karfe A Wuta book 1 Complete Hausa Novel By Ayshercool .pdf

Author :  Aysha Cool Category :  Romance

Chapter   17 / 19

48K to 51K   out of 54.3K words

sun fita wajen gari.
Dai-dai wani gidan gona ya ajiyeta, wurin duk shuke-shuke, da alama akwai mutane a daf da
wurin, amma sai an yi tafiya kan a tarar da in da suke. Shi kansa titin wurin, babu ababen hawa
da suke kaiwa suna komowa a wurin.
Sai rukunin manya manyan kamfanunnuka a wurin, na shinkafa da na taki, wurin shiru sai ƙarar
injinan da masana'antun ke amfani da su.

Sai da ta sallami mai a daidaita sahun, sannan ta fara tunanin, to ina ma za ta nufa?

Tsayawa ta yi, tana waige-waige, kawai ta hango wani mutum ya tunkarota, nan ta fara ja da
baya, tana tunanin ko zurawa za ta yi da gudu.

"Mu je" ya ce mata a kausashe.

Ta turje ta ce "Ina?"

"Ba ke ce baƙuwar Viper ba, mu je"

A raunane cike da tsoro ta ce "A'a, ka kirawo shi mu yi magana a nan, ni dama kaya nake son
saya a wurinsa"

Cikin mamaki ya kalleta ya ce "Wani irin kaya?"

"Wanda yake sayarwa" tayi maganar a tsorace tana kallon Walid.

Ya gyaɗa kai ya ce "Baki san waye shi ba amma? Kin yi kasada nafi muni, wuce muje kafin na
saraki biyu a wurin nan"

Cikin rawar jiki ta ce "Dan Allah ka yi mini rai, ni ka kirawo shi nan kawai".

"Wallahi zan saɓa ki a ka, wuce mu je"

Salati Nabila ta din ga yi, dan tun da ta yo dakon kasadar nan, sai yanzu ta ga zunzurutun
wautar da ta aikata.

Ya sakata a gaba, suka nausa bayan kamfanunukan.

A can gidan honorable kuwa, yana da office a cikin gidan sa, in da yake ganawa da mutane na
mussaman.
Hankalin sumayya ya ɗan kwanta, bayan da ta ga mutane na shiga suna fita a gidan, da alama
ba shikaɗai ne a gidan ba, kuma gidansa ne da yake zaune da iyalinsa.

A harabar gidan aka dakatar da wanda suka rako sumayya, aka ce itakaɗai za ta shiga.

Wani security yayi mata jagora, zuwa wani sashe na gidan, ya kaita wani falo, ya ce ta jira a
nan, ta samu wuri ta zauna, a kan kujera, tana zaune a falon office ɗin, tana ɗan kalle-kalle,
tana jira kamar yadda aka umarceta.

Cikin office ɗin kuma, Barrister Naja'atu ce suke magana da honorable.

"Ni fa na yi iya ƙoƙarina, amma da alama mutanen nan, su na da taurin kai, juyin duniya sun ƙi
saduda, sai iƙrarin a karɓar musu hakkinsu suke yi, ina ga kawai a ɗauki matakin da ya dace a

kan ta".

Indabo ya ce "Lallai dama haryanzu akwai masu ƙi faɗi a talakawa?"

"Akwai su fa, ku kuna gefe, mune muke shiga cikinsu da rufe bakunanansu a kan ɓarnar da ku
ke aikatawa, sai dai kan mage ya fara wayewa, babban abun damuwar sun gaya mini an
tabattar musu tana da ciki"

Yayi saurin ɗaga kai ya kalleta "Ciki kuma? Sau nawa yayi mata fyaɗen ne?"

Ta ɗage kafaɗa ta ce "Wannan kuma shi za ka tambaya, ba zan iya cigaba da ɓata lokacina a
kan wannan kucakan mutanen ba, ina da abubuwa masu muhimmanci kawai ayi abun da ya
dace".

