Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Karfe a Wuta Book 1 Complete Complete Hausa Novel by Aysha Cool

Author :  Aysha Cool Category :  Romance

Chapter   10 / 19

27K to 30K   out of 54.3K words

na tafi na
bar gidan nan, na gaji Allah ka amsa mini dan girmanka, kowane iri ne zan iya zama da shi".

Can falo kuma, jikin Abba ne yayi sanyi, ganin arfa na kuka ya san akwai wani abu a ƙasa, dan
idan tayi laifi, wataran ko kasheta zai yi ba zata yi kuka ba, duk da tana da saurin kukan.

Ya kalli Anty ya ce "Zainab je ki duba yarinyar nan, kar ciwonta ya tashi"

Anty ta jinjina kai, ta bi bayan arfa.

Mama kuwa a sashinta take yi wa Siyama mitar meyasa ba ta yi wa Nabila dukan da za ta kasa
tashi ba.

"Mama kin san yarinyar nan har aljanu take yi, haka kurum su tashi ni ta kashe ni, komai ta
rarumo buga mini take yi, ba ki ji kafaɗuna ba"

Mama ta yi ƙwafa ta ce "Na rasa yadda zan yi maganin yarinyar nan, wallahi bana sonta ba na
ƙaunarta, gaba ɗaya ba kwa gaban mahaifinku sai ita, in sha Allah sai ta zame masa masifar da
ba zai iya shawo kanta ba, sai ta kwaso abun kunyar da za ta kunya ta shi a idon duniya".

Nabila kuwa ƙin saurar anty ta yi, ta sha uban kuka, Anty ta sanarwa Major kukan da take yi, ya
basar kamar bai damu ba, amma ƙasan zuciyarsa sam babu daɗi.

Tsakar dare suke waya da sumayya, take gaya mata abun da ya faru.

Sumayya ta ce "Arfa, ke rashin haƙuri ne yake janyo miki wasu abubuwan, da kin yi haƙuri ba ki
tanka mata ba, dama neman magana ta zo yi".

"Sumayya kin san ba zan iya ba, ni ina wulaƙanta mutane ne?"

Sumayya ta ce "A'a idan na ce kina da wulaƙanci Nabila na yi miki sharri, sai dai masifa da
rashin haƙuri, ga jarababben taurin kai ba a gaya miki ki ji ko kaɗan"

Nabila ta ce "Sai dai ayi haƙuri da ni a yadda nake, ni ba zan yadda da wulaƙanci ba"

"Aikuwa zaki yi ta shan wahala dan ubanki"

Nabila ba ta damu da zagin da sumayya ta yi mata ba, domin idan da sabo ta saba, dan wasu
lokutan sumayya playing role take yi kamar na uwa a rayuwarta, ta kan ji maganarta idan ta ga
dama.

"Sumayya dan Allah ki yi mini addu'a, Allah ya bani miji kowane iri ne, in dai zai zame mini
alkhairi a shekarar nan na bar gidan nan na huta"

Sumayya ta ce "Ba ki da hankali, kowane iri fa ki ka ce"

"Eh, wallahi idan ba haka ba, zan gudu na bar garin nan, na bar musu gidan, sumayya baki san
me suke yi mini ba na gaji" ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa tana kuka.

Sumayya ta san komai, dan haka cikin rarrashi, ta kwantar da murya, ta din ga yi wa Nabila
nasiha, da rarrashin ta, har ta sassauta kukan da take yi.

Da haka suka yi sallama, ta kwanta bacci.

Sai dai ta kasa baccin, saboda yadda zuciyarta take zafi, ta rasa me ta tsarewa maman su
Sauda a rayuwa, da ita da yaranta suka tsaneta haka, Nasir ne kawai suke ɗasawa da shi, da
ƙyar bacci ya kwashe ta.

Da safe ta shirya cikin wata abaya baƙa, tayi kyau ko karyawa ba ta tsaya yi ba, ta fito falo
fuskarta babu walwala.

Kallo ɗaya zaka yi mata, ka san ba ta samu isasshen bacci ba.

