suka lalace da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi
ba ta da gobe mai kyau, matasanmu su ne tushen al'umma mai kyau"

Nasir ya ce "Na fuskanci abun da ki ke nufi, but is still not your field"

Tayi shiru ta mayar da hankalinta kan titi, tana ta tufka da warwara a zuciyarta.

Ko da ya kai ta wurin aiki, ta sauka suka yi sallama, ta shiga tana shiga office ɗin ta, sumayya ta
fara kira.

Sumayya ta ɗaga ta ce "Kin gama fushin ne?"

"Ke ware ba wannan ba, matsoraciya da ba ki je ba ni na je, na samo labari, ina ga bayyana
labarin ka iya janyo hankalin manya a cikin lamarin"

Sumayy ta gyara zama ta ce "Labarin me?" Nabila ta gaya mata komai, yadda yaran da aka
kama suka yi ɓatan dabo, da yadda aka fice da na asibiti ba tare da sanin ina aka kai su ba.

Sumayya ta ce "Nabila lallai wannan magana ce babba, bari zan yi magana da MD na ji mai zai
ce, gaskiya yakamata a zurfafa bincike a kan lamarin nan".

Cikin zaƙuwa ta ce "Dan Allah sumayya ki ƙoƙarta, ayi a sanar, a ji mai hukuma za ta ce a kan
haka, ko kin san shi kansa Aminu Viper ana zargin ko dai guduwa yayi daga gidan yari, ko
kuma sakinsa aka yi ba bisa ƙa'ida ba, shiyasa ake tsananta nemansa yanzu"

"Ke ya aka yi ki ka sani?"

"Yaya ne ya gaya mini, akwai lauje cikin naɗi a lamuran mutumin, mutum kamar wani sheɗani".

Sumayya ta yi shiru sannan ta ce "Bari, yadda mu ka yi da su zan gaya miki, amma maganar
nan ta ɗauki hankalina sosai"

"To shikenan, ina saurarenki, yadda ake ciki, ki sanar mini" suka yi sallama.

Haka kurum zuciyar Nabila ta cigaba da azalzalar ta a kan lallai tana son sanin wanene wannan
Aminun, akwai yiwuwar ta samu gagarumar nasara idan aka ce da saka hannunta wurin kama
shi, shahararta ita zai ba ta damar yin gaba da gaba da Naja'atu Bunkure.

Sai kuma ta tambayi kanta, for the first place, laifin me ya yi aka kai shi prison, har ake tunanin
ya fita ba bisa ƙa'ida ba?.

"Akwai ayar tambaya a kan abubuwa da dama" ta yi maganar a fili.
***
Ƙurawa wayar gabansa ido yayi, yadda take ta vibration kamar ta tashi, a wannan karon ma
private number ce, lambar da ko ta halin ƙaƙa yake fatan ganin ko waye mai ita ya bayyana a
gare shi.

Ɗan mama da ke kusa da shi ne, ya ɗaga wayar ya sanyata a hansfree, ya tura masa gaban
sa.

Daga cikin wayar aka ce "Manya gatan wasa, ko ka  tsorata ne ya sanya ka gagara ɗaukar
wayata?"

Yayi shiru bai ce komai ba.

"Idan za ka kwana dubu kana ɓarna, zan kwana dubu ina goge ta, ina ɓatar da sahunka. Ka na
ta cigaba da aikata ɓarna, saboda kana son lallai sai ka san waye ni ko?"

"Wanene kai?" Yayi maganar a ɗan hasale.

Mutumin yayi murmushi ya ce "Mutum, mai zuciya cike da muradai kamar ka. Ƴan kwanakin
nan ka fi mayar da hankali a kan sanin wanene ni, fiye da abun da yake damun zuciyarka. Ka bi
a hankali kar garin kallon ruwa kwaɗo ya yi maka ƙafa, kar ka saki reshe ka kama ganye, ya kai
wannan maciji mai hatsarin gaske"
Al-amin ya numfasa ya ce "Ni ba karen farauta bane ba, da za ka din ga wasa da ni, tamkar ɗan
kwiwiyon da ka raina, ka yi a hankali da ni, ƙarfe nake cikin wuta, na fi ƙarfin ɗauka da hannu"

Ya sake murmusawa ya ce "Ka huta mutumina, ka samu abun da zai ɗebe maka kewa, ta'amalli
da miyagun ƙwayoyi, ba za su taɓa rabaka da damuwa ba, matuƙar ba ka yi abun da zuciyarka
ke gaya maka ba, haryanzu ka na da sauran ƙuruciyarka, zaka iya amfanar da al'ummarka"

Kafin Aminu yayi magana, mutumin ya katse wayar.

