Author : Aysha Cool Category : Romance
din ga karɓa"
"Jami'ar tsaro ce ke?" Yayi maganar yana cigaba da kallonta
Nabila ta ce "Jami'an tsaron ai sun san da zamanka a nan, ina so ka haɗa ni da Aminu viper ne"
Waro ido yayi ya kalleta ya ce "Ke! Yayi maganar yana zazzaro mata ido"
Tayi ƙasa da murya ta ce "Kar ka ɗaga murya, ka taimaka mini, ɗan uwana ne, tun da ya fito
daga prison ban sake ganinsa ba"
"Ƙarya ki ke yi wallahi! Ban da ke mace ce, da namiji ce ke, wallahi sai na ciro hanjinki waje na
zubar a titi, bar wurin nan, kafin na karya ki"
Nabila ta marairaice ta ce "Ba ka da tabbacin ƙary.....
"Ki bar nan, kafin na tsarga ki biyu da makami" ta ja da baya a hankali, tana kallon sa.
"Ki bar nan na ce" ta juya da ɗan sauri, cikin tsoron yadda ya hayayyaƙo mata.
Wayarsa ya ɗaukko ya kira Walid yana huci, cikin sa'a ya ɗaga.
Walid ya ce "Maza ya ne?"
"Wata yarinya ta zo neman boss, wai ƴar uwassa ce, anya ba a fara bibiyar sa ba? Idan ba haka
ba, yaya aka yi ta san na sanshi".
Cikin mamaki walid ya ce "Kar dai yarinyar da gagare ya ce mini ta je dabar madaki neman sa?"
"Ban sani ba, amma zan so ka ganta, ka ga wani abun mamaki, mai ɗaure kai, dan na kusa
guduwa wallahi"
Walid ya ce "Kamar yaya?"
"Ka ga, ina hangota haryanzu, zan bita na yi mata magana, zan ce ta dawo gobe da safe, zaka
ga abun da na gani"
Walid ya ce "Kai liti, ka tabatta ba matsala?"
"Babu, kawai sonake ka ganta"
"Shikenan, idan ka tashi yau, ka shiga area wurin dila, ya baka balance, idan na zo zan karɓa"
"Sai da kai, an gama"
Nabila na shirin hawa ɗan sahu, ta ji an yi fito a bayanta, ta waiwaya ta ga liti a tsaye.
"Zo mana" yayi maganar yana kallonta.
Kawai zuciyarta ta raya mata, ko wuƙa zai soka mata.
"Ki zo mana" yayi maganar cikin tsawa.
Cikin rauni ta ce "Dan Allah ba wuƙa zaka soka mini ba?"
Ya ce "Ke da kashe ki zan yi, kin isa na bari ki bar wurin nan, shawara na canza, ban san alaƙar
ki da shi ba, dan haka zan haɗa ku"
Da sauri ta ɗan ƙarasa gabansa ta ce "Dan Allah, amma na ji daɗi na gode sosai da sosai".
"Mu haɗu a nan, gobe ƙarfe biyar na yamma, zan haɗaki da wanda ya san in da yake, amma
wallahi ki ka yi wani abu na rashin gaskiya, kin san sauran"
Nabila ta ce "Babu wani abu na rashin gaskiya da zan yi, na gode yayana Allah ya saka da
alkhairi"
Ya ce "Ke ki nemawa kanki tsari, da na zama yayanki, ware ki bar nan"
Hamadala ta yi, tare da jin kamar wata gagarumar nasara tana tunkarota.
Ƙwas-ƙwas takalminta yake bayar da sauti a kan tiles ɗin wurin, sai sauri-sauri take yi ta ƙarasa
ofishin manager.
Da sallama ta shiga, ya ɗago ya amsa mata, ta ɗan risuna ta ce "Afuwan sir, na tsaya ƙarasa
editing ɗin news ne, shiyasa ban zo kiranka da wuri ba".
"Bakomai sumayya, sannu da ƙoƙari, ina yabawa ƙoƙarin ki da himmarki".
