Author : Aysha Cool Category : Romance
ba ko?" Ta tsaya suka gaisa da admin ɗin da ke
reception, sannan ta ƙarasa kusa da Sumayya ta zauna.
"Arfa, ya na ganki yanzu ne? Lokacin tashi daga aiki bai yi ba?"
"Kema ya na ganki a nan kamar mara galihu, ke baki da office ɗin da zaki zauna ne? Ki zo
chambermu ki ga ofishin da aka bani hajiya, kamar wata sarauniya"
Sumayya ta ce "Eh ofishin da baki damu da aiki ba ko, sai sun dawo da ke gadin chamber
tukuna".
Nabila ta yi dariya ta ce "Kin san wani abu, wai nan aikena aka yi, zan je na lallaɓa na zo da
wata mata, ko in tattauna da ita, sannan in je shagari firm, zan haɗu da wani lawyer, kuma ni
wallahi kaina ciwo yake yi"
Sumayya ta kalleta ta ce "Ba zaki ba kenan?"
"Ai faɗa ma ɓata baki ne, sumayya wurin nan naku mai kyau, tashi ki rakani na zaga" duk da
ran sumayya babu daɗi, amma ganin Nabila ya sanya ta jin sanyi a zuciyarta.
Suka shiga zazzagawa, ta kaita news room, sai dai su na buɗewa suka tarar da MD da lawisa a
ciki, suna aiki.
Sumayya ta risuna ta ce "Am sorry sir, ban san ku na ciki ba, Arfa mu je ki ga....
"A'a tsaya mana na ga nan ɗin, Nabila ta shiga cikin fara'a ta ce "Yallaɓai ina wuni?"
Shima cikin fara'ar ya ce "Lafiya ƙalau, ya ki ke?"
"Lafiya lau sir, ina fatan ba zan takura muku ba, ina son sanin abubuwan da ban sani ba a
rayuwata, mussaman wanda ba field ɗina ba, sister ina wuni?" Tayi maganar tana kallon lawisa
da ta yi bala'in haɗe rai.
Lawisa ta takurawa Sumayya ne, saboda tana ganin ƴar gayu ce, ga ta baƙa amma baƙinta mai
kyau ga ƙwazo, tana gudun ta ƙwace mata matsayin ta, kuma ita bazawara ce, a da a wurin
babu wanda ya kaita gayu a wurin, amma yanzu sumayya ta fita.
Yanzu kuma ga Nabila, ita da take da hasken fata ma sosai.
Nabila ba ta san lawisa ta amsa ko ba ta amsa ba, ta ja kujera ta zauna, tana yi wa MD
tambayoyi, a kan abubuwan da suke cikin news room ɗin.
Lawisa ta ƙulu,ta din ga harar Nabila, amma ko a jikinta, ita kanta sumayya sai da haushi ya
kamata abun da Nabilan take yi.
Nabila ta ce "Yallaɓai, ko zaka saka mini lambarka, idan wani abu ya kama na aiki, zan iya
taimakawa i am barrister Nabila Yusuf"
Ya ce "Wow, what a very young and beautiful barrister, kin zama lawyer da ƙananan shekaru, ya
karɓi wayar Nabila, ya saka mata lambarsa, ta tashi ta yi musu sallama.
Sumayya kamar ta yi bindiga, su na fita ta din ga ɗurawa Nabila ashar, a kan abun da ta yi, tare
da gaya mata alaƙar Lawisa da kuma MD.
Nabila ta ce "Sumayya, dan Allah kar ki ɓoye mini, idan yana da kuɗi na ci rabona, na ga zai yi
son mata"
Ganin Nabila na neman mayar da ita mahaukaciya, sai ta canza maganar.
"Ke kin san menene? wai ni zan kai rahoto har kashi biyu, sakaryar matar nan ta ce ba za a
saka ba, wai ba sa buƙatar irin wannan labarin, MD ya tambayi me nake yi a reception ba na
aiki, wai ta ce masa ban iya aiki ba, na rasa uban da na tsare mata ta tsane ni, dama ni na
samu damar da ake baki, a wurin aiki, in yi wata shida ina aiki a wurin, wai ban iya aiki ba, da
yake kwanan nan ya dawo daga ƙaro karatu, tun da aka ɗaukemu ya tafi".
