Author : Aysha Cool Category : Romance
ta ce "Da na yi me?".
"Kin saka Abba ya yi wa mama da Anty sauda kaca-kaca saboda ke, sai da Anty sauda ta yi
kuka".
"To ai cewa zaki yi, Abba bai kyauta ba ni meye nawa a ciki?"
"Amma ke ki ka gaya masa ta ce miki Agola, bayan yayi musu mu ma ya iskemu a babban falo,
ya yi ta yi mana faɗa".
Nabila ta ce "Ashsha, ai kin san ni bana kai ƙara, ko dai na ɗauki mataki, ko kuma Allah ya saka
mini da gaggawa"
Asiya ta ce "Ai shikenan, kowa yayi na gari kansa".
Nabila ta ce "Allah ya yaye miki Aisya, ke ma fa matar nan idan ta tashi karta miki wulaƙanci, ba
saurara miki take yi ba, daga ke har umman, amma ku yi ta bin ta kamar wata shugaba, ni dai
ba mai takani ban ɗaga ƙafar na karya ba"
"A'a ai ke ki ka ce, ke ki na da ma dogara"
Nabila ta yi tsaki, tare da furta "Allah ka aurar da ni na huta da wannan kacaniyar gidan, Ya
Allah dogo mai gemu" ta fita daga ɗakin tana addu'a.
Bayan kwanaki takwas.
A tsaye yake ƙyam, kamar ƙofa, kasancewar in da yake a tsayen ba a iya ganinsa sosai saboda
duhu, sai dai inuwarsa ta nuna dogon mutum, kakkaura.
Ya ɗauki ɗankwali, ya ɗaure kansa da shi, tare da naɗo ɗankwalin ya rufe fuskarsa sai idanunsa
kawai ya bari a waje.
Ya laluba hannunsa, ya ɗaukko wata irin doguwar wuƙa, ɓangare ɗaya zarto, ɗaya kuma kaifi,
ga ta da uban tsini, a ƙalla za ta yi kamu uku, ya ɗaga rigarsa ya soketa.
Ya sake ɗaukar wata ya soke a jikin wandonsa.
Yanayin takun da yake kawai, ya isa ya tabbatar daƙaƙarfa ne, saboda yadda ƙasa ke amsa
takun nasa.
Bayan wasu awanni, duhun dare ya ƙara yi, sahu ya ɗauke, sai haushin karnuka ko ina.
A ƙofar wani gida ya tsaya, ya din ga waige-waige, ya tabattar da babu kowa. Tamkar ɗan biri,
haka ya cafke katangar gidan ya dira ciki.
Ya saka mukulli, ya buɗe wata ƙofa a cikin gidan da duk ta yi ƙura, ya buɗe ta ya kutsa kai ya
shiga ciki.
Tsayawa yayi ya kunna fitilar wayarsa, yana haske ɗakin, take ya ji wani abu mai tsananin ɗaci
ya fara kaiwa da komowa a ƙirjinsa, ya ji numfashin sa na barazanar barin ƙirjinsa.
Jikinsa ne ya fara rawa, ya ji tamkar hankalinsa zai gushe, ya durƙusa a wurin yana wani irin
haki, cike da wani yanayi na mai shirin fita hayyaci.
Hayaniya ya fara jiyowa a waje, hakan ya saka shi miƙewa tsaye babu shiri.
Cikin sauri ya fito daga ɗakin, ya kama katanga, ya leƙa, sai dai yana leƙawa ya ga ƴan ƙato da
gora da miyagun makamai, sun fara taruwa a kewayen gidan, kasancewar akwai hasken farin
wata, kuma akwai hasken ƙwayayen solar hakan ya bashi damar ganin makaman da suke
hannun su.
Babu tsoron komai, ya haye katangar, ya hau saman roofing gidan, ya dira ta wani ɓangaren, jin
sautin dirarsa, ya sanya suka rufa masa baya, ta in da suke jiyo sautin gudunsa har da karnuka
su na kururuwar a tare.