Da kamar ta yi fuska tayi tafiyarta, amma ta haura benan Abba ta je ta gaishe shi, sai dai
fuskarta babu annuri, babu raha da ta saba yi idan ta je gaishe shi.

Ya ƙura mata ido ya ce "Kin karya kuwa?" Ta ce "Idan na tsaya karyawa zan makara, zan karya
a wurin aiki"

"Dan zaki makara sai ki fita ba ki karya ba, yaushe ki ka fara tsoron makara? Menene ma ya
hana ki tashi da wuri?"

Tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta, idonta yana cika da hawaye.

Ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro kuɗi masu yawa, ya miƙa mata ya ce "Ga wannan na san
wata yayi nisa, babu lallai ki na da kuɗi a hannunki, ki sai wani abun idan kin je ki karya, saura
ki sai abun da zai ɓata miki ciki, ko ya cutar da lafiyar ki"

Kamar ta ce ya bar su, amma ta saka hannu biyu ta karɓa, ta ce ta gode, yanayin yadda take
tafiya kawai, zai tabattar mata da tana cikin damuwa ko rashin lafiya.

Gaba ɗaya jikin Abba ya yi sanyi, a tsakiyar zuciyarsa yake jin zafi, idan ya ga Nabila a cikin
damuwa, shiyasa wasu lokutan baya iya jure yi mata hukunci yake kawar da kai a kanta.

Duk iya ƙoƙarin da Nasir yake yi, a kan yaƙi da harkar daba, abu ya ci tura, dan yaran da aka
kama ya koma ya tarar da wai an yi umarni daga sama a sake su, abun ya ɓata masa rai sosai
da sosai.

*****
A farfajiyar wata bishiya suke zazzaune, suna ta shaye-shayen kayan maye, duk sun cika wurin
da ƙaurin hayaƙi.

Madaki ya karta wuƙa a ƙasa, ya kalli tarin matasan da sun fi ashirin a gabansa ya ce "Babu
rangwame ko sassauci, babu mace babu namiji, ko babba yaro ko tsoho, duk wanda aka samu
idan aka shiga operation ɗin nan a farmasa, ayi ɓarna ayi ta'adi a ɗauki fansar abun da Aminu
yayi mana, jini ya din ga gudana ko ta ina, duk shagon wanda aka samu a fasa ku kwashi
ganima, na yarje muku.
Haka zalika duk wanda ya gano in da Viper yake, muddin ya kawo mini shi, a mace ko a raye,
akwai tukuici mai tsoka"

Suka fara shewa cike da maye, ɗaya daga cikin su ya ce "Aminu fa ƙarfe ne a wuta, duk
wannan shewar kama shi ba abu ne mai sauƙi ba, da mai sauƙi ne na san da ka riga mu kama
shi"

Madaki ya ce "Rufe mini baki, ko na yi gunduwa-gunduwa da namanka, dole ne a kama shi, kai
gobe duk wanda aka gani daga tsallaken unguwar su, ya shigo unguwar nan ma a sara mini shi
kawai, a ɗauki fansa mafi muni na abun da ya yi mana, zan ga da ni da shi, waye zai sarara
waye gaba da wani"

Cikin haɗa baki suka dinga faɗin "An gama oga, gobe akwai ƙaramin yaƙi"

misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe, a sannu take tafiya a cikin unguwar, tana duba
kwatancen da barrister Habib ya tura mata.

Kasa ganewa tayi, ta tsaya a wurin wani mai kanti, ta sayi ruwa ta sha, kuma tambaye shi.

Tana tsaye tana duba wayarta a cikin shagon provision ɗin, wani matashi ya shigo, suka gaisa
da mai kantin ya ce "Bani ƙulli biyu da ruwa uku"

Mai kantin ya ce "Amma ka san ina binka sauran kuɗi ko?"

"Zan biyaka, wannan yawa ne, ka bani na ware mana, caji zan yi kaina gaba ɗaya babu
network,aljihuna kuma yayi gobara"

"Ba zan bayar ba" mai shagon yayi maganar yana miƙawa Nabila ruwan roba.