Maimakon Nabila ta tausaya mata, sai ta hau dariya, "Ai kawai ki fara soyyaya da MD ko ta
bala'i, shi ne zaki rama".
Sai da ta ga Sumayya ta yi fushi sannan ta ce "Sorry my sumy, maganar gaskiya babu daɗi,
kuma kishi take da ke kuma tana ƙoƙarin kare abun da take so, shikenan"
Idon sumayya ya tara hawaye ta ce "Sai kuma ta din ga daƙile ni a harkar aikina? Ta yi mini
adalci kenan?"
Nan ta ba wa Nabila labarin abun da ya faru, daga fitowarta daga gida, zuwa yanzu.
Nabila ta ce "Na shiga uku, sumayya me ƙasarmu ke son zama ne? A zahiri an nunawa mutane
ana neman mai laifi, a baɗini kuma hukuma na ɓoye shi? Duk yadda ake fama da ƴan daba da
masu ƙwace a garin nan, tirƙashi ana maganin ƙaba kai yana daɗa kumbura, ke ba ki san
sunan wanda ya yi laifin ba?".
Sumayya ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, bai faɗa ba, korata ma suka yi".
"Mu ƙarasa titi mu tari napep mu je asibitin, mu tattauna da shi mutumin, ni kin san ba na tsoron
a mutu ko a yi rai. Sannan zan je na samu Yaya Nasir na yi masa maganar wannan ai abun
kunya ne"
Sumayya ta girgiza kai ta ce "A'a, na tsorata da kashedin da aka yi mana, a bar zancen kawai,
ban san suwaye mutanen ba".
Nabila ta ce "Wallahi sai mun je, akwai wata shashasha da ta isa ta hana ki cigaba a rayuwa,
idan ma ba a saka radiyo ba, sai mu kwatsa a media ina da mabiya sosai a social media, sai ayi
duk wadda za ayi.!!!"
Ayshercool
08081012142
[7/18, 2:10 PM] null: ⚔️*ƘARFE A WUTA ⚔️
*AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Page 4
"No Nabila, abun da ki ke yi is too risky, mutanen nan da gaske suke, they mean what they said,
kar ki jefamu a matsala"
Nabila ta ce"Karatunki ya tashi a banza kenan sumayya? Idonki har da hawaye saboda takaici.
Wasu lokutan kin fiye sokwanci sumayya, da ni ce da tuni na ci buhun ubanta".
Sumayya ta ce "Ni ce sokuwa ko? na gode amma ni ba zan iya kasadar da ki ke yi ba, na rasa
aikina, but wait mu je na rakaki in da aka aike ki mana"
Nabila ta ce "Wa? Taɓ tuni na kira MD na bashi uzuri, dama barrister Habib ne ya aike ni, yadda
wannan matar ta wurin aikinku take, lawashi ko lotion take, haka yake yi mini, ba ya ƙaunata"
"A'a, naki ya sha banban da nawa Nabila, shi taimakonki yake yi ai"
Nabila ta kwaɓe fuska ta ce "Ke, idan fa kin ga ina zuƙewa a aikin nan, wanda za a kare ba shi
da gaskiya ne, MD zan saka ya canza mini team daga na su Barrister Habib, na Barrister Bashir
nake so, wata zazzafar shari'a za su kara, shari'ar manya ce, a kan kuɗi, zuwa zan yi na sha
kallo, kuma an ce akwai yiwuwar na haɗu da masoyiyyata kwanan nan"
Sunayya ta ce "Wa kenan?"