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Abdul, ban san lokacin da zai yi hankali ba, ina tsoron lokacin zaɓe, a
samu wani ya fito da miyagun halayensa, in the next couple of years, sonake ya samu ref, ko
deputy governor a tsayar da shi takara, saboda yarjejeniyar da muka yi, da jam'iyya kenan kafin
na yarda na zauna a cikinta, amma al'amarin sa kullum ƙara lalacewa yake yi"
Barrister Naja'atu ta ce "To, gara dai ka san abun yi"

"Anyway, shikenan, ki tura mini address ɗin su ita yarinyar, za ayi abun da aka saba" ta miƙe
tsaye ta ce "No problem"

Ta buɗe ƙofar office ɗin ta fito, kallo ɗaya sumayya ta yi mata, ta gane ta, saboda yadda Nabila
take ɗora hotonta a status ɗin ta a baya.

Cikin son tabattar da abun da Nabila ta gaya mata, a kanta, ya sanya  ta tashi da sauri tana
murmushi ta ce "Barrister Naja'atu Bunkure, baya goya marayu, dama zan ganki ido da ido?"
Sumayya ta yi maganar tana murmushi.

Kamar ta ga kashi, ta yatsuna fuska ta ce "Sannu".

Sumayya ta maze ta ce "Na tsinci dami a kala yau, ni ƴar jarida ce, a cikin ayyukan da ki ke
gudanarwa, zan so yi miki tambaya ɗaya zuwa biyu, na san masu sauraronmu, za su ji daɗin
hakan, kasancewar ki abar so da koyi ga al'ummar mu, mussaman mata. Dan akwai sister na,
die hard fan ɗin ki ce, ita ma lawyer ce.
Cikin fusata Naja'atu ta ce "Ke saurara mana, daga ganina sai tsare ni ki hau zuba dan kina ƴar
jarida, who permits you to do that?"

Sumayya ta dake ta ce "No, barrister, ba as ƴar jarida ba kawai, as a woman and one of your
fans, ko ƙorafi ne da ni, ta yaya zan same ki ki tsaya mini, atleast ko mintuna uku ki bani mana,

dan Allah. Na san ƴan jarida wasu lokutan mu na da zaƙewa amma a duba roƙona" kamar ta
zagi Sumayya, ta tsani baƙin naci irin na ƴan jarida, amma sanin halin su na yanzu sai su samu
abun ɗorarwa ta ɓata mata career ya sanya ta danne ta ce "Ina jin ki"

Fitowar honorable, ta sanya ta yin shiru, ya kalli sumayya ya ce "Mu je in da zaki ɗauki program
ɗin"

Tana ji tana gani, Naja'atu ta tafi.

Can wani surƙuƙi ya ja ta, da sai da ta fara jin tsoro, sai dai duk in da suka ratsa, akwai
ma'aikata.

Sumayya ta sha mamakin, irin dukiyar da aka yi ɓarna, wurin gida wannan gida da kamar ba za
a mutu a bar shi ba.

Daga ita sai shi a ƙaton falon, mai ɗauke da ɓangarori daban-daban.

Yayi mata iznin zama, yana ƙureta da idonsa, ta fito da kayan aikinta, ta fara saitawa, tana ta
addu'a a zuciyarta, dan kaɗaicewar nan ta su kawai, hankalinta a tashe yake.

Nabila kuwa, Walid sakata yayi a gaba, har suka zo ƙofar wani gida, a can bayan
kamfanunukan nan, babu kowa a wurin, ba gida gaba babu a baya, sai ma wani uban dutse
idan ka yi tafiya can gaban gidan, ba ta taɓa zaton akwai irin wannan wurin a kano ba.

Ya kalleta ya ce ta shiga.

Jikinta yana rawa ta ce ba zata shiga ba, sai dai ya kira wo mata shi nan waje, wanda har a
lokacin idan ta ganshin, ba ta san me za ta ce masa ba, tsabar fitina ce da son ta ɗaukaka ko ta
halin ƙaƙa ya sanya take wautar.

Wani makami ya zare mata, mai kama da kibiya ya buga mata tsawa ya ce "Ki shiga na ce" sai
a lokacin ta tabattar da ta tafka babban kuskure, haɗi da wauta mara amfani, idan suka illata ni
fa?" Ta tambayi kanta cikin tashin hankali, haka ta shiga, yana bin ta da wuƙa.

