Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
ji sai ya gigice ya dauko akwatin first Aids ya fara yi min Dressing. Na karkace na zuba masa qarya na ce daga bene na sinbule na fado, sannan qonewar da ya gani a qauri na ce a wajen koyan girki ne mai ya zubo min tafasasshe.
Tambayata yayi a gigice "Haidar a bayanki kuma ku ka fadi tare?"
Na ce "Allah Ya sa a lokacin yana hannun Safiya."
Ya tausaya min matuqa ya yi min addu'ar samun sauqi da fatan Allah Ya kiyaye gaba.
Ba da qafarta na shiga daki ba, daukana yayi har kan gado. Ya hana ni tashi ko da Haidar ya farka daga barci shi ya dauko min shi na bashi mama ya sha ya koma barci ya karbe shi ya mayar da shi kan gadonsa.
Itin soyayyar da muka yi cikin daren har na manta rabon da in samu kulawa irin wannan.
Washegari da sassafe na gama shirya yara, sai na cika da mamaki da naga Usman ya shirya zai tafi aiki, ya tabbatar min da cewa ya ji sauqi sosai zai iya zuwa.
Sau biyu yana dawowa ya yi hugging dina duk a cikin qauna. Na raka su qasa amma da shirina tsaf, na goyo Haidar, na dauko wayata dan gidan Safiya zan shiga, yau akwai hira. Su na daga min hannu ina daga musu har suka fita.
Babu motsi ko alamar Mufidah a gidan nan duk da ma dai motarta na nan. Ba gidan Safiya na nufa ba bakin get na je wajen Tanimu. Da sauri ya taso ya kwashi gaisuwa, na tambaye shi cikin hikima.
Na ce " ina ta kwankwasa qofar makwabciyata Mufidah zan yi mata yaya jiki amma shiru babu ko motsinta."
Ya duqa ya ce " Hajiya ai tun jiya da daddare ita ma ta wuce da qatuwar akwati kuwa, da alama dai zata jima acan koma in ce ta tafi kenan. Dan na ji tana waya da Bar.Godwin tana cewa ya nemo mata wani gidan fa."
Sai na saki wani murmushi lallausa har Tanimu ya fara mamaki, sai na tuna na tsuke fuska na langwabe kai na ce "kash! babu dadi gashi har an saba kuma za ta tashi. Me yayi zafi haka?"
Tanimu ya ce " ba gulma ba, amma Hajiya kin san halin 'yan duniyar nan yadda suke, in suka shiga cikin mutanen da ba irin rayuwarsu daya ba sai su takura.Ta ga mazan na ku ne kimtsattsu,bata ma isa su kalle ta ba. Musamman oga Usman yana ganinta sai ya bata fuska. Kin ga ai dole ta ji gidan ya washe ta babu customers."
Amma na ji dadin labarin nan na Tanimu, na tuntsire da dariya, ban san lokacin da na miqa masa naira dubu daya daga cikin kudin cefanen da Usman ya bani yanzun nan ba. Dadi ya kama Tanimu godiya har da durquso.
Dr. Isa na hango ya fito da sauri da alama ya makara, Safiya ta rako su da sauri riqe da hannun Mus'ab zai tafi da shi makaranta, sai ga Halima ma ta shirya da alama ita ma tana da lacca dan ta fara zuwa jami'a bana.
Su ka shiga mota ya qaraso bakin get, Dr.Isa ya zuge gilashin mota ya gaishe ni. Gami da cewa "madam yaya qoqari? Jiya kun wuni a wajen seminar duk kin sa an gajiyar min da matata. Ta kwana tana ciwon jiki, next time ki kular min da ita sosai kada ta sha wahala irin ta jiya."
Ai shikenan ma anan na sake tabbatarwa aiki ya ci. Dr.Isa ne yake fitar da irin wadannan kalamai akan Safiya? Ban taba ji ba tun da nake tare da su shekara da shekaru, ko a tsohon gidanmu ma tare muka zauna.
Na yi dariya na ce " ayi haquri zan qara kula da ita."
Ya tambayi jikin Usman na tabbatar masa ya ji sauki har ya tafi aiki.
