karfe A Wuta book 1 Complete Hausa Novel By Ayshercool .pdf

Author :  Aysha Cool Category :  Romance

Chapter   11 / 19

30K to 33K   out of 54.3K words

tayi.
Tayi shiru ba ta faɗi abun da ya faru ba, suka din ga yi mata sannu.

***
YALOKO ƘARAMAR HUKUMAR UNGOGGO

Matashiyar yarinya ce, wadda dudu shekarunta ba su fi goma sha huɗu ba, take ta iza wuta a
cikin murhu, gefe ga garin tuwo a cikin ƙwarya.

Yaro ne ya yi sallama, ta ɗaga kai ta amsa masa.

Ya kalleta ya ce "Ramma ki zo ana sallama"

Ta ɗan waro manyan idanunta ta ce "In ji wa? Ko Habu ne?"

"A'a, wani ne da mota"

Ta miƙe tsaye ta ce "To mota kuma, ina zuwa?"

Daga tsakar gidan ta ɗan ɗaga murya ta ce "Mama, wai ana nemana a waje, bari na duba
waye, ruwan ya kusa tafasa"

Daga cikin ɗaki matar ta amsa mata da "To ramma, hanzarta ki dawo, ina son zan fita ne"

Ramma ta amsa da "to" ta ɗauki hijjabinta ta saka ta fice waje.

Mintuna goma sha biyu ta dawo, jiki a sanyaye.

Mamanta ta kalleta ta ce "Menene?"

"Mama daga Kano ne, wai Anty mai jidda ce gidan da nake aiki, ta yi waya wai azo a ɗauke ni a
mayar da ni, a satin nan za su dawo"

Matar tayi sak ta ce "Da wuri haka, ba cewa aka yi sai bayan wata guda zaki koma ba?"

Ramma ta ja ta tsaya ta ce "Jikina duk yayi sanyi, wai yanzu-yanzu zamu tafi"

"To shikenan ai babu wani abu, ki yi haƙuri kin ji ramma, ni kaina ba a son raina ki ke barin
gabana ba, da Allah ya sa mun tara kuɗin kayan gado, shikenan sai ki dawo ki yi auren ki. Maza
mu je na tayaki haɗa kayan"

Cikin abun da bai fi mintuna arba'in ba, suka haɗa kayan, suka yi sallama ramma ta bi direba
zuwa gidan aikinta da yake Kano.

Yana zaune ya zuba musu ido, suna haɗa masa tea, Walid ya zuba ƙwayoyi a cikin kofin,
sannan ya zuba shayin.

"Ƙara wannan ba zasu ɗauke ni ba"

Walid ya ce "Amma boss, kai fa ka ke hanamu sha a baya, tayi yawa wallahi".

"Ka ƙara mini na ce" yayi maganar a hasale.

Ya ƙara masa ƙwayoyin yana kallonsa, saboda ƙwayar da suke yi wa laƙabi da raina kama, a
baya sam baya shan irinta, saboda yadda take bugarwa, wasu lokutan rabi suke ɓallawa su
sha, amma ya ce a saka masa kusan biyar yanzu.

Ya ɗauki kofin ya kai bakinsa zai fara sha, Walid ya ce "Yau fa madaki za su je ɗaukar fansa
cikin unguwa, daga majiya mai ƙarfi na ji zancen, daga jiya zuwa yau ya ce idan ɗan arearmu
ya shiga ta su, a aika shi kawai"

Ya cigaba da girgiza kofin ba tare da ya yi magana ba, ya sake yinƙunrin kai kofin bakinsa, walid
ya sake cewa "Wata ta je nemanka a arear, aka kaita dabar madaki, Allah ne ya yi da kwananta
a gaba, da kasheta za su yi"

Duk da cikinsa yayi wata ƙara, jin an ce mace ta na nemansa. Wace mai tsautsayin ce wannan?
Me take nema a wurina?, amma ya maze ya ɗago jajayen idanunsa ya kalli walid ya ce "Ni

kuma?"

