Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Karfe a Wuta Book 1 Complete Complete Hausa Novel by Aysha Cool

Author :  Aysha Cool Category :  Romance

Chapter   19 / 19

54K to 54.3K   out of 54.3K words



Nabila ta kaɗa kai ta ce "Kusan watana guda zuwa na biyu ma,  kawai ina fafutukar yaya zan
ganshi, na san dama zaki ƙaryata ni, ban gaya miki ba ma balle ki hana ni ko ki yi mini masifa.
Amma cikin ikon Allah, viper ya bar mini shaidar da zai tabattar da  ya ganni"

Cikin rashin fahimta, sumayya ta ce "Kamar yaya?"

Nabila ta ɗaga rigarta, sai ga plasta a gefen cikinta, ta saka hannu ta cire plastan, sai ga rauni a
wurin.

Sumayya ta waro ido, tare da rufe baki, ta ce "Na shiga uku, Nabila kin haukace ne? Wai dama
da gaske ki ke?"

Ta saki rigar ta ce "Ai kafin yayi mini haka, rannan karnuka sun kusa yin watanda ta. Sunayya
gayen nan ya wuce duk yadda nake tunani, ashe faɗar sunansa ne a baki kawai mai sauƙi,
wallahi idanunsa sun kusa sakani fitsari a wando, sumayya yaya zan kwatanta miki yadda yake
ne ki gane abun da na gani? Kwarjininsa ya wuce duk yadda zan kwatanta miki, wallahi da ya
shaƙe ni, na ɗauka mutuwa na yi"

"Har shaƙe ki yayi, kin ga Nabila ki rufa mana asiri, amma yaya aka yi ki ka samu in da yake?"

"Na gaya miki kusan watanni biyu kenan ina nemansa, na san idan na gaya miki, hana ni zaki
yi, duk ba wannan ne ya dame ni ba, yayi alwashin idan ya sake ganin fuskata, sai ya kashe ni,
kuma mummunar kasada na kuma tafkawa Sumayya".

"Ta me kuma?!

"Wayarsa na sato, kan na taho!".


Alhamdilillah, duka duka a nan mu ka kawo ƙarshen free pages, mu kasance a cikin paid pages,
domin jin ainihin gundarin labarin *ƘARFE A WUTA*.


₦500 ne kacal ta wannan account ɗin, masu so ta private special group 1k zasu saka a wannan
account ɗin.
0009450228
Aisha Adam jaiz bank

Ayshercool.
08081012143

19 / 19