Author : Aysha Cool Category : Romance
Mama ta kalleshi ta ce "Ya dai? Ya na ganka a birkice?"
Dai-dai lokacin Nabila ta fito daga ɓangaren ɗakinsu, hannunta riƙe da kofi, hakan ya sanya ya
kasa ba ta amsa.
Zuciyar sa ta tsananta bugawa da sauri, doguwar rigar material ce a jikinta, kanta babu
É—ankwali, tayi parking É—in gashinta.
Wani irin kyau ta ƙara yi masa.
"DSP yaushe ka dawo?" Tayi maganar tana kallonsa.
"Da magaribar nan, yanzu nake shirin nemanki, in ga ya jikin naki? Wayarki ba ta shiga"
Anty ta ce "Jiki yayi kyau, har fita tayi"
"Fita kuma, ki ka je ina? Kuma da iznin wa?"
"Dan ubanka ina yi maka magana ka shareni, maganarta ta fi tawa muhimmanci ne ko yaya?"
A ɗan rikice ya ce "A'a mama, yi haƙuri kiran gaggawa aka yi mini, faɗan daba ya ƙara ɓarkewa,
Æ´an daba sun rufe unguwar babu shiga babu fita, yaran Aminu Viper ne da wani madaki, wai
Æ´an sandan da aka tura, sun kasa kwantar da rigimar, kin san am incharge of his case, shi ne
zan je na ga abun yi"
"To ka kula da kyau, ni wannan aikin ya isheni, shikenan kai ba hutu, ni hankali a tashe".
Ya jinjina kai ya nufi ƙofar fita.
Jin an ambaci Aminu, ya sanya jikin Nabila ya hau tsuma, ya bishi da gudu ta riƙo rigarsa ta ce
"DSP, amma ba kai kaÉ—ai zaka je ba ko?"
"Eh, na yi waya za a ƙaro mini ƴan sanda"
"Ko mu je tare?"
Ya zaro ido ya ce "Ki yi me?"
Sai kuma ta rasa me za ta ce "Kawai dai ko zan iya taimakawa"
Murmushi ya yi ya ce "Ba fa kotu ba ce madam"
"Zaki sake shi ya tafi ko kuwa? Wane irin iskanci ne haka, Meye haka ne Nasir?"
Nabila ta saki rigarsa ta É—an É—aga murya ta ce "Take care, ka tsaya daga nesa nesa dan Allah,
kar wani abu ya same ka, kar mu yi asarar ɗan ƙasa na gari"
Dariya ya yi, ya fita da sauri.
Mama ta hayyayaƙo mata "Wallahi ki kiyayeni da rashin tarbiyyar ki a kan ɗa na, na gaya miki"
mama ta yi maganar tana nuna Nabila da yatsa.
Nabila a ranta ta ce 'Ni yanzu ba ke ce a gabana ba, akwai abubuwan da suka fiki muhimmanci
a wurina"
Tayi gaba tana kiran lambar sumayya, ta sanar mata da halin da ake ciki, na rikicin faÉ—an daba.
Sai dai kamar kullum, faÉ—a suka yi, sumayya ta gargaÉ—eta a kan ta fita sabgar harkar faÉ—an
daban nan.
Nabila tayi zuciya ta kashe wayarta, tare da jin da ita Æ´ar jarida ce, sai ta shiga unguwar nan, ta
samo rahoto, tana matuƙar jin haushin yadda sumayya take ɗari-ɗari da gudanar da aikinta, sai
dai ko ba dan sumayya ba, ya zama dole ta taimakawa Nasir, kuma ta taimaki tata career, dan
idan ba ta rama abun da Najar bunkure tayi mata ba, ba zata huce ba dan haka za ta cigaba da
bibiya.
Ayshercool
08081012143
[7/23, 1:37 PM] null: Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â
        *ƘARFE A WUTA*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Follow this link, to join autar manya channel, domin samun litattafanta na baya da na yanzu.
https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h
Masu neman book ɗin ƘARFE A WUTA daga farko, su bi wannan link ɗin, su yi following
channel É—in, za su samu previous pagesí ½í±‡í ½í±‡í ½í±‡.