Ɗan mama yana ɗan matsakaicin tsakar gidan, yana wankin kayansu, jin kukan mace ya sanya
shi ɗaga ido, cikin tsananin mamaki.

Sai dai yayi wata irin zabura ya ja da baya, yana bin su da kallo.

Yana cikin ɗaki a tsaye ƙyam, kamar an gina shi, ya bawa ƙofar baya, yana kallon bango. Ya
sha ya bugu, amma bai samu yadda yake so ba, tunanin da yake son dainawa ya kasa, dan
haka yana tsaye, yana ta nazarin abubuwa daban-daban a cikin ransa.

Ɗan mama biyo su yayi, yana bin Nabila da kallo.

Turus Nabila ta yi, duk da ba ta ga fuskarsa ba, amma yanayin suffar jikinsa, sai da ta ji tamkar
ta zunduma ihu, kallo ɗaya zaka yi masa ka san madakin maza ne, ingarman namiji ne, da
Allah ya yi shi da tsawo da kuma kakkauran jiki.

Idonta ya sauka a kan miyagun makaman da suke ɗakin, kamar za aje yaƙin duniya, gefen
katifar da take ɗakin kuma, sirinjai ne, da kwalaban allura a wurin, sai kuma satchets na
magunguna da kwalabe da kwalayen sigari. Ban da warin sigari, da wani irin ƙauri da ba ta
gama tantance ko na menene ba, babu abun da yake tashi.
Tirƙashi! Ai ko lokacin da aka rufta ta, aka turata dabar madaki, ba ta ga abun da ya razanata
ba, kamar yanzu ba, dan tarin ƴan dabar da ta tarar na su wasa ne, ba su firgita ta ba, tun da ta
samu ƙwarin gwiwar yi musu magana.

"Boss, ga ta na kawo maka ita, sai ka ji dalilin da ya sa take nemanka"

Babban abun da ya ƙular da Viper, bai wuce watsi da umarninsa, da Walid yayi ba, tun da fari
ya gargaɗe shi, a kan kawo masa wata mace, dan ba shi da alaƙa da su, amma ya yi burus da
maganar sa.
Kasancewar ya sha sai dai buguwar ta gagara yadda yake so, ya sanya ƙwayoyin suka taimaka
wurin tunzura shi, ya waiwayo a fusace domin ya sauke wa Walid rashin mutunci.
Sai dai gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa, adadin bugun zuciyar sa ya ƙaru da sauri da
sauri, wani irin gumi ya fara tsatstsafowa ta kafafen gashin sa, jijiyoyin jikinsa suka kukkumbura.

Shi dai ya san a farke yake, ba iya bacci yake mai nauyin da zai ɗauke shi, har ya sa shi
mafarki yake, balle ya ce mafarki ne, kuma ya san a hayyacinsa yake, domin kuwa bai yi
buguwar da hankalinsa zai gushe ba.

Sai dai a zahiri, sam yanayin sa bai nuna irin halin da ya shiga ba, dan babu abun da ya canza
a tattare da shi, ya zuba mata manya-manyan jajayen idanunsa.

Tirƙashi! Jin ka ya fi ganinka! Nabila za ta iya cewa, tun da Allah ya sa ta buɗi ido a duniya, ba
ta taɓa ganin mutum mai kwarjini da razanarwa kamarsa ba, kodayake ai ya wuce ta kira shi
kwarjini, sai dai mai ban tsoro.
Yadda ake faɗarsa a baki kawai, ta ɗauka wani ƙaramin alhaki ne kawai, sai dai yanzu ta
tabattar da  ya wuce duk yadda ta yi tsammanin ganinsa sa.