"Anty Naja'atu Bunkure mana, kin san am die hard fan of that woman, Barrister Naja'atu duniya
ce, ga gayu malam, harshenta akwai turanci, kamar wadda aka haifa royal palace ɗin Elizabeth"
Sumayya ta yi tsaki ta ce "Aikin banza ƴar wahala, ita ta zama abun da ta zama a harkar aiki,
har tana burgeki, ke kuma kina zaune kina shashanci, wallahi ƙarshe ki koma ƴar ɗaukar
jakarta"
Nabila ta ce "Kan uba, degree holder in yi dakon jaka, Kin ci mutuncina fa,
Sumayya ta girgiza kai, haryanzu Nabila shirirta da yarinta na damunta.
Ko da Nabila ta je gida, tun a tsakar falo take tambayar magajiya, ina DSP.
"Bai dawo daga aiki ba, na ji ɗazu yana cewa ko za su je ringin"
Nabila ta ce "Aikuwa ya yi ya dawo, sun bayar da maza, in mun zauna ya yi ta cewa police ya fi
lawyer, yau zai sha kunya idan ya ji me suka yi. Yau zazzafan debate ne tsakanina da shi, har
lemo zan yi mana aji daɗin yin musu"
Anty ta ce "Ka ji mashirirciya, musun da za ku yi za ki haɗawa lemo?".
"Eh mana, ɗan sanda sharri, lawyer kuma musu" tayi maganar tana dariya.
Wani mugun kallo mama ta yi mata, yaran gidan nan har take suke yi wa Nasir da discipline
master, saboda yadda suke jin tsoron sa, amma tsakaninsa da Nabila sam ba haka bane ba,
suna good time sosai da Nasir, kuma duk gidan bayan Abba ba ta da abokin hira ko shawara
sai shi.
Nabila ta share mugun kallon da maman ke yi mata, ta tafi ɗaki.
Misalin ƙarfe huɗu na yamma, Sumayya ta ga kiran lawisa, kawai ta basar ta cigaba da kallon
tv, ta kira ya kai sau huɗu sannan ta ɗaga.
"Ki na ji ina kiran waya ki ka ƙi ɗagawa?"
"A silent take, bacci nayi ne".
"Ki tura mini recodings ɗin nan, su murtala ba su sami wani samo rahotanni masu muhimmanci
ba, kuma na ga su Mikiya radiyo duk sun wallafa labarin yaron nan, ki turo mini mu ga wanda za
a iya tacewa a saka" Sumayya ta taɓe baki ta ce "To"
Ta kashe wayar, ta ce "Allah ya ƙara, da mu muka fara sanar da labarin, kuma mu ka saka a
internet, ai da ya fi, tun da ni ce ƴar jarida ta farko da ta fara zuwa wurin, amma ki ka ƙi"
Ta lalubo lambar Nabila ta kirata, ta gaya mata abun da ya faru. Nabila ta ce "Amma baki da
wayo sumy, ke yanzu sai ki tura mata, saboda ba ki da zuciya?"
"To yaya zan yi mata?"
"To amma kin san ko kin tura mata, sunanta za ta faɗa a mai rahoton ko wanda ya karanta ba
ke ba ko?"
Sumayya ta ɗan yi shiru ta ce "Kuma fa haka ne"
"To tun wuri ki ce mata kin goge kawai, gobe ba za ta ƙara yi miki wulaƙanci ba".
Sunayya ta ce "Haka za ayi, na gode sosai" cikin hanzari ta kira Lawisa, ta sanar mata da cewa
ba ta ga recordings ɗin ba.
Aikuwa ta hau ta da bala'i, Sumayya ta danna recording tana dariya ƙasa-ƙasa da niyyar ta
turawa Nabila.
Bayan sun gama wayar, ta turawa Nabila, suka din ga dariya, Nabila na ƙara bata ƙwarin
gwiwar, kar ta sake ta ɗauki raini ko wulaƙanci daga wurin lawisa.
Ta kuma cigaba da lallaɓa sumayya, a kan lallai ta koma asibiti, ta sake tattaunawa da mutumin
nan, ko iya sunan mai laifin ta samo.