Sai dai duk da wannan ƙira da Allah ya yi masa, ta siffar ƙarfi ba ya jin nauyin jikinsa, ya din ga
dukan ƙasar da dukkanin nauyin jikinsa, ba su ankara ba, ya ɓace musu ɓat kamar walƙiya.
A bakin titi suka tsaitsaya suna haki, su na mayar da yadda aka yi.
Ɗaya daga cikin su ya ce "Anya yaron nan, ba da layar zana yake amfani ba?"
"Ba wata layar zana, tsohon hatsabibi ne kawai, ni na yi mamaki ma da ya gudu ai, da da ne fa,
wallahi sai ya illata ku kan ya gudun. Ai kamar yadda na gaya muku ne, da na ji alamun ya zo,
zan kira ku a waya na sanar muku, ai ba zan sake sukuni ba sai ya je hannu, na za ta ma zaku
kira ƴan sanda ne"
Ɗaya daga cikin jami'an sintirin, ya ce "Ko zamu kira ƴan sanda, mu yakamata mu fara huɓɓasa
mu kama shi, sai mu miƙa musu shi, wannan gudun nasa yaushe muka kira ƴan sanda ma"
"Amma duk da haka, yakamata su san yana zuwa ai"
Shugaban su ya ce"Muddin suka sani, canza taku zai yi, ba zai sake zuwa ba".
Malam lawan da gidan sa ne a jikin gidan da yake zuwa ya ce "In ji wa? Ba zai taɓa iya daina
zuwa gidan nan ba, yadda ka san ya binne asiri a ciki, kodayeke sai ta yiwu ma asirin ya binne,
wannan hatsabibancin nasa akwai lamarin sihiri a ciki, amma zan cigaba da saka ido, da ya zo
zan kuma kiranku"
"To shikenan malam lawan mun gode, yanzu ka koma gida, bari mu koma bakin aiki, ko kuma a
raka ka ne?"
"Ahha haba, kamar ba namiji ba, ba wani abu bari na koma, ai ya riga ya gudu" Suka yi sallama
ya nufi layinsu.
Sai dai yana daf da ƙarasawa gidansa, kawai ya ji an yi ball da shi, kasancewar sa ɗan ƙaramin
mutum, sai jin sa yayi, ya yi sama ya dawo ƙasa kamar wani karmami. Ya tashi a gigice yana
zaton ko gamo yayi da aljani, ya hau waige-waige.
Haske shi ya yi da fitila, sannan ya ce "Kwana da yawa malam lawan, tsohon butulu, da na
ƙyale ka ban yi maka komai ba, shi ne ka cigaba da yi mini bita da ƙulli?"
Cikin kwakwazo, da tsananin razani ya ce "Na tuba, na bi Allah na kuma bi ka, dan Allah" kan
ya ƙarasa, ya karya shi ɓaras, ta hanyar saka ƙafa, ya yi masa wani irin duka a ƙafarsa ɗaya.
Malam lawan ya a kurma ihu, cikin tsananin zafin nama, ya cire hular kan malam lawan,, ya tura
masa a baki, sannan ya ciro wuƙar ƙugunsa ya yanke shi a damtsensa, aikuwa jini ya ɓalle.
Ya durƙusa a gaban sa ya ce "Yanzu ai ka ji daɗin bayar da rahoton zuwana, ragon maza
kawai" ya tashi tsaye ya ja da baya ya ɓace a cikin duhu, ya bar shi a mawuyacin hali, ga
karaya ga yanka, gashi kuma ya toshe masa baki.
Ko da ya koma gidansa da yake zaune, ciro wuƙar da ya yanki malam lawan yayi, yayi jifa da
ita. Ya tsaya yana haki, abun da ya yi alƙawarin dainawa, yau ya yi, ya zubarwa da wani jini.
Ya dafe kansa yana huci cikin tsananin damuwa.
**
Yau sumayya ba ta haɗa tafiya da Nabila ba, dan da wuri sosai ta fita, za ta shiga asibitin
murtala ta duba wata yayar babansu da aka kwantar a emergency, za ta kai musu abinci.
Su na tafe da mai adaidaita sahu, ta hango mutane na ta shiga su na fita a wani layi, duk da
lokacin gari bai gama hasken da za ace, mutane suna wannan tururuwar ba.