Walid ya ce "Ba zan yi maka ƙarya ba, da gaske nake"

Wani dogon tsaki ya ja, ya dungurar da kofin shayin, ya tashi ya ce "Ku ɗebo yaran nan na cikin
unguwa, da na can wajen gari, ku sake dira a dabar madaki, ina son ɓarnar da za ku yi ta fi
waccan, kar ku basu damar cutar da kowa. Ko kun gaya wa jami'an tsaro ƙudurinsu, babu abun
da za su yi musu, ku far musu kawai, ka shirya komai, a bawa yaran na shan sigari" bai jira
amsar walid ba ya fice.

Walid ya yi ajiyar zuciya, ɗan mama ya kalle shi ya ce "Da gaske ka ke wata ta je nemansa, ko
kuma ka faɗa ne, dan ka hana shi shan ƙwayar nan?"

Walid ya ce "Duka, kai da ya sha abun nan, zai iya mutuwa fa"

Ɗan mama ya ce "Ai rigimar da yake yi kwanan nan, ta ƙara yawa, sai an ƙara saka masa ido
sosai, kashe kansa yake son yi wallahi, wasu lokutan bana son muke watsewa  mu bar shi
shikaɗai a gidan nan".

Walid ya girgiza kai ya ce "Ba zai kashe kansa ba".

"Ya aka yi ka san hakan?"

"Yana da abun da yake son cimma, kawai kayan ne gaba ɗaya ba sa ɗaukarsa gaba ɗaya
yanzu, ka san yana cikin matsananciyar damuwa, duk kayan cajin nan kansa ba ya ɗauka
kamar aljani, amma ina bincikawa, an yi mini alƙawarin wata zazzafar ƙwaya, daga kudu suke
kawota. Yanzu dai wannan aikin da ya ce , maza-maza ka kira kwangila a waya, ya haɗa mana yara, a
basu kayan caji, zamu fasa ƙofa, ai Madaki shi da ɗaukar wata fansa a kanmu, sai dai a lahira
idan ana yi. Sai mun ga abun da ya turewa buzu naɗi.
Ɗan mama ya miƙe ya ce "Ok, bari na hanzarta na fara haɗo su ta arear wajen garin nan".

Walid ya ce "Nima fitar zan yi, wurin liti zani, zan shiga karɓar balance". Suka fice gaba ɗaya.

Bayan tafiyar su Aminu ya koma cikin ɗakin, ya fara duba in da walid yake ajiye ƙwayoyi, amma
ya dudduba bai gansu ba, ya zazzage ko ina, amma babu.

Wani irin takaici ya tokare masa ƙirji, ya ja dogon tsaki, ya ɗaga gefen katifarsa, allurar sa saura
kwalba biyu kawai, kuma ya san ba ɗaukarsa za ta yi ba.

Haka ya zuƙe ta ya yi wa kansa, sai dai kamar kullum, yau ma ƙirjinsa ne ya fara da zafi, kansa
yana juya masa.

Wuƙar da take gefensa yake ta kallo, zuciyarsa na raya masa abubuwa daban-daban.

Tun da Ramma ta suka isa cikin kano, gidan da take aikatau, kayanta kawai ta sauke a ɗakinta,
ta hau aikace-aikace.

Duk da akwai wata mai aikin, wadda ta girmewa ramma, sosai da sosai, amma matar gidan ita
ta yarjewa ta shiga sashenta, har uwar ɗaka da na maigidan ta gyara mata, a cewarta ramma ta
fi nutsuwa, kuma ba ta taɓa ƴar aikin da ba ta yi mata sata ba, sai ita.

Matar gidan da ƴaƴanta gaba ɗaya sun tafi dubai hutu, shiyasa ta sallame ta, ta ce ta je gida ta
huta, za su yi wata biyu kafin su dawo, kuma kwatsam yanzu sati biyu wai dawowa za su yi.

Tana falon matar gidan, tana ta uban aiki, ɗan kwanakin da aka yi ba a taɓa wurin ba, duk ya yi
ƙura.

Ƙofar falon aka shigo, ta tashi da sauri, tana kallon mai shigowar, dan ba ta yi tsammanin ganin
kowa a sashen ba, dai-dai wannan lokacin.