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
9
Har ƙarfe goma na dare, Nabila tana kiran wayar Nasir, domin jin ko yana lafiya, amma shiru
wayarsa ba ta shiga, abu kamar wasa hankalinta ya fara tashi, zuciyarta ta din ga raya mata
wani abun ya same shi.
Da sauri ta tashi ta fita farfajiyar gidan, tana cigaba da kiran wayarsa.
"Ke Arfa, me ki ke yi a wurin nan da daddare haka?" Ta ji muryar Abba babu tsammani.
Cikin damuwa ta ce "Abba Yaya bai dawo ba, kiransa aka yi kwantar da tarzomar faÉ—an daba,
kuma haryanzu bai dawo ba".
Abba ya ce "Yana nan lafiya in sha Allah, da ki ka dawo nan kina sintiri,ai ba bin sa zaki yi ki
nemo shi ba, harkar aiki ne yana nan lafiya in sha Allah"
Abba yana rufe bakinsa, sai ga ƙarar motar Nasir, yana ta horn ba ƙaƙƙaitawa, gaba ɗaya suka
nufi gate a tare.
Suka tsaye har ya shigo yayi parking É—in motar.
Ya fito yana kallon su da mamaki ya ce "Abba lafiya na ganku a nan tsaye?"
Major ya ce "Arfa ce ta fito tana jiran dawowarka, ya ya aka yi wayarka ba ta shiga gaba É—aya?"
"Tana cikin mota ne abba, ina ga network ne amma a kunne take"
Cikin zaƙuwa ta ce "Yaya, komai lafiya dai ko?"
Ya ce "Alhamdilillah, an sha artabu dai, yaran sun ninka yawan da muke tunani, mun kama
wasu, wasu sun gudu, amma mun kama su da yawa".
Mama ce ta fito ita ma, tare da su sauda, suna yi masa sannu da zuwa yana amsawa.
Arfa ta ce "Amma dai ba su yi maka rauni ba ko?" Yayi murmushi ya ce "Da sun yi mini rauni, ai
da baki ganni a haka ba"
Nabila ta ce "To Alhamdilillah, bari na je na kwanta na yi bacci a nutse, tun da kana lafiya"
Ya ce "Ki bar wayarki a kunne, za mu yi magana"
Ta jinjina masa kai ta bar su a wurin ta tafi, mama kuwa kamar ta bi Nabila ta naÉ—a mata duka,
ta kalli yadda Nasir yake wani sassanyan murmushi kamar shashasha, shi ma ji ta yi kamar ta
kwaɗe shi da mari, duk ƙoƙarin da take yi a kansa na nesanta shi da Nabila, abu ya ci tura.
Ta daure ta ce "Shiga ciki ka ci abinci, ka je ka nemi wuri ka kwanta".
"No na tsaya na ci abinci a hanya ma, sai da safe, gajiye nake kwanciya zan yi"
Major ya ce "To Allah ya tashemu lafiya" suka watse.
A galabaice suka koma mafakarsu, domin kuwa sun sha artabu da jami'an tsaro, duk da an
kama wasu, wasu kuma sun tsira da ƙyar. Sai dai sun yi wa su madaki mummunar ɓarna, dan
ma Aminu ya yi musu kashedin babu ruwansu da cewa za su kashe madaki, saboda ya san
hatsabibancinsa.
Yana zaune suka faÉ—o É—akin, suna ta mayar da numfashi, jikin rigar É—an mama face-face da jini.
Walid ya ce "Boss, an yi aika-aika amma kwaɓarmu ta so yin ruwa, dan an kama da yawa daga
cikin yaran nan da muka gayyato, amma fa yaran madaki sun yi ɓarna, dan sun taɓa wanda ba
su ji ba, ba su gani ba, duk da mun yi yinƙurin daƙile hakan".
Maimakon Al'amin ya yi magana, kawai ya tashi tsaye ya shaƙo wuyan walid, ya haɗa shi da
bango, ya ware masa idanunsa ya ce "Ina ƙwayoyin da ka kwashe a nan wurin?"