Tayi murmushi ta ce "Na gode sir"
"Ina sisternki, young barrister ne? Nabila ko, kwana biyu ba ta kawo mana ziyara ba"
Sumayya ta yi murmushi ta ce "Ayyuka ne suka yi mata yawa, amma ko ɗazu muna tare"
Ya ce "To Allah ya taimaka, yauwwa dama batun program ɗin nan ne, honorable ya ce ba zai
samu zuwa ba, sai dai aje can gidansa ayi recording program ɗin, dan haka driver zai kai ki, a
can badawa gidansa yake, za a kai ki ranar Friday, sunday zai yi tafiya ki yi recording program
ɗin"
Cikin mamaki da sanyin jiki, ta ce "Gidansa kuma sir? Amma ai yau murtala za su dawo, tun da
su maza ne sai su je....
Ya ɗaga mata hannu ya ce "Look sumayya, ya zama dole ki je, murtala ba zai dawo yau ba,
honorable ba wani abun zai yi miki ba, gidan da yake zaune da iyalansa ne, recording ɗin
program kawai zaku yi. Idan kuma ba zaki yi ba, you know the consequences"
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi, ta ce "Allah ya kaimu" ta juya a hankali ta fice.
₦500 ne, via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank
Special wanda ba sa son group 1k.
Wanda za su jira document, idan an kammala 1k ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
wannan layin
Sai a tura mini shaidar biya ta
08081012143 ko 07063065680
Ayshercool
08081012143
[7/25, 1:18 PM] null: *ƘARFE A WUTA*
AREWABOOKS: ayshercool7724
Watpad: ayshercool7724
What's app: 08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
11
Bayanta manager ya bi da kallo, ta bashi tausayi sosai da sosai, sai dai yana addu'a Allah ya sa
kar honorable ya cutar da ita.
Kamar ɓarawo, haka walid ya diro a tsakar gidan, maimakon ya biyo ta ƙofa, ɗan mama yana
zaune yana shan sigari a ɗan tsakar gidan.
Bai kula shi ba, ya wuce ɗakin da viper yake, sai dai ya duba baya ciki.
Walid ya dawo, ya kalli ɗan mama ya ce "Ina Viper?"
Ɗan mama yayi dariya ya ce "Har ka gama fushin, ka dawo?"
Walid ya ce "Kai ka san ba zan iya ba, ƙular da ni yayi ne, ina yi masa uzuri ne kawai na san
kansa ya taɓu, yana ina?"
"Baya nan" ɗan mama ya bashi amsa kai tsaye.
"Kamar yaya? Ina yaje?"
Ɗan mama ya zuƙi sigarinsa sannan ya ce "Ni na isa na hana shi fita ne? Ko kuma na ce sai ya
gaya mini in da za shi? Da dai kai ne zai iya ɗaga maka ƙafa"
A fusace walid ya ce "Dan me zaka bari ya fita?"
"Au so ka ke na hana shi, ya karya ni, ko ya illata ni, kaɗaici ne ya dame shi, gidan babu kayan
caji, sai na hayaƙi, shi ne ya fice. Yauwwa dama ina son gaya maka, ka daina kwashe kayan
cajin nan gaba ɗaya, idan wani yayi rawa an bashi kuɗi, kai idan ka yi, na jaki zaka ci a
hannunsa wallahi"
Cikin takaici Walid ya ce "Wai so ka ke sai ya kashe kansa ne? Kana kallon allurar nan ba ta
ɗaukar sa, farar ƙwaya ma fa ba ta yi masa komai, sai rikita masa ƙwaƙwalwa, idan ya haukace
fa?" Walid gani yayi ɗan mama yayi tsuru-tsuru, yana rarraba ido, dan haka ya waiwaya
bayansa, Al'amin ya gani a tsaye a bayansa.
Bai kula su ba, ya zo ya raɓa walid ya wuce.
"Master"ya kira shi.
Al'amin ya waiwayo, fuskarsa babu annuri, idanunsa sun yi ja, jijiyoyin kansa suka miƙe ya ce
"Me na ce maka a kan kirana da haka?"