Nabila ta din ga satar kallon matashin, yadda bakinsa ya karkace saboda shaye-shaye take
kallo, laɓɓansa duk sun zazzago.

Tayi gyaran murya ta ce "Ɗan uwa ka bashi mana, tun da ya haɗaka da Allah, in sha Allah zai
kawo maka, tun da ya yi alƙawari"

"Rabu da shi, ba ya biyan bashi"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Nawa ne kuɗin nasa?"

Mai kantin ya ce "Dubu biyu nake bin sa"

Ta yi murmushi, tare da ciro kuɗi a jakarta ta ce "Dubu biyu ai babu yawa, Ga dubu uku, na biya
masa kuɗin da ka ke bin sa, ka bashi wani bashin, ni kuma ka ɗauki kuɗin sayayyata"

Matashin ya kalleta ya ce "Sai kin yi babbar yaya, Allah ya ƙara arziki"

Ta amsa da "Amin ɗan uwa na gode sosai".

Wani abu ta ga an bashi a nannaɗe a leda, da ruwa ya sake yi mata godiya, ya fice.
Yana fita ta ce "Malam dan Allah menene wannan ya saya?"

Mutumin yayi murmushi ya ce "Ƙanwata wiwi ce" waro ido ta yi ta ce "Wiwi kuma, ka ke
sayarwa? Amma na ga kai kamar ba ka sha ko?"

"Ki yi ƙasa da muryarki mana, ya zamu yi sana'a ce, ni ba abun da nake sha. ga canjinki"

Cikin mamaki ta ce "Meyasa ka ke sayar da abun da ba ka sha?"

"Kar ki tsananta bincike malama" yayi maganar yana haɗe rai. Ta jinjina kai ta ce "To Allah ya
taimaka"

Fitowa ta yi daga shagon, ta hangi matashin yayi nisa, ta rufa masa baya ta bishi da sauri.

"Bawan Allah ɗan tsaya dan Allah" ta ƙarasa tana haki.

Ya tsaya yana kallonta ya ce "Ya dai?"

"Abu zan tambaye ka, amma kafin nan ka san abun da ka saya ɗin nan, yana da illa ga
lafiyarka?"

Tsayawa yayi yana kallon ta, tayi saurin cewa "Dan Allah taimako nake nema, wani gida nake
nema, amma na kasa gane layin, ko zaka taimaka mini?"

"Ina ne?"

Ta gaya masa ya ce "Na san gidan, amma ba hanyar ki ka biyo ba nan"

"Dan Allah kwatanta mini"

"Mu je na kai ki bakin layin"

Ta ce "Yauwa ɗan uwa, dan Allah mu yi wata magana mana, ka san wani mutum Aminu Viper?"
Wani irin burki ya ci yana kallonta.

"Yi haƙuri idan na ɓata maka rai, ɗan uwana ne shi, tun da Allah ya sa ya bar gidan yari, bamu
sake ganinsa ba, kuma na ji an ce yaransa sun tayar da tarzoma a unguwar nan a satin nan,
dan har asibitin da aka kai waɗanda aka yi wa rauni na je, na zaci zan ganshi, amma ban tarar
da shi ba"
Ya ware mata jajayen idanunsa ya ce "Ki ka ce ɗan uwanki ne?"

Cikin ƙarfin hali ta ce "Eh, ina da alaƙa da shi"

Ya ce "Na san shi, na kuma san in da yake"

Da sauri ta ce "Dan Allah ka taimaka mini a ina zan ganshi?"

Ya ƙare mata kallo ya ce, idan kin tashi, ki tambayi ina ne layin iraƙi a unguwar nan, idan ki ka je
akwai wata babbar bishiya zaki ga wasu a zazzaune a wurin, ki tambaye su, za su nuna miki
shi.

Cikin tsananin farin ciki, ta din ga yi masa addu'a. Amma fa sai dai ta kasa tantance irin kallon
da yake yi mata, hakan bai dame ta ba.

Har ƙofar gidan matar ya rakata, ta kuma yi masa godiya, ta ciro kuɗi ta bashi, sannan ta shiga
gidan matar.