***

Nabila kuwa kusan kwanaki uku curr, ta kasa nutsuwa da kwanciyar hankali, da ta kwanta
bacci, sai mafarkin karnuka, tayi ta ihu.
Haka Anty da baba magajiya za su danneta, su yi ta shafa mata man gelo da miski, ta ja
bakinta, ta yi shiru, ba ta gaya musu abun da ta aikata ba.

Yau kuwa gajiya ta yi da zaman gidan, dan baka cikin hijjabi ta shirya, ta ɗauki ƴar ƙaramar
wayarta, ta fito falo.

Umma ta kalleta ta ce "Ke da baki da lafiya, ina zaki je kuma?"

Nabila ta ce "Wurin aiki, akwai buƙatar in je zan kai wani bayani ne mai muhimmanci"

"Amma kin gaya masa, kar ya dawo ya tarar kin fita, ya yi ta faɗa"

"Umma ba daɗewa zan yi ba"

Saudat ta ce "Mhmm, a ma faɗi gaskiya, ko yawon banza za aje".

Nabila har za ta yi shiru, ta ga idan tayi shiru, za ta cutu, dan haka ta ce "Idan fitsari banza ne,
kaza ma tayi, idan yawon ma zan tafi, mai lasisi ne akwai riba, ke ki yi mana"

Umma ta kalli Sauda ta ce "Sauda dan Allah ki din ga jan girmanki, Nabila fa ba sa'arki ba ce
ba".

"Na saka da ke ne?"

Umma ta girgiza kai ta ce "A'a baki saka da ni ba, Allah ya taimaka".

Sumayya tana ta aiki a news room, Nabila ta yi sallama ta shiga.

Sumayya ta kalleta ta ce "Ina aikin?"

"Ban je ba, ya aikin?"

"Lafiya ƙalau, meyasa ba ki je ba?"

Nabila ta ce "Ke ba wannan ba, yanzu na ga managern ku a waje muka gaisa"

Sumayya ta ce "Good, ya aka yi?"

"Rahotonki na last week, a kan case ɗin yarinyar nan da aka yi wa fyaɗe, na ji shiru baku sake
cewa komai ba"

Sumayya ta ce "Eh ya aka yi?"

Nabila ta ce "ina da intrest a kai ne, ina son shiga lamarin, na ji shiru haryanzu babu wani
update, na an ɗauki mataki"

Sumayya ta ce "Dalla ware, kamar wata lawyer kirki, you are not even serious about the job"

Nabila ta ce "Ke ban son wulaƙanci fa, am serious, na ji an ce wanda yayi laifin mai lasisi ne a
garin nan, ina son sanin waye shi?"

Sumayya ta ce "Nima ban sani ba"

"Kamar yaya ba ki sani ba, am serious fa, da gaske nake sumayya ina son shiga case ɗin, free
of charge na taimaka wa yarinyar, na ji tausayin su sosai da sosai, yadda uwar take kuka. Kuma
daga ji ƴan karkara ne, masu ƙaramin ƙarfi".

Sumayya ta galla mata harara ta ce "Sannu ambulance uwar taimako, manyan lawyoyi sun riga
sun shiga case ɗin tuni, sai ki ja gefe"

"Suwaye manyan lawyoyin? Kuma wai waye dan Allah, waye yayi fyaɗen?"

"Ke! Nifa a rubuce aka bani, karantawa kawai na yi, hatta recording ɗin da aka saka, na muryar
uwar da ƴar, tararwa na yi an yi, ban ma gansu ba, ban ga suwaye ba, balle na samu wani

bayani. Case ma fa lamarin ya kusa zama a gidan nan, saboda saka muryar matar da aka yi,
murtala ne dama ya yi recording ɗin ya saka, sai da aka kusa korarsu"

Nabila ta ce "To fa, ina murtalan yake?"

Sumayya ta ce "Ba zan nuna ba, kin ganki Nabila"

"Ba wani abu zan yi ba, sonake kawai ya haɗani da matar da yarinyar".