Walid ya ƙarasa kusa da shi, dai-dai kunnensa, ya yi masa raɗa.
Viper ya kalli Walid ya ce "Kasheni ka ke so ka yi sannan hankalinka ya kwanta ko Walid?"
Walid ya ɗage kafaɗa ya ce "Duk yadda ka gani"
Viper ya hankaɗe shi gefe, ya wuce ɗakinsa, ya rufe ƙofa.
Walid ya bishi ya leƙa ta taga ya ce "Me zaka yi ka rufe ƙofa?"
Leda ya ciro daga aljihunsa, ya haɗa allura a sirinji, zai yi wa kansa.
Walid ya ce "Al'amin, ba zaka daina yi wa kanka allurar nan ba ko? Ba za ta yi maka ba, ka
haƙura mana"
Al'amin ya tashi, ya je ya ja tagar ya rufe, ya bar walid a waje yana surutu.
Sumayya kuwa tun da ta koma gida, mama ta lura da yanayinta, sai dai ta yi zaton ko gajiyar
aiki ce, amma har dare ba ta walwala.
Dan haka ta magantu, ta ce "Ƴar mama, wai ko babu lafiya ne?"
Sumayya ta ce "A'a lafiyata ƙalau?".
"To faɗa ku ka yi da mutuniyar ne?"
"A'a bamu yi faɗa ba mama"
Ba ta gaza ba ta sake cewa "To ko wurin aikin ne suka yi miki wani abun?"
Sumayya ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Hajiya mama, bamu yi faɗa da ƴar ki ba, lafiyata kuma
ƙalau, kawai kin san yanayin aikin namu ne, kayi ta ganin abubuwa na ban tausayi
daban-daban".
Mama ta ce "Ai baku ba sumayya, mu ma masu saurare, kusan kullum cikin zullumin kunna
radiyon muke, sai dai ku ƴan jarida ku ne idonmu, ta bakinku kawai muke jin wasu labaran da jin
halin da duniya ke ciki. Allah dai ya saka muku da alkhairi ya tsare mana ku baki ɗaya, daga ke
har Nabilan aikin tainakon al'umma ku ke yi, Ubangiji Allah ya tsare ku ya kawo mazajen aure
na gari"
Sumayya kamar ta gaya wa mama, abun da aka umarceta a wurin aiki, amma ta san hankalinta
tashi zai yi, zata iya hanata aikin ma, kuma Allah ne gatansu aikin nan ne gatansu, dan haka ta
ja bakinta tayi shiru.
***
Sannu a hankali barrister Naja'atu take bin titin ƙauyen, sai tsaki take yi saboda yadda garin
yake babu kyakkyawar hanyar shiga. Sai uwar ƙura da kwazazzabai a hanyar.
A hankali ta cigaba da tuƙin har ta ƙarasa in da take son zuwa.
Sai da ta shiga tsakiyar tsakar gidan, sannan ta yi sallama.
Daga cikin ɗaki a ka amsa sallamar.
Daga baya matar ta fito daga ɗakin, ta ce "Waye?" Ganin barrister Naja'atu ya sanya ta ɗan saki
fuska, ta bata damar shiga ɗakin.
Shame-shame taga rammaa a kwance a kan katifa, ta nemi wuri ta zauna a gefe.
Ta kalli in da ramma take, sannan ta mayar da idonta kan maman ta ce "Na dawo ne na ji me
kuka tsayar, kuma na ga haryanzu ba ta da lafiya, anya ramma ba shagwaɓa a wannan
lamarin? ya ci ace kin ware ai, da auren ma aka yi miki ai da kina gidan miji, ko shi ma hakan
zaki yi ta yi masa".
Fashewa da kuka ramma tayi, cikin tsananin baƙin ciki da takaici.
"Meye kuma na kuka? Wannan abun da ki ke yi, sai mutane sun san halin da ki ke ciki?"
Cikin sanyin jiki da damuwa, maman ramma ta ce "Tun da abun nan ya faru, take rashin lafiya,
jiya mun je asibitin sha ka tafi, na garin nan, an ce ciki ne da ita" tayi maganar tana fashewa
kuka mai taɓa zuciya.