"Amma Yallaɓai, kana ganin wannan abun da muke yi shi ne dai-dai? Akwai abubuwa da yawa
da yakamata ace mun mayar da hankali a kai, ba bawa ɗan daba kariya ba"

Ya ajiye jaridar hannunsa ya ce "Kalle ni da kyau, ba na abun da babu manufa a kansa, dan
haka kawai ka saka ido"

Waya ce ta fara ringing, ya ɗaga sannan ya miƙo masa.

Ya karɓi wayar tare da yin sallama.

"Wa'alaikum Salam, barka dai ya ƙoƙari?"

"Alhamdilillah sir, an yi clearing matsalar jiya, duk da an kusa samun akasi, yaron ba ya ji ko
kaɗan, idan aka cigaba da tafiya a haka, kar asirinmu ya tonu fa, dan hakan tamkar yi wa doka
karan tsaye ne, mu na saɓa ƙa'idar aiki"

Yayi murmushi ya ce "Kar ka damu, doka ce ta fara yi wa yaron karan tsaye, shiyasa nake
amfani da dokar, wurin bi da komai"

"Haka ne sir, amma fa police suna neman shi ne ruwa a jallo, mu kuma muna kare shi, muna
taka doka da yawa"

"ASC, ko sun kama Al'amin, ba zasu bari doka ta yi aiki a kansa yadda yakamata ba, za su bar
shi da masu son zuciya ne, su yi abun da suka ga dama da shi, ba wai hukumar ce kawai take
nemansa ba, akwai lauje cikin naɗi ne a neman da ake yi masa"

ASC ya numfasa ya ce "Shikenan, amma laifukansa sun yi yawa, duk wani ta'addanci da za'ayi
a garin nan sai ka ji yaransa ne, slide mistake za'a iya kama shi, duk da wani abun kuma idan
muka bincika, sai mu tarar ba shi ɗin ba ne ba"

"Haka ne, amma idan an kama shi ma, sunana na ko naka, babu wanda zai fito, haryanzu bai
san ko ni waye ba, kuma ba zan bari ya sani ba, kuma yana aikata wasu laifuka ne dan ya
tilasta na ƙyale shi, ko kuma na bayyana kai na a gare shi, amma ka rabu da shi, komai cikin
tsari nake yin sa, ka bar police su cigaba da neman sa, hukumarka kuma ta cigaba da aikinta,
kamar yadda na ce maka"

Ya amsa da "Shikenan sir, am always loyal to you, na gode"

"Yauwwa ASC, duk halin da ake ciki dai, ina buƙatar ka sanar da ni"

"No problem, sai an jima" bayan sun yi sallama, yayi wata irin dariya, da shikaɗai ya san
ma'anarta ya ce "Wannan shi ne jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya" yayi maganar yana kallon
yaronsa da yake tsaye yana kallon sa.

Ya ce "Lallai, amma zan so in ji wani irin shiri ne haka ka ke yi sir"

"Za ka gani a aikace, kai dai ka cigaba da biyayya ga abun da duk na umarce ka, nima zan yi
amfani da ƙarfin iko da kujerata, na yi abun da ya dace".

"Ok sir, in sha Allah".

***
Misalin ƙarfe takwas na dare, wasu daga cikin manya na ƙungiyar ƙato da gora na unguwar
suka tattaru suka zauna meeting a cikin ɗan madaidaicin office ɗin su. Duba da abun da ya faru,
na faɗan daba da aka yi da yaran Aminu da na Madaki a waccan unguwa, sanin ya na shigowa
unguwar lokaci zuwa lokaci, sannan kuma akwai yaransa a unguwar, ya sanya su zaman yin
meeting, dan ƙara ƙarfafa tsaro a cikin unguwar su, kar su gama da can su dawo nan.

Suna tsaka da tattaunawar, wasu zaratan matasa suka yi sallama, suka amsa suna bin su da
kallo.

Suka shiga cikin office ɗin, suka kewaye su, duk suka tsaya suna kallon su.
A hankali ya sauke face mask ɗin fuskarsa, a take suka shaida shi.

Kafin su yi magana ya ce "Awa ɗaya rak nake buƙata, zan gama abun da ya kawo ni na fita,
muddin na kuma shigowa unguwar nan, ku ka sako ni a gaba, kamar kare za ku kama ni,
wallahi sai na yi muku abun da na yi wa malam lawan".

Shugaban ƴan sintirin ya ce "Dan meyasa zaka din ga shigo mana unguwa? Kai da hukuma
take nema ruwa a jallo, ka san kai tauraruwa mai wutsiya ne, duk in da ka je sai ka yi fitina, tun
da yaranka suka yi ɓarna jiya, na san cewa nan ma zaka shigo. Duk ka lalata mana yara ka tafi
ka barmu da masifa, kuma yanzu ka dawo kana cigaba da bibiyarmu"

Cikin tsawa Walid ya ce "Kai, ka iya bakinka, wallahi ko na ɓare maka shi har ƙeyarka".