Da sauri ta tsayar da mai baburin, ta biya shi kuɗinsa, ta sauka, ta nufi layin da mutane ke
shiga su na fita.
Wurin duk babu mata, sai maza, amma hakan bai hanata kutsawa da son gano abun da yake
faruwa ba.
Tsayawa ta yi ta tambayi wani magidanci, abun da yake faruwa. Ya sanar da ita, gawar wani
yaro aka tsinta, a bayan maƙabartar unguwar, an yanke masa al'aura da wasu sassa na jikinsa.
Jikinta na tsuma ta cigaba da kutsawa tana faɗin "Ku matsa, ni ƴar jarida ce" tare da nuna musu
id card ɗin ta.
Ta ɗaɗɗauki hotunan yaron, sannan ta tsaya tattaunawa da mutanen da suka fara zuwa su ka
tarar da abun.
Sai kiranta ake yi a waya, ana jiran ta kai abinci, amma sai da rana ta ɗaga sosai, aka gama
komai ƴan sanda suka zo, sannan ta yi shirin tafiya, shi ma sai da ta karɓi lambar wayar wani
ɗan sanda, da zimmar zai din ga ba ta update na sakamakon binciken da za su yi, a kan gawar.
Ko da ta je asibiti ta sha faɗa,na rashin kai musu abinci da wuri, ko a jikinta, saboda ta samu
rahoto, dan haka tana ajiye musu abincin, ta yi waje.
Sai dai ba ta fito daga emergency ba, ta din ga jin ihun wani babban mutum, kamar mara
gaskiya, haka ta koma tana leƙawa ta ga abun da yake faruwa.
Magidanci ne, ake yi masa ɗinkin wani uban yanka a damtsensa, jikinsa yayi kaca-kaca da jini,
duk da ana ta yi masa allaurar kashe zafi, amma sai ihu yake yi.
Babu neman izni, ta afka ciki ta ce "Sannu bawan Allah, ka yi haƙuri Allah ya baka lafiya, ka
daure"
Duk sauka waiwayo su na kallonta, har da ma'aikatan, mutumin ya ce "Na gode sosai"
Ta ƙara matsawa ta ce "Amma hatsari ka yi ne? Kodayeke wannan ai yankan makami ne ba
hatsari ba"
Ya ce "A'a wani ɗan daba ne, ya sare ni jiya cikin dare, dama hukuma ta daɗe ta na neman sa"
Sumayya ta gyara tsayuwarta ta ce "Subhanallah, bawan Allah a wace unguwa ce haka? Ko
rigima ku ka yi da shi ne?" Ƙanin malam lawan da yake tsaye a wurin, a fusace ya kalli sumayya
ya ce "Dalla malama fita, mutum yana fama da kansa, kin zo ki na yi masa wasu surutan banza"
Ta ce "A'a Allah ya baka haƙuri, ka sani ko akwai wani taimako da zan iya yi masa. Kalli saran
da aka yi masa fa, idan ba za ka damu ba, zan naɗi muryarka, mu saka a radio, ko Allah zai
saka, hukuma su bi maka haƙƙinka, barin su da ake yi suna cin bulus ya sanya suke cigaba da
ɓarna".
Malam lawan ya ce "Ke rufawa kanki asiri, hatsabibanci da ta'addanci yaron, ya wuce tunanin
ki"
Sumayya ta zaro wayarta, za ta yi magana, sai ga wasu mutane guda biyu sun shigo da wani
kaki a jikinsu, da ba ta san na menene ba, suka mayar da ƙofar ɗakin suka rufe.
Malam lawan ya kalle su, ba su ne ƴan sandan da aka kirawo suka tsaya masa, likitoci suka zo
kansa ba ne.
Sumayya ta yi tsilli-tsilli da ido, ɗaya ya ƙirga mutanen da suke cikin ɗakin, da likita ɗaya, nurse
ɗaya, sai ƙanin malam lawan da sumayya. Dan duk maƙwabtan da suka kawo shi, sun tafi
wurin sana'oin su. ya ce "Ku biyar ne a ɗakin nan, idan ka sake mu ka ji labarin sunan wanda ya
yi maka wannan raunin, to za ka maye gurbinsa da ya bari na gidan yari, dan haka ka ja
bakinka ka yi shiru".