Sak Naja'atu tayi, tana kallon su.
Ta numfasa ta ce "Wai wannan kukan na menene ku ke yi haka, kukan zai yi muku magani ne?
Ai wannan ba abun ɗaga hankali bane ba"
Cikin tsananin mamaki, maman rahama take kallon barrister Naja'atu.
"Baiwar Allah, ce miki na yi fa, an ce mini ciki ne da ita, wanda ya dubatan ɗan garin nan ne, na
san dole maganar nan ta fita, auren yarinyar nan ba zai yiwu ba, amma kina nuna bakomai
bane ba, dan girman Allah a karɓowa yarinyar nan hakkinta".
Naja'atu ta ce "Baiwar Allah, ko fa an kai yaron nan kotu yayi prison, abun da zai faru ya riga
faru, ba kuma zai goge ba, ɓacin suna kuma ya riga ya ɓaci.
Matsalar mutanen mu na Arewa, kuna giramama al'ada da addini a kan ƴancinku. Da in da aka
cigaba ne, zata iya haife abun da ke cikinta, idan tana so, and rise him as a single mother, har
ta iya neman ya din ga biyanta wani abu a kotu, shikenan. But for now, za a iya zubar da cikin ta
cigaba da harkokinta sai me? Is an adolescent crises kowa ma zai iya faruwa da shi".
Cikin mamaki maman ramma ta ce "Baiwar Allah kuma ke musulma ce?"
"Ƙwarai kuwa, muslma ce ni gaba da baya, mafita nake baku da shawara. Zan je na yi booking
a saka rana a can cikin gari, private hospital, a cire cikin lafiya ƙalau za a cire shi, yanzu an
cigaba nesa ba kusa ba, ku karɓi kuɗin ku ku rage zafi".
Rma ta fashe da kuka ta ce "Ni mama tsoro nake ji, an ce mutuwa ake yi, dan Allah ni dai a kai
shi wurin alƙali, an ce kina taimako dan Allah ki taimaka mini, ji nake kamar na mutu na huta, ba
a taɓa cikin shege a garin nan ba sai a kaina, dan Allah ki taimaki rayuwata, wallahi wanda zan
aura ya ji labari ba zai aure ni ba, babu kuma wanda zai ce zai aure ni, cewa za ayi na zama ƴar
iska" ta ƙarasa maganar kamar ta shiɗe.
Barrister Naja'atu ta ce "And so what dan an fasa aurenki? Zaki iya zama duk abun da ki ke so
a rayuwa ko da aure ko babu, waye ya ce muku aure shi ne limit na rayuwar ƴa mace ne? dan
Allah ku fuskanci rayuwarku, ku daina bari ana cutar ku da addini da al'ada".
Cikin baƙin ciki maman ramma ta ce "Kin ga ya isa baiwar Allah, idan bawa bai riƙe addini ba
haka zai ta rayuwa kamar dabba a gari, babu ƙa'ida babu hukunci? Wannan ai salon bawa yaro
damar ya je yayi zina ne, ko ni da nake jahila a cikin ƙauyen nan, sam maganarki ba ta da tushe
balle makama a wurina, dan haka ki tashi ki tafi kawai, bana buƙatar taimakon naki, cuta ce an
cuce mu Allah ya isa kawai"
Naja'atu tayi wani irin murmushi ta ce "Ƙarshen abun fa kenan, ki yi Allah ya isa, na biyo miki da
masalaha amma kin ƙi, shikenan idan kin ƙi ji ai ba kya ƙi gani ba, duk abun da ya biyo baya
wannan shi ne abun da ki ka zaɓa. Sai dai ina sake yi miki gargaɗi da babbar murya, kar ki
kuskura ki sake shiga kafafen watsa labarai ki yi magana, idan kuma ki ka sake, ba ruwana"
Ta tashi ta sake ajiye musu kuɗi, da complementary card ɗin ta, ta ce "Akwai lambar wayata a
jiki, na san zai iya yi muku amfani, idan ku ka ga babu sarki sai Allah, domin kuwa barin cikin
nan, dai-dai yake da zama da ajalinta, dan kome zai ɗauka, uban wanda ya aikata laifin, ba zai
bari ba"
Gaba ɗaya bin ta suka yi da kallo, har ta tashi ta fita, ramma ta fashe da wani irin kuka, tare da
jin ƙarshen rayuwarta ya zo.