Cikin takaici walid ya ce "In fita yi maka aiki, in dawo da ƙyar amma ka shaƙe ni?" Yayi maganar
muryarsa na fita da ƙyar saboda shaƙar da ya yi masa.
"Suna ina na ce?"
"Na kwashe su na fita da su, dan ba zan bari ka kashe kanka ba, allurar da ka ke yi wa kanka
ma, ba abun da take yi maka sai ƙara maka zafin zuciya"
Fusata yayi da maganar Walid, ya ƙara shaƙe shi, Ɗan mama ya tashi da sauri yana yi wa
Al'amin magiyar ya rabu da Walid.
Walid ya ce "Idan ka kashe ni ma, ba zaka huce ba, ai na yi maka alƙawarin kawo maka
sabuwar ƙwaya, amma wannan kashe kanka zaka yi, idan ka cigaba da sha, dan ba ta karɓe ka
ba." A fusace ya hankaɗe Walid ƙasa, ya koma ya zauna ya dafe goshinsa.
Wayarsa ce ta yi haske, ya ja wayar yana dubawa.
"Aminu ka daina wannan gangancin da ka ke yi, idan ka sake shiga hannun mutanen nan, kar
ka yi zaton za su hukuntaka da adalci, dai-dai da abun da doka ta tanada, ka nutsu ka daina
wannan mugun wasan, ka mayar da hankalinka a kan burinka" iya ƙarfin sa ya saka wurin yin
jifa da wayar, ta dagargaje a tsakiyar É—akin, ya tashi zai fita.
Duk da mugun ciwon da jikin walid yake yi masa, saboda artabun da suka yi, amma haka ya
tashi ya sha gaban Al'amin ya ce "Ina zaka je ne?"
Hankaɗe Walid yake ƙoƙarin yi, amma walid ya sanya ƙarfin sa, ya tura shi baya.
"Ka rabu da ni walid, ya zan yi ne? So suke sai na haukace, waye wannan? Me yake nema da
rayuwata? Wace manufarsa ce da su a kaina? Me kuma suke buƙata yanzu?"
"Easy master"
Cikin ƙaraji ya ce "Na ce kar ka sake kirana da wannan sunan"
"Sorry boss, na san komai ai, ka kwantar da hankalinka"
"How? Duk abun da suka yi mini bai ishe su ba, wai yaya zan yi ne? Kalli idona walid, ba na
bacci fa, zuciyata kullum zafi take yi, ba na iya saka komai a bakina na ji ɗanɗanonsa, ya zan yi
ne?"
Walid ya ce na sani, ya amsa yana yi wa É—an mama inkiya da idonsa.
Viper ya a sake cewa "Ka san kwana nawa na shafe ba na bacci? Ba kwanaki ban ba fa kawai,
shekaru ne, ba na baccin da ya kai awanni biyar, ka san me nake ji kuwa?"
Walid ya ce "Ban sani ba, amma na san da yawa daga abubuwan da ka lissafa"
Jikinsa na tsuma ya ce "Wallahi zuciyata ci take yi da wuta, ka sani, wallahi idan na riƙe makami
sai na yi kisan kai" yayi maganar yana rintse idanunsa, a lokacin da ruwan allurar da walid yake
yi masa, ya fara ratsa jijiyoyin jikinsa.
A nan take jikinsa ya saki, ya zubawa walid ido.
Walid ya ce "Ko ba zaka yi baccin ba, ka rufe idanunka master, za ka samu releif" shiru yayi,
domin ba zai iya motsa kowacce gaɓa daga jikinsa ba.
ÆŠan mama ya ce "Walid, anya ba zamu yi wani abu a kan lamarin nan ba kuwa? Ba za a kai shi
ya ga likita ba? Kar ya haukace tuburan fa"
Walid ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa alamar ɗan mama ya yi shiru.
A hankali al'amin yake buɗe idonsa yana lumshewa, sai dai ya kasa ƙwaƙwƙwaran motsi.
***
YALOKO ƘARAMAR HUKUMAR TOFA.
Cikin tsananin ƙyanƙyami take ƙarewa ɗan ƙaramin ginin ƙasar kallo, rabin katangar gidan ta
zube, sai ciko aka yi da kara da buhu, aka rurrufeta.