Sumayya ta ce"Ban gane ba Yallaɓai, mutum mai laifi kuma ace kar a faɗi waye? Ba ka ga irin
illar da aka yi masa ba ne, ga karaya ga rauni, da ya kashe shi fa?"
Ya ba ta amsa da "Da ya kashe shi, bakinki zai iya sakawa, ki ɗauki hukuncin da za ayi masa
na kisan" daga nan suka juya suka fice.
Mamaki ya mamaye sumayya, ta ce "Kai kuwa bawan Allah, waye wannan shi kuwa, da har
jami'an tsaro masu kaki, za su hana bayyana laifinsa, ana sane aka ƙi kama shi kenan?"
Malam lawan ya ce "Ba zaki ja mini masifa ba, ki fita ki bar wurin nan, na ji da masifa ɗaya,
bayan ɗinkin nan a karye nake wallahi"
Cikin tsananin naci, da son samun rahoto, ta kwantar da murya za ta lallaɓa shi, ta samu labari,
amma da likitan da ƙaninsa suka koreta daga ɗakin.
Fitowa ta yi, tana ta mamakin abun da ya faru, yaya za ayi hukuma ta bawa mai laifi kariya,
wane irin abu ne haka?.
Ba ƙaramar makara ta yi ba, amma tunanin abun da ya faru, ya fi ɗaure mata kai.
***
Sannu a hankali yake yi wa kansa allura, yana yi yana fatan samun abun da yake so, a hankali
ya gama ɗurawa jijiyarsa ruwan allurar da yake fari tas a cikin sirinji, bayan ya kammala tsaf ya
fara jin kansa yana yi masa nauyi.
Take idanunsa suka yi mitsi-mitsi, ya soma lanƙwasa kansa, yana jin idanunsa kamar za su fito
waje, suna yi masa yaji, a haka ya kunna sigari, ya kashingiɗa, ya na bawa sama hayaƙi,yana
jin yadda jikinsa ke son bijirewa aikin allurar.
Wayarsa ce ta fara vibrating, ya miƙa hannu, ya ɗaukkota ya duba, yana zaton ko a cikin
yaransa ne, sai dai ya ga private number ce.
Har zai ƙi ɗagawa, sai kuma ya ɗaga ya saka a kunnensa, amma bai yi magana ba.
Daga cikin wayar aka ce, "Meyasa ba ka gajiya da neman magana ne? A wannan karon ma sai
da ka saka na yi abun da na goge ɓarnar da ka yi, yakamata ka nutsu Aminu"
Ya saki hayaƙi, tare da ɗan kaɗe tokar da sigarin ta tara, sannan ya ce "Waye kai? Sannan
waye ya saka?"
Mutumin yayi dariya, ya ce "Mutum mai ba ka kariya, domin cimma nasa muradin, yakamata ka
sauƙaƙa mini aiki, ka daina aikata abubuwan da za su din ga barin trace a kan ka".
"Ka yi muguwar kasadar ƙoƙarin cimma burinka da mutum irina, kar ka manta viper ake yi mini
laƙabi da shi, macijin da ya fi kowanne hatsari, idan ka bari na sare ka, ka gama yawo" yana
gama maganar ya cillar da wayar, ya ɓata fusaka kamar ya fashe da kuka.
Cikin fusata ya ce "Ni again? wani ya kuma amfani da ni? Impossible zan watsa dafina a in da
ya dace da in da bai dace ba, sai na tabattar da danganawa ga kunyar ƙarshe, ko da kuwa za
ayi mutuwar kasko" ya yinƙura da nufin ya tashi tsaye, amma ya kasa sarrafa gangar jikinsa,
hakan ya tilasta masa komawa ya nemi wuri ya kwanta.
Duk da irin faɗan da sumayya ta sha a wurin aiki a kan makara, bai dame ta ba, jikinta sai
tsuma yake saboda ta zo da rahotanni masu muhimmanci da ɗaukar da hankali.