Barrister Habib ne ya shiga office ɗin MD, ya zauna suka gaisa, cikin takaici Habib ya fara
magana, "Barrister, ni fa na gaji da iskanci yarinyar nan, idan a team ɗi na za ta zauna, ta
zauna, kuma dole ta yi biyayya ga abun da na sakata, idan wurin Bashir za ta koma, ta koma na
gaji da iskanci da rashin mutuncin da take aikatawa, ba ta san aiki ba ko kaɗan"
MD ya ce "Calm down Habib, na sani wallahi, na san ku na haƙuri da ita, wallahi nima nauyin
mahaifinta nake ji ne, abun da yayi mini a rayuwa idan na kore ta ban yi wa kaina adalci ba, shi
ma yana yawan bani haƙuri a kanta, marainiya ce kuma ba ta da cikakkiyar lafiya."
"Mu ma duk marayun ne ai, waye yake iskancin da take yi? Ta zo lokacin da ta ga dama ta tafi
lokacin da ta so, she's not serious at all"
"Na sani, kuma nima ina gani, ka rabu da ita, duk wani abu da za ku yi ku daina sakata a ciki,
ƙyaleta da bashir ɗin, shi ne daidai da ita, ku yi haƙuri dan Allah" MD ya din ga lallaɓa Habib,
dan ba zai so rasa gogaggen lawyer kamar Habib a law firm ɗin sa ba, a kan Nabila da ba aikin
ne a gabanta ba.
Yau weekends ne, gaba ɗaya iyalan major na babbn falo, kowa ya ja nasa wuri yana karyawa,
Nabila ce kawai babu a wurin.
Tun yana jurewa ya kasa, yayi gyaran murya ya ce "Ina arfa ne?"
Anty ta ce "Bacci take yi"
Ya kalli walida ya ce "Tasota, ta fito ta karya, sai an cinye an bar ta, ta cikawa mutane kunne da
kuka"
Kusan mintuna goma da taso ta, sannan ta fito, kayan bacci ne a jikinta, dogon wando da
rigarsa har gwiwa, kanta babu ɗan kwali.
Nasir ya tsura mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi.
Abba ya ce "Ina kallabinki? Ki ka fito da wannan gashin ba kyan gani, kamar totuwar masara?"
Ta saka hular hannunta ta ce "Haba Abba, dan daga bacci na tashi ne fa"
"Tafi can ƙazama, kullum kai babu kitso, ba za a rasa kwarkwata a wannan gashin ba" dariya
aka hau yi mata.
Ko a jikinta, ta zauna kusa da Abba, ta kalli Nasir ta ce "DSP, yaushe ka dawo ba labari, ya
hanya?"
Ya jinjina kai ya ce "Alhamdilillah"
Major da kansa, ya taya Nabila haɗa shayi, ga soyayyen dankali, ga bredin ta, amma tana buɗe
bredin ta ce ba za ta ci ba, kwantai ne.
Major ya miƙa mata nasa ya ce "Duba zaki iya cin wannan? Dankali kawai ba zai riƙe miki ciki
ba" ta duba buredin Abban ta ce "Eh wannan sabo ne, Abba ka ƙara mini ƙwan, ni ba na son
dankalin ma"
Ya ce "To shikenan, ɗauki nawa da ma ni yanzu ƙwai bai dace da ni ba, a shekaruna"
Idan da sabo, sun saba da ganin irin wannan fifikon da major yake nunawa, duk da mutum ne
mai ƙaunar yaransa sosai da sosai, amma son da yake yi wa Nabila na musamman ne, amma
fa hakan ba ya hana idan suka yi laifi, ya hukunta su kamar ba ƴaƴan cikin sa ba.
Anty ta ce "Arfa ba zaki bari Major yayi ƙiba ba, kalli yadda ki ke tara mazaunai, saboda ci"
Yayi murmushi ya ce "Tafi kowa girma a gidan nan"
Nabila ta ce "Abba, Allah ya ƙara arziki, ka yi ta sayowa mu na ci"
"Amin arfan Abba"
Nasir ma ya juye mata nasa ƙwan, ta tattare tana dariya, dan ta na son ƙwai sosai.