Tanimu ya wangale masa get ya wuce, Safiya na gefe na sai muka hada ido muka yi dariya muka tafa.
Umma da Dr.Musa ne su ma suka zo wucewa a cikin mota zasu je wajen aiki, shi likita ita kuma accountant ce a asibitin. Ita dai ta yi karatunta, ba irinmu ba ce. Allah dai bai basu haihuwa ba duk da ma dai basu fi shekaru biyu da yin auren ba.
Mu ka gaisa suka tambayi lafiyar Usman na ce ya ji sauki ya tafi aiki. Su ka wuce su ma. Gida ya zama daga ni sai Safiya dan haka yau zamu sakata mu bararraje mu sha hira.
Na ce ta kira mana stephanie dan mu sake yi mata godiya mu bata tukuici. Mu na shiga falon Safiya sai ta kira wayar stephanie. Ta ce zata zo amma sai qarfe sha daya saboda yau litinin dole sai ta je aiki ta yi signing an ganta sannan ta fito.
Kowacce ta bada labarin irin qaunar da aka nuna mata cikin dare zuwa safe. Sannan labarin Murjanatu da Mufidah tas na bata. Babu tantama babu kokonto aiki ya ci yadda ake so. Mu ka yi shawarar kowa ya bawa stephanie atamfa sabuwa dal tukuici tunda bamu da kudi.
Stephanie bata iso ba sai qarfe goma sha biyu, ban hau sama ba, ina zaman jiranta dan anan muka karya kumallo ni da d'ana Haidar .
Stephanie na isowa tun kafin ta zauna ta gane muna cikin murna.
Ta ce " daman ban fada muku ba, ai kadan ma ku ka gani. Ta bamu labarin yadda ta mallake mijinta da dadewa sai abinda ta ce baya sauraron iyayensa da danginsa haka albashinsa a hannunta yake damqawa sai yadda ta yi da su.
Mu ka ce ai kuwa zamu sake tara kudi mu koma wannan karon mai qanqat zaa yi mana wato a sake sabunta aiki a kulle zuciyoyinsu da mu kadai a ciki. Na hau sama na dauko tawa atamfar, mu ka bata atamfofin nan guda biyu masu kyau, daya Holland daya chiganvy.
Ta yi murna kwarai da gaske sannan muka yi sallama ta koma wajen aiki. Ni kuwa ban koma sama ba sai da yamma, bayan na aiki Tanimu ya yi min cefane kuma mai tasin da yake kwaso yara ya kawo su. Danan sai qarfe hudu suke dawowa bayan sun yi lesson.
Na shiga tunanin irin abincin da tufafin da zan shiryawa Usman yau, tarya ta musamman zaa yi masa cike da so da qauna.
Haka kuwa aka yi abinci kala-kala na shirya masa, na gyara gida, na gyara jikina, ina ta qamshi.
Usman ya dawo gida bayan magrib cikin so da qauna. Na tare shi, shima ya tare ni da murna, cimak ya daga ni sama yayi min lilo ya kira ni da Baby kuma ya tabbatar min ni ce rayuwarsa yana fatan mu rayu tare mu mutu tare.
Ai shikenan na fi kowacce mace saa a duniya kuwa, in har zan rayu din-din-din ni kadai tare da Usman, mutumin da yake da kulawa, ga iya soyayya.
*** *** ***
Rayuwa mai dadi mai cike da kwanciyar hankali, bacci nake yi har da munshari dan na tabbatar bani da sauran fargaba. Ko a ofis bana zargin wata zata iya qwace shi. Na yi qiba kuwa, na murmure, na kwantar da hankalina dan ina son komai na wa ya ciko kamar irin na Mufidah, ta na da kyan jiki komai cif cif.
Kimanin watanni biyu kenan ana ta shagali da cin sabon amarci ni da Safiya, har fita mazanmu ke yi damu wajen shaqatawa. An yi mana alqawarin zuwa wajen shaqatawa na 'Yankari Game reserve' idan aka yiwa yara hutun makaranta. Usman ya ce kwanaki masu yawa zamu yi acan, shima daidai lokacin zai dauki hutu. Dr.Isa ma ya tabbatarwa da Safiya tare da su za mu yi wannan tafiyar.