Ashe waɗanda take gani ƙaryar daba suke yi, ga ɗan daba na gaske yau ta gani,kamar ta fashe
da kuka a cikin zuciyarta ta ce "Na shiga uku, wani tsautsayin ne ya kawo ni? Daga ni sai su
idan suka kashe ni fa? Na san ko gawata ba za a gani ba, balle ayi mini salla, kamar yadda
addini ya tanada" So take ta ɗaga ido ta kalle shi, amma abu ya gagara, saboda daga kallo ɗayan da ta yi masa,

ba ta fatan sake yi masa na biyu, duk da zuciyarta na azalzalar ta, ta sake yin hakan, ba zata
iya tantance abun da take gani a cikin idanuwanta ba, da kuma ma'anar irin kallon da yake yi
mata ba.
Ƙoƙarin sake satar kallonsa tayi, amma suka yi ido huɗu, tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa,
saboda mummunar faɗuwar gaban da ta ziyarci zuciyarta, tabbas cikakken mashayi ne duba da
yadda launin idanunsa suke, sai dai Allah ya yi shi da siffar girma da cikar zati, ya isa a kira shi
da cikakken namiji. "Shi kuwa wannan meya haɗa shi da aikin daba, a irin ƙira da Allah ya yi masa, da aikin office
ya dace, ko na tsaro, ya ɓata wayonsa, da ya ƙare a shaye-shaye da daba.
Duk da ta sunkuyar da kanta, a tsakiyar ƙirjinta take jin kallon da yake yi mata.
Walid ya zagaya saitin kunnensa ya ce "Ka ga abun da nake gaya maka?"

Jinjina masa kai kawai yayi, taku ɗaya yayi, ba tare da Nabila ta ankara ba ya danƙi wuyanta.

Ba wani riƙon kirki yayi mata ba, amma idanuwanta suka yo waje, jikinta ya hau kyarma, tamkar
ana kaɗa mata gangi.
Ta saka hannunta ta riƙe nasa, numfashinta na fita da sauri da sauri, cike da tsoro take ta
gwagwarmayar ƙwatar numfashinta, saboda yadda take jin yana barazanar barin ƙirjinta.
Ba ta ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da ta ji tsini a cikinta, ga wani irin azababben zafi da ya
ratsa fatar cikinta.

Ba ta san bata tsorata ba, sai da ya buɗe baki yayi magana.

"Wacece ke? Me ki ke nema a wurina?!!"

Numfashinsa ya sauka a fuskarta, warin sigari ya daki hancinta, jikinta ya hau tsuma.

A rikice Walid ya ce "Boss zaka kashe ta fa, ka kalli abun da ka ke yi"

Bai saurari walid ba, ya sake buga mata tsawa, tare da ƙara nutsa wuƙar da ya saita a cikinta.

"Viper, jini ya fara zuba daga cikinta, ka dawo hayyacinka mana" yayi maganar yana ƙoƙarin kai
hannu ya ƙwace wuƙar hannunsa.
Idan ka taɓa ni, kai zan cakawa!" Yayi maganar yana kallon idon Nabila da suka yo waje, ga
jikinta ya saki, sai numfashi da take yi da kyar.
Buɗe baki tayi, da niyyar ta yi magana, amma jikinta ya saki, ta daina ganin komai sai duhu.

"Viper kar ka kashe yarinyar nan" Amma kan walid ya yi wani yinƙuri, Viper ya watsar da ita a
wurin, ta faɗi sumammiya.

Ayshercool
08081012143
                 *ƘARFE A WUTA*





AISHA ADAM AYSHERCOOL




Arewabooks : ayshercool7724
Watpad: ayshercool7724
What's app :08081012143

What's app channel
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Paid book ne ₦500 via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda ba ss som group akwai special 1k.




13

Cike da takaici Walid ya nufeta da sauri, ya kalli Viper ya ce "Amma meyasa zaka yi haka? Da
ka kasheta fa?"

Aminu ya kalli saman tsinin wuƙarsa da take ɗauke da jinin Nabila, bai kalli Walid ba ya ce "Ban
gaya maka kar ka kawo mini kowa ba?"

Walid ya ce "Ka gaya mini, amma na tabatta ka ga abun da nake son ka gani, ai ko?"

"And so, me hakan zai amafana mini? Ka ƙaddara ban ga komai ba, kuma gargaɗi na yi mata a
kaina, dole na san tana da manufar son haɗuwa da ni, wataƙila wata ƙulalliyar ce, sai dai
amafani da mace ba zai hana in illata ta ba, idan ta shiga gonata"

Walid ya ce "Yanzu abun da ka gani, ba shi da muhimmanci kenan?"