Matar ta karɓi Nabila hannu bibbiyu, bayan da Nabilan ta yi mata bayanin barrister Habib ne ya
turo ta.

Ta bawa Nabila duk wani information da take buƙata, tana gama abun da take yi ta tashi ta ce
tafiya za ta yi.

Babu yadda matar ba ta yi da ita ba, a kan ta zauna ta ci abinci ta yi salla, amma taƙi, ta tashi ta
tafi.

Babu tunanin komai, tana fita, ta tambayi wasu yara, ina ne layin iraƙi?.

Duk sai da suka kalleta, ganin tana mace tana tambayar wannan layin da ƴan daba suka mayar
mallakinsu, abunka da yara, babu tunanin komai suka sakata a hanya, ta yi musu godiya ta nufi
kwatancen.

Tana ta addu'a Allah ya sanya ta dace, duk tana da burin cikar nata muardin, amma za ta yi
farinciki sosai idan aka ce Nasir ne yayi nasarar kama Aminu, koba komai likkafarsa za ta sake
ɗagawa, ta nufi layin ba tare da ta san idan ta ganshin me za ta ce masa ba.

Layin shiru babu kowa, babu gina-ginan kirki, sai kangwaye, sai da ta je tsakiyar layin, ta hango
wata ƙatuwar bishiya, da mutane.

Kamar ba mace ba, babu razani ko fargaba ta tunkari bishiyar.

Gaba ɗaya suka zuba mata ido, har ta ƙaraso.

Wiwi kawai suke busawa, ta ɗan tsaya nesa kaɗan da su, saboda hayaƙi.

"Ina wuninku"

Suka amsa mata da lafiya ƙalau, suna mamakin ganin mace a wannan chamber.

"Dan Allah tambaya nake yi, wani nake nema, aka yi mini kwatancen nan aka ce zan sameshi".

Ɗaya daga cikin su ya ce "Waye shi?"

Ta ce "Amm, sunansa Al'amin, amma ana ce masa Aminu Viper, tun da ya fito daga prison ba
mu sake ganinsa ba"

Ɗaya ne ya miƙe tsaye ya ce "Ke, ba ki da hankali, a dabar madaki ki ke naman wannan ɗan
iskan? Kai kan taba, sako su mass su rakata, tun kan oga ya zo ya saka ayi gunduwa-gunduwa
da namanta"

Sai yanzu ta fuskanci shigo-shigo babu zurfi wanda ya yi mata kwatancen ya yi mata.

Cikin sauri ɗaya ya ce "Meyasa za'a bari ta tafi? Bayan ka san yau zamu fasa ɗaukar fansa, ta
kanta ya kamata mu fara" yayi maganar yana ƙoƙarin zare makami.

Sai dai tuni suka sako wa Nabila wasu irin murguza-murguzan karnuka, masu kama da zakuna.

Cikin ihu ta kwasa da gudun tsiya, tana kururwar neman agaji, saboda yadda take ganin kamar
karnukan za su cinyeta ɗanya, sai dai gudun da suke yi ya wuce hankali, ga takalminta mai tsini
ne sosai, dan haka suka kusa cimma ta.

Babu tsammani ta faɗi, saboda yadda numfashinta ya fara sama-sama.
Ayshercool.
08081012143
[7/22, 1:49 PM] null:               *ƘARFE A WUTA*

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

P8

Ta saka hannu, ta kare kanta, tana jiran su hauta da cizo.

Wani irin fito ya yi wa karnukan, suka juya suka koma da gudu in da yake.

Matashin nan ne na ɗazu, da ta biyawa bashi, ya kalleta ya ce "Kin san meyasa na taimake ki?"

Bai jira amsar da za ta bashi ba ya ce "Ba na tunanin Aminu yana da wata ƴar uwa mace, dan
haka ƙarya ki ke yi, akwai wata manufa a ranki da yasa ki ke nemansa. Sannan ya taɓa yi mini
alfarma a lokacin da ya samu damar da zai kashe ni, kuma kin kyautata mini, alhalin baki sanni
ba. Ɗan daba ba mahaukaci bane ba, shaye-shaye ne yake ruɗa mana tunani.