Mama kuwa kamar za ta yi bindiga, saboda baƙin ciki.
Bayan an kammala cin abinci, su walida ne suka kwashe kwanukan da aka ci, Nabila kuma ta
hau labartawa Nasir, abun da ya faru da sumayya da ta je Asibiti.
Fafur Nasir ya ce ƙarya take yi.
Ta haɗe rai ta ce "Yaya, wai meyasa a duniya jami'an tsaro ba kwa yadda kun yi laifi, ko wani ne
daga cikinku yayi, sai kun ƙaryata, kun kare mutum"
"Wa ya gaya miki hukuma tana laifi?"
"Ba mutane ne hukunar ba? Ai mutane na laifi, kuma hukuma ma suna yi, wallahi da gaske
nake, ka bincika ka ji kuma, koma na kira maka sumayyan"
Ya ce "A'a ai ƙarya ki ke yi, ni zaki zauna kawai dan ki ƙure"
Duk yadda ta so, ta fahimtar da shi, amma ya ƙi fafur.
Abba dai kallonsu kawai yake yi yana dariya, ganin ba zai yarda ba, ya sanya ta ƙyale shi, ta
koma wurin Abba.
"Abbana" tayi maganar tana ɗan murmushi.
Abba ya ce "Kuɗi zaki tambaya kenan?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a Abba, abu zan tambaye ka"
"Ina jin ki"
"Abba dama, wata amarya ce, suka kira ni a waya, zan je gida na yi musu make up, ita da
ƙannenta na biki, za su biyani, VIP ne har gida"
Haɗe rai yayi sosai sannan ya ce "Me na gaya miki a kan wannan sheɗancin? Kin san na hana
ki sabgar banzar nan, ban da kalen sheɗanu jikinku, me wannan shashancin zai amafana miki,
na fuskanci kin fi fifita wannan kwalliyar a kan aikinki, to babu in da za ki je".
"Dan Allah Abba, wallahi zan samu kuɗi fiye da salaryna, dan Allah"
"Ba in da zaki, tun da babu abun da ki ka rasa a gidan ubanki, ba matar da zaki bi gida ki na
shafawa hoda, idan ta matsu tayi da kanta mana, banda shashanci ace mace ta zauna sai an
bita gida shafa mata hoda da gazar"
"Abba!"
"Shut up" yayi mata tsawa, hakan ya tilasata mata yin shiru.
Walida kuwa faɗan Abban dariya ya bata, wai idan sun matsu su yi da kansu, ba wadda za aje
gida shafawa hoda.
Nabila ta din ga jin ko a ɓoye sai ta je, tana son sana'arta ta kwalliya, Abba kuma ba ya so, wai
shashanci ne da fatan aljanu, ita kanta idan tayi a fuskarta wasu lokutan, ya din ga faɗa kenan.
Akwai ranar da za ta je biki, ta yi kwalliya ta saka eyelashes, ya kirata dan ya ga meya samu
idonta, gashin idonta yayi tsawo haka, tun da ta ce masa sawa tayi, ba ta ankara ba, ya saka
hannu, ya fige shi sai da ya haɗa da gashin idonta, ya ce ya kuma ganinta da shi sai ya zaneta.
Har a gaban saurayi, ya taɓa korata gida, wai ta je ta wanke fuskarta, ba za ta cuci ɗan mutane
ba, duk ta damalmala fuska da hauka, ta zama kamar wata bebin roba.
Ta rasa meyasa Abba yake adawa da sana'ar nan tata.
Nabila tun a weekend, take cigaba da zuzutawa Sumayya trial ɗin da za su je, kotu ranar
laraba, farincikin ta ya kasa ɓoyuwa, wanda hakan ya samo asali ne, da yadda ta ga Barrister
Habib ya ƙyale ta, ta koma team ɗin Bashir, kuma ta samu labarin barrister Naja'atu ma tana da
shari'a ranar a kotun, dan haka za ta haɗu da ita.
Nabila uniform ɗin ta, tamkar su yi magana, saboda ɗaukar guga, ita kanta a bar kallo