Usman ya na neman shawarata a komai sai ya shawarce ni kafin yayi. Ya na so ya sayi wani fili a kano yana da wasu kudi sun kai naira miliyan biyu, kuma zai karbi bashi a bankinsu na naira miliyan daya da rabi. An yi masa tallar wani fili a wata babbar unguwa a kano kudin filin naira miliyan uku ne, sai ya zagaye filin da sauran kudin.
Da na yarda shima sai ya yarda ya tafi Kano cikin qarshen sati ya je yayi aikin filin ya siya ya zagaye ya dawo. Wannan abu yayi kyau rayuwa sabuwa kullum muka zauna maganar tsarin ginin gidan muke yi. Ya ce da kaina zan tsara duk yadda nake so hakan yayi masa. Daman a tsarin kun san babu maganar bangare biyu ni kadai ce da yarana.
Bayan wasu 'yan satittika sai nake kula da yanayin Usman ya canja kamar ya na cikin damuwa idan na tambaye shi sai ya ce babu komai. Ya na yawan tashi cikin dare ya kwana ya na sallah, ya na ta karatun kur' ani amma na san da cewa muddin ya shiga wannan yanayin na tabbatar akwai damuwa sosai. Nima na shiga taya shi da addu'a duk da bai fada min komai ba.
Watarana ranar talata sai ga Usman da tsakar rana ya dawo gida daga wajen aiki, abinda ban taba gani ba.
Ransa a bace yana ta gumi idanuwansa sun kada sun yi jajawur. Riqe yake da wata farar takarda a hannunsa, ya kasa amsa jerin tambayoyin da nake jero masa kawai sai ya miqa min takarda ya tafi kan kujera ya zauna a galabaice.
Na bude takarar da sauri hannuna na rawa na karanta na sake maimaitawa, amma ban fahimci komai ba.
Na je na miqa masa takardar cikin gigita da daga murya na ce "ka fada min da baki meye yake faruwa?"
Ya cije baki ya ce "an kore ni daga aiki gaba daya ma."
Na zabura na ce "wannan karon Mufidah ta wacce hanya ta bullo? Wanne tuggu ta sake hada maka?"
Ya girgiza kai ya ce" babu ruwan Mufidah, kudi ne suka b'ata kuma an bani sati biyu kacal in dawo da kudin da suka b'ata naira miliyan shida."
Na maimaita "miliyan shida? Kai ka batar da su? Ta yaya?"
Ya ce "haka aka ce a ranar da suka bata ni ne mai kula da kantar, na b'ace a lissafi ina ganin na qarawa wasu, dan a ranar an fitar da kudi sama da biliyan. Na kasa gano in da matsalar take. An kore ni kuma an ce sai na biya, shiyasa kika ga wajen sati guda ina cikin damuwa na kasa fada miki."
Sai na sulale na zauna akan kafet ina hawaye.
Na tambayi Usman "ina zamu samo kudin nan mu biya bashin nan?"
Ya yi shiru can ya dago da jajayen idanuwansa ya ce "a waje daya ne, nan nake saka rai amma alamu sun nuna ba zai samu ba. Na fuskanci akwai matsala."
Na ce "ina ne? Wajen waye? Ko ba zaka je ba ni ka fada min zan je maka ko nisan ya kai daga nan zuwa bangon duniya ne zan iya zuwa."
Ya ce "a wajen Murjanatu Bibi, ita kadai ce za ta iya ranta min kudin nan ba tare da ta takura ba, kuma zata daga min qafa in biya ta a hankali, sannan za ta iya yafe min wasu daga cikin kudin ma. Kai tana da hanyar ma da za ta shiga in da nake zargi kudin ya fada ta binciko min a dawo da su, saboda ta san mai kamfanin mutuminta ne. Amma bashi da kirki, da muka je ya qi ya kula mu ma balle a samu a yi maganar kudin, a binciko in da matsalar take."
Gabana ya yanke ya fadi na ce "Murjanatu bibi? Toh ka je ka same ta mana."