Wannan shi ne kaɗan daga abun da ka iya samunki, idan ki ka cigaba da neman sa, ko
bibiyarsa, wannan dabar babu abun da suke buri da fata, sama da su riga ƴan sanda kama
aminu, mace ce ke ki kiyaye kanki, tashi maza ki tafi gasu can tahowa, idan suka cimmiki babu
lallai na iya hana su illata ki"
Da ƙyar ta tashi, ta yi gaba da sauri, tana cigaba da haki, adaidaita sahu ta hau, ta yi masa
kwatancen in da zai kai ta.

Kasancewar mai rabon shan duka, baya jin bari, suna tafe tana sauke numfashi, tana tunanin
son sanin su kuma waɗan nan me yayi musu suke son su riga ƴan sanda kama shi, suna ƴan
uwansa ƴan daba.

"Ko wani ya kashe musu?" Ta tambayi kanta.

"Yayi kisan kai, kuma a sake shi?
Aikuwa sai na ga ƙwal uwar daka" ta furta a hankali.

Ta so ta gaya wa Nasir, abun da ya faru yau, amma ta san tsaf zai ce zai zaneta, saboda
kasadar da ta yi, dan haka ta bar wa ranta cewa sai ta samu wata gagarumar nasara, sannan
za ta sanar da shi.

Ko sumayya ma ba ta gaya wa ba, tayi shiru da bakinta, sai dai faɗuwar da tayi, duk ta goge
gwiwa.

Haka kurum tausayi, da tunanin makomar rayuwar matasan da ta gani, a harkar daba da
shaye-shayen nan, ya dami zuciyarta ta rasa abun da yake yi mata daɗi, tana matuƙar son
sanin me suke ji a cikin kayan shaye-shaye? Tabbas da ita wata ce, sai ta taimakawa rayuwar
su, ko a mutum goma, idan biyu suka shiryu ai an rage.
Kamar wadda ta sha kayan maye, haka yau tayi bacci da wuri, gudun da tayi jikinta duk ciwo
yake yi mata, ga numfashi sai wahala yake ba ta.

A wani ɗaki ta ganta, mai duhu sai haske kaɗan a ciki, ga karnuka duk a cikin ɗakin, sai haushi
suke yi mata, an ɗaure su da sarƙa.
Ihu take yi tana neman agaji, amma babu wanda ya san tana yi.

Can sai ga wani mutum ya shigo, dogo sosai, mai cikar halitta, ba ta ganin fuskarsa saboda
duhu, ya shigo ɗakin bai ce mata uffan ba, ya danƙo hannunta ya biyo tsakanin karnukan ya fito
da ita daga ɗakin, ya ciro wuƙa zai caka mata a ciki.

Wani uban ihu ta saki, tana kiran sunan Allah, da na Abba da Nasir.

Tana buɗe ido, ta ga Abba a kanta, da Nasir, da su walida har da Anty da baba magajiya, ana ta

tofa mata addu'a.

Kallonsu take yi ɗaya bayan ɗaya, ta ce "Abba ya na ganku a nan? Meyafaru?"

Nasir ya ce "Sannu"

Abba ya ce "Arfa ba kya addu'a ko?"

Ta girgiza kai ta ce "Ina yi Abba"

"A'a ba kya yi, da kina addu'a babu yadda za ayi, ki kwanta kina yi mana ihu da safiyar nan,
shiyasa nake hanaki wannan shegen fentin da bulbula turare a jikinki, dole sheɗanu su yi ayari,
su yi ta binki"

Nasir ya ce "Dan Abba ka yi haƙuri, haryanzu a tsorace take ma, a bari ta dawo hayyacinta
gaba ɗaya, sannu Arfat, ki ɗauro alwala ki zo ki ɗauki Alqur'ani ki karanta".

Abba ya miƙe ya ce "Aishikenan, zan yi waya da Barrister, su baki day off, ki samu ki huta"

Nabila ta yi shiru tana rarraba ido, ta san lafiyarta ƙalau, tsabar tsorata ne da

10 / 19