"Ko kaɗan" ya bashi amsa kai tsaye.

Walid ya tsuguna a kanta, amma ya rasa abun da yakamata yayi.

Wani irin numfashi Nabila ta fara fitarwa, mai sauti wanda hakan yake tabattar da, numfashin
yana ba ta wahala.

Ɗan mama ya ce "Mun shiga uku, wane irin numfashi ne wannan,ko mutuwa za ta yi ne?" Walid
ya sake dirircewa ya rasa abun yi.

Viper ya goge jinin Nabila da ke jikin wuƙarsa, a jikin rigarsa.

Ya ɗaga kai, yana kallon yadda take jujjuya kanta, tana neman iska.

Wata drower ya saka mukulli ya buɗe, ya ɗaukko wata ƴar ƙaramar akwati, ya ajiye, ya ƙarasa
ya ɗauki jakar Nabila, ya zazzageta yana neman inhaler, amma bai gani ba, ya ja uban tsaki ya
tashi, ya sake buɗe wardrobe, ya ɗaukko inhaler, sai dai sai da ya tsaya yayi ta kallon inhaler,
yana kallon Nabila, sannan ya ƙarasa kanta, ya tsaya, ya ɗagota ya fesa mata a cikin bakinta.
Kamar zata haɗiye inhaler, haka take sake buɗe bakinta, ya mayar da ita ya kwantar, ya ɗaga
gefen rigarta, da wuƙarsa ta huda, ya saka auduga da spirit, ya goge jinin tsaf, ba wata huda ce
ta kirki ba, kawai dai ta zubar da jini ne sosai.

Gaba ɗaya suka zuba masa ido, ya zuba iodine a jikin audugar, ya saka a kan cikin nata, ya
kawo plasta, ya saka.
Dama ya saba yi musu dressing, idan suka je aka sare su, a wurin rashin jin su.

Ya mayar da akwatin in da take, ya koma gefe ya kunna sigari. Mamaki yake da tunanin, uban
me take nema a wurinsa, sai dai ya fi yarda da cewa, tarko ce ake son yi masa da ita.

"Amma ya aka yi, aka samu wannan coincidence ɗin?" Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.

Duk suka koma gefe, suka zubawa sarautar Allah ido.

Tari ta fara yi, ta yinƙura ta tashi zaune, ta kalli kayan cikin jakarta, da suke a watse, ta fara
tattara abun ta, sai kuma ta dawo hayyacinta,bayan da suka yi ido huɗu da shi.

A rikice tayi jifa da jakar, ta ƙwala wani uban ihu, nan take mafarkin da ta taɓa yi ya dawo mata,
tabbas sai yanzu ta fuskanci inuwarsa take gani a mafarki.

Ƙoƙarin tashi take ta gudu, cikin zafin nama, ya bar in da yake ya cafkota.

Tausayinta ya kama Walid, tare da dana sanin kawo wa Viper ita, ko haɗa bakin aka yi da ita a

cutar da shi, atleast ita macece ya ɗaga mata ƙafa, amma ya san in da ya matsa, sai Viper ya
illata ta fiye da yanzu.

"Waye ya aiko ki?" Yayi maganar a kausashe.

Ta girgiza kai, amma ta kasa magana.

"Waye ya turo ki na ce?" Yayi mata tsawa.

A rikice ta ce "Wallahi ba kowa" tayi maganar tana zubar da hawayen tsoro.

"Me ki ke nema a wurina?"

"Dan Allah ka yi mini rai, na tuba na bi Allah, ba zan sake ba, dan Allah kar ka kasheni, wallahi
ni marainiya ce, tayi maganar tana kawar da kanta gefe, ta kasa kallonsa, sai azabar bugu da
zuciyar ta take yi, cikin tsoro da fargaba.

"Look up kalleni" muryarsa ba a iya kunnuwanta take jin ta ba, a tsakiyar zuciyarta take yi mata
amsa kuwwa, gashi ya matso daf da ita, warin sigarin da

17 / 19