"Babu fa abun da zaki iya yi a kai, shi ma bai san waye wanda yayi fyaɗen ba, yarinyar aiki take
a gidan, baƙo ne daga zuwa yayi mata. Dan Allah ki haƙura da case ɗin nan"

A ɗan fusace ta ce "Saboda me?"

Sumayya ta yi murmushi ta ce "Na ji an ce mutuniyar ki da jama'arta sun shiga cikin case ɗin,
shiyasa na ce ki haƙura"

Nabila ta ce "Wa kenan?"

"Naja bunkure mana, antynki mudubinki, a bar ƙaunarki" Sumayya ta yi maganar tana dariya.

A take annurin fuskar Nabila ya ɗauke, haka kurum jikinta ya bata babu gaskiya a lamarin nan.

"Uban mudubin nawa, in dai wannan mudubin ne, Allah ya fasa shi na huta, wallahi sumayya
tun daga abun da matar nan ta yi mini, kawai nake ji a jikina fuska biyu ce da ita, wadda take
kallon jama'a da ita, da kuma wadda take ɓoyewa"

"To ko ma dai yaya ne, sun shiga case ɗin, kin san kuma ba zasu tsaya su saurareki ba,
mussaman da ta iya yi miki kallon ke ba komai ba ce ba"

Nabila ta ce "Haka ne, amma rai dai an cire wa fara kai, lokaci ne, yana nan zuwa da zan bawa
duniya mamaki, sai na saka ƙafa na bi ta kanta ko da halin ƙaƙa"

"To ki bi a hankali, kar ke duniyar ta baki mamaki"

Nabila ta yi shiru tana tunani.

Sumayya ta ce "Ya dai?"

Tayi guntun tsaki ta ce "Sumy zaman gidanmu babu daɗi, kamar in gudu wallahi".

"Wai Nabila ba zaki daina wannan iƙirarin ba?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba zaki gane ba, faɗa muka yi da Siyama, har da Abba ayi mini faɗa,
sauƙinta ɗaya ta ci duka da tukunya na din ga dukanta"

"Haba Nabila, wannan ai yawa ne, degree holder da dambe?"

"To yaya ki ke so in yi? In zuba mata ido ta yi mini duka? Ga uwarsu ta addabi rayuwata, ba ta
san yadda ta tsane ni, nima haka na tsaneta ba, kawaici kawai nake yi mata ba.
Duk uban ƴan matan gidan nan har da zaurawa, babu wanda duka sanyawa ido sai ni, da na
motsa ayi ta janyo mini jafa'in karuwanci" ta ƙarasa maganar hawaye na cika mata ido.

Sumayya ta ce "No dear, dan Allah ki ƙara jurewa, lokaci ne da kin yi aure zai wuce"

"Yaushe zan yi auren? Dan Allah ni mummuna ce Sumy? Duk saurayin da ya zo, sai za a fara
maganar aure, sai ya gudu kamar wata jaɓa"

"Nabila kina da matsala, Babu wata halittar Ubangiji mummuna. Ga ki fara, ga gayu da ilimin
addini da na zamani, kina da kwarjinin da ki ke bawa maza tsoro ne, ai ke kalar manya ce
tawan, ba duk kai ba"

Cikin takaici Nabila ta ce "Ba wasu manya, manyan da suka din ga yaudarata Allah ya isa da ba
su aure ni ba suka ɓata mini lokaci, ni yanzu kowaye ma zan aura na bar musu gidan, ko ba na
son shi. Idan ba haka ba wallahi wataran sai na gudu"

Sumayya ga tausayin Nabila ga dariya, tabbas Nabila akwai farijinin samari, masu kashe mata
kuɗi ma kuwa, sai dai Nabila ta fiye zaɓe-zaɓe, kuma ba ta fiye ba wa masu sonta da gaskiya
muhimmanci ba.

"Ki gudu ki je gidan uban wa? Gaki ga Abba nan maza ki gudu kar ki fasa"

Sai kuma ta koma rarrashinta, har bayan azahar suna tare, sai da sumayya ta tashi suka fito
tare.

A reception suka tarar da wani mutum, ana ta yi masa fadanci, yana hura hanci cikin manyan
kaya na alfarma, reception ɗin ko ina security.