Abunka da mutumin ƙauye, cikin mutunci da girmamawa, matar gidan ta karɓeta, tana yi mata
sannu da zuwa.
Ta yi mata iso, har cikin É—akinta, ta ba ta abun zama.
Kamar ta zauna a kan kashi, haka ta É—an É—osana ta zauna, tana kame jikinta ta kalli matar ta ce
"Baki gane ni ba ko?"
Matar ta ce "Eh ban waye ki ba"
"Ni ce barrister da na karɓi case ɗin ƴar ki, na zo mu tattauna ne, in yi magana da ita"
Nan da nan hawaye ya cika idon matar ta ce "Tana banÉ—aki, bari ta fito"
rufe bakinta ke da wuya, yarinyar tayi sallama a ɗakinta, muryarta ƙasa-ƙasa.
Mahaifiyarta ta amsa, barrister kuwa zuba mata ido ta yi, yadda yarinyar take É—ingishi, take
tafiya da ƙyar, har ta zo ta zauna.
Ta kalli uwar ta ce "Kun kaita Asibiti ne?"
Ta ce "A'a, tun dai a can an kaita, maigadin gidan ne ya kaita, har aka yi mata ɗinki a goshinta,
gashi nan in da aka ya ji mata rauni. Dan Allah baiwar Allah ki taimake mu, kamar yadda Allah
ya taimake ki, a karɓar wa yarinyar nan hakkinta. Saura ƴan kwanaki aurenta, ya lalata mata
rayuwa, idan zancen nan ya fasu a garin nan yaya zan yi?"
Ta kalli yarinyar sannan ta kalli uwar ta ce "Baiwar Allah kuma hadda halinku, na son abun
duniya duk yadda hukumomi ke jan kunne a kan kai yara aikatau meyasa ba kwa ji? Meyasa
zaki kaita aikatau, maimakon makaranta?, a ƙa'ida fa kema sai an hukunta ki"
Cikin rauni da damuwa ta ce "Baiwar Allah da ina da yadda zan yi yaushe zan kaita aikatau? An
yi garkuwa da mahaifinta an ce mu kai kuÉ—in fansa, mun tattara dabbobi da gonaki mun sayar,
mun bayar a kai a sako shi, sun rike ƙanin mahaifinta da ya kai kuɗin, sun haɗa su su duka sun
kashe, gona ɗaya ta rage mana, ita ma wani mutum duk ya tarkata ya ƙwace, wai zai gina
kamfani, an ce za a bamu diyya, gonar miliyan uku an bani dubu bakwai, abun da zan girka na
basu su ci, ita da Æ´an uwanta, bani da shi, nima ba cikakkiyar lafiya ce da ni ba, kuma ita ce
babba, makaranta tana zuwa ajinta uku a sakandare, kuÉ—in da ake biya na makarantar ba ni da
su, ya zan yi?" Tayi maganar kuka yana ƙwace mata.
"Shikenan ya isa haka?, Amma kuma irin haka kin yi gaggawa zuwa gidan radiyo ki faÉ—a, ai
wurin jami'an tsaro yakamata ki je".
Maman ramma ta ce "Na je, dan da aka kira ni na je can birnin asibiti, da ƙyar aka karɓe ta wai
ba ɗan sanda, daga can na je wurin ƴan sanda naga suna nema su cuce ni, wai ƙarya muke yi,
babu yadda za ayi a É—auki Æ´a ta aiki a wannan gidan har ayi mata fyaÉ—e. Ba ki ga sintirin da na
yi ba, na rasa abun yi shiyasa na kai wurin masu radiyo ko Allah zai saka a taimake mu"
Ta jinjina kai ta kalli yarinyar ta ce "Ramma ko?" Ta jinjina kai alamar eh.
"Gaya mini yaya aka yi abun ya faru?" Ta É—aga kai ta kalli mahaifiyarta, sai ta fashe da kuka ta
kasa magana.
"Hajiya É—an bamu wuri mu yi magana" babu musu, ta tashi ta fita ta bar É—akin.