Ya girgiza kai ya ce "ta qi yarda ta ganni. A bakin shagonta da gidanta nake yini, daga ta hango ni daga nesa sai ta koma cikin gida da sauri ta datse, ko ta juya mota ta koma. Na kasa gane wannan al' amari. Me na yiwa Murjanatu bata son ganina? Qawata ce fa kuma aminiyata ce sosai ai kina ganin komai a zamanta na gidan nan. Kowa a ofis din nan cewa yake ai bani da matsala tunda ina da Murjanatu, amma na yi-na yi abu ci tura. Ni in samu mu hadu ma, ta ji bayaninaina amma ta qi.
Na tura abokaina na wajen aiki wajenta daga sun kira sunana a maganar toh ba zata qara sauransu ba. Sai ta yi musu karar kare, daman lambata ta toshe kira da sakonnina basa tafiya.
Daman tsoron da nake ji kenan kada azo ban mayar da kudin nan ba, masu duba mu (inspectors) su na zuwa daga Lagos da Abuja. Kuma gasu har sun zo shekaranjiya, sun bincika sun ga gibin kudi, kuma an tambaye ni na kasa kare kaina, nan da nan su ka rubuta takarda suka aika babbar shalkwata aka turo da takarda an kore ni gaba daya ma ba dakatarwa ba.
Duk dan in rufawa kaina asiri kafin su zo na sa aka siyar da filin nan da na siya kwanaki na Kano, naira miliyan uku kacal ma na siyar na fadi, na saka kudin a ciki, na ci bashin naira miliyan daya a wajen abokaina na ofis da su Dr.isa amma ina har suka zo ban iya cikawa ba."
Tuni na hada zufa da hawaye, na tabbatar aikin boka ne ya hana Murjanatu ta saurare shi, gashi zurfin cikinsa ya jawo bai fada min da wuri ba, da tuni na je an karya asirin, gashi har abu ya gama dagule.
Na tashi tsaye na dora hannayena akai na dinga safa da marwa daga farkon falo zuwa qarshe ina surutai kamar tabbabiya.
Ban san sanda na tsinci kaina ina fadin " na shiga uku, a cikin watanni uku, mu ka tafi mu uku, akan babura uku, da qarfe uku daidai aka farraqa mutane uku."
Ya na ta hana ni yana cewa in dinga karanta lahaula walaquwwata da innalilahi wa inna ilaihi rajuun, shi ya fi alkhairi akan wadannan surutan da nake kiran shiga a uku-uku-ukun nan.
Bai san dalilin da ya sa nake ta kiran uku-ukun nan ba ne da bai hana ni fada ba. Shiga a uku fa na riga na shiga, kuma mu uku muka je akan babura uku, da qarfe uku, mu ka fararraqa mutane uku, wato su ne shi da Murjanatu da Mufidah.
Haka muka yi jugum daga ni har shi abin duniya ya ishe mu, ina ta tunane- tunane da saqe-saqen yards zan yi in shawo kan wannan matsalar dan ni ce sila. Tabbas ba dan asirin da na yi na raba tsakaninsu da tuni Murjanatuta shawo kan matsalar.
Bayan da Usman ya yi sallar asuba ya koma bacci da safe yayi ta yin wani irin bacci mai nauyi kamar matacce, na dinga tashin sa akan ya kai yara makaranta ya ce ya cire su ba zasu qara zuwa ba. Da na ga da gaske dai ba zai tashi ba gashi ban iya mota ba na kira me tasin da yake dauko su ya zo ya kai su. Daga nan na tabbatar mun fara shiga damuwa, abin nan na da gaske ne. Na sauko qasa gidan Safiya na iske ta a kicin mai gidanta da d'anta sun fita. Yadda ta ganni a gigice ta san akwai matsala dan haka ta tare ni da sauri tana tambayata. Mu ka wuce falonta na zauna kafin in fara magana hawaye ya fara zuba, Safiya ta rungume ni tana lallashi ta bani tissue na goge hawaye sannan na gyara zama na bata labarin halinda muke ciki.
Ta yi salati ta sallame ta dafe qirji banda kiran 'innalilahi wa inna ilaihi rajuun' babu abinda muke kira.
Ta ce ai kuwa Dakta bai fada mata