Ofishin head of news ta je, ta shiga da sallama.
Matar ta ɗago ta amsa mata da ƙyar, ta ƙarewa sumayya kallo, ta ce "Yanzu ne lokacin shigowa
aiki ko? Gaba ɗaya yaran yanzu ba kwa ɗaukar aiki da muhimmanci, kodayeke karatun ma ba
wani na kirki ku ka yi ba, duk da satar amsa ku ke gamawa. Ki shiga hankalinki kafin na kai
maganar nan wurin MD"
Sumayya ta risuna ta ce "Afuwan anty, in sha Allah ba zan sake ba, na samu wasu rahotanni ne
masu muhimmanci, da ya san na tsaya a hanya, shiyasa na makara na kawo miki a tantance ne
ko za a saka su a news"
A yamutse matar ta ce "Na menene" cikin farinciki da jin ƙwarin gwiwar ta yi abun arziki ta fara
da gaya mata abun da ya faru a asibiti.
Amma matar sai cewa ta yi"Amma ba ki da hankali ko? Ta yaya zamu saka wannan shirmen a
news?"
"Anty ai a rahotanni, ko a janyo hankalin hukuma.... "Dalla yi mini shiru, business mu ke yi a nan
mu, ke fa iyayinki da rawar kanki yayi miki yawa sumayya. Meye hujjarmu idan aka tsutsiye mu,
cewar hukuma na ɓoye mai laifi?"
Sumayya ta ce "Wallahi a gabana aka yi, mutumin yana nan a emergency"
"Kin ga idan ba ki da abun faɗa, fita ina da abun yi"
Sumayya ta yi iya ƙoƙarin ta, ta danne abun da yake taso mata na fushi ta ce "To shikenan, sai
kuma akwai abun da na gani, ina kan hanyar tahowa nan, a nan wajen gari, an tsinci gawar
yaro an cire masa wasu sassan jikinsa".
"Almara kenan, wa zai yadda da wannan zancen?"
"Ba zance ba ne ba, na yi recoding ɗin maganar wasu daga mutanen da suka fara cin karo da
abun".
"Sumayya, ba irin wannan labaran mu ke buƙata ba dan Allah, je ki su murtala sun fita neman
rahotanni, ki din ga kawo sensitive abubuwa"
Summaya ji tayi wata irin ashar na kai komo a wuyanta, da take ƙoƙarin narkawa matar nan, ta
rasa abun da ta yi mata, haka kurum ta tsane ta. Ta yi ta kyararta ba ta son ta ga tayi wani abu
na cigaba.
Sumayya ta fice daga office ɗin kamar ta yi kuka, ta koma reception ta nemi wuri ta zauna.
Ba uwar da ta tsinana a aikin yau, tun da head of news department ta yi mata wulaƙanci.
Kasancewar a makare ta je, ya sanya lokaci yayi gudu, Lawisa, wato head of news ɗin, ta din
ga shiga tana fita, ta na kaiwa tana komowa, idan ta kalli in da Sumayya take sai ta haɗe rai.
Wannan karon bayan ta fita, a tare suka shigo da managern director, sai karairaya take yi masa,
tun da ya shigo ma'aikatan suke ta gaishe shi.
Ban da sumayya da ɓacin rai ya saka ta cika ta batse.
Sai da yayi gyaran murya ya ce "Wannan ba sabuwar staff ɗin mu ba ce? Ya na ganki a nan?
Wane department aka kai ta ne?"
Lawisa ta yi caraf ta ce "Sir ba ta da ƙwarewar aiki ne haryanzu, ana ɗan nunnuna mata aiki ne,
kafin ta gama gogewa".
Ya ce "Ok, babu laifi" sumayya kamar ta kwaɗawa lawisa mari, a fusakarta da ta sha uban
bleaching, duk tayi taruwar jini.
Ta daure ga gaida MD, sannan suka wuce gaba.
Tsaki Sumayya ta ja, tana duba wayarta.
Sai dai jin sallamar Nabila a reception ya sanya ta ɗago da sauri tare da amsa mata.
"Ya na ganki a nan?"
Nabila ta ce "Ke baki iya karrama baƙo