"Kin ga ki yi shiru ki kwantar da hankalinki, ki yi mini bayanin yadda abun ya faru, in ga ta ina
zamu ɓullowa lamarin"
Shiru ta yi tana tuna yadda lamarin ya kasance.
"Ke!" Ya kirata cikin tsawa, bayan sun haɗa ido da ya shigo, ƙara razana ta yi, dan ba ta yi
zaton wani zai shigo yanzu ba, a dai-dai wannan lokacin, da ta duƙufa tana ta aiki a falon gidan.
cikin tsuma ta kalleshi ta ce "Na'am".
"Ina masu gidan?" Yayi maganar yana ƙare mata kallo, matashiyar yarinya ce, da ba ta wuce
shekara goma sha huɗu ba, irin farkon tashen balagar nan, ƙirjinta ya fara tasawa, wannan ne
karo na biyu da yake ganinta a gidan. Tun a ranar farko yake jin wani abu na fuzgar shi a kanta.
Cikin rawar murya ta ce "Ai ba su dawo ba tukuna, gyaran gidan dai muke yi".
"Ke kaÉ—aice a gidan kenan?"
Cikin rashin wayo ta ce "Eh, amma zulai ta je sayo katin waya, zata dawo, tare muke aiki da ita,
wai a satin nan za su dawo".
Yayi wata irin ajiyar zuciya ya ce "ÆŠaukko mini ruwa a kitchen zan sha" ta jinjina kai, ta ajiye
duster hannunta, ta tafi da sauri har da gudu.
Sai dai tana shiga kitchen ɗin, ya bi bayanta, ya mayar da ƙofa ya rufe.
Turus ta tsaya tana kallonsa, jikinta yana rawa, taga ya fara tunkaro ta.
Ta ja da baya ta miƙa masa ruwan, amma ya haɗa da hannunta ya riƙe.
"Dan Allah ka sakeni, in ƙarasa aikina"
Babu tausayi ko imani, ya ce "Nawa aikin zaki fara yi tukuna, kafin nata"
Ganin akwai alamun ƙarfi a tare da ita, ba zata tsaya ba, ya sanya ya gaura mata wani
lafiyayyen mari. A take hancinta ya fara zubar da jini.
Ta ƙwala ihu, ya sake buga kanta da cabinet na kitchen, goshinta ya fashe, nan ma jini ya hau
zuba, ga goshi ga hanci, dan haka ta kasa magana, jikinta ya saki.
Haka ya keta mata haddi, ta hanya mai muni da rashin tausayi ya tashi ya fice ya barta.
Idonta biyu, amma ta kasa taɓuka komai, ko ɗaga hannunta ta kasa yi.
Zulai ce ta dawo ta tarar da ita cikin mummunan yanayi, a rikice ta fita ta kira É—aya daga cikin
masu gadin gidan, suka É—auke ta suka kaita Asibiti.
Aka ƙi karɓar su, sai da aka kira matar gidan aka sanar mata, suka yi magana da likitoci ta
waya.
Sai dai duk abun nan, ramma ba ta san ko sunansa ba, balle ta san É—an waye shi.
Kafin matar gidan ta dawo, ta aiko a bawa ramma kuɗi, a bata haƙuri su koma ƙauye, ko
warkewa ba ta yi ba aka sallame su, shi ne mamanta ta É—auke ta suka tafi gidan radiyo.
Ramma ta bawa barrister labarin komai, tana kuka mai taɓa zuciya, goshinta ga ɗinkin da aka yi
mata a asibiti, ga na ƙasanta da yake addabarta da raɗaɗi.
Tayi ajiyar zuciya ta ce wa mahaifiyar ramma ta shigo.
Bayan ta shigo ta zauna, ta kalle su ta ce "Baiwar Allah, dan cuta na san an cutar da ku, amma
za ki sake jefa kanki a halaka, gara ku yarda ayi masalaha.
Babu wata kotu, ko wani alƙali, da zai tsaya miki ya ƙwato muku hakkinku, saboda yaron nan
ɗan gata ne gaba da baya, ubansa suke da ƙasar.
Dan haka ki yi haƙuri, a baku wani abun, ki samu ku sai abinci, a kuma kaita asibiti, idan ta
warware ta koma makaranta.