Cikin tamkakiyar fuskarsa Viper ya ciro zungureriyar wuƙar da take ƙugunsa, ya karta ta a ƙasa
tayi wata irin ƙara, sannan ya ɗora ta a gefen wuyan mutumin ya ce "Ƴaƴanku za su cigaba da
yi mini biyayya, sai na mayar da unguwar nan mafi munin sansanin ta'adancci da zubar jini,
komai ya faru ai ku kuka so, yanzu dan Allah kai ba ka ji kunyar faɗar abun da ka faɗa ba? Duk
in da zan je zuciyata na tsakiyar unguwar nan, kuma zan cigaba da shiga da fita yadda nake so,
har sai na yi maganin azababbiyar ƙishirwar da ta addabi ruhina. Duk abun da na aikata muku
na ɓarna, ku kuka so, mutanen banza masu butulci, kun taki sa'a da nake dakon alƙawari mai
nauyi a kaina, ban da haka tun a fitowa ta, ɗaya bayan ɗaya zan yi muku kisan gilla. Idan na
sake shigowa unguwar nan, kai da wannan mutanen, ku ka yi yinƙurin yi mini wani abu, duk
wanda na kama, zai zama mutum na farko da zan yi wa yankan rago!" Gaba ɗaya suka zuba
masa ido, suka kasa ko motsin kirki, saboda yadda suka zagaye su da miyagun makamai.

"Ku karɓe wayoyinsu, ku rufe mini su, ku saurari order da zan bayar. Duk wanda yayi muku
gardama ku karya mini ƙafarsa, ko ku tsarge masa cinya".

"Angama boss"

Yana fita daga office ɗin, suka mayar suka rufe, suka ƙwace musu wayoyi, sannan suka tsaya a
kansu da wasu irin zabga-zabgan wuƙaƙe, kamar a abba tuwa.

Babu wanda ya iya wani ƙwaƙwƙwaran motsi, dan a yadda matasan suke muzurai, kuma
shaye-shaye ya huda su, duk umarnin da ya ba su za su bi.

Sannu a hankali yake tafiya, har ya kawo cikin layin, ya tsaya a ƙofar wani gida, ya shafe
tsawon lokaci kawai ya zubawa gidan ido, yana zancen zuci, daga bisani ya ƙarasa ya
ƙwanƙwasa na kusa da shi, ya ja mask ɗin sa, ya rufe fuskar shi.

Yaro ne ya fito ya ce "Waye?", ya cewa yaron "Ka je ka cewa babanka an zo duba shi"

Mintuna kaɗan yaron ya dawo, ya ce ya shiga.

Bai yi sallama ba, haka ya kunna kai cikin gidan, har tsakiyar falon maigidan, ba tare da an yi
masa iznin hakan ba.

Daga maigidan har matar gidan, da ƴan matan yaran, tsuma suka hau yi, ganin wanda ya shigo
har cikin gidansu.

Ya zaro wuƙarsa ya ajiye a gaban malam lawan, sannan ya ɗaga wani mukulli ya ce "Na rufe
gidan nan da kwaɗo ta ciki, kuma duk wanda ya yi wani ƙwaƙwƙwaran motsi, zan zaunar da shi
kamar yadda na zaunar da kai" yayi maganar yana kallon malam lawan.

Ya durƙusa kama ƙafar malam lawan, da aka naɗe da bandeji, ya dudduba sannan ya ce "Ɗori
yayi kyau, sai dai na yi mamakin yadda aka dawo da kai gida, maimakon ka yi jinya a asibiti"

ya saita tsinin wuƙarsa a cinyar malam lawan ya ce "Waye ya ɗauko ka daga asibiti?"

Cikin tashin hankali matarsa ta fara kuka ta ce "Dan girman Allah Aminu kar ka yi masa wan....

"Wallahi ki ka sake magana, sai na karya ɗaya ƙafar, ka gaya mini kafin na huda cinyarka" yayi
maganar cikin razananiyar muryarsa.

Cikin matsanancin tashin hankali ya ce "Wallahi wasu mutane ne, ban san su ba, su ne suka
sauya mini asibiti, lokaci zuwa lokaci, suke zuwa da likitansu ya duba ƙafata, kuma sun
gargaɗeni a kan muddin wani ya ji kaine ka yi mini haka, sai sun kashe ni"

"Waye ya kai ka asibiti ranar da abun ya faru?"

Cikin kyarma da rawar murya malam lawan ya ce "Wallahi kana barin wurin, ina wannan
kakarin,

8 / 19