Sumayya ta risuna ta gaishe shi ya amsa, amma Nabila ko kallonsa ba ta yi ba, ta sunkuyar da
kai, kamar alla-alla take yi, ta yi ta bar reception ɗin.

Ɗan rikicewa yayi, ya ƙura mata ido, amma ta basar ba ta gaishe shi ba, sai so yake yi ta ɗago
su haɗa ido, dan ya tabattar da abun da yake tunani, amma taƙi ta mayar da kanta gefe.

Mamaki ya shiga yi, yana tunanin ko dai gizo idonsa yake yi masa? Sai dai ya rasa abun yi kafin
ya yi wani yinƙuri, sun bar reception ɗin.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan ya kalla ya ce "Wannan mai hijjabin ma'aikaciyar ku ce ita ma?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a sir, she's just a guest here"

Ya ce "She looks familiar to me, anyway shikenan dai" yayi gaba.

Cike da takaici Sumayya ta ce "Kina kallon babban mutum ki ka basar ba ki gaishe shi ba, sai
kallonki yake yi, ki ka sani ko shi ne mijin a dace a daidaita ko ƙyasawa yayi? Da irin wannan
halin naki, ki ke korar samarinki na kirki wallahi".

"Kin fi kowa sanin bani da baƙin hali, wasu lokutan ma cewa ki ke yi na fiye zaƙewa"

"Haka ne, amma baki kyauta ba, ko dan kallon da yake yi miki, ai kya kula shi".

Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ban taɓa jin na tsani wata halitta a kallon farko da na yi mata a
rayuwata ba, sai wannan mutumin. Gaba ɗaya ya canza mini mood lokaci guda"

Sumayya ta waro ido ta ce "Meyasa kun taɓa haɗuwa ne? Me yayi miki?"

"No, ina ganin shi a poster dai, ba ɗan majalisa bane? Ban taɓa jin komai idan na ganshi a
poster ba, sai yau da na ganshi ido da ido, bana fatan Allah ya sa na sake sanya shi a idona.
Kin san me? ji nake kamar ya taɓa cutar da ni, cuta mai muni"

"Arfa, kina hayyacinki kuwa? Tayaya mutumin da ki ka fara gani yau kawai, ki ce kin tsane shi,
ya cutar da ke how?"

"Ban san tayaya ba, amma haka nake ji a raina, kuma da gaske nake jin hakan"

"Ki daina irin wannan wasan, kar ki saka a din ga yi miki mummunar fassara"

"Forget, ba zaki gane ba" tayi maganar a daidai lokacin da suka ƙaraso titi.

Tun ba ayi sallar magariba ba, walid ya riga ya gama tatara gayyar matasa zauna gari banza,
wanda suka yi bankwana da fatan samun ingantacciyar rayuwa, suka kama makamai da
ta'amalli da miyagun ƙwayoyi.

Kasancewar ba a cikakken hankalinsu suke ba, haka suka raraka kowa da kowa gida.

Yaran madaki, na ta shirin shiga ɗaya unguwar sare-saren ɗaukar fansa. Labari ya iske su
cewar, yaran Aminu sun rigasu yin dirar mikiya.

Ba su yi zaton gayya guda, yaran aminun suka ɗaukko ba, dan haka suka fita domin su far

musu.

Kamar ba jikin ɗan Adam ba, haka suka din ga sara da sukar junansu, mutanen unguwa duk
suka shiga gida suka rufe.

Aka yi rashin sa'a madaki baya nan, ɗaya daga cikin yaransa, ya kira shi ya sanar da shi halin
da ake ciki.

Nasir yana zaune ya idar da sallar magariba yana lazumi, so yake ya tambayi ina arfa, ya ga ya
jikinta, amma mama na babban falo, ya san da ya yi hakan, za ta yi masa faɗa, tare da sake
gargaɗinsa a kan Nabila.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya shafa addu'ar, ya ɗaga tare da yin sallama.

Da sauri ya tashi tsaye, yana faɗin gashi nan zuwa.

Da sauri ya ɗauki mukullin motarsa, ya fito daga sashin mama, zuwa falo.

11 / 19