Mahaifiyarta ta kalleta ta ce "Ki yi haƙuri ramma, ina tare da ke in sha Allah, na san ko menene
ya faru, ni ce sila, da ban tura ki aikatau ba, da haka ba ta faru ba, amma babu yadda zan yi ne,
ki yafe mini dan Allah" tayi maganar tana kuka ita ma.
Sumayya na ta aiki a kan computer, sai dai hankalinta baya kan aikin sam, kawai dai tana yi ne,
amma ƙasan zuciyarta tsoro da fargabar dalilin da ya sanya, aka ce ta je gidan honorable
Indabo ta yi hira da shi take ji, idan a kan laifin da ta yi wancan karon ne, ai ta bayar da haƙuri,
kuma lokacin tana farkon zuwa ne.
Sallamar murtala ce, ta dawo da ita hayyacinta, tayi murmushin yaƙe ta ce "Uncle murtala,
saukar yaushe?"
Ya nemi wuri ya zauna ya ce "Agogo sarkin aiki, yakamata a ƙara miki matsayi a gidan nan fa"
Ta waro ido ta ce "Ni a wa?"
"Ke a ma'aikaciya jajirtacciya mana, wai ya aka yi mutuniyar take ɗaga miki ƙafa yanzu,
lawisa?"
Sumayya ta ce "Hmm, Arfa ce ta ce na daina jin tsoronta, nima na nuna mata bani da kirki idan
ta takura mini, shi ne fa ta sarara mini".
"Ai matar nan ƴar bala'i ce lamba ɗaya"
Sumayya ta sake tattara nutsuwar sa a kan sa ta ce "Yauwwa ncle murtala, akwai matar da ka
yi recording, ta zo an yi raping ƴar ta, an ce Barrister Naja'atu ta shiga case ɗin, ina aka tsaya
ne?"
Da sauri ya ce "Rufa mini asiri, ni da aka kusa korata a kan case ɗin, kuma lawyoyi da masu
kare hakkin ɗan adam, sun yi casa a kan case ɗin, sai dai tun da ta shiga cikin lamarin, kowa ya
ja da baya"
Sumayya ta ce "Ikon Allah, to ai haryanzu ban ji a ina aka tsaya ba, wai ɗan waye ne yayi?"
"Taɓ ba zaki ji mutuwar sarki a bakina ba, nima ba ta faɗa mini ba matar, wai dai yaron ɗan
masu kuɗi ne, wai ɗa ne ga wani ɗan majalisa, ba ta san sunansa ba, a gidan ƙanwar ɗan
majalisar yarinyar take aiki, sun je gidan ta bi ba'asi, an hana su shiga, masu gadin da suka kai
yarinyar asibiti ma duk an canza su"
Cikin tausayawa Sumayya take girgiza kai ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shikenan akwai
Allah, amma kana ganin ita Bunkuren za ta yi wani abun kirki a kai? Meyasa ba za a bibiyeta
ba, a ji a ina aka tsaya a case ɗin ba, atleast a gurfanar da shi a kotu mana"
Ya miƙe tsaye ya ce "Lallai ƙanwata baki san ƙasar nan ba, ai dokar ƙasar nan a kan talaka
kawai take aiki, ko ɗan kansila ne, ba za su hukunta shi ba, ita kanta barrister nan akwai ayar
tambaya a kan ta, duk da a zahiri ta Allah ce, amma yadda ake tsoronta komai tayi, babu wani
mai challenging ɗin ta, akwai wata a ƙasa".
"Gaskiya dai, Allah ya sa mu dace "
Ya amsa mata da Amin.
Nasir yana ta yi